RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 5 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 5 BY HALIMA K/MASHI
mata na zalunci tunda iyayenta sun kasa daukar mataki, ni zan dauka
Munnir zai sake magana, Kaka ta ce,
“KuJe kawal Shatima ya ce,
“Hajiya amma ta fada miki
gà abin da ta yi?Hajiya Kaka ta ce,
“Na ce dai ku wuce,
bana bukatar sake ganinka in har ba takardar
sakin Salma ka kawo min ba Cikin fushi Shatima ya ce,Ku tashi muJe Kiran da Hajiyanshi ke masa ya sa suka yi
sallama da su Munnir, ya dauki dubu daya ya ba mai rukiyya. Yana
shiga falo ya samu Hajiya
tana zaune ta sake kiranshi. Ya shiga wayarshi
tana ringin, ya ce,Hajiya ga ni na shigo
Ranta a bace, ta ce,In nice uwar da ta
haife ka ban yarda ka maida Salma ba
Ya kasa zama yayi tsaye yana kallonta
Ta ce,Ka tsare ni da ido, da ma ni na gaji
da zamanta da kai tunda kai ma ba wai kana
sonta ba ne, ka sake ta mana. Ni na taba jin
wannan masitar?Zai yi magana ta ce,Yimin
shiru,umarni na ba ka Ya lumshe ido, a zuciyarshi yana nanata innalillahi, sai da ya kai aya sannan ya ce,To zan iya tafiya?”Tace
“‘In ka so, amma ka tabbatar ka cika
umarnina Bai amsa ba ya wuce
Hadiza ta shiga gidan Inna don amsa kiran
Inna. Suna gaisawa Innar ta sanar da ita a kan
zuwan Salma a daren jiya. Hadiza ta ce, “Kash
Inna, da ba ki kore ta ba kin ji dalilin zuwan
nata Inna ta ce,Ai ta ce sakinta ta ce ya yi
Hadiza ta ce,Duk da haka Inna, in babu
dalili ta ce a sake ta? inna ta Ce,Ina tsoron kada a ce yar mace Hadiza ta ce,
“To kin ce jiya sha biyu
saura mijin ya kira Auwal?”
Inna ta Ce, yana nan muna maganar ya
kira shi. Shine yanzun nike son ki kira min shi
Auwal din Hadiza ta ce,
“Bari dai in kira ita Salma
Kira ya fi goma ba ta daga ba tana bacci.
Hadiza ta ce,Inna ba fa ta daga ba. Allah dai yasa lafiya inna ta Ce,To amin dai. Ki Kira shi yayan naku Hadiza ta kira shi ta sanar da shi sakon Inna. Ya kira Shatima suka gaisa, ya tambaya ko Salma ta dawo? Shatima ya ce,
“Tana can gidan
kakarmu a nan unguwar taku, Ni ma yanzun nike shirin dawowa daga Zaria zuwa Kaduna
Auwal ya ce,
“To a yi dai hakuri
Bayan sun yi sallama Auwal ya kira
Hadiza ya fada mata, Hadiza ta fada ma Inna
yanda suka yi Inna ta ce,
“‘To Hadiza zuwa za kiyi ki je Kiji a can gidan Hajiya Kakar Hadiza ta Ce.
“A a Inna, sai yamma ZanJe insha Allahu
Biyar saura Hadiza ta isa gidan Hajiya
Kaka, ta samu Salma tana zaune tana cin tuwon shinkata, suka gaisa da Kaka.
Kaka ta rufe Hadiza da fada sai ka ce ita
ce ta koro Salma, ta ce,Don hauka sai yarinyar
ta zo da kukanta, amma a kore ta? To yanzun Ita ce ta aiko ki duba ta?”Hadiza ta ce,
“Ita ta turo ni, ko bacci ta Kasayi
Hajiya Kaka ta ce,
“Da gangan ta kasa
baccin al, tunda ta kore ta da ta fada hannun
Mugu da ta kasa baccin da nujja Hadiza dai ta yi ta ba wa Kaka hakuri, sannan suka dore da hirarsu, inda Kaka ke ba
Hadiza labarin abin da ya faru, da kuma matakin da ta dauka.
Hadiza ta ce,
“Amma da ba a yi haka ba Kaka, ai gara dai a sasanta” Kaka ta ce,To ke ma bana son zuwanki in dai ba za a zuba min ido ba”
Hadiza ta yi ta ba Kaka hakuri.
Salma kuwa ta kasa gane yanayin da ta ke
ciki game da matakin da Kaka take shirin dauka. Amma ta san dari bisa dari tana bayanta, domin
zama da wanda ba ya sonka bai ma taso ba.
Shatima dai abubuwa sun dame masa, har
ma ya rasa matakin da ya kamata ya dauka.
Kaduna ta ishe shi, ta fita ransa, don haka a
daddafe ya sake kwana dakin Amna ya kwana dama ita ba ta ma san ana wani bidirin tafiyar
Salma ba, ita dai ta tashi da fushin ambatonta da Nafisa da ya yi a daren jiya da zai ce ta kawo masa caja ya jona waya. Tun daren yake
lallashinta da cewa mantuwa ce,
‘ da kuma kasantuwar zamansa da Nafisar a Abuja, duk da haka bata yarda da zancen nashi ba, don haka da
safe shine ya yi wa kansa komai har ya hada kayansa tana kwance. Ya ce, To ni na yi shiri
zan tafi”Ta ce,Don ka kosa ka tafi gurin wadda
ka ke so shi ya sa, amma ai ba da safe ka ke
tafiya ba Ya ce,
“To ina da uzuri a can Ta ce,
“Ni dai na kusan gajiya
Shatima ya ce,To in kin gaji din sai ki
fada min, na daina damun kaina a kan kowace
yarinya a gidan nan, duk wadda ba za ta zauna da ni ba, ga hanya nan
Shatima ya sauka Abuja cike da damuwa.
Bai samu Nafisa a gida ba, hakan ya ba shi
– haushi kasancewar ba ta fada masa za ta fita ba,- ta san kuma ba ya son hakan. Nan zuciyarsa ta fada masa cewa, Nafisa na
fita ba tare da izininshi ba. Ya yi kamar ya kira wayarta, amma sai ya fasa, yana son ya ga tsawon lokacin da zata dauka.
Dakinshi ya shiga ya kwanta yana nazarin
rayuwar shi yana son sanin ainahin abin da ya yima Salma, Gaskiya tun farko ya yi kuskure da bai saurari dalilin da Salma ta nemi saki ba,
amma kuma ai ita ce ta zo da raini. Wata zuciya ta fada mishi haka. A fili ya ce, kuma na
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe