RANA DAYA CHAPTER 16 KARSHE BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

 

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Wanka ya fada, da ya fito yayi sallah tun daga lokacin ya fara nuna shi ango ne. Gizna ce ya sha fara sol sai aikinta mai ruwan kasa da ratsin gwal.Aka soka hula kube
takalmi. Turare kuwa yanda ka san zai yi
magana. Ya sakko suka hadu a falo.
Hajiya tana aiken Direbansu, ta tsaya tana kallonshi. Yayi mata kyau sosai. Ya ce, “Hajiya sannu da fitowa.” Ta ce, “Kai ne da sannu Ango, wannan irin wanka haka?”
Ya ce, “Ai karamin wanka ne wannan sai ma anjima.” Ta ce, “To zo muyi magana mana.” Dakinta suka shiga ta ce, “Naji Alhaji yana cewa wai za a daura aure da safen nan?”

Shatima yace “Na Kano ne?” Ta ce “A’a Idan da na Kano tunda asubahi fa naji yana ta waya wai saboda abokanka ko mene ne?”
Shatima ya ce, “Ok, na Aliya ne za’a daura yanzun da safe, saboda ‘yan nesa, in mun yi walima za su tafi.”
Hajiya ta fadada fara’a “Ayya, na gane. To ya za ayi da abincin daurin auran tunda ba mu san za’a zo da zancen ba?” Ya ce, “Ba akwai snacks da nama ba?”
Ta ce, “Eh to, bari sai in sa a zuba a take away.” Ya ce, “Yauwa to sai su Munnir su zo su dauka.”
Gurin abokansa ya nufa inda suka yi masauki,
ya same su kwance wasu kuma suna danne
dannen waya. Ya ce, “Don Allah ku tashi ku
shirya daurin aure karfe takwas.”
Nan suka shiga yabon kýan da yayi. Ya ce Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ko zama ba zan yi ba kar su yamutse.” Cikin zolaya ya yi maganar. Haka dai ya matsa musu har suka shirya wasu


suka wuce gurin Hajiya don dauko abin da za a
ci a gurin da abin sha. Sun je kofar gidan su Salma Karfe bakwai da
wani abu. Babu kowa, Shatima yaje har kofar
gidan ya yi sallama Auwal ya fito, yaga ko
wanka bai yi ba. Ya ce, “Auwal kun manta ne?” Ya ce, “Muna
sane, yanzun zan yi wanka.” Shatima ya ce, “Ka zo kawai ga abokina kuje da mota ku dauko kanin Baban naku.”
Haka ya matsa musu aka tafi, shi burinshi kawai a daura auren nan, dama motocinshi uku duk suna gurin, da wadda a ka ba shi a gidan su Amna, da wadda ya zabo abokin Babanshi ya bashi.
Da kanshi yaje gidan waliyyin ya fito dashi cikin shiri. Shatima ya dan ji dadi ya ce, “Dama nazo ne in ji ko ba ku manta ba.”
Ya ce, “Ai lokacin bai cika ba ko?” Shatima ya kalli agogon hannunshi, “Eh saura minti talatin.” Ya ce, “Ba komai, shi Auwal ko ya tafi ya zo da dan uwan Baban nasu?”
Shatima ya ce, “Na hada shi da abokina su Www.bankinhausanovels.com.ng
tafi.” Ya ce, “Nan ma na sa an sanar a Masallaci,
kuma da safen nan nasa an fadawa makota.”
Shatima yayi godiya ya koma gurin abokansa, sannan ya ce “Munnir don Allah ka je ka taho da su Alhajin ku.”Munnir ya ce “Shatima wai me yasa ka kasa nutsuwa ne? kar ka manta ba wannan ne kadai auran da za a daura maka ba ko?”
Shatima ya ce, “Ni dai burina a daura
wannan, don shi kadai ne me matsala.” Munnir
yayi tsaki, sannan ya wuce.
Salma bata san ma wai an dawo da daurin auranta na safe ba, don ita ko kunshi bata yi ba, ta bari sai da rana tukunna.
Umar ne ya shigo yana cewa “Mutane sun taru a waje.” Yaya Hadiza da wata kawarta itama lokacin sun zo za su amshi kudin cefane gurin Inna suje kasuwa, suka ga guri tam! Da ta shiga take tambayar Inna.
Ta ce, “Ummi ni dai wannan lamari ina nan
ina ta addu’a, jiya fa har mun kwanta ya buga
gida, wai a maida daurin aure na safe.”
Hadiza ta ce, “Insha Allahu alkairi ne.” Itama Salman sai lokacin taji. Hadiza ta dube ta, “Wai Salma kin tsefe kanki kuwa?”
Ta ce, “Na tsefe da dare.” Ta ce, “To in an watse ki dauki wannan man da na ciro miki a akwati na shampoo din ki je shagon wankin kan.Ta ce, “To, kuma wadda zata min kunshin ta ce karfe goma zata zo.” Kawar Hadiza ta ce, “A fara yi mata kunshin mana shi ne mai wahalar.” Salma ta ce, “Nima haka naga zai fi.”
Iyayen Shatima sun iso cikin zauran gidan aka sa tabarma suka zauna, sauran mutane suna waje. Guri fa ya cika tankam. Nan aka daura auren Salma da Muhammad Ja’afar Shatima.
Ana gamawa abokan suka shiga raba-abin da
suka zo da shi. ‘Yan unguwa kam sun shaida
lallai Salma ta tako. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga nan kai tsaye suka soma daukar hanyar Kano don karfe tara ta gota. Shatima ya ce, sai ya je gida ya canza kaya, Munnir ya jira shi. Bayan an ragu ya kira Auwal ya ce ya kira
mishi Salma. Dogon hijabi tasa ta same shi a
zaure. Ya kalleta cikin mamaki, ya ce “Salma ya
ban ga kina kyalli kamar sauran Amaran ba?” Gabanta ya fadi, “Wai da gaske ka ke yi mu hudu ne?” Bata san lokacin da tambayar ta zo mata ba. Ya ce, “Wannan ce amsata.” Ta dan yi shiru, sannan ta ce, “Nima ban sani ba, kila don ban wanke kai ba ne sai anjima zan yi.”
Ya ce “A’a su fa naga fuskarsu duk tana ta kyalli, ga kunshi, ke in ga hannunki.” Ta nuna mishi. Ya ce”Haba Salma! Me yasa za ki yi haka?”
Ta ce, “Zan yi ai.” Ya ce, “Je ki shirya ki zo in kai ki gurin da za’a wanke miki kai.” Ta ce, “Yaya zan je Allah.” Ya ce, “Ai daga yanzun na koma miji ba Yaya ba, kuma ba a musu da miji.”
Ta ce, “To.” Ta juya ta koma ciki ya fito, Munnir ya ce, “Ka zo muje don Allah kada lokaci ya kure.”
Shatima ya ce, “Ai yanzun ma gurin gyaran gashi zan kaita.” Munnir ya ce, “Don iskanci ka bar ni in tafi tare da mutane ka tare ni.” Ya jeho masa makullin sabuwar motarsa, “Ga makullinka, bari in bi su Bello don a karshe ba zuwa zaka yi ba.”
Shatima ya ce, “Ka bari mu bi jirgin karfe יי goma.” Munnir ya ce, “Goman dare ko? Duba agogonka kafin muje filin jirgin ma ai ‘yan daurin auran sun juyo, kaga ni bari in bi su sai mun dawo, don nasan kai ba zuwa zaka yi ba kana gurin wannan yar mitsitsiyar yarinyar.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Shatima yayi murmushi. Ya ce, “To Allah Ya tsare, amma ina mai tabbatar maka ina gabanka can zaka same ni.” Munnir bai sake magana ba ya shiga motar abokansu wadda da suka tsaya za su jera tare, ya ce, “Ku mu je wannan angon ba zuwa zai ba.”
Salma ta sanar da Yaya Hadiza yanda suka yi da Shatima, Hadiza ta ce “Muje muji ta bakin Inna.” Inna ta ce, “Anya kuwa sa fita?”
Wata kawarta ta ce, “Ai yanzu matarsa ce.” Hadiza ta ce, “Shi ne nima na gani.” Inna dai tayi shiru.
Hadiza ta ciro mata jallabiya baka da mayafinta, sai takalmi mara tudu duk na cikin lefan, ta ce “Gashi ke ko wanka ba ki yi ba.”
Salma ta ce, “Bari in dauraye jiki.” Suka bata turaruka ta fesa ta dauki saitin man da zata yi amfani da shi.
Yana jingine a jikin mota, ta fito ta nufo shi.
Ya bude mata gaba ta shiga ya zagaya ya shige.
Ya dan dube ta bayan sun hau titi.
“Bana son kazanta fa, amarya har yanzun bata gyara kai ba.” Ta ce, “Zan gyara dama, ni ban san da safe za’a daura auran ba.” Ya ce, “Amma ya ki ka ji da aka ce ya dawo na safe?”
Tayi dan murmushi, “Ban ji komai ba.” Ya ce, “Har yanzun ba ki fara sona ba ko?” Ta dan ja mayafinta ta rufe fuska. Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce, “Ai ban san so ba ni. Ta yiwu ina yi maka.” Ya ce “To na baki lokaci ki soma sona kafin mu hadu, ki bincika ki san ya ya ake so? Ya ya so yake? Kuma mene ne so?” Ta kalle shi tayi
murmushi ta ce, “To.”Katon shagon da ya kaita lokacin ma suke budewa. Ya ce suyi mata gyara me kyau amarya ce. Ya ji mamakin ganin gashin kanta mai cika da tsawo. Ya ce, “Dama kina da gashi haka?”
Tayi ‘yar dariya. Duk da kiran da ake ta yi ma
wayoyinsa bai ji ko da a ransa wai ya tafi ya bar ta ba,
Hajiyar Shatima tana ta kai-kawo a cikin
jama’ar da suka taru a gidan ‘yan uwa da abokan
arziki, amma zuciyarta tana can gurin tunanin
Hajiya Azumu.Wai ina ta shige ne oho! Ba ita ba labarin yarinya. Sai kusan goma da kwata sannan Hajiya Azumi tayi sallama a gidan.
Hajiya ta mike da sauri tazo tana fadin, “Hajiya Azimi haka muka yi da ke?” Ta ce, “Muje daki da labari.” Can kurya suka shiga, Hajiya Azumi ta ce, “Hajiya da matsala katuwa, kuma gashi me afkuwa har ta afku.”
Hajiya ta ce, “Kar ki ja min rai muje labari.” Hajiya Azumi ta ce, “Yarinyar nan sunanta Ummu Salma, iyayenta talakawa ne na tsiya har gidan da suka tashi sai da aka nuna min wanda suke haya. Www.bankinhausanovels.com.ng
A cikin bikin nan Shatima ya sai musu gida suka koma saboda kada danginsa su gane tsiyar su.”
Hajiya ta dafe kirji, “Ya sai musu gida?” Hajiya Azumi ta ce, “Har gidan na shiga. An ce barin kudi yayi musu ba kadan ba kuma ance abin sai wanda ya gani, kuma kullum yana gidan.”
man Hajiya ta ce, “To wai yarinyar wani mugun kyau gare ta ne?” Hajiya Azumi ta rike baki tare da fadin “Wane irin kyau, ni da na ga yarinyar ma sai kunya ta kama ni, na soma tunanin ya ya aka yi ya ganta har ya ce yana so? ‘Yar mitsitsiya, figigiya ko nonon kirki babu, ke ina ‘yar aikinki Masa’uda!”
Hajiya ta ce, “Kar ki ce min kamarta take?” Hajiya Azumi ta ce, “To ai Masa’udar ta fi ta cika ido. Hajiya ina ga asiri suka yi masa.”Hajiya ta soma zufa, “Lallai wajibi ne in kira Alhaji Musa tun kafin ma su dawo Kano.” Hajiya Azumi ta ce “Ki hana me? Ai lokacin da naje gidan an tashi daga daurin aure ke nan na shiga gidan nayi musu murna don dai in ga dil!”
Hajiya ta zauna dabas! “Wai dama auran da aka daura da safen nan nata ne?” Hajiya Azumi ta ce, “Shi ne, kuma a gabana ya dauke ta a mota suka wuce…”
Aliya da kawayenta guda biyu Aisha da Madina, sun tafi babban saloon don gyara gashin Amarya.
Suna sauka a dan sahu suka bashi kudin, sai taji gabanta ya fadi. Ta kalli Aisha ta ce, “Kin ji wata wawuyar faduwar gaba da naji! Allah yasa alkairi ne.”
Aisha ta ce, “Insha Allahu alkairi ne.” Madina
ta kalli dankareriyar motar da ke kofar saloon din
ta ce, “Dubi wata mota mai shegen kyau.
Aisha ta ce, “Wai! Gaskiya motar nan tayi karshe a kyau.” Aliya dai bata yi magana ba duk da bata san motar ba, amma da ta kalli motar sai da gabanta yayi wata mummunar faduwa
Cikin rashin kasala suka tura Kofar gilashin shagon, Aisha ta soma shiga sannan Madina. Ba su lura da cewa Aliya tayi mutuwar tsaye ba ne sai da Aisha ta waiwayo da nufin yi mata magana, ta zaci guri ta basu su fara shiga. ” Ta waiwaya ta kalli inda Aliyar take kallo, sai Www.bankinhausanovels.com.ng
taga Shatima zaune ya tasa Salma an gama wanke
mata kai ana tajewa da handrayer…
Wash! Bari in tsaya a nan sai mun hadu a littafi na biyu don jin ya ya za ta kasance?

Wane mataki Hajiya zata dauka? Ya ya Aliya zata yi da taga Shatima da Salma da ba ta san labarinta ba? Ya Amna zata amshi maganar Salma? Wane
ma irin zama za’a yi? Wai wace ce ma uwargida? Wa ya fi so?

Ku biyo ni.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE