RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 29 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 29 BY HALIMA K/MASHI
kasuwancinsa, kuma cikin dabara ya
nema shawararta sosai, kuma tana ba shi. Haka
Badi’atu yanzun komai zatayi Salma ce abokiyar shawararta. Tana gama hidimar kasa ta sami aiki a gidan talabijin mai zaman kansa, wanda dama tana zuwa neman sanin makamar aiki. Sun yaba da kwarewarta. Salma ta cika burinta na zama
‘yar jarida, ta kan yi labaran Hausa da Turanci.
Lokacin Auwal yaranshi biyu, kuma sun hada
gwiwa da Hadiza da ita Salma suna ta ginin
filin da Salmar ta sai ma su Inna. Daki hudu ne
da bandaki biyu da kuma kicin. Shatima ne ya
rufa musu tare da karasa sauran gyaran suka
tare har Auwal din.Inna ta dage sai Salma ta dauki dan gidan Auwal. Matar ba ta so, don haka Salma ta ce,Inna barsu, gidanmu cike da
“ya’ya yake, suna debe min kewa. Ban da matsala Abin da Salma ta yarda da shi ba komai
da ka ke so Allah yake ba ka ba, don haka tuni
ta yarda da kaddara,kuma komai yana da
lokaci. Sannu-sannu sai ga Salma ta samu aiki
daga gidan talabijin na jihar kaduna,wannan ya sakata ta yi suna, ta samu kwarjini ta san
aikinta.Tana zaune Shatima ya ce, “Lokaci ya yi
da za ta koyi mota. Ta yi murna, shi ne ya koya
mata bayan ta iya kuma ya ba ta ta hannunshi,
kwana uku da haka ya shigo da sabuwa dal.
Salma cikin albashinta take hidima da duk
wanda ya rabe ta, ko ya rabi mijinta, kuma in
ta ga abu tana so ko Shatima na so tana cire
kudi ta siya don ta burge shi. Hakan ya kara
mata kima da daraja a gurinshi. Ita kuma
kullum tana kallo ai komai ta zama shine sila,
don shine ya tsaya ma karatunta. Shatima kan
zauna ya kalli labarai yana mai alfaharin
matarsa ce wannan abar sonsa.Salma Sadik Dankasa za ta yi aure,lokacin tana aiki a wani kamfanin Babansu, an sha bikin Salma inda aka kai ta Abuja. Sun dawo bikin da kwana uku Salma ta kamu da wata irin mura mai tsanani. Jurewa tayi jin labarin cewa Shatima yana can kwance ranga-ranga. Dukkansu suka je duba shi a asibitin da yake kwance, Salma da Amna ne a gurinshi, su kuma Nafisa da Aliya sun je su yo abinci. Salma ta tashi za ta yo alwallar la’asar sai ko jiri ya dibe ta, sai ko ta zube. Nan ita ma aka
saka ta gado. Binciken likita ya gano tana da ciki wata daya. Shatima ya mike ya je gadonta ya kamo ta ya rungume yana yi wa Allah godiya. Sai ma ya ji shi fa ya ma samu sauki. Salma kuwa
kuka ta saka wanda ba za ta iya tantance kukan
na mene ne ba. Taimako daya ta samu cikin ba mai laulayi ba ne, don haka ta ci gaba da zuwa
aikinta. Shatima kuwa lelenta yake kullum da
mamakin ciki irin nata wanda bai hana ta kula
da shi kamar da lokacin da ba ta da cikin ba.
Lokacin ne Kaka jiki ya ki har sai da aka fita
da ita waje, Kafa dai. An yi mata aiki sun dawo
da sati daya ajali ya sauka, Hajiya Kaka ta
rasu.Salma ji take tamkar ita kadai aka yi wa
rashin. Bayan an yi bakwai suka koma gida.
Badi’atu lokacin saiga ciki, danta
watanshi goma. Ta kira Salma har da kuka wai
Safwan ya ce kar ta sake ta cire masa. Salma tace,Da ke wane tsautsayi ya kai ki wai zagin
mahaifi? Saurare ni sai yanzu na samu shi ya sa
in zan yi ciki yau gobe in sake yin wani ba zan cire ba. Shawara, kar ki sake ki fusata mijinki,in
‘yan goma ne ki ka haifa mijinki yana da
karfin rikewa, don haka sai ki taka sannu’Badi’atu ta ce,Da ma ya soma cewa don
bana sonshi tun asali shine dalilin da
bana son cikinshi”Salma ta ce,Kin ji daya, to ta biyun saita fi haka muni, daga nan kuma sai batun kara aure Badi’atu ta ce,Na hakura, wai! Ni
kishi? Allah ka raba mu Salma ta ce,
“Kuma tana da dadi, ni yanzun duk da kowa huldarta take yi Allah da an ce dayar mu ta yi tafiya duk sai in ji kamar babu rabin gidan”
Badi’ atu ta ce,Gara ku kun saba, ni ko
daga ni sai mijina kullum muna manne da
juna Salma ta ce,To in kin tsaya yanga shi
yanzun ya soma aje *ya’yan sai ya nemo wata”
Cikin bacci ta ji ciwon baya, da sauri ta
farka. Ba ta saka ran cewa haihuwa ba ce, don
lissafin likitoci suna hasashen saura kwana
hudu, don haka ba ta tashi Shatima daga bacin
da yake yi ba, kai kawonta take yi ciwo yana Kara yawa. Innalillahi da take ta ambata shi ne
ya farkar da shi. Bai jira komai ba ya sure ta
zuwa asibiti a cikin daren, har shi aka kai ta
dakin haihuwa. Suna cewa ya jira, kafin minti
goma sai ga shi ya jiyo kukan jariri, komai na-
maza ta siya don namiji ne a takardar hotonta
na cikin da ta yi, sai ga shi ta haifo yarinyarta
mace, kyakkyawa, ita ma dai tamkar yayunta.
Shatima ta kwaso, don yaran kaf in ka gansu ka
san cewa nashi ne. har kudi Shatima ya ba wa
mai kawo masa albishirin haihuwar. Nan ya yi
ta waya yana shela, Salma ta santalo mishi da
‘yar budurwa. Tun kafin wani lokaci asibitin ya
cika har da su Hajiya, kowa ya zo sai ya ce an
samu Hajiya. Salma kuwa tunda ta dauki
jaririyar ta soma hawaye, domin ta so a ce
Kaka ta ga danta a duniya.
Babu irin maganin da ba ta nemo ba don
ganin Salmar ta haihu, kuma ita gaskiya sunan
Kaka ya dace a sa wa yarinyar ba Hajiya ba.
Har yanzun ba ta manta da tarbiyyar da Kakar
ta yi mata ba.
Hajiya ta ce, ai da Salma za ta tafi Zaria,
Shatima bai ki ba don shi alfaharinshi ne
Hajiyarshi ta zama mai kula da Salma, hakan
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe