RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 28 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 28 BY HALIMA K/MASHI

 

Mun tsaya

Salma ta ce,

“Shine burgewar kowane namiji, kuma na san dole kudinta ya kare ka koda kuwa yaranka ta sai ma dan takalmi” Ya Ce,To na ji sarkin jawabi, a zo a yi

min tausa, duk jikina ya yi nauyi Ta ce,

‘”Mu je gado to yanda zan lallaba

kayi bacci yaro mai kyau”

 

Da dariya suka nufi cikin dakin.

Bayan Badi’atu ta gama idda ta zuba ido

ko Safwan zai ce yana sonta, amma sai ta ji

shiru, kuma sai ya dauke kafa. Hakan ya daga

hankalinta, kuma ga shi babu wanda za ta

tunkara da batun su tattauna ko za ta ji dadi,

Salma ta soma yi wa zancen da suna chatting,

ta ce, wani son Safwan ta ke ji a ranta, ga shi

ma ya dauke Kafa, tana tunanin zai barta ne

tunda yanzun ita ba budurwa ba ce.

Salma ta ce,Wannan ba zai zama silar

daina sonki ba,. Tunda shi so ba ruwanshi da

wannan. Sai dai ko in wata ya samu”,Badi’atu tace,Da na shiga ukuna, don na dora raina a kan sonshi Salma Salma ta ce,

“‘Amma ki gwada tura mishi

gaisuwar juma’a ko da ta whatsapp ne”

Badi’atu ta ce,Shi kenan za ta gwada.

Juma”a uku tana yi masa babu amsa, hakan ya

dada karya gwiwarta, har ta samu kanta da

zubda hawaye a wasu lokutan. Kullum Salma

take yi wa zancen, wanda hakan ya sata shiga

damuwa tare da son ta ga ta fidda Badi’ atun.

Ba tare da shawara da Badi’atun ba ta kira layin Safwan cikin mamaki ya daga, don

bai zaci har yanzun lambar tana nan a wayarsa

ba. Ta yi sallama ya amsa tare da cewa,

“Matar Shatima, Allah ya sa lafiya ki ka kira ni?”

TaCe,To ba lau ba dai, kodayake karambani zan yi, wallahi ba a saka ni ba Ya ce,Ina jinki, me ya faru ne?”Ta ce,Antyna Badi’atu”Cikin sauri ya ce,

“Me ya same ta?” Salma tace,Sonka ta ke

wallahi kullum cikin damuwa take, ba ta san zan fada maka ba da ta hana” Ya ce,To don me za ta hana a fada min? ai ko ita in dai gaske ne za ta iya fada min, sai dai don dama ba wai tana sona ba ne” Salma ta ce, Yaya tana sonka gaskiya,

cewa ta yi ko ta fada maka yanzun kila ka ce

don ta ga wani ya yi mata wulakanci ne”

Safwan ya yi dariya,Don haka ne ma Salma ta ce,

“Ba don haka ba ne Yaya,

domin na lura da abubuwa da dama wadanda

babu lokacin da zan yi maka bayani. Amma ka

zo ku yi magana, na sani kai din malami ne na

soyayya, za ka fahimta in ta kamu ko kuma

don ta rasa wani ne Ya yi dariya,

“Gaskiya har yanzu ina son Badi’atu, amma da na hakura tunda kin zo kinmin dadin baki zan gwada zuwa yau”Bayan sun yi sallama cikin murna Salma ta kira Badi’atu ta ce,Albishirinki?”

Badi’atu ta ce,Goro”Salma ta ce,Wallahi bana cin goro,wannan takalmin za ki ba ni buku mai igiyoyi” Badi’atu ta ce,Zan ba ki kuwa? Safwan

ya sai min lokacin yana mugun sona”Salma ta ce,

“Zai kara sai miki wani don yau zai zo tadì”

Badi’atu ta ce,Don Allah zai zo, ya aka

yi ki ka sani?” Salma ta ce,Baiwa ce Allah ya yi min na san zai zo. Amma ki sani in har ya z0 yau

din takalmi ya zama nawa, kin yarda?”Cikin sauri Badi’ atu ta ce,Na yarda Salma ta ce,Shawara, in ya zo babu kunya, ki fito da tsantsar son da ki ke masa. babu wata kunya da za ki tsaya”.

Badi’atu ta ce,Insha Allah zan yi haka”

Safwan ya je kuma ya yarda Badi’atu na

sonshi. Kwana kadan zancen ya zaga dangi aka soma shirin biki. Ba a saka rana mai tsawo ba

aka sha biki, inda aka kai Badi’atu dankareren

gidan da ya dankara a unguwar Turawa da ke

Zariya. Amma kwanansu shida suka shiga duniya don zagata, su kuma ci amarci.

Haushin Badi’atu daya da ma shine ya riski

budurcinta. Kwanci tashi Salma sun shiga shekara ta Karshe a jami’a lokacin ne Amna ta haifi danta

mai kyau. Shatima ya zama baban maza, an sha

suna lokacin Nafisa za ta je makka, Shatima ya

biya musu da Amna sai ta haihu, don haka ya

ce wata shekarar sai ta je. Ita ba ta damu ba,

don ta je hajji da ummara sosai. Salma tana son

ta samu ciki duk da karatu take, amma shiru

har ga Badi’atu da nata, haka ya sa Hajiya har

da Kaka nema mata maganin haihuwa.

Da yake ita ta Allah ce, shiru don har ga

Aliya da wani cikin, Nafisa ma haka. Shatima

ya lura da sallar dare da Salma ke yi wasu

lokutan har da kuka, sai ya shiga lallashinta

tare da ba ta misali da Aliya. Haka ta dangana

tana jiran lokacinta in kuma ba ta cikin

wadanda za su haihu a duniya Allah ya sa haka

shine mafi alkhairi a gare ta. Ta gama karatu cikin nasara, Shatima har dan biki ya shirya mata don faranta mata rai. Sannan lokacin aikin hajji za su su uku har da shi da Amna, sai Amna ta ce ya bata kudin ta canza mota. Ya kuwa ba ta shi da Salma suka tafi. Salma ba za ta manta da wanna tafiyar ba, don ba ta taba samun lokaci ita da mijinta a tare irin haka ba. Har sai ta ji ina ma a ce daga shi sai ita a duniya? Sun dawo inda Salma aka zubo hakorin makka an yi kyau an murje.

Aliya da Nafisa duk maza suka haifa,

Shatima gida ya cika da ya ya har bakwai.

sannan ga arziki sai karuwa yake.

Ya sai sabuwar mota ya bar ma Nafisa

da Aliya nashi na da don an gyara, shine ya

koya musu yana son halin Salma, domin ba ta

daga kai ta kalli batun motocin ba, haka ko

yayin zuwa koyon aka yi aka gama ba ta nuna

damuwa ko a kan fuskarta ba. Zaman gidan Shatima zama ne da kowa halinsa ke zaune da shi. Burin Salma na ganin ta shiga jikin Shatima ta kowace fuska ta samu shiga, domin da

ita kadai yake zancen

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE