RANA DAYA CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 4 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Mun tsaya
wannan mashirmancin ya zo da zancen zai auri mata uku rana daya, wannan ai labari yake yi. Dubi masu mace daya ma yanda suke fama a wannan zamani, ni dai na ce masa a’a ya dai zabi
daya, in ma karin ne sai ya bari ya ga kamun Www.bankinhausanovels.com.ng
ludayin zaman, in yaso can gaba ya kara.” Kaka dai ba ta ce kala ba, har Hajiya Halima ta kai karshe. Kaka ta ce, “Zubo min abin da ki ka zo da shi in lasa ko nafi samun abin fadi.”
Dariya suka yi su duka sannan ta ce, “Farfesun kajin zan zubo miki, ko na kafar Sa? Sannan akwai kus-kus, ga kuma faten acca.” Kaka ta ce, “To fa! Duk a cikina? To zubo min
faten sai ki sa farfesun kafar Sa din a ciki.”
zubo mata ta bata sannan ta kwala ma Badi’atu kira, suka fito. Ta ce, “Ku je ku kawo ma Hajiya ruwa, sannan
ku zo ku kwashe kulolin nan zuwa kicin.” Suka ce, “To.”
Sai da Kaka tayi nak! Ta koshi, sannan ta kalli Hajiya Halima.
“Zancen Shatima, ina son ki cire rashin yardarki da kin amincewarki, ki aje su a gefe. Ki bi da ido, sannan ki hada da addu’a.
Shatima gwarzo ne ba irin mazanku ba, mutum ya zauna da mace daya kamar fasto.” Ta gyara zama sannan ta ci gaba, “Yanzu bari in yi miki wani lissafi, mata nawa Maigidanmu ya aura? Nasan kin samu labari mu hudu ne ko?”
Hajiya Halima ta daga kai alamun “Eh.” Ta ci gaba da cewa, “Kowace mace ta haifi ‘ya’ya da yawa, babbarmu tana da goma sha daya, mai bin ta na da takwas, wadda ni ke bi tana da goma, cikinmu ni ce kadai me ‘ya’ya hudu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Babbanṣu ya kwanta ya mutu shekara biyu kenan, matarsa na nan a Kaduna da ‘ya’ya biyar. Ke naki mijin ‘ya’yanku uku daga shi Shatima sai Mustapha, sai ko Badi’atu, sai dan uwansa Baban Nafisa.
Suma su uku ‘ya’yansu duka mata, Nafisa da
kannenta biyu. Saude ce ma me ‘ya’ya shida har
na samu aka bani Maryama. Tattara ki kirga min
jikokin nawa duk guda nawa ne?
Ta dafa kirjinta tare da fadin “Ni fa nan da ki
ka ganni yanda Allah Ya halicce ni ina son zuri’a,
naso a ce cikin ‘ya’ya mazan nan guda uku da
Allah Ya bani naso in samu wanda zai gaji
Babansu a ‘ya’ya, don sai da ya bar talatin da
uku a duniya.
Kuma Alhamdulillahi kin dai san komai ba sai
na fada miki ba, cikin ‘ya’yan nan babu mai irin
mukamin da babu. Akwai Soja, akwai Dansanda,
ga yan kasuwa, ga Malamai na duka bangare
biyun boko da Islamiya.
Ga Sarakuna duk da dai wannan gado ne, don
haka ina son ki bi Shatima da addu’a don ina ga
shi ne zai zama magajin Kakanshi, dama sunansu
daya. Ina so ki sa masa albarka a cikin duk
lamuranki.”
Ba ta da zabin da ya wuce mika wuya don
tasan ma babu wani abu da zata fada har ya yi
tasiri. Don haka ta ce “To Hajiya, Allah Ya shi
albarka, ya zaba abin da yafi zama alkairi.
Kaka ta ce, “Yauwa hali dubu rubutun dutse,
dama ni nasan ke komai naki cikin sauki ne da
fahimta, Allah Yayi miki albarka.
Hajiya Halima ta ce, “Amin. To amma Hajiya
an bincika sauran da ya ke son an ji ya’yan asali
ne ko? Ta ce, “Ke dai ki kwantar da hankalinki,
komai na jan namiji daban ne, burinmu dai ki bishi da
addu a.Nafisa tana zaune a cikin lambun gidansu kan
kujera irin mai lilon nan, sanyi da kamshin lambun
yana kara ma zuciyarta nishadi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta lumshe ido tana kallon surar Shatima a
idonta, cikin shiga ta kasaita da kamshi. Gaskiya
tana matukar son Shatima har ma ba za ta iya
misalta son ba.
Tasa hannu ta dauki wayarta da ke kan cinyarta
ta bankado hotonsa wanda tasa Badi’atu ta turo
mata. Zuciyarta tana dadi in ta kalli fuskarshi.
Lallai za ta tura mishi sakon gaisuwar Juma’a
yanzun nan tun da yau take babbar rana. Message
ta shiga ta soma tura masa sako kamar haka:
Ya Allah Ya tsareka, Allah Ya tsare gabanka
da bayanka, ya daukaki rayuwarka. Ya sa ka
Cimma duk abin da ka ke nema.
Allah tsare idonka, da kunnenka, da ji da ganin
haram. Allah Yasa Aljanna ce makomarka.
Barka da Juma ‘a.
Ta karanta ya kai sau goma kafin ta runtse ido,
gabanta kuma yana faduwa ta tura masa.
A fili ta ce, “Allah kasa kar in yi da na sanin
tura sakon nan. Abin da ya bata mamaki kuma
bata yi tsammani ba shi ne, jin karar sako ya shigo
wayarta.
Bata ba tunaninta wahala ba, kawai ta yanke
hukunci cewa sakon daga shi ne Cikin nutsuwa ta
duba ga abin da ya ce:
Zan shigo misalin karfe biyar ni da Aminina,
zan kasance cikin farin ciki in na same ki a gida.
Sannan abincin gidan Babana shi ne zai zama
abincin rana na a yau.
Ki húta lafiya.
Tayi ta maimaita karanta rubutun. Ta dai
fahimci yana nufin zai zo yau shi da abokinshi,
amma ba ta gane batun cin abinci ba. Ta ce a fili,
Bari in je gun Mama tayi min fassara.”
Uwar ta gama karanta sakon sannan ta saki
murmushi.
To in ba ki gane ba yau a nan gidan zai ci
abincin rana, nan ba gidan Babanshi ba ne? Nafisa ta ce, Har nayi tunanin haka, sai kuma
na ce kila in yaci abincin rana a gidansu sannan
zai zo. To Mama yanzun me za’ayi masa kenan?
Ta ce, Ki binciko irin abincin da ya fi so mana
koda gurin Badi’atu ne.” Da sauri ta dauki wayarta
ta nufi dakinta. Badi’atu ta kira tana tambayarta
irin abincin da Yaya Shatima yafi so. Kusan duk
abincin gargajiya yana so, amma babu kamar
burabisko.
Sosai tayi kwalliya ta fesa kalolin turaruka, ta
kame tana yawaita kallon agogo. Tsinken agogon
ya sauka kan digon da ke nunas biyar daidai,
kararrawar kofar falo tana bugawa.
Cikin dakinta ta shige da sauri kar ya soma
karo da kwalliyarta, ba birgewa ba ne. Hamida ta
ce, Yaya Nafisa in ba su ba nefa ki ka boye?
Ta ce, “Ke dai kije ki gani. Kunnenta na gurin
taji Hamida na fadin “Sannun ku da zuwa. Sai da
Suka gaisa da Mama sannan ta ce Hamida ta kai su
lambu inda aka yi musu shimfida. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Mami zo ki cema Yayarku ga su
Yayanku sun iso, sai ki je ki taimaka ma Hamida
ku kai musu abinci.Cikin shadda doguwar riga mai ruwan goro ta nufi inda aka sauki bakinta. Tayi musu sallama
suka amsa, ita da shi suka kalli juna cikin ido. Tayi
murmushi tare da jan dan mayafinta ta rufe
fuskarta alamun kunya Sannan ta zauna a kusa da dayan tuntun wanda
ba a jingina da shi ba. tuntu uku aka saka a kan
kafet din da aka shimfida. Cikin girmamawa ta gaishe su. Ya ce, “Sunana
Muhammad Jafar Isa, lakabina Shatima. Wannan
abokina ne sunanshi Munnir Khamis, dukkanmu
muna aiki ne a karkashin Gwamnati. Nazo gurinki
ne don ina son ki zama daya daga cikin matana. Da sauri ta dago ta dube shi, suka hada ido ya
sakar mata murmushi. Bakinki da magana amma ki fara gabatar
mana da kanki tukunna. Cikin’ son taja ra’ayinsa
da muryarta ta ce, “Sunana Nafisa Musa Shátima
kuma ni daliba ce a Jami ar Ahmadu Bello da ke
nan Zariya.Ina cikin shekarata ta biyu. Sai dai abin da ban
fahimta ba shi ne, ka ce zan zama daya daga cikin
matanka, shin kana da wasu matan ne ko ko ya ya
abin yake?
Sallamar su Hamida ce ta sa shi yin shiru. Suka
Aje kuloli da kofuna. Hamida ta dauki plate biyu
ta soma zuba musu burabisko.
Yace, Kanwata sa plate daya wa abokina, ni
matata ce zata sa min in gani ko ta san cikin
mijinta.
Nafisa ta amsa ta zuba mishi komai ta jere a
gabanshi. Bayan tafiyar su Hamida ne, Shatima
suka soma cin abinci.
Matso ki ci tare da ni. Ya fada cikin
murmushi. Ta ce, “Ni naci tun lokacin da aka
gama. Ya ce, “Ba ke ki ka girka ba ke nan? Ta
ce, “Ni nayi, bai yi dadi ba ko?
Ya ce, Bari in gama tunda babu kyau magana
in ana cin abinci.” Ta dafa hannuwanta “Bari in
tashi ku gama. Ya ce, “A’a zauna ina son ina cin
abinci ina kallonki.” Ta zauna tare da jan mayafi ta
dan rufe gefen fuska.
Sai da suka gama ci da sha, sannan suka koma
hira.
Ya ce. Meki ka ce dazu? ta ce, “Batun
matanka da ka ce zan zama daya daga ciki.” Ya
ce, “Eh gaskiya ke ce ta uku.
Ta zata zolayarta yake yi, don haka bata ji
Komai ba sai ma ta ce, Ban san lokacin da ka auri
Biyun ba, ko kuma mu ne ba a gayyata ba.
Ai rana daya za’a daura da naki, kuma ina
zaton ma hudu za’a daura duk da ban san wace ce
dayar ba.”
Ta ce, “Zan fi son mu aje batun wasa, ni da kai
muyi zance na gaskiya.” Ya ce, Ai ke ce ki ke
ganin wasa ne, amma babu wasa cikin zancena.
Fuskar Nafisa ta canza launi daga fara’a zuwa
kalar damuwa, shi kan shi ya lura da haka amma
bai bi ta kan haka ba, sai ma ya mika mata
karamar wayarsa.
Ban yi saving din lambar ki ba da na amsa a
hannun Badi’atu, ki saka sunan da ya dace, don da
shi zan kira ki a gaban kowa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta amsa ta saka tayi sav ing da (Sweety). Ya
kalla sannan ya dube ta. “Sweety! Har a gaban
Mama da Hajiya, da Kaka, da su Baba?
Tayi dan murmushi “Eh. Ya ce “To kema
hakan za ki kira ni.
Sun dauki lokaci suna dan tattaunawa, kafin a
kira Magriba. Suka mike da zummar tafiya. Ya aje
mata kudi ‘yan dubu dai-dai guda goma.
Ki sai omo ki wanke kwanuka, abinci ya yi
dadi.” Ta dube shi, “Haba dai, ka bar shi kawai.”
Ya ce, “Ai ba ki tambaye ni ba. Tayi musu rakiya
har gurin mota.
Bayan tafiyar su tazo a rude gurin Mama. Ta
ce, “Mama Yaya Shatima ya yi min wata magana
da ta sa naji komai na duniya ya ishe ni, wai mu
uku zai aura rana daya!
Mama tayi ‘yar dariya, “Ina ga ba ki san
tsokana ba ko? Wasa ya ke miki.” Hawaye suka
soma zubowa daga idanunta.
“Wallahi Mama babu alamun wasa a tare da shi
sam-sam! Ta ce, “To bari Babanku ya shigo mu
Ji, in dai zai auri wasu ai shi ne waliyyin shi.
Yana Yana daga kwance ya kalli agogon wayarshi,
sha daya ta gota. Ya danna lambar Amna, sai da
tayi ruri ta katsee. Yayi murmushi, ya san kadan
daga cikin jan ajin Amna.
Ya sake kira, can ta daga muryarta can kasa ta
ce, “Hello!” Ya ce, “Ba ki yi bacci ba Amna?” Ta
cc, “Eh, ban yi ba tukunna, sai yau ka ke kirana?
“Kiyi hakuri zan shigo gobe.”
Ta ce, “Sai kuma ka daga zuwan, don gobe
duka gidan ba mu nan.” Ya ce, To fa? Ina za ku
haka har da ba za ku amshi bakuncina ba?”
“Ni dai Umra zamu je da Mom, da Dad sai
Sisters dina guda biyu. Amaryar Dad da sauran
yara za su je (London) hutu.
Ya sauke ajiyar zuciya, “Sai yaushe za. ku
dawo? Ta ce, “Sati biyu zamu yi, ba dadewa
zamu yi ba.” Ya ce, “Shi kenan. Don Allah ki sani
cikin addu’arki.”
Insha Allahu, amma dai zamu yi waya in mun
sauka ko?
Dole na, ina son wannan muryar taki sosai
Amna. Ya fada cikin murmushi.
Muryata kawai ka ke so ban da ni?
Ke ma kin san fada bata baki, ina matukar
sonki.
Nima ina sonka da yawa, sai dai ina ja baya ne
don ina ganin kamar ba ka damu da ni ba.
Ya ce, Me yasa ki ke ganin kamar ban damu
da ke ba?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tayi yar dariya tare da sake matse wayar a
kunncnta don dadin hira da shi. Ta ce Tun ranar
da na kira ka ka ce zaka kira ni in ka samu sukuni,
sai yau ka samu sukuni din?
Ya canza kunne da ya manna wayar zuwa
dayan kunnen don ya ji SOsai, saboda Amna bata
magana da karfi ko. kuma ba ta
son hayaniya. Wannan tsarin nata yana matukar
birge Shatima.
Ya ce, “Ba za ki gane ba, amma lokaci ya kusa
da zamu zama tare. Ta ce, “Wane lokaci kenan?
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG