RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 26 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 26 BY HALIMA K/MASHI
Da safe bayan sun yi sallah da karatun
‘al kur”ani sun koma sun kwanta, sai Salma ta ji
wayar Shatima tana ruri. Ba ta motsa ba don ta
san shi ma yana ji. Yana dagawa sai ta fiji yana
•gaisuwa cikin girmamawa, ta ce a ranta, kamar
Alhajinsa? Sai kuma ya tashi daga gadon ya
tafi daf da fita yana fadin,Daddy ba haka ba
ne. ban san Amna da karya ba sai dai in yanzun
za ta fara tunda idonta ya rufe tana son ta cutar
da ni. Wancan karon kun sa baki Daddy a kan
maganar tsarin iyali na hakura don bana yin
jayayya da iyayena, tana ta tsarinta don ni dai
naira ban bayar ba, kuma ba ni da niyyar
bayarwa. Allah ya nuna mata ikonshi duk da
tsarin ya ba ta ciki sai ta ce sai ta zubar da shi?
In ba ta tsoron lafiyarta ni ina son cikina, kuma
wallahi Daddy a fada mata gaskiya komai zai
iya faruwa inta cire man ciki?? Daddy yace
“Kai saurara ka ji! Shi fa ciki yarjejeniya ne na mutum biyu, don kai ka yarda ita ba ta amince ba kenan babu dole ta barshi, musamman da yake ita ce za ta yi kayan daukarshi a jikinta. Sannan kana ta fadin cewa,in ta cire komai zai iya faruwa, ka san dai ba zaka iya shara’a dà ita ba, karkari dai ka ce ka sake ta, kuma ta fada min ita ta shirya ma haka.Ni na kira ka ne in ba ka shawara ba wai rokonka zan yi ko hana ka daukan duk matakin da ka so ba, a’a shawara ta ka lallaba, ka lallashi matarka in ta ki ku je a cire, ba kana da
wasu yaran ba? Kuma sauran matanka za su ci
gaba da haihuwa, wannan shine kawai
Shatima ya ce,Gaskiya dai ni wannan
shawarar ba duka zan dauka ba, don ba zan
bari fa ta cire min ciki ba wallahi, kuma babu
saki a tsarina amma zan bi hakkina
Daddy ya ce,Shi kenan, tunda ka ki ka
iya yin duk yadda ka so Sai ya kashe wayar.
Shatima ya ja dogon tsaki yana fadin,
“Za a yi haka da mana sani. kullum suna bayan
‘yarsu don son rai ga gaskiya kiri-kiri.
To ni ba zan zama sakarai ba Yana kwanciya
tare • da wani tsakin,Salma ta kai hannu ta kamo shi zuwa jikinta,
“Don Allah ka yi hakuri Yaya. Duk da ni
yarinya ce bai kamata in saka bakina cikin
zancen manya ba, don na fahimci komai daga
zantukanku, ko in ce daga amsarka. Ka lallaba
ka bi ta a hankali, kuma ka sa hikima”. Ya ce,
«Wace hikimar zan saka mata ga gaskiya ana kallo?”Salma ta ce,To yanzun in ka bi ta ta
kuna ta fada da gaba, cikin wanna rikicin ma
sai ta je ta cire ba ma ka gari. Amma in ka
lallabata ka nuna mata kamar ka yarda, sai ta
saki jiki har ma ka nemi shawarar ina take ga
za a cire, in ta fada kai kuma sai ka yi maza ka
samu gurin da asibiti ke ko likita mai zaman
kanshi, ko dai ina ne a nan in ka je kana da
zabi biyu. Ko dai ka ce masa in kun zo ya yi
mata dabara ya ba ta abin da ba zai zubda ciki
ba, gaba baya sai ya nuna mata in ta nace sai ta
zubar zata rasa ranta.Na tabbata dole ta
hakura, ko kuma ka gargadì shi wanda za ku je
din kafin ku je, kan cewa hukuma za ta raba ku
matsawar ya yarda ya cire mata ciki. Kuma
dabarar zuwa gurin wanda ta sani shine, don
za ta fi yarda da wanda ta ke son ya yi mata
aikin fiye da wanda kai ka ke so. Sannan in ka
kai ta gurin wanda ka ke so za ta iya komawa
gurin wanda ta ke so, sai dai fa Yaya ka yi
hakuri.shawara ce ba dole sai ka dauka ba,
kwakwalwarmu ce ta yara sai ka yi watsin da
zancena Cike da al’ajabi ya dube ta, har zai yaba
mata, sai kuma ya tuna da Aliya da irin sigar da
ta zo masa kenan amma da ya saki jiki karshe
sai ta ba shi mamaki. Ya aje numfashi, ba zai ci
gaba da yin shawara da wata game da matsalar
wata ba, abin da kawai zai yi shine, kowacce
zai tafi da ita a kan matsalarta, YaCE,
«Salma ba lallai in dauki shawarwarinki ba duk da cewa kin yi basira”.Ta Ce,Da ma ban ce sai lallai ka yi amfani da ita ba, da ka saurare ni mana gode Duk shawarwarin da Salma ta bada su ya
bi, kuma cikin sati hudu ya cimma nasara,
Amna ya hakura bisa gargadì da tsoratarwar
likita,wanda ya samu suka tattauna bayan
Amna ta fada masa cewa gurinshi za ta je. Har
ma ya tambaye ta yanda aka yi ta sanshi, ta ce,
shine ya saka mata abin tsarin iyali, kuma ta
sanshi ne ta hanyar kawarta Maman Afra
wadda ta ki yarda da shawarta a wannan karon.
Har ma sun dan yi yar sa’insa sakamakon ta ki
bai wa Amna goyon bayan cire cikin.Shatima
ya ji dadin yanda shirin na Salma yayi
kai tsaye bai samu kowace tangarda ba. wata juma’a gurin Salma zai diro, da wuri ya taho jirgin sama ya biyo don cike yake da kewarta, wancan zuwan da ya yi bai samu kwananta ba duk da kwana biyu yake yi. •Da ma wani satin da
ya gabata kafin wannan ya samu ba ta sallah. Ta zuba kitso shuku Kanana, ga lallenta hannu da kafa an watsa mata tamkar amarya,kayan turawa ta saka riga da wando, wandon siriri bai kai kasa
ba, rigar kuwa kadan tafi gwiwa.Tunda
Shatima ya shigo da runguma ta tare shi, haka
kuma kai kawon shirya masa abinci da take yi,
shi’awa take ba shi ga mayen Kamshinta da ya
nace a dakin.Waina ta yi masa da miyar tantakwashi, ga lemon zo6o mai sanyi ya ji kokonba. Tare suka ci abincin cikin wasannin bai wa juna tare da hirarrakin miji da mata masu fahimtar juna.Wayar Shatima ta shiga ruri, Nafisa ce ta kira shi don jin ko ya sauka lafiya? Wannan
halin yana cikin halayen Nafisa wanda Shatima
ke so, wato nuna kula da tafiyarsa in ba ya tare
da su. Lura da hakan ya sa Salma kwaikwayon
Nafisar domin ita ma ta kara samun mazauni a
zuciyarsa,Shatima ya daga wayar cikin jin dadì yana fadin, ‘Matata
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe