RANA DAYA CHAPTER 1 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 1 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
**FARKO **
Tana fitowa daga dakin ta soma rera kuka kallon dakin da Mahaifinta ke kwance a cikin. Kafadarta taji an dafa tare da kiran sunanta.
“Ummu Salma, kiyi hakuri Allah zai ba mu
mafita.” Ko bata dago ba ta san Yaya Hadiza ce. Cikin kuka ta ce, “Yaya Hadiza abin nan da bakin ciki, Naira dubu goma tasa za mu koma da Baba gida a haka?”
Yaya Hadiza ta kama hannunta. “Zo muje kafın Yaya ya fito mu ga ya za’ayi.” Www.bankinhausanovels.com.ng
A harabar asibitin suka tsaya can in da ba kai kawon mutane, sai motoci da ke aje a gurin. Suka jingina da wata mota ba tare da sun damu da zafin da jikin motar ya yi radau ba.
Yaya Hadiza ta ce, “Salma yanzun ke nawa ne a gurin ki?” Ta ce, “Jarin Awarata gaba daya Naira dubu ne da dari bakwai, kuma kin ga dai kullum in nayi za a samu dari bakwai, dari shidda. Da shi fa muke cin abinci, in kuma an kwashe an ba da ina zamu samu na cin abinci, har ma a kawo asibiti?”Yaya Hadiza ta numfasa, sannan ta girgiza kai. “Taba wannan jarin ba zai yiwu ba, sai dai bari Yaya Auwalun ya fito muji, kin san shi aikin shi na gidan Biredi sai karshen Wata suke ba shi albashi, in dai ba Allah ne Ya kawo mishi dan gyaran wuta ya yi ba.”
Salma ta ce, “To Yaya Hadiza ke babu wani kokari da za ki yi?” Ta ce, “Salma me ya rage min yanzun? Sai fa Gadon da muke kwana a kai.
Shi ma Baban Amira kin san dai ba wani karfi gare shi ba, sai ya fita ya nemo sannan za mu dora.”
Salma ta hango Yaya Auwalu yana ta waige waige alamar yana nemansu. Ta ce, “Ga Yaya can. nasan tabbas mu yake nema.
Yaya Hadiza ta ce, “Yaya Auwal!” Ta kwala
-mishi kira, ya kalli inda suke, sannan ya nufo su
Suka ci gaba da tattauna yanda za su samu kudi. Sa dai kusan minti talatin ba su cimma matsaya ba, zancen dai daya ne na kudi kuma ba su da shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga cikın motar suka ji ana kwan-kwasa kofar, Salma ta zabura da sauri ta matsa gefe,sannan ta ce Yaya Hadiza matsa, wani mutum ne Ya fito daga cikin motar sanye da shadda mai ruwan kasa, kanshi babu hula. Kyakkyawa ne wankan Tarwada, fuskarshi babu annuri sam-sam.
Hakan yasa gaban Salma faduwa. Ta ce, “Alhaji don Allah kayi hakuri ba mu san da mutum ba.”
Ya kalli sashen cikin asibitin, sannan ya soma latsa wayar da ke rike a hannunsa, suna dai kallon shi ya karata a kunne ya soma magana.
“Haba abokina! Ka fito mana ko in je in dawo ne tukunna?” Ya dan yi shiru, sai kuma ya ce, “To babu matsala, bari in dawo minti sha biyar.” Sai lokacin ya kalli Salma wadda idanunta suka
kasa daina kallon shi. Ya ce, “Nawa ku ke nema
don ci gaba da kula da Mahaifinku?”Salma ta zaro ido tana in ‘ina.Am… in…kudin da muke so?”
“Samu nutsuwa mana yarinya, kin ga sauke numfashi tukunna.” Ya fada a hankali. Ya kalli Yaya Auwal.
“Nawa ku ke bukata a yanzun?” Har suna hada baki shi da Yaya Hadiza gurin cewa, “Dubu goma ne dai yanzun.”
Ya ce, “To cikinku wa zai bini ya amso? Don in na fita sai na kai minti sha biyar kafin in dawo cikin asibitin nan in dauki abokina.”Yaya Auwal ya ce, “To bari in bika, mun gode sosai Alhaji, Allah Ya saka maka da alkairi.” Hadiza da Salma ma suka yi godiya. Ya ce, “Kar ku damu, ku gode wa Allah.”
Nafisa ta kalli Mahaifiyarta wadda take zaune bakin Gadonta, tana shafa mai. Ta ce, “Mama har yanzun ina shakkar yiwuwar
aurena da Yaya Shatima.” Uwar ta dubi Nafisa, sannan tayi dan murmushi. “Yau ita ce rana ta uku da ki ka tambaye ni, ko in ce da ki ka fada min cewa kina shakkar yiwuwar aurenku, amma kin kasa fada min dalilinki na fadin haka. Nafisa ta dan kalli saman silin din dakin uwar,
kamar wadda take son tuna abin da zata fada.
Uwar ta gama shafa mai, şannan ta mike ta nufi gurin durowa tana duba kayan da zata saka. Nafisa ta ce, “Mama nayi la’akari ne da yanda ya ki ya zo gurina, ko ya kira ni a waya. Tun sakon da ya turo min cewa ina jin zan iya auren shi? Na ba shi amsa da cewa zan iya, shi ke nan fa.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Uwar ta ajiye kayan da za ta sa a kan Gadon, sannan ta zo ta zauna kusa da ‘yar, ta kai hannu ta dafa yar.”Nafisa zan ba ki shawara, kar ki sake ki saka wannan a zuciyarki, aurenki da Shatima kin san babu abin da zai hana shi faruwa sai in dayanku ya mutu.
Kar ki manta Babanki da Babanshi uwa daya uba daya. Kuma su ne suka yanke su hada ku aure ba tare da neman izininku ba, fatana dai ki zama ‘yar zamani mai kula da abin da zai ja hankalin mijinki.
Abin da za ki lura shi ne, Shatima matashi ne dan zamani, mai ilimi, mai kudi, mai kyau. Mata da yawa irin shi suke nema, sai kin dage kin zama jaruma sannan ne za ki zama ‘yarlele, ki dauke hankalinshi daga kan kowace mace.”Nafisa tayi murmushi, “Ni dama matsalata guda daya ce, ya zo mu fahimci juna.Maman ta ce, “Kin san kowane namiji yana da irin nashi ra’ayin, da kuma irin nashi salon. Kila shi nashi kenan irin wannan salon.”
Nafisa ta ce, “Amma Mama kina ganin ba laifi ba ne in nayi masa sakon gaisuwar Juma’a ban yi laifi ba?” Ta ce, “Babu laifi, amma yana da kyau mace ta zama mai kama ajinta a gurin namiji, ba kowane namiji ba ne ya ke son a dame shi ba.
Haka kuma ba kowane namiji ba ne ya ke son mace mara aji, shima yaja aji bare ke mace. Amma dai ki masa sakon sau daya a Juma’ar nan mai
zuwa mu gani, daga yanda ya dauki abin za mu iya fahimtar wani abu.” Nafisa ta ce “To shi kenan Mama, na gode da samun uwa irin ki. Ina alfahari da samun ki matsayin Mahaifiya. Nasan duk duniya babu wanda ya kai ni dacen uwa tagari mai dora ya’yanta a kan turbar daidai.
Bari in je in ci abinci har naji yunwa, da dazu na kasa cin komai, ko in ce cikin kwanakin nan na kasa cin komai.” Uwar ta ce, “Je ki ci kar ki damu kanki ko kadan.”
Munnir ya kalli wayar da ke jone a jikin chajar motar, sannan ya kalli mai jan motar.
“Abokina wayarka tana ruri fa. Mai wayar ya kai hannu ya dago wayar sannan
ya kalli fuskar wayar, da sauri ya daga wayar.
Ta ce. “Hello! Manyan kasar Nijeriya.” Ya ce, “Amna ba dai kin shigo Nijeriya ba?” Ta ce, “Ba ka kalli number din ba ke nan?” Ya ce, “Shi yasa ai na tambaye ki, saukar
yaushe?” Ta ce, “Saukar kwana hudu da suka gabata.
Ya ce. “Amma shi ne sai yau ki ke kirana?” Ta ce, “haka ma za ka ce? Har ma kana da bakin magana tunda ka baro Dubai sau daya rak! Ka kira ni.
“Kin fi ni gaskiya Amna, amma ina da dalilin haka. Cikin satin da na dawo Nijeriya aka sace min wayoyina da Laptop dita, sai da na rasa lambar kowa sai wanda ya kira ni.Ban da haka ma littafin da ni ke ajiye abubuwana na rasa in da na saka, ke kuma kin ki kirana bare in samu lambárki.”
Ta ce, “To yanzun dai yaushe za ka zo?” Ya ce, “Ban da wannan satin, satin da za mu shiga.” Ta dan yi shiru. Can ta ce, “Ko dai ka canja ni ne a zuciyarka?”Ya ce, “Matsayinki yana nan daram! Me yasa ki ka tambaye ni?” Ta ce, “Yanda naga kamar ba
ka yi dokin ganina ba.” “In da kin san tarin ayyukan da suke gabana da ba ki fadi haka ba. Zan tsallake da dama ne fa in zo in gan ki, kin san sabon ma aikaci, ofishin da na samu cike yake da tarin ayyuka.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na gamsu, don tunda muke tare ba ka taɓa fada min karya ba.” Ta fada cikin kwantar da murya.
“Na gode da lambar yabon da na samu a gurinki. In na samu lokaci zamu yi waya.”Ta ce, “Sai na ji ka.” Ya mika ma Munnir
wayar tare da fadin “Maida min ita a caji.” Daidai ya karya kwana. Munnir ya amsa tare da fadin “Abokina wai me ya ke shirin faruwa ne?”
Ya dago ya kalli Munnir, sannan ya yi murmushi. “Wallahi nima ban sani ba abokina, amma tabbas ina ji a jikina babban al’amari zai faru, kuma zai faru din. Nayi wani mafarki kwanakin baya, kuma naji a jikina mafarkin alkairi ne.”
Munnir ya ce, “Allah Ya tabbatar mana da
dukkan alkairi.” Ya ce, “Ameen.” Kofar gidan su Munnir ya sauke shi, sannan ya nufi gidansu da ke Kwarbai a garin Zaria. Www.bankinhausanovels.com.ng
Damfareren gida ne mai girman gaske, wanda daga gani ka san ma su gidan da kunbar susa, kila ma da jibin sarauta.
Ya nufi ɓarayinsu ya aje motar ya kwashi
wayoyin shi ya nufi cikin dirkeken falon. Tana
zaune a kan kujera Badi’a tana shafa mata man zafi a kafa.
Ya zauna kan Dardumar da ke gabanta tare da fadin “Sannu da hutawa Hajiya.
Badi’a ta tashi da sauri tare da fadin “Sannu da zuwa Yaya. Ya ce, “Sannu Badi’a.” Hajiya ta ce, “Sannu Shatima, har ka dawo?”