RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 20 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 20 BY HALIMA K/MASHI

 

 

kudin juma,a kuma mu a da ta yanda ki ke

gane mijinki yana sonki, ta kula da ke. Ya

damu da damuwarki in kuna da yara ya damu

dasu, kuma in yana da hali ya sauke dukkan

nauyinki da ke kansa. Kisan wani abu,

mazanmu na Hausawa suna fadin ina sonki da

fatar baki ne kawai, amma kafin ki shiga

gidansa. Da kin shiga ba za ku shekara ba ya

daina wadamnan kalaman. Lokacin kauna za ta

yi aikinta sai kuma hakuri.Wofintar da ke da Shatima ya yi na tsawon lokaci shine ya bani harma nike ganin ba sonki yake ba kamar yanda ya fada baya.Shatima bai cika karya ba don haka na yarda da maganar da ya fada min cewa, Hajiyarsa ce.Mijinki yana sonki na gamsu, sai dai ina son mahaifiyarshi ta zo da kanta don in ji dadin jankunnenta. Kuma ke ma kina sonshi na sani. tun lokacin da ku ke yawan waya da shi”.

Salma ta Ce «Kaka ni ba ni da tabbacin

ko ina sonshi gaskiya”.Kaka ta ce,

“Abin da ki ka yi yau ya tabbatar da cewa, kina sonshi. Yini guda kin

kasa ci abinci tunda ya shigo,  nayi alwala

don yin sallar dare, ke ma ki ke yi kiyi ta

addu’a Allah zai daidaita tsakaninku da shi»

Salma ta ce,Zan kula”

Washegari litinin Salma sun tashi karfe

uku, tafe suke da abokan karatunta su uku,

daya namij dayar mace, duk yan

unguwarsu ne, tare sukan dawo. Suna cikin

tafiya sai suka ga cak! Salma ta tsaya, Hauwa’u

tace.Mu je mana Salma”

Ta kalli inda take kallo, ga mamakinta

sai ta ga Salmar tana kallon wata mota. Shatima

ya fito sanye da kananan kaya da. riga mai

ruwan kasa, wando baki na jeans. Shatima

yana da kwarjini sosai. Ya nufo Salma har ya

iso gurinta. Cikin ido suke kallon juna, kafin

Salma ta kauda kanta gefe. Ya ce,Mu je zan

yi magana da ke”Tace,Ni babu inda zan je”

Wanda suke tare, ya ce,Malam lafiya

kuwa?”Shatima ya mika masa hannu tare da

sallama,suka yi musabiha sannan

ya ce,Matata ce”. Hauwa da Haruna suka kalli Salma da sauri, ta daga kai alamun haka ne, suka ce, “To sai anjima Suna tafiya Shatima ya ce, ‘

“In kuma kinki zan dauke ki in kai ki da kaina Allah”.Salma ta dan ja baya, sannan ta soma

tafiya cikin sauri. Ya bi bayanta,

“Salma wai me kike nufi ne?”Ta ce,

«Don Allah ka bar ni ka tafi abinka

Ya sha gabanta tare da rike mata hannu,

“Salma gaskiya bari ki ji, zuciyata ba za ta

dauki wannan wulakancin naki ba, kuma ina

son ki sani ba zan sake ki ba. Haka kuma

hakkina ba zai barki ba, na kasa komawa

Abuja gurin aikina saboda ke. Na yarda in rasa

aikina don in samu fariin cikinki. Kada ki bi

zancen Kaka ba ta san yanda nike ji a zuciyata

game da ke baNe Salma ta ce,Ni don Allah ka ga ko azahar ban yi ba Ya ce,Mu je to in kai ki gida”.

Babu yanda za ta yi dole ta je suka shiga motar. Ba ta ankara ba sai ji ta yi ya rungume ta tsam a

Kirjinsa. Mutsu-mutsun take alamun ya barta amma ta kasa furtawa. Ya dago fuskarta, ina sonki Salma kinji na rantse miki da mahaliccina. Ban taba jin so mai kona zuciya

ba sai da ki ka bar gidana. Da alama na jima

ina sonki Salma ba tun yanzun ba”.

Ta sabule daga jikinshi, “Na ji ka kai ni

hanyar gida in tafi”Ya ce,Har gida zan kai ki”

Salma ta soma magiya,Don Allah ka

säuke ni kafin gida, Kaka Za ta yi zaton ko nice ma nace ka zo”Ya ce,Har kofar gida sai dai ba zan shiga ba, kina jin yunwa mu je gidan cin

abinci?”- Ta ce,Yaya ban yi sallah ba fa. Don

Allah ka bari na je gida, Kaka ta san lokacin da

nike dawowa, in na jima zan sha tambayoyi”.

Ya ce,Shi ya sa ma ban damu ba da ki

ke gurinta za ta kula min da ke”.Ya tada mota suka soma tafiya. Kadan-kadan ya kalle ta, ita ma ta kalle shi. Dadì kawai yake ji kasanacewarsu

tare.YaCe,Salma kin canza gaba daya, ba Salmata da na sani ba mai girmama ni da shakka ta Ta ce,Au yanzun kuma kuma mai yi

maka rashin kuna ne?”Ya ce, “Tunda ki ka zama *yar jami,a kika waye, ki ka goge, ki ka Kara kyau. Ga ki da Kamshi na musamman, ga shi kina gayu ina jin kishin lallen nan fa, haka ki ke tafiya mutane suna kalle min? Ta kalli lallen sannan ta dube shi.Ya ce, ‘Ina kallon sona fa a kwayar

idanunki Salma, kina sona fa!”Ta maida kallonta ga titi,Ni bansan wani so ba fa gaskiya Ya kai hannunshi ya damki nata,Ki bani dama, in koya miki so Ta sabule hannunta, Yaya ka lura kar

ka wuce gidan”Ya rage tafiya tare da fadin, “

“Har munzo? Na yi mamakin saurinmu”Ta kama kofar za ta bude, ya ce, “Salma

don Allah kimin wani abu da zan dinga

tunawa da ke in na tafi, matata Ta lumshe ido, sannan ta bude cikin shagwaba ta ce,

“Masa na gaji, ga shi ban yi sallah ba?.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE