RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY HALIMA K/MASHI
dama kiranki na yi in fada miki cewa Baban
Ashraf yana neman, wata yarinya a nan kuma na rasa ko neman me yake mata tunda mu
hudu gare shi, kuma da na taka na je gidan su
yarinyar har tana min ikirarin suna lalata da shi, yanzun ma zai saki wata cikinmu ya aure ta”Duk zantukan da Nafisa ke yi ban da
innalillahi babu abin da Aliya ke fadi. Duk ta
rikice kafafunta sun hau rawa, Nafisa dai ta
kashe wayarta tana fadin,
“Ai gara kowa ta ji abin da na ji”Ta kira layin Amna. Ita ce ma sai a kira na uku sannan ta
daga, Nafisa ta ce,
“Maman Jafar nice maman Ashraf”*
Amna ta ce, “Ok, a dayan wayana ne nike
da laynki, ya ku ke?”Nafisa ta ce,
“To lafiya, amma ba lau ba. Mijinmu dai ya kama neman mata, dazu don in
tabbatar na tafi gidan su yarinyar muka yi zage-zage, kuma ya mata alkawarin sakin dayanmu ya aure ta. Ban da haka ma ta tabbatar min suna fita. Don haka na ce bari in sanar da ku don kowa ya sani, na kuma fada masa ni zai saki in ya tashi,
domin ba zan zauna ya zo ya sa min ciwo ba”
Amna ta yi shiru cikin mamaki, sai dai tana ganin kamar a dai kara bincike. A gaskiya
‘za ta iya yarda da wani abin, amma ban da
neman mata domin sun zauna da Shatima a wata duniya in da ba su da mai kwa6a musu da sunan karatu, amma Shatima bai taba ko da rike hannunta ba sai da ta zama matarsa. Kuma lokacin ta lura sosai bai nemi wasu ba ma. Nafisa ta katse mata tunani da cewa,
“Kinyi shiru Maman Jafar” Amna ta Ce,
“Ina shakka ne, amma mutum
yana iya canzawa daga yanda ka san shi”
Nafisa ta ce, Ai ki cire shakka Amna ta ce,
“‘To yanzu mene ne abin yi?” Nafisa ta ce,
“Kowa ta nema wa kanta mafita, ni dai ba zan zauna ba Amna ta ce,Ke ta gaban goshi kin fadi haka bare mu? Allah ya kyauta Nafisa taCe,Kaji dai Maman Jafar, ni ce ta gaban goshi ko Aliya? Ni dai sai anjima”
Har lokacin Amna ba ta gaskata Nafisa ba.
Sai dai tana fita don tafiya shagonta Aliya ta
tsaida motarta a kusa da gate, take tambayar ko Nafisa ta fada mata zancen mijinsu? Amna ta ce, ta ji, Aliya ta ce,Me ki ka ga za mu yi?”
Amna ta ce,To ni yanzun ba zan ce
komai ba tunda ba ni da wata shaida da zan riqe”Haushi ya kama Aliya, ta ce,To bari ki
ji, ni na yarda domin yanzun ya yi wa Salma duka jiya, kuma ya kore ta. Kin ga kenan zai auri karuwar Amna ta kasa dauke ido daga kan fuskar Aliya kamar a nan ne za ta gano gaskiya, Aliya ta ce,Da za ki sauko a motar nan ki leka falon Salma na san za ki gaskata zancena, har kayanta ta hada”
Amna ta sauka ta je ta leka falon Salma,
mamakinta ya tsananta, Amna ba ta ce komai ba ta zo ta shiga motarta ta fice. Cike da murna Aliya ta shige daki tare da fadin,
“Ai gara ku tarwatse, Salma tana can, ke ma ki tafi, Nafisa ta dawo Zaria. Wai ai tuni zan watsar da aikin nan in koma Abujan in ma da karuwar ne mu fafata, ita ma aijeho ta daga gare shi mu sha zamanmu”
Ta yi rawa da juyi cikin murna.
Shatima ya zo daidai layinsu sai ya tuna
da motarsa da ya barta a kusa da gate, don haka ya juya neman masu batir. Abuja ba gari ne da zaka samu abin da ka ke so a ko’ina ba, don haka ya nufi inda ya san zai samu. Sai da ya hau tasi sannan ya dauko mai batir. Ya shiga falon ba kowa sai dai ya jiyo maganar yaranshi a dakin
Mamansu. Ya nufi dakinsa ya dauko kudi ya
sallami mai batir, ya mika ma mai tasi nashi
kudin, ya ce ya maida mai batir sannan ya amshi lambar mai batir saboda in yana bukata. Ya maida motar gurin zamanta, a ranshi yana raya tuni ya kamata ya canza mota, hidimar yau da gobe sun hana.
Kai tsaye ya nufi dakinshi yana kwala ma
Ashraf kira. Yaran suka fito da gudu a tare, suka nufe shi. Ya daga su duka yana cewa,
“Babana da babana”. Su kuma suna fadin,
“Oyoyo Daddy Shatima ya zuba su a tsakiyar gadonshi shima ya hau. Take ya ji duk wani kunci ya yaye daga zuciyarsa, ya yi rigingine suka haye ruwan cikinsa, ya ce,
“Ban ganku ba da na dawo.
Jafar da Abulkhairi sun ce in gaishe ku
Ashraf ya ce,Yau ba su bada sweet a
kawo mana ba?”Shatima ya ce,
“Sun ba ni mana, su ma na
ba su wannan biskit din da ku ka ce in kai musu”Ashraf ya ce,To Daddy dauko mana”
Ya ce,Sai za ku je islamiyya zan ba ku”
Wannan wata dubara ce da Shatima yake
yi don cusa kaunar juna a tsakanin yaransa, yana daukar abu ya ba kowa ya ce in ji dan uwansa na wancan dakin, sannan ya yi musu hirar juna. Ashraf ya ce,
“Daddy muna gidan Mama
Nana muna wasa ne fa, shi ne da ka zo ba ka
ganmu ba” Ya ce,Amma dai ba kwa fada ko?”
Ya ce,Ba ma yin fada. Ita ko Momi tana
ta kuka a gidan Mama Nana, wai za ta je gidan wata, Maman Nana tana cewa kar ki je, kar ki je Shatima ya ce, Gidan wata mata?”
Ya ce;Eh, wai ko ina ne ai mu ba mu je
ba ko Shahid?”Ya dubi Kaninsa, wanda ke ta
wasa da wayar Baban. Shahid ya ce cikin maganarshi da ba ta gama gogewa ba,
“Momy ta she za mu she gidan
Mama Ashraf ya amshe da cewa,
“Kai ne za ka kai mu a motanka ko Dady? Ai tana hada mana kayanmu yanzun”
Shatima kanshi ya sake kullewa, wai me
ke faruwa ne? ya ce,Ku tashi mu kalli
talabijin”Ya kuna ya kamo musu cartoon.
Yana ganin sun tare hankalinsu, ya kwaso musu sweet ya ce,Ga shi in ji Jafar da Abulkhairi ina zuwa
-_Ya fita bayan ya kauda wayoyinsa da
laptop don kada su yi masa barna. Ya nufi dakin Nafisa.
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe