RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 2 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 2 BY HALIMA K/MASHI

 

 

Nafisa ta samu guri ta zauna cikin

damuwa, in Shatima neman mata zai fara lallai

za a samu katuwar matsala. Ta tashi ta dauko

waya da nufin kiranshi, amma sai ta tuna fa tana cikin damuwa da zakuwar ya dawo.

Badi’atu tana kwance a kan gadonta,

zazza6i ne a jikinta rijib, mijin ya shigo ya dube

tà,badi’atu wai har yanzu jikin?”Ta ce,

“Eh don Allah a kai ni asibiti Bari Maman Kausar ta gama ku je Badi’atu ta ce,

“Haka jiya ka ce za mu je

tare da ita, ta ce ta yi baki sai haka na kwana da ciwo. To ni kawai in ba za ka kai ni ba, ka min kwatance Ya ce,Yau za ku je insha Allahu, jiya ma don tayi baki ne”Badi’atu ta koma ta kwanta,Ya ce,

“To ni zan fita, sai na dawo”

Don haushi ba ta tanka ba. Maman Kausar

ita ce kishiyar Badi’atu, kuma ita ce za ta raka ta zuwa asibiti Badi’atu ta sauko da kyar ta yi

wanka ta canza kaya, ta kwanta a kan kujera a falonta tana jira. Sai sha biyu da kwata mai aikinta Sahura ta shigo,

“Amarya wai ki fito in ji Maman

Kausar Badi’atu ta tshi tana ganin jiri, a haka ta nufi gurin mota. Bayan motar ta samu a bude,nan ta shiga ta kwanta. Maman Kausar

ta waiwayo, “A’ a tashi zaune, bana son langwai Badi’atu ta ce, “Gaskya jiri nike gani ba zan iya zama ba Ta ce,

“To ki sani ko mun je ba zan iya

kama ki ba, gara ma kin karfafa jikinki”

Ta dubi mai aikin,Sahura shigo sai’In

sauke ki bakin kasuwa ki sai min nama, ki wuce gidan Anty Baby zan biyo in dauke ki

Da yake asibiti ne mai zaman kansa suna

zuwa suka ga likitan, anyi gwajin jini nan take dana fitsari. Ciki ne babu tantama, likitan ya bara shawarwari da kuma magungunan da ya rubuta.Suka fito a zaton Badi’ atu a bi a sai magani tunda ya ce ya ba ta kudin, sai ta ga tunda suka fito Maman Kausar ta hau yin sabgarta. Sun je gidan Anty Baby sun shantake, ita ga zazzabi ga yunwa ba ta ci komai ba, don ba ta karya ba, ga

shi ba a sai mata magani ba, sannan suka wofintar da ita a falo tana jin irin zagin da suke yi mata, wai don tana da ciki ta lankwashe

sai shagwaba take yi.Na ce, to da

‘ya ya gidan ba haihuwar

fari ba ce bare a ce za a yi na marmari. Shima ya shigo da rawar kai tun jiya, wai a kai ta asibiti, nace bai dai wuce ciki ba, don haka ba kanta farau ba, na yi bala”in taka masa birki” Tana jin Anty Baby din tana fadin,

“Kin kyauta, gara dai ki rike ajinki, kuma ba a raina kishiya komai kankantarta, bugu da Kari kina da daurin gindi a gurin uwar mijinki”

Suka kuma sa dariya, maman Kausar din

ta ce, Tabdi! To ba ita ba ko shi sai Hajiya ta

Saba mishi a kaina bare wata ita Sun jima dai suna zantukansu kafun ta ji tace. “Ga cikon kudin kayan nan Ta kawo wasu,

“Wannan ma da cewa ya yi mu sai magani amma ba ‘zan siya ba, takardar zan kai mishi”

Badi’atu ta ce, “Lallai na shigo matsala”.Ta mike ta je kofar,

Tace Maman Kausar don Allah kizo mu tafi, yunwa nike ji kuma kin dai ji likita ya ce in sha magani Ta fito fuska a daure,

“Ki je ki tari abin

hawa in kin matsu, ni sai sun gama girkinsu naCi Zan tafi Badi”atu ta mike ta dauki jakarta a tsakar gida ta tambayi Sahura mai aikin

Maman Kausar, sunan inda za ta ce a sauke ta. Ta fada mata don haka ta wuce abinta. Ba ta sha wahala ba ta je gida, tana shiga wayarta tana ringin ta ciro, mijin nasu ne ta yi zaton zai ji ya jikin ko sun dawo, ko dai wani abu makamancin haka,amma sai ta ji ya rufe ta da fada, wai kan me za

ta taho don sun biya gidan yayarta? Badi’atu ta rasa me za ta ce; sai kawai ta saki kuka.

Ya ce,To mene ne na kuka daga magana?”

Badi’atu cikin kuka ta ce,Gaskiya ni ban

san ya ku ke so da ni ba, Ta kai ni ta aje ga ciwo likita ya ce in ci abinci in sha magani, sai kuma mu je mu zauna kuma bayan ina jinsu suna ta yi da ni Ya Ce,

“To yanzun-kin ci abincin?”Ta Ce,

“Tea na sha kuma fa ba a sai maganin ba”.Yace,Ta fada min kudin sun kare, inna dawo zan sai maganin, don Allah ki ke  karfafa

jikinki ciki ba ke ce farau ba”Cikin jin haushi tace,Ai ko a gurina sabon abu ne tunda ban.taba yinshi, ba?”Ta kashe wayar ta kwanta tana ci gaba da kuka. Wani sashe na zuciyarta tana fadin, tun yanzu zan soma

ganin sakamakon kin bin shawarar iyayena? Na shiga uku ni Badi’atu!” Sai ko da ya dawo da yamma sannan ya amshi takardar maganin ya je ya siyo, lokacin tana kwance kan abin sallah tunda ta rarrafa ta yi sallar la ‘asar ba ta iya tashi ba. Ya ce, “Sannu, ya jiki?”

Ba tare da ta dago ba ta ce,Umhum”

Ya ce,Bari in siyo miki maganin Ta dago kai,

‘Don Allah ka zo min da abin da zan ci, yunwa nike ji”• Ya ce, “A’a ga abinci ba za ki girka ba?”Ta ce,Dubi mana yanda jikina ya yi

laushi, ba zan iya aikin komai ba”Ya ce,

“To ni zan yi miki girkin kenan?

Kin san dai ba zan sa Maman Kausar ba, tunda kowa da gurinsa

Badi’atu ta ce,Ni ban ce ka sa ta ko kamin girki ba, in ba zaka samo min ba ka barshi”Ta soma kuka,Ni kawai ma ka kai ni gidanmu”

Jin haka sai ya ce,To kiyi shiru, ina zuwa Ya fice da sauri. ya kawo mata sakwara da nama da kuma magani, ta ci ta koshi ta sha magani. Ya

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE