RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 24 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 24 BY HALIMA K/MASHI
atamfar da ta dinka, kayan sun bi jikinta ga
gashi ya zuba kafadarta abin shi’awa. Kaka’ tace,
“Salamatu kin zuba kyau. Allah ya kafa ki a
gidanki ki zauna lafiya da kishiyoyinki, zuciyarki
daya. Domin na fuskanci babu ha”inci a tare da ke Salamatu, a zamanmu ba ki da gundira ga biyayya, ga hankali. In Shatima ya fahimce ki nasan za ku yi zama mai cike da tsafta”
Salma ta Ce,Kaka ni ma na ji dadin
zama da ke, kuma na koyi tarbiyya kala-kala.
Kaka Allah ne kawai zai biya ki”Sallamar Shatima ta ratso gidan,maryama wadda ta fito daga falo ta amsa, ta bi shi da kallo. Ya yi matukar kyau cikin yadin mai ruwan kasa, wanda layinshi ke nuna tsadarshi. Kamshinsa ya bide ko’ina, Maryama ta juya ciki da sauri tana fada ma Salma cewa,Kin ga Yaya Shatima tamkar ango? Ya yi kyau sosai”.Salma ta Kosa ta ganshi, sun zuba ma juna ido, har sai da Kaka ta ce,
“To ina wuni?”Shatima ya dube ta da sauri,
“Kaka yi hakuri” Ya hau hannun kujera suka gaisa, yace,Salma ta zo, ya kai ta ta sallami su Inna. Kaka tace, sai sun dawo.
Suna shiga tsoron da zai fidda su waje,
Shatima ya rungume Salma tam tamkar ya sa
ta a cikinshi don kauna. Ya ce,Salma, wannan kamshin naki tun jiya nike jinshi ban yi bacci ba
Ta shafi kumatunshi,Ka mu je kada
wani ya shigo ya ganmu”Shatima ya ce,
“Yanda ni ke jinki ban damu wani ya ganmu ba. Zan iya daukarki in zagaya Zariya da ke a
hannuna, komu gwada?” Salma ta ce,A’a mu tafi kawai A cikin mota Shatima da hannu daya
yake tukin, dayan yana rike da na Salma, ya
game su guri daya, jifa-jifa sai ya kalle ta ya yi
murmushi. Ji yake kamar su biyu ne kadai a
duniya. Salma kuma kallon Shatima take tana
yi wa Allah godiya da baiwar da ya yi mata ta
samun miji mai sonta, irin mijin shiga taro. Ba
wai mugun kyau Shatima ke da shi ba, amma
akwai shi da iya wanka ga kwarjini, ga shi yanzun yana samun kudi hankalinsa ya kara kwanciya.
A gida Inna tare suka jera dan ma Salma
ta ki da hannunta ya so wai ya rike. Inna tana
yankan kubewa danya ta ji sallamarsu. Da
sauri ta fito daga kicin tana fadin,Sannunku
da zuwa”Ta ji dadi sosai da ganinsu, kuma ta yi
wa Allah godiya da Shatima ya ce mata sun zo
sallama ne. ta yi musu nasiha sannan suka
mike suka nufi gidan su Hajiyan Shatima.
Suka same ta a falo za ta nufi kicin, ta
tsaya cikin fara’ar da Salma ta sha mamaki.
Har kasa ta bi Salma inda ta durkusa ta kamo
hannun Salman, ta ce,Taso Salma”Ta saka ta a jikinta tana fadin,Allah yayi muku albarka”
Badi’atu ta fito tana murna ta ja Salma
suka shige dakanta Suka balle da hira,Badi’atu
tace ma Salma, akwai wasu magungunan mata in an kwaso kayana zan kawo miki har gida”
Salma ta ce,Nifa ban taba shansu ba,
ko da aurena lokacin biki ba a yi min ba Badi’atu ta ce,Lallai, suna can tunda na
ga babu mutunci na fasa, bana sha”
Sun dan jima sannan suka yi bankwana
suka fice, sun je sun dibi kayan Salma har tana
kuka domin ba ta son rabuwa da Kaka. Kaka
ma cike take da kewar rabuwa da Salma har ta
ce da Shatima don Allah ka kula da Salma
sosal, yarinyaCe mai biyayya da girmama
mutane, ga ta da shiga rai, karka sake ka sake
cutar da ita Shatima ya ce,Insha Allahu zan kiyaye, kuma ba ki fadi diyyar da zan ba ta ba
Kaka ta ce,Diyyarta dai ka kula da ita”.
Nan dai suka rabu cikin kewar juna.
Tun kafin su isa Shatima ya tsaya ya sai
mata kayan abinci. Sun iso ana kiran magriba,
Salma ta shiga dakinta wanda ta yi ta kewarshi
a lokutan baya ba ta zaci za ta kuma shiga
dakin da sunan zama ba, ko jiya da suka zo
suka gyara shi ba ta yi tsammanin za ta kuma
dawo shi cikin sauri ba. A fili ta ce,
“Allah ka kore duk wata fitina da za ta taso
cikin wannan sabon zaman da za mu yì
Ta yi sallah shi don ya nufi gurin su Aliya, ta yi sallah ta je tana gyara abin girki. Ta sake yin
yan gyare-gyare sannan ta nufi bandaki ta yi
wanka tare da alwalar isha.
Bayan ta idar ta zauna tana shafa mai, zuciyarta
cike da tunanin ci gaban da ta samu sakamakon
karance-karancen littattafan Hausa. Da tana
kallon karance-karancen nan duk bata lokaci
ne, sai haduwarta da Hauwa da A.BU. ta yi
jinjina ga marubuta don yanzun ta koyi darussa
masu yawa a littattafan, kuma zuwa yanzun ta
san yanda za ta kula da mijinta, ta koyi
abubuwa da dama wadanda mahaifiyarta ko
yayarta ba za su yi tunanin koya mata ba.
Tana fesa turare Shatima ya shigo
hannunsa leda ce. Ta amsa kayan marmarin da
ya sai musu a hanya ne, ta amsa, tana dubanshi,
“A yanka maka yanzun?”Ya ce,To ke ba za ki sha ba?”Ta ce,In ka sha ai ni ma na sha”
Cikin jin dadi ya ce,Haka ne,
Me Hajiya ta zubo mana a wannan doguwar kular?” Ta ce,Burabisko-ne sai miyar kaji da ta
ba ni ta ce na kwana biyu ina amfani da shi”
Shatima ya ce,Yanzun kin zama
“yar gatan Hajiya
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe