RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY HALIMA K/MASHI
shadda mai ruwan jibi, ta yafa mayafinta kalar kayan.
Ta kama hannun Salma ta ce,
“Zo ku gaisa da Antyna
Nafisa cikin jan aji ta gaisa da Salma, Salma ta
kalli Hamida wadda take kwashe kayan da su abokan
na Shatima suka ci abinci, ta ce,
“Hamida ya sallah?
Kin yi kyau fa”.
Hamida cikin “yar dariya ta ce,
“Na gode. Kema
kin yi kyau Salma, dube ki kamar amarya”.
Suka saki dariya a tare. Ta dafa kafadar Salma Dankasa ta ce, “Ga kawata ita- ma Salma sunanta Hamida
tace,
“Sannunki fa, ni sunana
Hamida”
Salma Dankasa ta ce,
“Sannu, ya sallah?”
Salma ta ce,Lafiya
Shatima wanda idanunsa suke kansu suna burge
shi, yanda suka yi gaisuwar. Salma ta katse shi da fadin,
“Yaya zan iya tafiya?”Ya cè,
“Eh, ku je abinku, da ma gaisuwa ce
kawai”Ta dube su,
“Sai anjima, mun gode”.
Wani daga ciki ya mika mata sabbin *yan dari
biyu da dan yawa,
“Ga goron sallarmu”.
Ta kalli Shatima tana fadin,
“Ku barshi kawai,
mun gode”
Wani daya cikin abokan yana fadin,
“Kina dai
neman izimi né a gurinsa kafin ki karba
Shatima ya yi dan murmushi,
“Ki karba, ai
goron saliah ne*
Da hanna biyu Salma ta amshi kudin tare da
rusunawa tqce
“An gode”
Ta nufi gurin Shatima ta nuna masa tare da
cewa,Ka gani?’
Ya ce,Na gani, kin god’e”
Ta mika ma Nafisa
“Anty mu raba
Harara ta sakar ma Salma domin wannan
kinibibin ya ishe ta, duk ta dauke hankalin Shatima ta kosa ta tita.
Shatima yace
«Wannan naiki ne, ita ma sun ba
ta”
Salma ta dafa kawarta tare da fadin,
“Mu je”Bayan ta dube su ta ce,
“Ku gaida gida”
Suna fita Salma Dankasa ta dubi Salma ta ce,
“Kawas wannan yayan naki ya hadu fa”
Kafin ta yi magana sai ta hango Aliya ta fito
sanye da farin leshi doguwar riga, ta yafa mayafi shima fari. Salma ta ce,
“Sannu anty, ya sallah?”
Ta dube su a yatsine, ta ce,
“Lafiya”
Salma Dankasa ta ce,
“Wannan fa?”
“Duk matansa ne!”
Dankasa ta zaro ido tare da fadin,
“Salma Bash
da gaske ki ke yi? Har su nawa ne?”
Salma ta nuna dakin Amna,
“Ga dakin wata
can ma ta tafi ummara
Salmar ta kai dubanta dakin sannan ta ce,
“Tabdi, kuma yaranshi nawa?”
Salma ta Ce,
“Ai auran bai shekara ba, duk
kuma rana daya ya aure su
Salma ta zaro ido tare da fadin,
“Rana daya?”
Salma ta sa dariya,
“Kar ki sa ya jiyo mu, ki yi
magana a hankali”
Ta ci gaba da fadin, “Rana daya wallahi”
Salma tace
“Tabdi, amma kun sha bidiri.
wace.ce uwargida?” Salma ta ce, ‘Wannan da ta wuce”.
Dankasa ta ce, ‘Tabdi,, ni mamaki ma naji, gashi gaye da shi. Ko da yake ni kaina zan yarda, in shiga
jerin matansa da zai so ni
Salma ta dube ta da sauri,
“Da wasa ki ke?” Dankasa ta ce;
“Za ki min hanya?”
Salma ta ce, “Ba ruwana”™ Dankasa ta kai mata duka, tace Kina tsoron
matansa ko? Don naga ba sa wani yinki”
Ta yi dariya,
*Ni dai ina yinsu”.
Da suka koma daki suka ci gaba da hira: Salma
ta kula Dankasa ta fi son a yi hirar Shatima, in kuma taci gaba da amsa: tambayoyinta akwai yiwuwar ta gane,
ita ma matarsa ce don haka ta ce, “Ashe fasalin gininku
iri daya ne da na matansa, wai ni uwa daya. uba dayas ku ke ne?”
Salma a ce, “Nice auta, kuma nan ya sa ni nake kula da nan din in zai yi mata ta hudu sai in koma gurin daya daga.
cikin matan”Dankasa tace Iyayenku na raye? Wallahi ni nice
ba zan zauna ba, sam-sam. Ina son zama da mamana Salma ta ce, “Ni mun shaku da shine sosai, ba
kin ga na nuna miki Mustapha da Badi’atu ba? Su ke binshi, amma da tazara tsakaninshi da
Mustapha Salma ta ce, “Mu canza labari, kin damu da batunsa”Ta kurbi lemun da ta dauka
“Saura kwana
nawa mu koma makaranta?Dankasa tace
“Saura kwana tara Ta ci gaba
da fadin,
“Ni ya min ne shi ya sa ko a dakin ina ta
kallonsa, shi kuma sai ke yake kallo. Da muka shiga fa har da cire gilashin idonsa
Salma ta tashi ta nufi cikin daki, don ba ta son
zancen ya ci gaba.
Turaruka da kayan kwalliya ta dibar mata,
sannan ta dauko mata mayafi daya wanda ba ta taba
sawa ba. Ta hada mata kaya masu yawa, ta aje a kan
gado. Tana fitowa Salma ta ce,
“Ni zan tafi
Salma ta ce,
“Ba kin ce sai kin yi la ‘asar ba?”
Dankasa ta ce,Na fasa
Salma ta ce,
“Ba ki isa ki tafi ba”.
Da Kyar ta kai uku. Ta kira Hajiyarsu wai
direbansu ya zo ya dauke ta. Hajiyar ta ce ta aike shi Marafa zai kai abincin sallah gidan kakarsu. Salma tace,
“To bari ta taho.
Salma ta ba ta kayan da ta ari style, sannan ta
ba ta wanda ta yi niyya, sannan ta ba ta dubu biyu a
cikin dubu biyar din da abokan Shatima suka ba ta. Ta ce,
“Gaskiya kin ba ni abubuwa da yawa, na
gode sosai. Yanzun sai ki raka ni titi”
Salma ta ce,
“Wai bari dai in kira Yaya ko zai
bar ni”Ta ce,
“Ai ko ba ki isa ki bar ni a bakin ni daya
ba”Salma ta ce,
“Ba za ki gane ba ne”. ta daga
wayarta ta kira shi.
Ya daya, ta sa a handsfree don Salma ta ji, tace
“Yaya Kawala zata tafi”
Ya ce,
“To mun gode, ki ba ta dubu daya zan
ba ki”Ta ce,
“To Yaya, daman ba ta san hanyan titi ba
ne, shi ne zan raka ta”
Ya ce,A’a, me na ce miki?”
Ta ce,Please Yaya, ka ga a motar gidansu aka
kawo ta, kuma.
Kashe wayarsa ya yi.
Ta kalle ta,
“Kin gani ko kawata?’
Salma ta ce,
“Zo mu je har gabansa
Ta ce,
“Kai! Ina tsoro
Salma ta ce,
“Ke dai zo mu je”
Sun fito su ma za su fita, Shatima ya tsaya suka
isa gurin motar. Kafin Salma ta yi magana ya ceKi
koma, ke kuma titi ne ba ki sani ba?”
Dan Kasa ta ce,
“Eh”
Ya ce, “Bari mu sauke ki”
Ta ce,To”
Salma ta ce
“To sai mun yi waya kawata”.
Shatima ya ce,Ina ne unguwarku?”
Ta ce, “N.D.C Ya ce,
‘”To bari mu sauke ki a kan layinku”
Tana idar da sallar isha ta shiga hada kayanta,
in ta tuno gobe za su je Zaria farin ciki a gurnta kamar
me, hatta kayan da za ta sa tuni ta aje su. Takirga
kudinta dubu sha biyu da ‘yan canji don ba makaranta,
kuma wanna lokacin naman dubun take saya, saboda
azumi. Ta yi komai jiran zuwan washegarin take yi.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE