RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 18 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 18 BY HALIMA K/MASHI
jikan jaririn nata. Da suka zo falo kuwa Shatima ya ce, “Kakata ina ta gaisuwa?”
Tayi banza dashi tana fadin,Maryama tashi mu je kin ji don ita ba ta bi su ciki ba, sai kuma taga ya kamata ta yi masa gori Daidai lokacin da ya ce,Kaka na san ni mai
laifi ne Ta ce, “Kai wa ka ke da suna ma? Karkaga na zo gidanku ka zata bikonka na zo, ni awa har da za ka gaida ni? Shi ke wulakanci a duniya dama yi min ne in maka, yanda ka daki wata ka kora ta kai ma ga shi nan an kusan kashe taka yar uwar. In ka- ji zafin abin da akai wa Badi’atu to ka sani haka dan uwan Salma yaji. Sannan in uwarka da ubanka sun ji zafi, to su ma iyayen Salma sun ji. Bugu da Kari ga ta nan ita ma za ta soma zaman gida kamar Salma, ita ba bazawara ba ita ba me aure ba. Mu gani ko sai yaushe fim din zai kare!”Zancen Kaka ya doki Hajiya, Shatima
kuwa cikin sauri ya sha gaban keken Hajiya, ya durkusa yana fadin,Hajiya, ina son Salma
Ya kalli duk *yan dakin,Ku zama shaida
ina son Salma so mai tsanani, kuma matata ce” Salma ta kalle shi ta san wani sharadì
yake son cikawa nata. Ta tabe baki tare da girgiza kai alamun bai yi ba, ya ce,
“Ina sonki Salma Kaka ta ce,Mu je Salamatu kin ji wai saida ya ga an wa kanwarshi sannan ya san da yana sonki Ta karkata kujerar suka wuce ta gefenshi yana tsugunne. Ya mike ya bi su da kallo. Matanshi daga mai tsaki, sai mai kau da kai. Amna dai waya take dannawa ta yi kamar ba ta san ana yin wani abu ba.
Suna isa gurin mota Kaka ta rufe Salma da
fada tana cewa,Ke kuma da ma kyale ki na yi
duk waye-wayen da ku ke yi da shi ina jinku, nadai barki ne don na ga ba ki bada min kasa a ido ba. Saura da ya zo babu wani kamun kai da man martaba ki kwasa riba ki ba ki koma, ya kuma koro ki”Salma ta yi kus don ta ji kunya, ashe Kaka ta gane tana waya da Shatima?A daren ranar ba ta daga wayarshi ba, don haka ya turo mata sakon cewa, ya cika alkawari ya bayyana sonsa gare ta, kuma
a gaban wadanda ya bayyanar musu dakinta.
Ta ce,Aikinka bai yi ba, domin babu
kusan mutum uku a gurin. Ya yi lissafin su waye a wancan lokacin, kuma su waye yau? Sannan tace, ya yi hakuri ya daina kiran layinta. Hajiya ta zabga tagumi, ko ba a fada mata ba dole ta yarda cewa, duk abin da kayi ma dan wani sai an yi ma naka, hakan ya sa ta dauri aniyar cire bakinta daga kan harkokin cikin gidan Shatima, don haka ta samu Alhaji da kanta ta ce masa tana son ya shiga don Allah Salma ta koma dakinta. Ya ce,
“Yanzun da ki ka ga ke ma an yiwa
“‘yarki ko? To ni dai ba zan ce komai ba don
kuwa na shiga tun baya Kaka ta ce babu ruwana, kin ga dole ni ma in yi wa uwata biyayya ba zan yarda in saba mata ba. Don haka ke da ki ka hana shi zuwa sai ki tasa shi ku je Hajiya Amina ta ce,Ni ba zan iya zuwa
ba, don na jima ban je gidan Kaka ba”
Ya ce,Wannan kuma ruwanki Salma ta ki daga wayar Shatima, duk da irin sakwanni na magiya da yake turo mata tare da nuna son jin muryarta.Ranar juma karfe biyar na yamma Salma ce a kicin tana yi musu faten doya, Kamshinsa ya cika gidan. Shatima ya yi sallama tare da shiga falon. Kaka da ke zaune kan kujera ta amsa,amma tana ganin Shatima sai ta gimtse fuska. Ya zauna jiki a sanyaye ya sunkuyer da kai yana gaida ta. Sau daya tacE
“Lafiya Daga nan bata sake magana ba.
Maryama da ke shafa mata man zati
Kafa ta gaida shi, ya amsa yana son ya ce ina
Salma, yana tsoron kaka Salma ta fito daga kicin tana sanye da riga da siket na atamta.
A zamanta gidan Kaka ta koyi abubuwa masu yawa, cikinsu har da girki kowane kala. Da
yake yar aikin Hajiyar kwararriya ce gurin girki, sannan ta koyi tsafta duk da dama ita
din ba kazama ba ce. Hajiya Kaka ta ce.
“Ki sani zama da kwalliya a ka san
mace, ba wai mace ta zauna don tayi wanka ta saka kaya ki yi kwalliya sosai, kuma ki sa sabbin kaya ba wai sai in za ki fita ba”
Sannan ta koyi yin lalle, ta ce, mace ta
zama hannu da kafa fari tas? To me ya
bambantaki da namiji? In ba za kiyi irin namu
na da ba, to lallai ya kasance ki yi irin naku na
zamani. Wannan ya sa Salma ta kulla abota da falle da kitso. Haka kuma ta koyi zama cikin
kunshi. Tun kafin ta shiga falon ta ga takalman
Shatima a kotar daki, haka kuma Kamshin
turarensa ya cika gidan. Ta dubi jikinta ko da makusa? Sannan ta shiga falon.Kofa yake
fuskantowa, ya yi kyau cikin farin boyel tamkar
matashin saurayi,. Babu wanda zai kalle shiya
ce ya aje mace bare har da ya’ ya.
Salma ta yi saurin dauke kai daga kallon
Shatima ta dubi Hajiya Kaka. Ta tsare ta da
idanunta duk da suna cikin gilashinta mai kara
wa ido gani Salma yarinya ce mai hattara, zamanta à gidan Kaka ta gama sanin wace ce Kaka, domin ko kallo Kakar ta yi tana iya tantance abin da kallon yake nufi, don haka kai tsaye sai ta nufi cikin daki don ta fahimci Kaka tana kallonta ne ta ga Ina za ta? Kuma
wace karba za ta wa Shatima
Ganin ta shige daki sai Kaka ta maida kai
ga Maryama,Ba ni ruwan can in sha
Shatin’ wanda ya bi Salma da kallo har
sai da ta shige daki sannan ya kalli Kaka.
“Kaka don Allah kiyi hakuri, gani nazo
na kawo kaina Kaka Ta ce,
“Ni a wa? Da na isa ai tuntuni za kazo. Amma tunda sai da ishara ta sauka a gidanku
sannan kazo ai ba ni da ta cewa
Ka je in matarka taga ta iya Kaka babu ruwanta
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe