RANA DAYA CHAPTER 13 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 13 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Sai ta ce, “Kaka ina ruwanta da ni, ni fa ban kula kowa ba tunda nazo.” Shatima ya dubeta fuskarshi babu walwala, “Kije gida na gode kawai.” Mamanta ta ce, “Ai ita sakarya ce, shegen kishi ta dora ma ranta.” Hajiyarshi ta ce, “Nafisa ai dole kuwa ki koyi hakuri da danne kishi tun da Allah Yasa ba ke kadai ce za ki zauna ba.” Fuu! Ta fice ta nufi gida.

Su Amna suna dawowa suka soma shirin.. tafiya. Shatima ya ce, “Ni dai ba ni ki ka zo dubawa ba.” Ta ce, “Waye ne nazo dubawa?”
Ya ce, “Kin zo danna waya ne da zama a waccan kujerar.” Ta ce, “To ina zan zauna?” Ya nuna bakin gadonshi.
“Ga guri nan.”Ai tafiya zamu yi, tunda ka ji sauki. Haka
ma ya yi min dadi.” Ta fada cikin yake. “Ban gaji da ganinki ba.” Ya fada yana kallonta. Ta ce, “To kayi ta kallona na minti biyu.” Anty tayi dariya ta fita. Kaka ta ce, “Ikon Allah! Yaran yanzu ba kara.” Amna ta ce, “Kaka ban ce komai ba.” duk suka sa dariya, sannan suka fice. Rakiya gurin mota har da Hajiya.
Zuwa washegari Shatima yayi sarai. Da safe iyayen sun zo duba shi, don Mustapha ne ya kwana. Ganin jikin nashi, shi ne ya ba su damar saka shi tsakiya suna tambayarshi wannan damuwa da Likita ya ce za su nesanta shi da ita. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shatima ya yi shiru. Hajiya ta ce, “Haba Shatima, kana son saka mu a cikin damuwa ko?” Yayi murya irin ta yaron da ke gaban iyayensa irin ‘yan gatan nan.Ya ce, “Ku bar shi kawai, ko na fada ba lallai ne ku amince ba.” Alhaji ya ce, “In kaga ba a amince ba to abin ya shafi addini ko mutuncinmu.”


Shatima yayi shiru don dai ya dan kara ja musu aji. Alhaji ya ce, “Kayi magana mana Babana.” Shatima ya ce, “Wata yarinya ce ni ke son in cike ta hudu da ita su Hajiya suka ce a’a, kuma ni gara in fasa auran duk ukun nan in aureta ita daya. Yanda ni ke ji kamar zan rasa raina…”
“Kai yi mana shiru!” Hajiya ta katse shi. “Na ce ban yarda ba da karin wani aure.” Shatima ya koma ya kwanta a hankali, bai ce komai ba.Alhaji ya dubi Hajiya, “Wai kin manta da
zancan Likita ne?” Ya sake matsowa kusa da Shatima. “Babana ‘yar gidan wane ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Shatima ya ce, “Alhaji marainiya ce, ubanta ya mutu. Na yi ma Allah alkawarin kula da ita, aurenta shi ne zai fi bani damar lura da ita, domin zata kasance kusa da ni, in ko na barta na ce zan ke taimaka mata, kila wani lokaci yazo wani yanayi na daukaka ko akasin haka ya sani in manta da ita. Wannan ce damuwata, in har zan samu yardarku zan zama a cikin farin ciki mai dorewa.”
Hajiya ta ce, “Ka san Allah…” Alhaji ya daga mata hannu tare da cewa “Kiyi min shiru.” Ya kalle shi, “Yaushe ka ke son aje zancen auren?”
Ya ce, “In an sallame ni gobe ko zuwa jibi ne sai aje. ” Ya ce, “Shi kenan ka Kaddara cewa ka aureta an gama.” Ya kalli Hajiya, “Na haramta miki sake ďauko zancan nan in dai na isa.”
Kwafa tayi sannan tasa kai ta fice daga dakin. Alhaji ya ce, “Kar ka damu, zata sauko da zaran na lallasheta. Zan sanar da Babanka Musa sai aje gidan iyayen yarinyar, sun san dai da kurewar lokacin ko?”
Ya ce, “Sun sani.” Ya ce, “To ba ka da sauran damuwa in dai wannan ce. Yanzun dai zan wuce da Hajiya gida, ku ci gaba da zama da Mustapha in ta huce zata dawo.”
Suna tafiya ya dauki wayarshi ya kira Munnir ya ce yana gurin aiki. Shatima ji yake kamar a sallame shi yaje yayi aikin da zai saka Munnir. Haka dai ya hakura har karfe biyar, Munnir ya taso. Ya ce “Don Allah yana son yaje gidan su Salma ya bata wayarshi zasu yi magana.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Munnir bai so ba amma ba ya son ya bata masa rai, tunda duk sun ji labarin abin da Likitan ya ce a kansa, ya tafi.
Yana zuwa kofar gidan Yayanta yana fitowa. Suka gaisa, ya ce “Ina Alhajin yau?” Munnir ya ce, “Shi ne ya aiko ni, ina yarinyar nan?’
Yaya Auwal ya ce, “Umma Salma tana ciki, bari in kira ta.” Duk zatonshi Munnir ne mijin da Shatima ya ce zai kawo mata, har yana fada mata.
“Kin gane abokin nan nashi? Ina jin shi ne zai aure ki. amma kije ki gani.” Tare suka fito, ta gaishe shi tare da tambayar Alhajin. Ya ce “Shi ne ma ya ce in nazo in kira shi za kuyi magana.”
Ya soma kiran layin Shatima. Shi ko Yaya Auwal yana can gefe yana lura da su saboda tsaro. Shatima ya daga wayar Munnir ya mika mata tare da fadin. “Gashi.” Ta amsa tayi sallama. Shatima ya amsa. Ya ce, “Salma.” tace”Na’am! Yaya.”
Ya ce “Ina Yayanki Auwal?” Ta ce, “Gashi can tsallaken titi.” Ya ce “Kira shi ki ba shi wayar.” Ta kalli gurin da Auwal yake suka hada ido.
Ta yafito shi da hannu alamun yazo. Ya zo, ta ce “Yaya zai maka magana.” Auwal ya ansa tare da cewa “Alhajin ne?”
Bayan sun gaisa ya ce, “Salma ta ce min haya ku ke yi ko?” Ya ce, “Eh haya ne Alhaji.” Shatima ya ce, “Ina wanda gidan ke hannunsa?” Ya ce, “Makocinmu ne.”
Shatima ya ce, “Ina son ya samo muku wani gidan hayar za ku tashi a wannan gidan, ko ba ya nemowa?’ Auwal ya ce, “Yana yi.” Shatima ya ce, “To ina son duk yanda za’ayi gobe a samu gidan da zaku koma saboda za a zo neman auran Salma.
Ka amshi lambata a hannun wannan abokin nawa, koda wayar wani ne ka kira ni ka fada min. Www.bankinhausanovels.com.ng
Auwal ya ce, “To Alhaji, Allah Ya saka da alkairi.” Shatima ya ce, “Ba komai, ba Salma to.” Ya kalli Munnir ya ce, “Ka bani lambarsa.”
Ta amsa ya ce “Sai ma na fada ma Yayanki ne zaku canza gidan haya kin ji ko?” Ta ce, “To
Yaya.” Naji muryarka kana yin mura ne? Ya ce, “A’a na gaji ne, abubuwa sun yi min yawa ba ki ganni ba, zan zo.”
Ta ce, “To Yaya amma yaushe ne za ka zo
din?” Ya ce, “Ko jibi haka, kada ki damu ba
Munnir wayar ta ce to sai anjima.” Ta mika ma Munnir tare da fadin “Gashi Yaya.” Ta dan durkusa ta bashi. Suna tsaye ya tafi, Auwal ya ce, “Muje ciki muyi magana da su Inna.”
Auwal ya fada musu abin da Shatima ya ce.. Inna ta ce, “Kai ku tsaya! Ni fa ina tsoran wannan al’amari, kar fa garin son abin duniya mu sa kanmu uku! Yanzu in tsakani da Allah za’ayi ga inda aka ganta ba za a zo neman auranta nan ba?” Yaya
Auwal ya ce, “Inna babu kyau munanan zato, mu
fa ya ce mu nemo gidan hayar zai biya. Kuma manyan mutane ne za su zo kin ga ai mu ma ba za mu so su same mu a kaskance ba.” Yaya Hadiza ta ce “Inna yanzun dai a bar wannan zance a nemi índa za’a samu gida tunda dama kudinmu ya kare tun wancan watan. Masu gidan suna ta yi mana rashin mutunci.
Salma ta ce, “Allah ne ya kawo mana mafita dama muna ta ya ya za a yi a samu dubu sha biyu da za a baiwa masu gida?
Suka ce, “Haka ne kam!” Auwal ya ce “Ina ga ba zan yiwa Maigidan nan maganar wani gidan ba, gara in je in sa samu Bala dillali. Hadiza ta ce, abin da zance kenan, ba za’a rasa gida a hannunshi ba.”
Ya mike “Ina zuwa ma dai ku gani, da zafi zafi a kan bigi karfe.
Cikin sa’a Bala ya ce masa “Akwai gida guda
biyu, daya na zaman mutum uku, daya kuma na zaman mutum biyu. Daki nawa za ku kama?” Auwal ya ce, “Daki biyu ma ya ishe mu.” Bala ya ce, “To me zai hana ku kama gidan can na kusa da ku, gidan dan kurma wanda ya saida
Auwal ya ce Matsalar dai biya mana za’ayi Www.bankinhausanovels.com.ng
kila kudin ya yi yawa ko?” Ya ce, “Dari ne da goma sai mu da za’a sallama.” Auwal ya ce, “A dai yi mana sauki mu gani.” Ya ce, “To magana daya dubu tamanin ne, sai mu kuma a sallame mu.”
“To duk yanda aka yi zan same ka gobe.” Bala ya ce, “In kuma na wancan ku ke so daki biyu dubu talatin da biyar ne. Auwal ya ce zan fada masa duka. Haka kuwa sai washegari da misalin karfe goma Yaya Auwal ya kira lambar da ke jikin katin da Munnir ya bashi..
Shatima ya daga, ya ce Ni ne Auwal lambar Alhaji ce? Shatima ya gane ya ce, “Ni ne.” Ya kalli Mustapha da ke hada kayan su don Likita ya fita yanzun bayan ya sallame su.
Ya ce, “Kaje waje. Bayan fitarsa Shatima ya ci gaba da magana. “Auwal ka samu gidan?” Ya ce “An samu alheji.” Ya fada mishi farashin su. Ya ce, “To ku kama naku kadai din zan ba abokina dubu dari ya kawo muku anjima, in da dan wani gyara sai kuyi.”
Auwal ya shiga godiya, Shatima ya kashe.” Nafisa tana isowa asibitin suna fitowa. Ta ce, “An sallame ku ne? Suka ce “Eh.” Don haka tare suka juya.
Da suka isa gida Hajiya ta ce “Kar ya hau samanshi, a bude masa falon Babansu saboda mutane za suke zuwa duba shi.
Ya yi Transfer din dubu dari a cikin account din Munnir. Ya ce, “Ya cire ya kaima su Salma. Da ya taso aiki kuma ya ciro yazo ya yi sallama da Salma ya bata..Ranar kuwa suka biya kudin gidan aka ba su mukullin. Ranar suka share, washegari da safe, suka dan yi saye-sayen labule da ‘yar ledar kasa suka tafi suka gyara suka shiga.
A daren ranar Alhaji da dan’uwansa Alhaji Musa Baban su Nafisa, suka zo gurin Shatima suka ce, “Batun wannan yarinya za a je gurin iyayenta.
Shatima ya ce,. “Su bari sai washegari. Da yammacin washegari kuwa Shatima yayi fes cikin kananan kaya, in ka ganshi dole ya birge ka ya dauki makullin mota ya fita. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya ta ce, “Ina zaka?” Ya ce, “Zan dan zaga gari ne, na gaji da zaman gida.” Ta ce, “To sai ka dawo.”
Kai tsaye gidan su Salma ya dosa, cikin
zuciyarshi yana son in ya zo gidan su nada
ya tambayi inda suka koma.
Cikin sa’a ma yana fitowa sai ya ji Auwal yayi masa sallama. Ya waiwaya ya bashi hannu suka gaisa, ya ce “Ai ina can naga wucewar motarka.” Shatima ya ce, “Ina ne gidan naku?” Auwal ya ce, “Baya ne kadan.” Ya ce, “To shiga muje. Ya ji dadin ganin gidan har ciki ya shiga. Su Inna da sauran ‘yan’uwansu da basu wuce ba suna ta godiya. Ya samu Salma tana wanke wanke ta saki tazo ta tsugunna ta gaida shi. Ya ce, “Salma nan yayi?” Ta ce, “Kai! Sosai
ma.” Cikin mamaki tayi maganar. Ya dubi Inna, “Gurin wa za a zo neman auran na Salma, saboda anjima za sú zo?”
Inna ta ce, “Gurin kanin Babansu ne a can Kofar kaura ya ke, in an ji lokacin da za su zo sai a je a dauko su da aminin Babansu nan makotan da muka taso.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Shatima ya ce, “Yau za su zo karfe takwas na dare Sannan kuma Inna bikin yau saura kwana ashirin da biyar.” Inna ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce “In sun zo iyayen namu za ku ji komai.” Ta ce. “To shi kenan, Allah Ya kawo su. Shi kuma Kawun nasu za a je a zo da shi.”
Da zai tafi ya ce Salma ta zo, a zauren gidan suka tsaya. Ya kalleta yana murmushi.
“Kin shirya aure nan da kwana ishirin da biyar?” Ta dan juyar da fuskarta cikin kunya ta kalli bango. Ya ce, “Kiyi magana.” Ta ce. “Zan yi mana.” Ya ce “To juyo ki kalle ni.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE