RANA DAYA CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Ya nuna mata hanya da hannunshi, “Je ki
sallami Kaka.” Ta tsugunna a gaban Kaka ta ce,
“Zan tafi gida.” Kaka ta ce, “Har kun gama hirar?
To Allah Ya tabbatar muku da alkairi.” Har bakin falo ya rakata, sannan ya dawo gurin Kaka. Ya ce, “Kin ga abin Allah ko Kaka!”
Ta ce, “Ai ni na zaci ita ce ta biyun.” Nan ya bata labarin Amna. Ya ce, “Goyon bayankı kawai ni ke nema.” Ta ce, “Shatima nemi komai gurin Allah. ni ai in hudu za ka yi ina murna, don bana son ragon namiji.

Shatima mai sunanka gwarzo ne, mu hudu ya aje, ba dai rana daya ba. Amma tsakaninmu babu nisa. Duk ciki ni ce kararmu, yau ina abokan zaman nawa? Ina shi Maigidan namu? Duk sun amsa kiran Ubangijinmu.
Mun zauna da dadi-ba-dadi, kuma an yi zaman mutunci, kullum ina yi musu addu’ar samun rahamar Allah, kuma. Allah Yasa tawa tayi kyau irin tasu. The de jah manch slara ar Tilb 2
Ya ce, “Amin Kaka.” Ta ci gaba da fadin, “Mata hudu ba matsala ba ne matsalar tana tasowa ne daga gurin namiji in ya kasa adalci a gidansa.”
Ya ce, “Kaka ni ai renonki ne ko? In sha Allah zan yi ba zata.” Ta ce, “In dai sunanka Muhammad Ja’afar, kuma ka amsa lakabin ka na Shatima, to kuwa nasan kai gwarzo ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng

*******
Tun da aka soma yi wa Malam Adamu gashin kashi sai jikin ya soma sauki. Dubu ishirin da suka samu a gurin Alhajin nan ta taimaka musu sosai.
Ummu Salma ta sauka daga cikin Adaidaita dauke da kwanukan samira tuwo da miya. Ta shiga cikin asıbitin da hanzarinta don kaiwa Mahaifanta tuwon da ta yo bayan ta gama suyar Wara, ta samu riba tayo cefane ta girko.


Tana taka matakalar da zata hau sama in da dakin maza yake, sai ko kafarta ta zame, takalmin kafarta silifa mai soso ya taimaka gurin zamar da
ita har ta kai kasa.
Ba damuwarta faduwar da zata yi ba, damuwarta kawai kar abincin Mahaifanta ya zube. Sai dai ta makaro, domin tuni abincin ya tarwatse a kan siminti.
Wata ma aikaciyar gurin ta soma yi wa Salma fada. “Ke da Allah can! Kin zo kin bata wa mutane guri da wannan kazamin tuwon naku, da Allah zo ki share shi.”
Ta mike tana kukan bakin cikin asarar abincin
iyayenta. Daidai lokacin da wata mai sharar asibiti
ta iso. Wannan ma’aikaciyar tana ci gaba da yi wa
Salma sababi. Mai sharar ta ce, “Irin kazantar da ku ke yi a gidanku shi ne kin zo kina yi mana a nan guri din?” Ta tambayi Salma cikin hausarta mara dadi.
Salma dai sai kallon su take yi. Ma’aikaciyar ta ce, “Ba za ki kwashe mana warman kazantar a nan gurin ba? kalli wai wannan ne abincin da za’a ba mara lafiya. Ta ya ya zai warke yana cin irin wannan kazanta?”Cikin mutanen da suka taru a gurin suna kallo sai wata daga ciki ta ce, “Gaskiya bai kamata ku saka yarinya karama a gaba kuna mata ihu ba, ita ma ai ba za ta so ba tayi asarar abincin da Allah ne kadai yasan yanda suka samo shi Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan suka dawo kan matar, hayaniya ta soma yin sama. Tasa hannu zata dauki tuwo, sai ta ji an ce”Bari kar ki taba.” Tana dagowa sai taga Alhajin nan shi da wani a cikin jerin mutanan da suka taru a gurin.
Ya ce, “Ina ma su yin sharar asibitin?” Matar ta ce, “Mu ne muke shara, amma ita ne ta kwashe wannan din da ta zubar.”
Ya ce, “Zo ki wuce, ku ku bar shi in ba za ku
kwashe ba.” har ta nufi sama ya ce, “Zo nan.” Ta
nufo gurinshi, ya ce “Bimu daina kukan.” Ta ce,”To.”
Tasa kasan hijabinta tana share hawaye. Ya ce.. “Kin gane ni kuwa?” Bayan sun je gurin mota. Ta ce, “Eh, na gane ka. Kai ne wanda ka taimake mu shekaranjiya.”
Ya ce. “Sunana fa?” Ta sake kallonshi, sannan ta girgiza kai “Ban san sunanka ba.” Yayi murmushi, sannan ya ciro kudi a aljihunshi ya nuna mata wata hanya.”Ki bi nan ki dan mike za ki ga shagunan saida abinci, su wanke miki kwanukan sai ki sai musu abinci.”
Hannu biyu tasa ta amshi kudin, tana ta godiya. Shima abokin yana cikin mota lokacin, ya ciro dubu daya ya ce, “Kara mata.”
Salma tayi godiya, sannan ta mike hanyar da ya
nuna mata cikin murna tana kirga kudin, dubu
hudu ne cas! Duk da dubun abokin.
Sakwara ta sai musu da miyar agushi, ta sai musu lemon roba da ruwan sanyi. Tana isa Innarsu ta idar da sallar La’asar. Ta ce, “Yau ba kasuwa ne hala muka ji ki shiru
Ummu Salma?” Ta ce, “Ai nazo tun dazu ɓarewa
ya yi. Nan ta basu labarin komai, sannan ta kawo
sauran kudin ta ba Innarsu. Inna ta ce, “Ba na amsa duka ba Salma, bani dai dubu guda sai ki rike dubu biyun, ke da ki ke dawainiya da mu. Shi kuma Allah Ya shi masa albarka, ya saka mishi da alheri, ya biya masa bukatunsa shima.” Salma ta ce, “Amin Inna.
Sai bayan Isha’i sannan Innarsu ta ce, “Maza ki zo Salma ki wuce dare yana yi.” Ta ce, “To Innarmu, bari in zo in je.”
A bakin titi tana jiran mota, wata ma’aikaciyar jinya ta fito itama tana jiran mota. Salma ta dube ta cikin faduwar gaba, don tana zaton matar dazu ce da ta yi mata cin mutunci.
Ta saci kallon matar duk da akwai duhu ta gane ba fuskar waccan ba ce. Dan Adaidaita ya zo wucewa, tare suka hada baki gurin fadin. “Tudun Wada.”
Ya tsaya ya dauke su, ma’aikaciyar ta ce, “Ashe unguwa daya za mu?” Salma ta ce, “Eh, nan za ni.” Ta sake cewa, “Kin zo duba mara lafiya ne?”
Salma ta ce, “Eh, Babana aka kwantar.”
Ma’aikaciyar ta ce, “Allah Ya ba shi lafiya.”
Salma ta ce, “Amin.” A zuciyarta ta ce, ‘Ashe dai
ba duka Nurses din nan ba ne suke da wulakanci, da ko har na tsane su.” Alhaji Isa Shatima yana zaune a falonsa da
misalin karfe tara da rabi, labaran kasa suke kallo
tare da matarsa Hajiya Halima. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dukkansu Tea suke sha wanda suka maida shi al’adarsu duk dare Daidai wannan lokacin ya kalli wani daurin auran da aka gama nunawa na ‘yar. wani Minister daga cikin Ministoci.
Ya ce, “Au! Hajiya Halima har na tuna.” Ta ce, “Ka tuna me?” Ya ce, “Da na je duba Hajiya yau da safe take fada min wata magana da na kasa ce mata komai.” Ta maido da hankalinta kanshi sosai. “Meta ce?” Ya ce, “Shatima wai mata uku zai aura…”
Kofin hannunta ya kusan faduwa, sannan ta kware da ruwan zafin da ta kurba. Dan tari ta shiga yi har ta yi zaton asmarta ce zata tashi, sai sannu Alhaji ya ke yi mata.
Kusan minti biyar sannan ta dawo hayyacinta. Idanunta jajir ta ce, “Amma dai wasa ya ke yi ko?” Alhajin ya ce, “Babu alamun wasa a fuskar Hajiya lokacin da take yin maganar.”
Hajiya ta ce, “Hmm! Wannan hira ce ya ke yi. Ban da Shatima ina zai kai mata uku?” Ya ce, “Na fadi hakan sai Hajiya ta min gorin da na gwammace ban yi magana ba sannan ta saki zancen alamun an wuce gurin.
Hajiya Halima tayi shiru tana tunani. Badi’a ta shigo falon zata dauki takardarta wadda tayi home work da rana. Hajiyar ta ce, “Badi’a zo nan, kira min Yayanku a samansa.
Kammala aikinsa ke da wuya ya rufe Laptop din yana hamma, ya sani ba bacci ba ne yunwa ce ke damunsa, don bai ci komai da rana ba.Ya ji an kwankwasa kofa. Ya ce, “Shigo.” Tayi sallama ya amsa, ta ce “Hajiya tana kiranka Yaya.” Ya ce, “To ina zuwa Badi’atu.”
Gabansu ya zauna ya gaishe su, sannan ya ce, “Gani Hajiya.” Ta gyara zama ta hanyar dora kafarta daya a kan daya, duk lokacin da tayi hakan ya san umarni zata ba da na dole, don haka sai ya sake nutsuwa don jin abin da zata zo da shi.
Koda yake tuni ya soma hasashen abin da zata yi magana a kai, zancen auransu da Nafisa…
Ta katse tunanin shi da cewa, “Yanzun Mahaifinku ya ke bani labarin wai za ka auri mata uku rana daya?”
Ya sunkuyar da kai cikin mamakin har zancen
ya riske su da sauri haka! Yana tunanin lallai da
gaggawa lamuran za su ke zuwa masa. Ta ce. “Kayi shiru Shatima?” Ya sake sunkuyar da kai. Ya ce, “Haka ne Hajiya.” Ta ce, “Amma ka fita a tunaninka ko? Ya ya za ka yi da mata uku rana daya? Yaron ka da kai Shatima za ka dora ma kanka matsalar iyali da yawa furfura ta fito maka ko? To ka sani ban amince ba sam-sam!”
ya dan gyara zama. “Hajiya duk al’amarin ya zo ne ba da shirina ba, sai da shirin Ubangiji. Kuma Hajiya shekaruna talatin da shida, ai ko na girmi yaro.Sannan addinina bai hana ni ba, Allah a cikin Alkur’ani mai tsarki ya fada mana cewa, mu auri mata biyu, ko uku, ko hudu. In ba za mu iya adalci ba sai mu auri daya.
To ni kuma ina da tabbacin zan iya adalci, don ina alfahari da irin tarbiyyar da ki ka bani, adalcin da ki ka tsaya a kai ki ke yi ma kowa da shi muka dogara.
Kuma shi ni ke kwatantawa a ko’ina, da shi
kuma zan zauna da mata ko nawa ne. Ina son ki sa albarka a cikin wannan auran, albarkarki ita ce ginshiki Hajiya.” Ta ce, “Ai kai Shatima ko dan siyasa ya fi ka iya zance kuwa? Ni dai kaje kayi tunani a kai, rike Www.bankinhausanovels.com.ng
mace ko guda daya ce sai jan namiji. Amma kai ka
ce rana daya guda uku!” Ya ce, “Hajiya ki sa albarka.” Ta ce, “Yanzu dai ba zan saka ba, in kana son in saka sai dai ka duba a cikin ukun ka dauki guda daya, ka zaɓa in ma ba Nafisar ba ce dai wadda kafi so.
Don ka san an ce so daya ne tak! Kuma mace daya ka ke wa a cikin ukun, don haka sai ka cire ta.”
Ya kalli Mahaifin nashi wanda bai ce kala ba tun da suka soma magana. Ya ce, “Alhaji ba ka ce komai ba?” Ya ce, “Ba ni da ta cewa Shatima, duk abin da yafi alkhairi Allah Ya zaba, tunda ka samu daurin gindin Tsohuwa a ta gefena ka kai makura.
Shatima ya yi murmushin nasara a ta wannan gefen. Hajiyar ta ce, “Ka je kayi tunani nan da jibi.” Shatima ya mike cikin rangaji tare da fadin “Badi atu ta kawo min abinci Hajiya.”

**
Tunda Kaka taji sallama tare da kamshin kalolin abinci ta tabbatar cewa Hajiya Halima ta diro gidan, domin wannan ita ce shaidar farko da take fara alamta mata cewa Surukar arziki ta shigo gidan.
Ta fito daga cikin dakinta tana dogara ‘yar sandarta mai kyau, wadda ta ke taimaka ma kafafunta wadanda suka yi rauni.
Ta amsa sallamar cikin murna, ta zo ta zauna kan kujera. Hajiya Halima ta zauna kasa kan kafet. Badi’a da Maryama suka shiga jere kulolin da Hajiya Halimar ta zo da su.
Suka sake fita suka shigo da sauran. Kaka ta ce, “Ba ki gajiya Hajiya Halima, kowane lokacin in za’a zo duba ni sai an zo min da abin tabawa. Allah Ubangiji yasa ke ma ‘ya’yanki suyi miki. Ga jarumin namiji nan Shatima, cikin matansa Allah zai sa wata ta miki fiye da abin da ki ke min.
Hajiya Halima tayi murmushi bata amsa ba don nuna kara ga uwar mijin tata.
Bayan sun gaisa ne suka shiga hirar duniya, Badi’atu autar Hajiya Halima, da Maryam yar gidan Hajiya Saude kanwar Baban su Shatima wadda ke gaban Kaka, sun kule a daki suna tasu hirar.
Hajiya Halima ta kalli Kaka ta ce, “Hajiya sai kuma wannan mashirmancin ya zo da zancen zai auri mata uku rana daya, wannan ai labari yake yi. Dubi masu mace daya ma yanda suke fama a wannan zamani, ni dai na ce masa a’a ya dai zabi
daya, in ma karin ne sai ya bari ya ga kamun Www.bankinhausanovels.com.ng
ludayin zaman, in yaso can gaba ya kara.” Kaka dai ba ta ce kala ba, har Hajiya Halima ta kai karshe. Kaka ta ce, “Zubo min abin da ki ka zo da shi in lasa ko nafi samun abin fadi.”
Dariya suka yi su duka sannan ta ce, “Farfesun kajin zan zubo miki, ko na kafar Sa? Sannan akwai kus-kus, ga kuma faten acca.” Kaka ta ce, “To fa! Duk a cikina? To zubo min
faten sai ki sa farfesun kafar Sa din a ciki.”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE