RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY HALIMA K/MASHI
da ya kamata a saya game da jarrai da kuma maijego,
don haka ka bar komai a hannuna
Ya dago ya kalle ta Fuskarsa
dauke da
murmushi, ya ce,
“Haka ne, amma bana son korafin
Natisa. Bari in yi magana da ita, sai in kai ku ku zabo har da na Amna tunda an tabbatar mana cewa duk
maza ne”
Aliya ta zaro ido, “Da ma ita ma Amna namiji
ne?”Ya ce,Eh”
Ta hadiye wani wahalallen yawu sannan ta
kirkiro murmushi,
*Ka ce gidan namu duk sojoji ne
ashe?”Ya kai hannu ya shafi cikinta,
“Ke kuma sai ki
kawo mana ‘yar budurwa ko?”
Ta saki dariyar yake, *Eh mana”
A cikin ranta
kuwa fadi ta ke,
“Allah ba zai biya bakinka ba, ni ma
namijin zan santalo, Kila yan biyu ma”.
Cikin wasa ya lakaci kumatunta tare da fadin,
“Ga shi ma kinki ki yi cikin”
Maganar ta sosa mata rai har ta kasa dannewa
sai da ya gani a kan fuskarta. Ya ce Ki yi hakuri ban
yi da nufi ba. Ina yi miki wasa ne
Ta dai cije suka canza hira.
Washegari Shatima ya tunkari Nafisa da batun
siyan kayan jarirai. Ya ce,
“Ina son ki shirya mu je
kasuwa ke da Aliya ku za6o kayan jarirai naki da na
Amna, in kuma babu damuwa sai mu je ni da ita”Natisa ta fusata,
“Nima fa na san hanyar nan ba sai an je min ba ko an raka ni”Ya ce,
“To amma ai ke daya ga ciki, kuma ina
ki ka sani a Kaduna ba sai ku je tare ba?”
Nafisa ta ce,
“Ni dai a ba ni kudin kawai
Ya ce, “To na ji, yanzu nawa zan ba ki?”
Ta Ce,
“Abin da za ka bai wa Amna, ko don ita
daban ce tunda su masu kudi ne?”
Ya ce, “Au abin da ki ka tsiro da shi kenan? To
bari in ta dawo na baku tare don bana son zargi Ta ce,
“Na yarda
Ana jibi sallah Shatima ya shigo da shanu gidan
don bai san ko kaji nawa zai siya ba. Ana gobe sallah
ya sa aka gyara shanu aka raba hudu, ya bai wa kowa
nata, aka zuba na Amna a freezer. Nafisa ta yi waya
aka zo mata da Hamida har ta zo mata da dinkunanta,
don ta taya ta aiki. Ita ma Aliya ‘yar wansu ce Amira ta
zo don ta taya ta aiki,. Haka kuma ita ma ta zo mata da
Dinkunanta, Shatima da ma shine ya kai musu kuma
ya biya kamar yanda ya biya na Salma.
Salma sanye cikin riga da wando cikin irin
kayan da ta siya gurin wata makociyarsu da ta kawo
musu tallah. Sauran ba su siya ba, amma Salma ta
zazza6a ta biya abinta.
Tana ta aikin namanta,
matsalarta cincin don gaskiya ba ta iya ba. Ga dai
kayan fulawa ya kawo musu kamar yanda Aliya da
Nafisa suka rubuta mishi, amma ba ta san yanda za ta
sarrafa shi ba. Ta san kuma in har ta tambayi Aliya ba
za ta fada mata gaskiya ba, Kila ma ta sa tayi Bata.
Bayan ta gama suyan naman ta nufi gurin Nafisa
domin ta jiyo tashin Kamshin cincin. Hamida ta samu a
kicin din, ta ce, “Ke ce ma ki ke aikin?”
Nice sannu da zuwa
Salma tace Ina Anty?”
Hamida tace “Tana cikin dakin Yaya ta kulle
kanta, wai ba ta son Kamshin cincin din nan’
Salma tace, “To fa! Ga shi nazi ta koya min
yanda zan kwaba cincin da sauransu?*
Hamida tace, “Wai! Gaskiya da kyar in za ta
yi, don wannan ma ni na kwaba”
Salma tace, “To don Allah dan kwaba min”.
Hamida tace,
“Da kamar wuya in miki, don
aiki ya yi mini yawa. Sai dai ga wannan littafin na baki aronsa, zai taimaka miki gurin yin duk, irin cincin
din da kike so
Salma ta amsa tare da godiya, sannan ta nufi
sasanta.
Ranar idi da safe Salma ta dora abincinta na
sallah da wuri, shinkafa fara ta dafa ta yi miyarta
tun jiya. Tana wanka tana ta sauri don kawarta Salma
Dankasa zata zo mata yau. Shatima ya gama shirinsa
tsaf don dakin Nafisa yake. Ya kalli Nafisar tana zaune
turus kan kujera tana cin nama, yace Wai ba zaki je
sallar idi din bane?”
Ta ce “Ba zan je ba
Aliya ma ta ce ba za ta je ba aiki, Salma kuwa
yana shiga ya ce mata, “Zo mu je masallaci”
Babu damar musu tace to
Hijabi ta zura suka nufi motarsa, wai kuma
halin kishi sai hakan ya bai wa Aliya haushi. Sun yo
sallah cikin murna da farin ciki, suka nufo gida. A hanya ne take fada mishi zuwan Salma Kawarta. Ta ce,
“In da hali ya sai mata lemon roba. Ya ce jiya ya siyo
*lemuka, ya manta suna cikin but Din wannan motar har
dà na kwali. In sun je gida zai ciro musu kowaccensu
ta dauka.
Ta ce, “To mun gode”.
Salma ta Ki yin kwalliya tana jiran sai Salma
Dankasa ta zo ta yi mata kwalliya, don ta iya sosai. Sha
biyu da mintuna maigadi ya z0 kofar Salma ya ce tana
da bakuwa mai suna Salma. Tare da maigadin suka
nufi gate din, cikin doki Salma da Salma suka
rungume juna. Cikin murna suka shiga falon, Salma ta
ce, “Ina su Anty in gaida su?”
Salma ta ce,”
“Suna sashensu, kun gaisa
kafin ki wuce’
Ta shiga jera mata abinci da na sha, nama da
kayan cincin. Sai da suka ci suka yi dam, sannan suka
yi gaban madubi don a yi wa Salma kwalliya.
Tun kafin su gama Salma ta ga irin kyan da ta
Yi haka kuma Salma Dankasa take ta koda kwalliyar.
Salma tace, “Da bana kwalliya, amma yanzu zan koya
ina yi wa kaina”
Salma da aka daura mata dankwali, ita da kanta
take fadin ta hadu karshe.
Hotuna suka yi ta dauka kala-kala. Suna zama
za su soma hira sai wayar Salma ta yi ruri. Da sauri ta
daga ganin sunan Yaya a fuskar wayar. Ta ce, “Yaya?”
Ya ce, “Ki z0 ku gaisa da baki”.
Tace.’
“A gurin Anty Nafisa?”
Ya ce, “Eh’Ta ce,
“To ga ni nan”
Ta kalli Salma Dankasa, “Zo mu je”
Ta ce, “Ina?”
Salma ta ce, “Ciki gurin su Anty sai ku gaisa da Yayana
Salma Dankasa ta yafa mayafinta sannan suka fita.
Tun kafin su shiga suka jiyo hayaniyar mutane
a falon Nafisa, a ran Salma ta ce, to fa, ga shi ban ko
yafa mayafi ba. Suka shiga da sallama, Shatima ya
canza kaya daga yadin da ya saka suka je idi zuwa
shadda mai ruwan hoda mai duhu. Tana da matukar
tsada, ya yi matukar kyau, kanshi da aski yayi masa kyau. Salma a ranta ta ce su Yaya har da canza
kaya? Ta shiga gurin su ta tsuguna tana gaida su.
Shatima ya cire gilashin idonsa yana kallon Salma, ya
zaci ko gilashin idanunsa ne ya sa yake kallon salma ta
dan kara girma, kuma ta yi kyau sosai. Sai kurum ya ji
kishinta musamman da ba ta yafa mayafi ba.
Salma Dankasa ta gaida su. Ya dubi Salma,
“Wannan ce bakuwar?”
Salma ta ce, “Sunanta Salma Sadik Dankasa”
Ta kalli Salma, “Ga yayana”
Salma ta sake dubanshi tare da sake fadin,
“Sannu Yaya
Ya amsa tare da cewa,
“Kullum ina jin
labarinki, yau mun hadu. Sannunki da zuwa”
Salma ta sake duban abokan su shida, da alama
akwai wadanda ba musulmi ba. Ta sake yi musu sannu.
Ta dubi gurin da Nafisa,ta ke zaune, ta ci kwalliya
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE