RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 31 END KARSHE BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 31 END KARSHE BY HALIMA K/MASHI

 

 

‘ya’yanshi, amma ba a sanar da shi ba sai

lokacin tafiya.

Nafisa kuwa kishinta kesa ta zarge-zarge, musamman da Salma da suke guri daya, sai son dukan yara wanda kusan koyaushe sai

Shatima sun hau sama da Nafisa.

Salma mai bakar dabara yana da wahala a ji kanta da mijinta sai ko in tsautsayi ya gifta, wanda za ta yi maza ta kashe wutar kafin ta tashi. “Yar mace ta take goyo lokacin mai sunan Hajiya, amma ba ta yi farin jini da kwarjinin Ifti ba, don ita irin yaran ne masu shegen shiga rai, ko a hanya ki ka ganta sai kin tanka, ga kuma gyara tana sha. Babu laifi a gurin Shatima mai mata hudu duk yana sonsu, kuma kowace yana zama. da ita bisa ga nata halin, haka kuma yana yin kokarin ganin ya sauke dukkan wani hakki nasu. Hadin kan ‘ya’yanshi da ya jajirce shi ne ya fi burge kowa, kuma ya fada ma matan duk wanda ya raba mishi kan ‘ya’ ya ko ya mutu bai yafe ba. Yaran suna son junansu musamman Ifti Kanwa, kowa yayyunta suna matukar sonta, komai nasu nata-ne, Aliya ce ma ta so ta canza ra’ayin ‘ya’yanta, amma da yake Shatima ya cusa musu ra’ayi in Abulkhairi ya ce wannan na Ifti kanwa ne, sai ta ce ba ga kaninka nan na kusa da kai ba, ka aje ma wadda ba ta nan? Sai ya ce, ai shi namiji ne, Ifti kanwa kuwa mace ce, Dadi ya ce mu tausaya mata. Dole ta saki don tana tsoron kar yaron ya je ya shelantawa: uban, da ma har yanzun ba kima gare ta ba.

Salma tana ta linke kayansu cikin akwatinta da na yaran, hutun makarantar yaran ya zo daidai da nata hutun da ta nema, tana son zuwa Zaria da Kaduna ta zaga dangi an yi abubuwa da yanayin aiki bai ba ta damar zuwa* ba. Riga ce Karama da wando siriri a jikinta irin kayan da ta fi zama da su a gida. Ko da taji turo kofa ta zaci Ifti ce ko su Ashraf don’ haka ba ta waiwaya ba tana yi tana ‘yan. wakokinta na wani fim da ta kalla. Sai dai ta ji an rungume ta ta baya, da sauri ta dago ta juyo tare da rungume shi tsam,

“Yaushe ka shigo mutumina?”Ya ce, “Yanzun nan mana”Ya dago habarta, «Kina ta hada kaya kin kosa ki tafi ki barmu ko?” Ta kalli cikin idonshi, “Ya zan kosa in bar rabin raina. Mu je a yi wanka ko abinci za mu fara ci?”Ya lumshe ido, “Na gaji da yawa, kuma kwana biyu ba ki min tausa ba. Ina ga ki matsa min jiki kafin magariba in yi bacci ko na minti goma ne”.Ta ce, “To bari in yi maganin wadannan yan biri-birin yaran naka don in sun san ka shigo ba za ka runtsa ma*

Makulli ta sa ta kulle dakin, sannan ta same shi inda ya yi rubda ciki a kan gado, ta haye bayanshi ta shiga matsa masa jiki.

Idanunsa a lumshe yake fadin, “Na gode Salmata, in kin tafi wa zai kula da ni? Kin shagwaba ni da yawa”Salma ta ce, “Dole in shagwaba ka, kai ne babban yarona”

Suka yi ‘yar dariya, ya ce, “In na yi laifi kuma sai a ce za a yaye ni ba Ta matsa wuyanshi, “Ai kai ba za a taba yaye ka ba ko?”

Ya ce, “Salma yau zan ba ki wata amsa da ki ka jima kina tambaya ta” Ta ce, “Wace kenan?” Ya ce, “Ai yanzu kin gaji kin daina, kina tambayar wa na fi so”.

Salma ta ce, “Ai kaqi ba ni amsa duk da

na san so daya ne tak, kuma dole mutum daya ka ke mawa”

Ya ce, “Na jima ina fada miki sirrikana

ba tare da na san ina fada miki ba, sai dai ina

alfaharin ban taba jin zancen a wani guri ba, ko

ga Kanwata da ta ke babbar aminiyarki ba”

Ta ce, “Haba Yaya, kai fa na musamman

ne a rayuwata. Tilo a duniyar nan babu irinka,

ta ya ya zanyi galala da sirrinka har ma wani

ya ji.Ya juyo ya rungume ta tsam,

.”Ina sonki Salma, amsar tambayarki kenan. Duk cikinku wallahi ke na fi so. Duk inda nike kina

zuciyata, gurinki nike samun dukkan wani, abu da nike so a mace, in ina tare da ke ina manta

cewa ina da wasu matan. Salma wannan sirrin

zuciya ta ne na ba ki amana don bai kamata in

fada ba. Sai dai na sani tuni ni da ke a bu daya

ne”Hawayen Salma ya ji a kirjinshi, cikin sauri ya dago da su zaune, ya ce Salma akwai

abin bacin rai a cikin maganata?” Ta sake kankame shi, “Yaya wannan ne babban burina, Allah na gode maka da naga – ranar nan. Na san tsananin sonka da nike yawaita addu’a a gare ka Allah zai amsa”.Ta sa hannu biyu ta tallabi kumatun sa ni da kai amana ce”

Ta kwantar da shi, “Ka yi dan barci kafin magariba sai ka yi wanka ka je masallaci ka dawo sai in ba ka abinci”Ta shiga yi masa tausa har ya yi bacci, ita ma ta manne a jikinshi ta yi shiru, duk da ba bacci ta ke ji ba.

Tunani ta tsunduma, lallai duk matar da ta jajirce ta daure ta saka tsoron Allah a lamarinta, ta zauna da kowa zuciya daya babu shakka za ta zama tauraruwa.a gurin mijinta.

Alhamdu lillahi.

Laifin dadi Karewa. Nan muka kawo karshen littafin rana daya daga marubuciyarsa HALIMA ABDULLAHI K/MASHI FTAN ALKHAIRI

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE