RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 30 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 30 BY HALIMA K/MASHI
zai sa Salma ta sake manta da abin da Hajiyar ta yi mata duk da cewa ya shide Salma ba ta ruko bare gaba. Tunda ta haihu ba su kebe da Shatima ba, ga shi ‘yar tana neman cin sunan Hajiya. Sako ta tura mishi a waya cewar tana
son ganinshi, sai ko ga shi washegari da sassafe.
Ta yi mamaki, don ta zaci yana Abuja, ta fito wanka kenan wanda Hajiya ke mata. Yana zaune bakin gado yana kallon kofin da Hajiyar ta shake mata da shayi, ya ce, “Shi ya sa ki ka yi ko
Ta yi dariya, “Yanzun na yi katuwa?” Ya ce, “Sosai ma, kuma sai ki ka fi kyau” Ta ce,To ruwan nono, ya ki zuwa, sai da Hajiya ta dama kunu ga wannan tea, nama gasasshe har ya ginshe ni”
Ya ce,Yar gata, amma yanzun nonon
ya kawo ruwa ko?’Ta janye zaninta tana fadin, «Ga su nan har ciwon kirji suka sa ni, sun yi mata yawa. Cikin mamaki yake kallon maman nata suna tsaye kyam har yanzu duk da sun cika. Yace, “A’a ban ga sun kwanta ba kamar yanda suke yi in an haihu da ruwa kenan?”Ta yi murmushi, “Kwanciyar halitta ne haka ma tsayuwarsu. Irin tawa kirar da Allah ya yi mini kenan”Ya ce, “Salma ke ta daban ce, ban so in fada miki ba, amma kar ki yi amfani da hakan gurin yakata Ta ce, “Wane yaki zan yi maka? Sai dai in yaki kaina”Ya ce, “Ina Maman tawa?”
Ta ce,’Haiiya tana mata wanka. Da ma
don haka na kira ka, sunan Kaka yarinyar nan ya kamata ta ci, don Kaka ta yi mana komai a rayuwa”Shatima ya ce, “Kuma fa ni ma na raya haka sai in ji kowa ya ce Hajiya shi ya sa na yi shiru” nan Ta ce, “Na san Hajiyar ma ba za taqi ba, mu yi shawara da ita” da Hajiya ta shigo dauke da yarinyar, ta ji mamakin ganin Shatima. Ya ce, “Jirgin safen nan zan bi, Salma ta nemo ni kan wata shawara” Suka fada mata, ta ce, “Hakan ma yayi Nan ta je ta sanar da Alhaji batun, murna ya yi sosai tare da godiya ga Salma. Ranar suna jaririya ta ci suna Halimatus
Sadiya, sunan Kaka. Yarinya kuwa ta ga jama’a, ga abin arziki kala-kala. Maijego kuwa ta sha gayu ita da ‘yarta, abokan aikin Salma duk sun zo. Su ko su Salma Dankasa har da kwana a Zaria, daga nan maijego ta ci gaba da wankanta cikin kula da tattali. Yarinya Iftihal ake kiranta, wasu kuma in sun so tsokana sai su ce mata Kaka.Shatima ya yi nasara gurin hada kan
“ya’yanshi, haka kuma ya cusa musu son Ifti Kanwa, ya ce musu ita Karama ce, kuma mace ce tana da rauni ya zama dole su tausaya mata.
Sai ya zama kowa da sun zauna zai ce Dadi ina Ifti Kanwa, yaushe za a kai mu? Ya kan nuna musu hotunanta wanda yake daukarta in ya je, ko kuma wanda Salma ta dauka ta turo mishi.
• Wani zuwa da zai yi haka ya taho da su
Ashraf suka kwana gurin Aliya, washegari ya hada da Jafar da Abulkhairi ya nufi da su gurin Ifti kanwa. Ta sha dakuna, Salma ko ta hada su ta yi ta daukarsu hotuna. Yaran kamarsu daya hakan yana sa Shatima alfahari tare da godiyar Allah. Salma ta gama da wanka tana dawowa ta dora da aikinta, sannu-sannu Kwarewarta da basirarta ya sa take ta samun gaba-gaba har ya zuwa babbar tasha ta kasa gabadaya. Hakan ya sa dole Salma ta koma Abuja.Nasara da Kalubale wani lokacin sukan zo tare, wani lokacin kuma dayan ya riga daya.Salma dai za ta iya cewa tare suka zo mata, don samun iliminta shi ne nasararta. Halayenta masu kyau sun tilasta zaman lafiya tsakaninta da kishiyoyinta, musamman Nafisa mai dan banzan kishi, amma ga shi zama ya hada su, kuma ta dubi duk wani hali mai kyau da Shatima ke so kuma yake samu daga sauran matan ta kwashe ta hade da nata halin mai kyau ta ke yi wa mijinta.
Shatima ya dora rai a kan Ifti, yana tausayinta kullum zancensa Ifti za ta sha kula daga gare shi da yayunta. Yakan ce, shi dai duk mijin Ifti zai sha bincike, don ba zai kai ta inda za ta sha wuya ba. Salma kan ce in kuma aka samu wata macen fa? Ya ce, ita ma hakan zai so ta, sai dai son Ifti daban ne.Sosai lokaci ya ja, Salma kanta ta mallaki abubuwa na kashin kanta, haka ma kishiyoyinta kowa yana da bakin rabonshi.
. Zaman kuma zama ne na babu wadda za ta daga wata, ga Aliya wadda ke da.
“ya’ya biyu ba ta Kara ba, kullum tana son Karawa don Shatima bunkasa yake, duk da ita ma ta dan daukaka gurin aikinta, har ma ta bude kyamis a Zaria, amma nashi take kallo. Kuma zuwa yanzun ba Salmar ce kadai ta gane cewa, ita din annamimiya ba ce, har da su Nafisa da Amna, saboda ta so ta dinga rura wuta tsakaninsu, wannan ya sa duk wanda ta kawo wa magana sai ya gwasale ta. Haka ta zauna babu nauyi.
Amna kuwa ba ta da wata matsala don ba ta damuwa da shirgin kowa. Haka kuma ba ta damu ta sake haihuwa ba don ta cire wani cikin Shatima ma bai sani ba, sannan in ka ji su da Shatima suna sa’ insa to an shigar masa hakki, kila za a bar kasa tare da su ko
Hmmm