RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 10 BY HALIMA K/MASHI

 

 

Shatima ya ce, “Hajiya zan kira ki in na

sauka, ba a mota ta nike ba, haya na hau. Zamu yi maganar

Tagumi Shatima ya yi yana ta mamakin

wa yake kai ma Hajiyan sirrin gidanshi? Wata

zuciyar ta ce, Lallai dole ya tsanana bincike, ko dai Nafisa ce tunda ga shi ita ta fada ma Amna? Ba shi da hujja don haka ya tsaya a kan zai yi bincike. A Abuja Nafisa ta ki ba shi hadin kai su fahimci juna, don haka shi ma kyale ta suka koma zama na rashin dadi, sai dai sukan yi kokarin kauce wa abin da zai sa yaransu su fahimta.

Salma sun gama jarabawa kuma sun yi

hutu, duk da hutun nasu na sati biyu ne, amma

tana sa ran kafin karewar hutun Shatima kila yazo su warware, ko dai ta koma gidanshi, ko

kuma ya kawo mata takarda.Tana kwance

a falon Kaka suna ta chatting da Salma Sadik Dankasa, kullum Salma tana mita da mamakin ashe Shatima mijin Salma ne, amma shekara nawa suna tare shine ta boye

mata? Salma ta ce,Zuwa yanzun ki hakura da

mitar nan haka” Ta ce, ita ma yanzun an kawo gaisuwarta, Salma cikin murna ta ce,

“Wa za ki aura?” Salma Dankasa ta ce,

“Lawal din nan dai na gidanmu da nike ba ki labari yana sona”› Salma ta yi murna, suka

ci gaba da zantukansu. Sako ya shigo wayar Salma, sai taga daga bankinta ne, don haka ta sauka daga online ta duba. Dubu dari biyar ce in dai ba kuskuren idanunta ba ne. Ta tashi zaune cikin sauri, Safwan El-Nasir ne ya turo mata. Cikin mamaki ta ce, ina ya samu account dinta, kuma kudin mene ne? sako ta rubuta ta tura mishi cewa. ‘Lokaci baiyi ba da za mu ji daga juna.Har yanzun ni matar Shatima ce, don haka zan maido maka da kudinka. Ko minti uku ba ta karasa cika da tura

sakon ba, sai ga amsa.Ban ba ki da wata manufa ba, ki dauka ko kina gidan Shatima zan iya zuwa har gabanshi

in miki kyauta. Sai abu na gaba, banso yanda kika zafafa abin har ki ka bar gidansa ba. Da fatan za ki koma ki jira har shi da kansa ya yi yanda yace tun farko.

Salma ta tura masa cewa. ‘Ina ganin wannan ba huruminka ba ne, ka jira tukunna. Sai dai zan maido maka kudinka.Ya turo mata cewa.

NO Ni dai baki na yi, amma ki shawarci

wadanda ki ke zaune da su, in sun ga lallai ki

dawo min da shi, ba sai kin sanar da ni ba, kawai ki maido min. shi ya sa na ba ki kadan don gudun kar ki zarge ni Salma ba ta Kara tura sakon ba, kuma ba

– ta da niyyar fada ma kowa, za dai ta bar kudin a cikin asusun nata tukunna.

Badi’atu cikinta ya soma kwari zuwa

yanzun ta murmure tana dan aikinta. Amma fa ta gama gano cewa, mijin nasu mijin tace ne Domin Maman kausar ta kan zo har sashenta ta fada mishi duk abin da ta ga dama cikin gadara da isa,

kuma ba ya taba gani ko fadin laifinta. Sannan

a tuni ta gano uwar mijinsu ba ta sonta domin tasha fada mata cewa, lallai in tana son zama a, wannan gidan sai dai ta bi Maman Kausar, don gidan natane, mahaifinta ya sai musu shi su zauna. Sannan Yarta ce ta zumunci, don

mahaifinta wane na Hajiyar cikinsu guda.

” Badi’atu ta gama yin nadama da aurensa,

kuma ta danganta halin da take ciki da rashin

daukar shawarar iyayenta, don haka ma ko da Anty Momiyo suka zo duba jikinta ba ta yarda ta sanar da su halin da ta ke ciki ba, kuma ko da suka ga irin gadarar da Maman Kausar din take mata, sai ta dinga karewa.

Sai dai ta ci kukanta wanda ya ishe ta, ta koma ta zauna. Hakan yasa ta rame kuma ta yi baki. Sannu-sannu lokaci yana Kara ja, Salma sun koma makaranta. Dubu ashirin Shatima ya turo mata a asusunta. Ta sanar da Hajiya Kaka, ta ce,Ciro ki yi bukatunki, muna nan zai samemu”

Duk da Kaka tana a’a’aa sai da Salma ta

ba ta dubu biyu don ta ki karbar biyar. Ta je gida ta ba Innarsu dubu uku. Koyaushe ta je sai Innar ta nuna takaicinta ga zaman Salman a Zaria, wanda ba ta san asalinshi ba. Salma ta kan ce mata.Inna ba na ki komawa ba ne, Kaka ta ce sai ya zo, kuma shi ya ki zuwa. Har Alhajinshi sun zo sau biyu wai za su maida ni, Kakar ta ce sai ya zo. Shi kuma ko waya ya Ki yi, shi ya sa ni ma ban damu ba” Inna ta ce;

“Makota har sun soma tambaya ta”. Salma

ta ce,Mutane da gulma, ina ruwansu da ni? Kuma ba fa a gidanmu nike ba,

gidan danginsa nike Inna ta ce,To, ni dai ina ta addu°a, Allah ya sa a sasanta”Tuni Shatima ya fada kasuwanci, duk da

Hajiya ba ta ba shi kudin gurinta ba sai da ya yi mata alkawarin ba zai dawo da Salma ba. Dukda ya san ba har zuciyarsa ya yi maganar ba,kasuwancin ya soma burinkasa a cikin *yan

watanni kalilan. Haka kuma sun sake shakuwa

tsakanin Safwan da Shatima, Safwan din ya yi ta bai wa Shatima shawarar zuwa ya bada hakuri ya dawo da matarsa, a duk lokacin da Shatima ya yi masa zancen Salman.

Kakar su Salma Dankasa ta rasu, ranar

uku ta kama juma’ a, don haka Salma ta sanar da Kaka. Kaka ta ce, ta je ta kwana daya.

Can ko ta kwana, ranar asabar Salma suka

rako ta titi don ta hau mota. Ta sha mamaki da taji zuciyarta tana ta ayyana mata Shatima zaizo,kuma tamkar an ce ta dago ta ga motarshi. Ta fito daga yuton. Kai tsaye

gabansu ya tsaya,Aliya da danta suna zaune a gefensa. Salma ta

kure shi da ido duk da faduwar da gabanta ke yi, kamar ta taka da gudu. Shi ma itan yake kallo

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE