RANA DAYA CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 12 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Hajiya ta ce, “Shi ke nan gashi nan zai zo yanzun.” Ta kalli Mustapha, sai kaje ka dauko ta dan sarki a surutu da ka tada mata hankali.”
Aliya tana asibiti lokacin da Mustapha ya kirata ya fada mata ciwon angonta, duk hankalinta ya tashi. Taso taje gida ta canza kaya amma zuciyarta ta fada mata ciwon da aka kwantar da mutum, kuma har aka kira ta aka faca mata gaskiya da matsala.
Ta dauki uziri, sannan ta dubi kawarta Aisha ta ce, “Kina ga in tafi a haka?” Ta ce “Kijo mana ai kayan ki a goge suke tsaf!” Ta kira

Ya ce, “Ko kin shiga sai na bi ki. Dama dai ta hudun ce na samu, shi ne ni ke son ki sa ba ki a jone ta cikin bikin.”
Ta hade fuska, “Kai bana son maida bara bana, an riga an wuce nasan tunda kayi uku ai dole zaka yi ta hudu, amma ka bari sai can gaba.”
Ya ce, “Haba Kaka! Don Allah ni a hada rana daya, dama su hudu na gani a cikin gara kawai mafarkina.” Taja tsaki, “Mafarkin ka na banza tunda kai ba Annabi ba ne ba wani tabi’i ba ko Malami, har wani mafarki ke gare ka?”
Munnir ya ce, “Shi ne nima na gani da anyi magana sai ya ce mafarkin shi.” Shatima ya dubi Munnir, “Haba abokina! Kai fa ka san komai.”
Ya dubi Kaka, “Wallahi yarinyar Marainiya ce, na san ki da tausayi.” Ta ce “Ni har a fada min maraici, ni da ubana ya mutu tun ina ciki, uwata kuma ran da ta haife ni ta rasu?”
Shatima ya ce, “To ni dai kiyi hakuri in Alhajina ya zo ki ce kin yarda. Ta soma yunkurin mikewa. Munnir ya yi saurin mika mata sandarta. Ta amsa tare da fadin “Na gode dan nan kaje gida gurin iyalinka ka fita batun wannan uban wautar. Shatima ya taimaka mata har cikin daki yana kara rokonta amma sam ta ki magana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan ya sauke Munnir ya nufi gida. Bai zaci zai samu Hajiyarshi a falo ba tun da sha daya ta gota, bai ma lura tana nan ba sai da ya nufi samanshi ya ji ta ce, “Kai zo nan.
Gabanshi ya fadi, don tun jiya ta fada mishi cewa tana son ganinshi. Da safe a gurguje ya gaishe su wai yayi latti, da yamma ma haka ya yi ta goce ma haduwarsu, yanzu kuwa an ritsa shi.”
Ya zauna gabanta, “Gani Hajiya.” Ta ce, “Wai ka manta na ce ina son ganinka ne ka ke ta yi min goce-goce?” Ya ce, “A’a abubuwan ne, kiyi hakuri.”
Ta ce, “Ni ban yi fushi ba amma zan yi “Ai matsawar ka kasa fada min gaskiya.” Ya ce, ” ban taba yi miki karya ba Hajiya.” Ta ce, “Mene ne gaskiyar zancan da Momiyo ta fada min, wai ka samu mace ta hudu, haka ne?”

Munnir ta tambaye shi asibitin ya fada mata. yace, “Shima zuwansa kenan.”
Ta ce, “In ta zo zata kira shi.” Shima Munnir ya samu asibitin cankas da mutane, don ma wasu suna tafiya. Ya tsugunna ya gaida Hajiya, kuma ya tambayi abin da ke damun aminin nasa, har ya kara da cewa jiya har sha daya saura suna tare lafiya.
Hajiya ta.ce “Ikon Allah kenan! Ai baya bata da kadan, ko mutuwa ce ma haka ne, ka shiga yana bacci.” Ya shiga sun gaisa da Nafisa, yaje yana taba jikin abokin nasa sassan wuyanshi, ya ji jikin babu zafi, har yana zufa duk da fanka da kuma (AC) da suke ta aiki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya kalli Nafisa “Ke ce mai jinyar?” Tayi murmushi tare da sunkuyar da kai ta ce, “Ka zauna.” Zata tashi ya nufi kujerar da ke can gefe mai zaman mutum uku da yake dakin aminiti ne.
Bai fi minti hudu da zama ba kiran Aliya ya shigo, ya daga. Ta ce, “Nazo bakin asibitin.” Ya ce, “To gani nan fitowa.”


Shi ne ya yi mata jagora har gurin Hajiya, cikin kunya ta tsugunna har kasa ta gaida Hajiya da mutanan da ke gurin. Hajiya ta ce, “Munnir wannan kuma wace ce?”
Gaban Aliya yayi wata muguwar faduwa, don ta gane ita ce, mahaifiyar Shatima domin sun yi matukar kama. Munnir ya ce, “Hajiya Aliyan Shatima c
Aliya ta saci kallon Hajiya don taga irin karbar da ta samu. Ta kuma gani don fuskar Hajiya ta yamutse, ta kuma kallon Aliya sannan ta ce, “Yana ciki.”
Jiki babu karfi ta tura kofar tare da sallama ta shiga. Nafisa ta waigo don taga mai shigowa tare da amsa sallamar. Dukkansu gabansu yayi mugun faduwa da ganin juna.
Sun san juna tunda Shatima sau biyu yana kai
Aliya gidan su Nafisa a wancan zamanin da suka
yi soyayya a baya. Nan da nan Nafisa ta hade rai
tamkar bata taba dariya ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Aliya ta lura da haka amma bata ki ce mata ina yini ba. Da kyar ta amsa, don ma Munnir yana ciki ne. Aliya taje kanshi ta tsaya, ta karanto addu’ar da tazo a Musulunci zaka karantawa mara lafiya.
Sannan taje ta dauki folder din sa tana duba abin da ke damunsa. Ta kalli. Munnir, gajiya da rashin bacci ne ke damun abokinka kenan.” Ya ce  Haka naji ana fadi.Ta dawo kusa da hannunshi, hannun ya kumbura. Ta ce, “A’a.” Ya motsa hannun ne?” Da alamu ruwan ba ya tafiya. Munnir ya taso da sauri ta duba sosai ta ce, “Tabbas ruwan nan baya tafiya.
Nafisa ta fita da sauri kiran Hajiya. Aliya ta saka safar hannu da ke aje gurin da aka jera abubuwan amfanin da suke mishi aiki da su.
Tazo ta soma cire ruwan ta sakale, sannan tasa hannu tana sabule allurar tun da ta cire. Ta ce da Munnir tunda an fi bukatar ya yi bacci, in ya farka sai a maida mishi ruwan.”
Daidai lokacin Hajiya da Nafisa da Nurse suka shigo. Aliya ta kalli Nurse din ta ce “Na cire mishi ruwan don naga yafi bukatar bacci, na duba allurar da aka yi mishi.”
Nurse din ta ce, “Haka ne, kin kyauta. In ya tashi sai a maida masa.” Aliya ta kalli agogo “Nan da karfe uku zai tashi, ko da mintuna.” Nurse din ta ce, “Haka ne” Nafisa ta tabe baki ta zauna. Hajiya ta juya ta fita.
Nurse din ta ce “Ku ragu a dakin.” Aliya ta mike “Bari in je daga wajen.” Munnir ya ce, “To muje.” Nurse din ta ce, “Ke ya kamata ki tsaya tunda kin san yanda za a kula da shi.”Aliya ta ce, “Babu komai, ai an cire mishi ruwan.” Suka fito ta cire safar ta zuba a kwandon shara.
Amna suna ta waya da Mustapha wanda yaje ya dauko Kaka. Yana kara yi musu kwatance yanda za su iso asibitin don sun shigo Zaria din.
Domin Mustapha yana fada mata hankali tashe ta shiga gurin Anty Amaryar Babansu ta fada mata, don Mom sun tafi Dubai da China don hado kayan kicin na ita Amna din.
Nan suka shirya zuwa duba shi, ita da Anty da kanwarta Sumayya. Amnarko bayan ta da ruwan gora zuwa kayan Tea da lemukan gora dana gwangwani
Mustapha ya riga su isa asibitin, ya fito da kujerar Hajiyar da ake tura ta don bata iya yin doguwar tafiya. Har da Maryama suka zo suka taimaka mata ta zauna a kujeran, ya tura ta suka nufi cikin asibitin. Nan kowa ya tashi ana gaida ta cikin girmamawa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya ta tsugunna a gabanta tana yi mata sannu da zuwa. Ta gaida ta, Kaka ta tambayi jikin Shatima, ta ce, da sauki. Mustapha ya turata zuwa ciki.Tana ta fadin “Sannu dan nan, ciwo haka da gaggawa, jiya muna tare.” Nafisa ta durkusa ta gaishe ta. Mustapha ya fita da sauri sakamakon kiran da Amna ta masa cewa gasu sun iso.
Ya same su a harabar asibitin. Yayi musu jagora. Amna sanye da doguwar riga dinkin Dubai, kalar ja da ratsin baki, ta yafa dan karamin mayafin rigar.
Har gaban Hajiya ya kai su yana fadin “Ga Amna daga Kano amaryar Yaya. Ta gaban Aliya suka wuce, tunda taga Munnir ya tashi ya bisu ta zargi cewa wannan Amna ce.
A fili ta ce, “Lallai kuwa Shatima ya hada mata.” Ta maida hankalinta don taga irin karbar da ita zata samu a gurin surukar tasu. Sai ta hanagi bakin Hajiyar har kunne, tana yi musu sannu da zuwa. Ta ce “Wace ce ‘yar tawa?” Sai Amna taja gefen mayafinta ta rufe fuska.
Hajiya ta ce, “A’a na ganta masha Allah, to Munnir kai su ciki.” Anty Amarya ta ce da Mustapha suje da Sumy su kwaso abu a boot. Sumy cikin shagwaba ta ce, “Anty zamu iya kuwa? Akwai fa yawa.” Hajiya ta dubi Hamida kanwar Nafisa, da
Maryama ta ce. “Kuje ku taya su. Amna tana shiga suka kalli juna da Nafisa. Amna ce tana shiga suka kalli juna da Nafisa.Amna ce ta fara kauda kanta,domin faduwar dataji gabanta yayi, tabbas wannan daya daga cikin kishiyoyinta ne.Anty ce kawai tagaida Nafisa tare da tambayar jikinshi.Amna tana tsaye tana karema Shatima kallo,so da kaunarshi azuciyar ta suka nunku.
Uku da minti biyar Aliya ta sake dosar dakin dan tasan yana daf da farkawa. Tasamu Anty ta fito gurinsu Hajiya,ga kuma kayanan ana ta jibgewa wanda su Amna suka zo dashi acikin dakin Munir da Amna suna kan kujera Nafisa tana zaune inda take. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka kuwa daidai lokaci yayi mika gami da salati yayi juyi kamar zai cigaba da bacci, sai ya ji gadon ba irin nashi ba. Ya dan yi shiru don son ya tuna ashe fa bashi da lafiya, sai ya bude ido ya kalli Hajiyar.
Yayi yunkurin tashi, sai ya ji Munnir  yace “Yi a hankali Shatima.” Ya kama shi ya tayar zaune. Mamaki ya cika shi ganin Aliya da Nafisa Ya ce, “Har an taso mutane haka Hajiya?” Ta ce, “To ai abokin kuka shi ake fadama mutuwa.” Ta nuno Amna wadda ke zaune tana danna waya tayi tamkar ba ta san suna yi ba. Ta ce, “Ga ma mutan Kano yanzu suka zo. Ya kai duba Amna ta dago suka hada ido. Ya
saki dan murmushi “Har da ke honey?” Ta dago
mishi yatsunta guda biyu alamun sannu.
Ya ce, “Daga nesa? Ban amsa ba.” Nafisa ta cika tayi tam! Ya kalli Hajiya “Ina Alhaji?” Ta ce “Bari Mustapha su gama ya kira shi ya ce ka farka sai waya yake, bai dade da barin nan ba shi da sauran iyayenka.”
Mutanan waje suka soma shigowa suna yi masa sannu suna fita. Ya ce, “Munnir ya ba shi rigarshi yasa. Ya ce zai yi fitsari. Munnir ya taimaka masa. Yanzun ba in da yake masa ciwo sai dai bakinsa babu dadi, jikinsa kuma babu karfi.
Ya dan ci abinci kadan, Likitan ya shigo lokacin Kaka tana ciki tana ta yi wa ‘yanmatan nashi tsiya, wai sun kasa sun tsare. To ita ce dai me shi.
Nafisa ban da kumburi ba ta komai. Aliya ce tayi dan murmushi ta ce “Ai ba zamu ja da ke ba.” sai lokacin Amna ta dago ta kalli Aliya,yanzu har da wannan a cikin matan da honey dinta ke so?
Ita duk kallo take yi ko Malamar asibiti ce mai kula da shi,  Likita yayi masa tambayoyi, sannan ya ce “In ya gama za’a maida masa ruwan da ya goce.
Shatima ya ce, “Ka sallame ni in je gida aurena ya kusa.” Likita ya ce Sai ka huta nan da kwana biyu. Ko dama auren ne kasa a ranka ka ke neman ja za ma kanka wani ciwo?”
Ya ce, “A’a Likita, waccan matsalar daban.” Kaka ta ce, “Likita kar ka sallame shi sai ya yi sarai. Yaron nan ya jaza min tun jiya bacci ya gagari idona, rabon da in fito kusan shekara guda da rabi, amma yau silar shi gani na fito.”
Likita ya ce “Kaka ai ya taimake ki, fita tana kara lafiya, ki daure ki ke fita ko sau daya a sati.” Ta ce, “A’a ni ba in da zan je ko da ba mu saba yawo ba mu.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiyar shi ta sake shigowa, bayan tayi ma wasu rakiya. Ta ce, “Shatima ga fa kaya nan da su Amna suka zo da shi, babu gurin ajiya sai dai a rabawa jama’a ko?”
Kaka ta ce “Wai ni ana ta Amna har yanzu ba ku nuna min ita ba?” Shi da kanshi ya ce, “Ki duba duk matan gurin nan ki nunata da kanki.” Ta hau waige-waige. Amna ta ja dan mayafinta ta rufe fuska.
Kaka ta ce, “A’a na ganta, to bude in gani kin kai ni kyau!” Nafisa ta mike fuu! Ta matsa. Aliya ta kalle shi, “Bari in maida maka ruwan in tafi gida basu sani ba, daga gurin aiki nazo.”
Ya kalle ta, “Dama ke ki ka sa min dazu?” Cikin zolaya ya tambayeta. Ta yi dan murmushi. Ya ce, “Shi yasa ban ji zafi ba.”
Ta dauki abin neman jijiya. Ya miko hannu yana murmushi yana kallonta cikin ido. Ta ce, “Ba wannan hannun ba ya kunbura, bai daina kallonta ba ya miko daya hannun. Ta ki su hada ido ta daure masa hannun, sai ya ce “Ash!” alamun zafi.
Ta kalle shi da sauri, sai ya daga mata gira. Ta kalli su Hajiya da ke kallonsu, ta dauki auduga tana shafawa don jijiya ta fito, ta dauki allura ta tsira. Jini yana biyowa ta kalle shi. Ya sake kashe mata ido.
Ta jona masa ruwan ta daidaita. Ta dube shi “Ka aje hannu da kyau, kada ya sake gocewa.” Ya ce, “To my love.” Ji tayi tamkar kasa ta bude ta shiga don kunya Ta kalli gurin su Hajiya, “Allah Ya kara sauki, zan tafi.” Suka ce “Ki gaida gida.” Kaka ta ce “Allah Yayi miki albarka, kai ka huta ga ma aikaciyar jinya a gida, in larura ta samu ba a fata ba sai an je asibiti ba.
Aliya dai ta kalli Amna ta ce, “Ku gaida gida, an gode.” Amna ta dago kai ta dubi Aliya, da ido tayi alama tare da dan daga kai. Ta kalli Nafisa, “Sai anjima, Allah Ya kara sauki.”
Nafisa taja tsaki, hakan ya ba kusan duk wanda ke dakin haushi har da Mamanta.
Su Amna suka fita don yin sallar La’asar a Masallacin asibitin. Nan take Kaka ta shiga yiwa Nafisa fada, ta ya ya ‘yar uwarki tana miki sallama ki ka ja mata tsaki? Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai ta ce, “Kaka ina ruwanta da ni, ni fa ban kula kowa ba tunda nazo.” Shatima ya dubeta fuskarshi babu walwala, “Kije gida na gode kawai.” Mamanta ta ce, “Ai ita sakarya ce, shegen kishi ta dora ma ranta.” Hajiyarshi ta ce, “Nafisa ai dole kuwa ki koyi hakuri da danne kishi tun da Allah Yasa ba ke kadai ce za ki zauna ba.” Fuu! Ta fice ta nufi gida.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE