RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 25 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 25 BY HALIMA K/MASHI
Salma cikin wasa ta ce,”Ya ya son
ranka?”Ya ce,Fari kar”. Suka sa dariya.
A ranar Salma da Shatima sun kwana
tare kuma cikin soyayyar ma’aurata, Shatima
ya yi alfahari da samun Salma budurwa, da ma
ya zaci haka. Salma ba ta yi wani raki ko nuna
wahalarta game da ranar ta farkonta ba, kuma
ta cire kunya don ganin ta sa shi farin ciki.
Washegari tamkar kada Shatima ya bar
dakin Salmar, jinshi yake wani sabon mutum a
yau. Ban da makarantar Salma da ta yaronshi
da ke yi can Abuja da gaskiya sai Salma ta
koma Abuja.’ Da zai tafi ya shiga dakin Salma tana shara, ya ce, Salma ta aje tsintsiyar hannunta ta rungume shi. Ta ce;Yayana za ka tafi?”Ya ce,Zan tafi Salmata,wallahi ina
sonki, zan yi kewarki”Ta dago ta dubi fuskarshi, hawaye ne a idanunta suna bin kimatunta.
Ya cika da mamaki Salma mene ne?”
Ta ce, Yaya yanzun bana son ka yi nisa
da ni” Ya sa hannu yana share mata tare da
fadin,Salma za ki sa in tafi cikin damuwa ki
daina hawaye”Ta yi murmushi,Bana son ka zauna da damuwa mijina, Allah ya tsare’Tamkar kada ya barta haka suka rabu cike da kewar juna.
Safwan koyaushe in dai yana gari, to
yana zirya gurin duba lafiyar Badi’atu, sai
hidima yake ta yi mata, kawo wannan kawo
wancan. Tun tana jin kunyarshi saboda kinshi
da ta yi, ga shi yanzun yana fama da hidimarta,
har dai ta dake ta daina jin nauyinsa. Ko da bai
mata maganar so ba tana sane har yanzun yana
sonta, kuma ya ga ba ta yi idda ba ne. sai dai
tana shirye duk randa ya furta kalmar so za ta
amsa masa.
Aliya dai kima ta riga ta zube, ko magana za ta fadawa Shatima sai ta dinga shakka, domin ta ga yanzun hira in ba abin da ya shafi shi da ita, ko kuma zancen danta, tana dauko wata maganar za ta ga ya yi mata shiru. Domin shi dai a gurinshi yanzun duk sun fi ta mutunci da kima.Ranar wata asabar Shatima yana kwance a gadonshi dakin Salma yana danna waya,Salma tana kicin tana
“yan girke-girkenta. Da* ta dora ta dawo ta kwanta a jikin Shatima ya sake mannota sosai, ya ce,Wai me ki ke dafa mana?’Ta ce,Ba ka ce ka jima ba ka ci tuwon semo ba?”Ya ce,Miyar me ki ke min?”Ta ce,Danyar kubewa”Wayarshi ta yi ruri, Amna ce. Ya daga da sauri don tun jiya ta ce masa ba ta jin dadì.Ta ce,Baban Jafar zazzabi fa ya rufe ni”Ya tashi da sauri,Bari in z0″Salma ta kalle shi cikin mamaki, ta rasa me ya sa kullum Shatima yake rawar jiki a kan Amna? Ya kalle ta tare da miko mata hannu,Zo mu je ki gaida ta
Babu musu ta mika hannu ya kama suka
tafi. Tana son sanin abin da amna ta ke masa
wanda yake sa shi maida kai cikin lamuranta.
Har cikin dakinta suka shiga tana kudundune a
kan gado cikin bargo. Shatima ya zauna tare da
bude sassan fuskarta ya sa hannu a dokin
wuyanta. Ta dan bude ido, Salma suka hada baki gurin yi mata sannu ita da Shatima, ya ce,
“‘Kin kuwa sha magani?”Ta ce, “A’a Salma ta ce,
“Ko dai a kai ta asibiti ne Yaya?”Ya ce, “Ina ganin zai fikawai”Amna ta ce,Ka ba nì parasitamal kila
ya sauka Ya ce Salma ta dauko, ya nuna mata
gurin aje magungunan. Ta ba shi, sannan ta
nufi firji don ba ta ruwa. A nan ne ta ga gororin
tsumi a wani dan lungu, ga gumba. Salma ta yi
dan murmushi, da ma ta zargi haka, tana gani a
cikin littattafai Shatima ya ba ta da kanshi ta sha,
sannan ta kwanta. Ba su bar dakin ba sai da
bacci ya kwashe ta.
Salma yarinya ce mai dabara, sannan ta
samu Karin basira a cikin karance-karancenta,
sannan cudanya da wayayyun yan boko ya sa
ta zama wayayya, ga girke-girke da ta kware
na gargajiya gidan Kaka, na zamani kuma a
karance-karancenta.- Sannan kuma ‘ tana
fahimtar abin da mijinta ke so da wanda ba ya
so. Sabuwar rayuwa ta bude a gidan na Shatima, cikin dabara za ta shige mama duk
wani daya danganci Shatima tun daga
matanshi,ya’ yanshi zuwa danginshi.
Azumi ya kama ga makaranta, sai dai cikin
goman faro aka tafi yajin aiki duk daukacin
jami’o’in garin nan, ko in ce kasar sai
daidaiku. Wanna ba sabuwar matsala ba ce a
Kasar nan domin zai wahala ka soma karatu
jami’a ka kare shi lau ba tare da ka ci karo da
matsalar yajin aiki mai bata lokaci ba.
Salma ta lura sosai Shatima yana da
matsala da matanshi biyun nan na cikin gidan
Amna da kuma Aliya kwarai ta sha mamakin
na Aliyan, amma ta san abu ne mawuyaci ta ji
daga bakinshi. Inda ta gane na Aliya in ya zo
ya sauka dakinta wanka yake ya fice, kuma in
ya koma washegari zai sake ficewa, in ya
kwana gurin Amna ba ya fita har lokacin
tafiyarshi sannan ya wuce. To in ya sake zuwa
ita kuma dakinta zai sauka, kuma ba ya fita,
haka washegari har sai in ya koma dakin. To
kuma ita ma Amna din yanzun sai Salma ta
– lura in yana dakinta ba ya zama. Lallai akwai
dai wani abu, tsoronta kar dai Shatima ya canza
hali yana yawo.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe