RANA DAYA CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Mun tsaya
Munnir ya ce, “Allah Ya tabbatar mana da
dukkan alkairi.” Ya ce, “Ameen.” Kofar gidan su Munnir ya sauke shi, sannan ya nufi gidansu da ke Kwarbai a garin Zaria. Www.bankinhausanovels.com.ng
Damfareren gida ne mai girman gaske, wanda daga gani ka san ma su gidan da kunbar susa, kila ma da jibin sarauta.
Ya nufi ɓarayinsu ya aje motar ya kwashi
wayoyin shi ya nufi cikin dirkeken falon. Tana
zaune a kan kujera Badi’a tana shafa mata man zafi a kafa.
Ya zauna kan Dardumar da ke gabanta tare da fadin “Sannu da hutawa Hajiya.
Badi’a ta tashi da sauri tare da fadin “Sannu da zuwa Yaya. Ya ce, “Sannu Badi’a.” Hajiya ta ce, “Sannu Shatima, har ka dawo?”
Ya ce, “Na dawo Hajiya. Akwai aikin da zan yi “a gida ne.” Ta ce, “To, cikin laptop din taka za ka yi kenan?” Ya ce, “Eh.” Hajiya ta ce, “To bari in sa a kawo maka abinci daki, gashi kuwa abin da ka ke son aka yi.
“Burabusko ke nan?” Ta ce, “Eh, kuma akwai farfesun kafar Sa, su zubo maka ko?”
Ya ce, “To Hajiya bari in shiga ciki.” Ta ce “Badi’a!” da sauri ta iso ta ce, “Gani Hajiya.” Ta ce, “Kira min Uwa a kicin.”
Shatima ya nufi sama in da dakinshi yake. Uwa ta iso falon cikin girmamawa ta ce, “Ga ni Hajiya.” Ta ce, “A shirya ma Shatima abinci.” Ta ce, “To Hajiya, kunun zaki za a zuba mishi ko zobo?”
Ta ce, “Kin san shi fa in bani na hada da kaina ba ba zai sha ba, ku kai masa ruwa mai sanyi da lemon kwali kawai.
Yayi nisa cikin aikin sa, Badi’a ta kwankwasa kofa. Ya ce, “Shigo.” Ta shigo da sallama ya amsa. Ta aje ta fita. Ya kalli abincin, tabbas yana son ci amma
yanzun aikin nan ne a gabanshi. A fili ya ce, “Ina
ma nayi aure da sai a ke bani a baki ina aikina.” Daf da kiran Magariba ya rufe komai ya ci
abinci, sannan ya yi wanka ya fito. Lokacin da yaje Masallaci ana raka’ar karshe, don haka ya jone da su. Abin da ke ranshi shi ne in ya idar ya nufi Tudun Wada don kai gaisuwa ga Kakarshi,
Mahaifiyar Babanshi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kusan kullum sai ya samu sakon korafinta daga bakin Mahaifinshi, tunda shi kullum ya ke zuwa kai gaisuwa ga tsohuwar tasa.
Daf da kwanar da zata kai shi gidan Kakar ya daga ido ya kalli gidan su Aliya, duk da yasan tarihi ya shafe babin Aliya, kuma ba zai sake ganinta ba yana da kyau ya kalli gidansu don kauna. A fili ya ce, “Alherin Allah Ya kai miki a duk inda ki ke Aliya.”
A cikin gidan Kaka tana fadin tayi fushi, ace tunda ya dawo ba ta samu arzikin ya zo ya duba ta ba, ko sau daya ta ma gan shi taji dadi.
Sai dai ya kira waya ya ce a bata. Ya ce yau gani na zo Kaka kiyi hakuri, yanayin aiki ne Kaka ina dawowa Gwamnati ta bani aikin nan.
Na samu aiki jingim a cikin wannan office din, so ni ke in karkare da komai, in kuma fahimci komai.” Ta ce, “To shi ke nan ka wanke kanka. Har ina cewa ko har yanzun bakin cikin Aliyar da baka samu ba ne.”Ya ce, “Kaka ni fa na jima da sa ma zuciyata hakuri, ba kin zuga su Baba sun ce in auri Nafisa ba?”
Ta ce, “In ji wa ke nan? Ni ban ma san lokacin da suka shiryo abin su ba, ni dai sun fada min kuma nasa albarka.
Nafisa tana da hankali, kuma tana da ilimi.” Ya ce, “Kaka sai dai fa ina zaton zan auri mata biyu ne rana daya, ya ki ke ganin yiwuwar hakan? Ban taba yin shawara da kowa ba sai ke yanzun. יי
Ta ce, “Shatima in kana bukatar sama da haka addini ya baka dama, ni ko iyayenka ba mu da ikon da zamu ja da haka. To da Aliyar za ka kara kenan?” Ya ce, “Wace Aliya kuma, na sani yanzun tayi ‘ya’ya sun kai guda biyu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kaka ta ce, “To ai bata yi auran ba.. Tsaye Shatima ya mike tare da maimaita kalmar “Bata yi auren ba?” Kaka ta ce, “Ni kar ka fado min, tana nan gidan da suka ce ba za ta jiraka ba.” Ya ce, “Kaka cire batun wasa!”
Ta ce, “Shi ke nan kowane lokaci ne ake yin wasa? Zancen gaskiya kenan. Amma zauna ka nusu sai Maryama taje gidan ta kira maka ita.
Ya ce, “Ni fa in kin bar ni tuni Aliya tayi aure.”
Ta ce, “Tana nan takan zo gaishe ni a kwanakin
baya.” Ta daga murya.”Maryama zo nan.” Ta zo ta tsugunna ta gaida Shatima. Kaka ta ce, “Je ki kawo masa abinci da ruwa.” Ta kalli Shatima wanda ya yi nisa cikin tunani, ta ce, “Sai dai fa tuwo muka yi.” Ya ce, “Iye! Me ki ka ce?” Ta ce, “Abinci na ce.” Ya ce, “Ba zan ci ba Kaka, ban dade da cin abinci ba, ki aike ta ta kira min ita don in shaida Kaka.
Ta ce, “To goga na Aliya, duk ka birkice, Maryama je gidan Alhaji Garba ki ce ina kiran Aliya.” Ta ce, “Wannan me aikin asibitin?” Kaka ta ce, “Ita.”
Ya bi Maryama da kallo kamar ita ce Aliyar, sannan ya maido da kallonshi kan Kaka. “Naji kuma kin ce mai aikin asibiti.”
Ta ce, “Eh, ai bayan tafiyarka Makarantar koyon aikin jinya ta shiga ta gama yanzun tana aikinta.” Ya mike ya nufi window yana leke tare da fadin “Naji kamar motsi ne.” kaka ta ce, “Ikon Allah sai kallo. To kuma fa in ka faye zumudi Nafisa jikata ce sai in saka takalmin karfe in murza kasa in ce ita kadai za ka aura.”
Ya ce, “Kaka ai in har ta tabbata Aliya ta ce, “To akwai yiwuwar zan yi mata uku rana daya.” Kaka tasa dariya sannan ta ce, “Ashe zaka kafa tarihi a Zaria ” Sallamar Maryama suka ji, bai amsa sallamar ba amma ya ce “Ina take?” Ta ce, “Tana sallah, Mamansu ta ce in ta idar zata zo.
Ya sake kallon Kaka ya ce, “In ko Aliya ce, ban san ma wane irin albishir zan yi miki ba a duniya da na ba ki kujerar Makka, sai dai babu kafar zuwa.
Ta ce, “In ka yi niyya ai ko zuwana na karshe kan kujerar turi nayi aikina, Babanka ya biya askarawa suka yi ta dawainiya dani. Shatima ya yi murmushi, ni dai ki bar batun Makka, zan siyo mimiki kaji ayi miki farfesu mai laushi ki sha kayanki.
Ta ce, “Aikin banza, don kaji kullum Babanka sai ya kawo min.” Ya ce, “To kan Shanu fa..?” Sallamar da suka jiyo ce ta hana Kaka maganar Www.bankinhausanovels.com.ng
sai amsa sallama tayi. Shi ko kasa magana ya yi,
ya lumshe ido yana tunanin yanda zai ga Aliyarshi. Tayi sallama a kofar falon, nan kaka ta amsa. Kanshi yana kasa, ta isa can gefen wata kujera ta zauna, sannan ta gaida Kaka tare da cewa.
“An ce kina nemana, Allah Yasa lafiya?” Kaka tayi yar dariya. “Ga me nemanki nan.”Sai lokacin ta kalli gurin da mutumin yake, don da ta shigo hakika taga mutum amma ba ta tsaya dalle
kallonshi ba. Ya dago ido suka kalli juna. Zumbur! Suka mike tsaye suka zubama juna ido.
Shatima ya yi ta maza ya ce, “Aliya dama kina nan ba kiyi aure ba?” Ta sauke ajiyar zusiya, sannan ta sunkuyar da kai
“Ina yini?” Ta gaida shi. “Lafiya lau.” Ya amsa.
Kaka ta ce. “A tsaye za ku gaisa?” Ya kalli Kaka, sannan ya kalli Aliya. “Zo mu zauna can kujerar kada Kaka taji abin
da zamu fada.” Aliya taja mayafinta ta rufe gefen
fuskarta alamun kunya, zuciyarta kuwa fal murna.
Gani take yi ma kamar ba gaske ba ne, wai
Shatimanta ne a gabanta. Sai da suka zauna ta sake gaida shi. Ya ce, “Ya ya ki ka ji da ki ka ganni?” Ta ce, “Har yanzun bangama yarda cewa ba mafarki nake yi ba.”
Yayi murmushi, “Ni mamakina ashe ba kiyi auran ba?” Ta ce, “Duk wanda suke son in aura ni kuma bana sonsu, sai wan Babanmu na Katsina ya ce su bar ni in zabi miji da kaina.To sai Yayanmu Aliyu ya kawo min form din School of Nursing, shi ne ma na maida hankalina a kan karatu.Ya ce, “Yanzun kin gama kenan?” Ta ce, “Eh,
har na gama Practical dina, kuma na fara aiki a
wani asibitin kudi da ke nan unguwar.
Ya ce, “Shekarunmu nawa da rabuwa ne har da ki ka yi karatu ki ka gama?” Ta ce, “Shekaru uku fa da watanni kenan.”.
“Hmm! Haka ne. Za ki iya tuna rabuwarmu ta
karshe?” Ta daga kai kamar mai son tayi tunani. Ta ce, “Mun rabu ne wata ranar Asabar wadda ba zan taɓa mancewa da ita ba.Mun rabu kafin Asabar din a kan magabatanka
zasu zo, amma maimakon haka sai na ganka da
labarin wai Mahaifanka sun ce za ka tafi Dubai don kayo Degree na biyu. Ta lumshe ido kafin ta ci gaba da magana. “Ba zan iya misalta bakin cikin da na tsinci kaina a wannan ranar ba, domin a cikin gida ina fuskantar
matsin lamba a kan in fitar da mijin aure. Na ce to, ka sa a zo a fadawa iyayena ko za su amince in jira ka. Washegari Lahadi ku ka zo kai da abokinka Munnir don neman yardar iyayena su bar ni in jira ka dawo, sai Mahaifana suka ce sam! Ba zan jira ka ba, aure za su yi min.” Ta sake yin shiru tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ta kalle shi. “Haka ne?” Ya ce, “Ashe dai
ba ki manta ba. Ni Yayanku Aliyu ma ce min yayi
dama wani abokinsa yana sonki, shi yasa na yanke
hukunci cewa yanzun kin yi ‘ya’ya biyu.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tayi ‘yar dariya, “Duk sun zo na ce ban son Ya ce, “Ashe rabona ce, amma kina da su. kishiyoyi fa!”
Ta zaro ido, sannan ta dube shi “Kayi aure ne?”
Ya ce “Rana daya za a sa ku a lalle.” Ta ce, “Nasan kana zolayata ne.” “Zancen gaskiya kenan Aliya, ku uku ne. Bayan na tafi Makaranta cike da bakin cikin
rabuwa da ke, sai Allah Ya hadamu da Amna, ‘yar
asalin jihar Kano ce, tana da dangantaka da
Masarautar Kano., Babanta mai kudi ne sosai.
Amna ta birge ni da halayanta na kamun kai, da nutsuwa, haka yasa wasu dalibai ke surutun tana da girman kai. Gidan da take kusa da namu ne mu kan hadu lokuta da dama in Makaranta, ko in mun je sallah. zamu shiga
Ni dai tana birge ni, kuma ina son mu ke magana. Sai wata rana nayi mata sallama ta amsa muka gaisa, na ce ita ‘yar Nijeriya ce a wacce jihar? Ta ce Kuno. Tun daga lokacin muka soma magana har
soyayya ta shiga tsakaninmu, sai ma na gane son
da take min ko kwatanshi bana yi mata. Har mun
shirya batun aure da ita.
Kasancewar zan rigata dawowa sai muka shirya zan jirata. Na rasa sadarwa tsakaninmu da ita sakamakon wayoyina da Laptop da barayi suka sace. Yau din nan ta kira ni ta ke sanar min dawowarta kasar.”
Aliya ta danne kishinta ta ce, “To ka ce mu uku ne dayar fa?” Ya ce, “Nafisa jikar Kaka ce, ina ce kin santa ma?”
Aliya ta ce “Dama kuna soyayya da Nafisa ne? nasan ta mana.” Ya ce, “Kafin in dawo iyaye suka kulla, yanzun su ba su san ma da batun Amna ba bare naki. Yanzu dai za mu gyarota da Kaka, saboda in ta yarda dole Baba ya yarda, shi kuma in ya cije dole Hajiya ta saki.”
Aliya ta ce, “Tab!” Ya ce “Ba za ki iya ba ko?” Ta ce “A’a in ana auren mata dari Shatima ka aura ba zan ki ba, na dai tausaya maka ne.” “In kuma na samu ta hudu sai in cike kawai.”
Ya fada cik zolaya. Aliya ta ce, “Ni dai yanzun
ka fada min wa ka fi so?””Wadda ta fi sona.” Ya bata amsa a takaice tare da mikewa. “Bari in tafi ko, amma kafin nan ki tashi kije gida zamu yi magana da Kaka.” Ya mika mata wayarshi karama.”Sa min lambarki, ki ajiye da sunan da ki ka ga
ya dace.” Ta saka lambar tayi shiru tana tunanin
sunan da zai dace.
Ya ce, “Ki zabi duk sunan da ki ka sa shi ne sunanki a bakina.” Cikin sauri ta rubuta (My Love) ta mika mishi. Ya amsa ya kalleta.My love?”
Tasa hannu ta rufe fuska cikin jin kunya. Ya ce, “Zan kira ki da wannan sunan a gaban kowa ma, kuma ina son ke ma ki kira ni da shi a gaban kowa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya nuna mata hanya da hannunshi, “Je ki
sallami Kaka.” Ta tsugunna a gaban Kaka ta ce,
“Zan tafi gida.” Kaka ta ce, “Har kun gama hirar?
To Allah Ya tabbatar muku da alkairi.” Har bakin falo ya rakata, sannan ya dawo gurin Kaka. Ya ce, “Kin ga abin Allah ko Kaka!”
Ta ce, “Ai ni na zaci ita ce ta biyun.” Nan ya bata labarin Amna. Ya ce, “Goyon bayankı kawai ni ke nema.” Ta ce, “Shatima nemi komai gurin Allah. ni ai in hudu za ka yi ina murna, don bana son ragon namiji.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG