RANA DAYA CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 6 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Mun tsaya
kullum, don da ina tunanin duk su zauna nan Zariya, ni kuma ina Kaduna sai su ke zuwa.”
Kaka ta ce, “Hakan shi ne daidai.” Ya ce, “Kaka a taya ni godiya gurin Alhaji, sannan a nema min alfarma, a rubuta takarda na yarda zan ba da cikon amma sai nan gaba, don kudin hannuna zan tada ginin da su.”
Ya ce, “Wannan hutun na karshen mako sai muje kaga gurin.” Ya ce, “Allah Ya kara girma da lafiya Alhaji, Allah Ya jikan Mahaifinku, ya raba ku lafiya da Kaka.” Suka ce “Amin.”
Nan suka ci gaba da tattauna al’amuran da suka shafe su.
Ya idar da Nafilfilinsa na dare ya zauna yana istigfari, sai ya tuna wannan lokacin a Saudiya tamkar rana ce, zai iya yin magana da Amna. Ya tashi ya ciro wayarsa a chaji ya kunna yana neman lambar da Amna ta kira shi shekaran jiya.
Ya kira sau biyu bata daga ba, ya mata uzuri kila bacci take yi tunda ba kowa ne ya saba da zama har wannan lokacin ba.
Ya sake kira kashi na uku, sai gashi ta daga cikin mayen bacci. Ta ce, “Hello honey!” Ya dan zaro ido, don bata taba kiranshi da wannan sunan ba, ta kan dai ce mishi ‘Dear’.
Ya ce, “Honey kiyi hakuri na tashe ki a bacci ko?” Ta ce, “Ba komai, ya ka ke?” Ya ce, “Ina lafiya. Kina yi mana addu’a kuwa ki ke bacci?” Ta ce, “Ina yi mana.” Ya ce, “Wace iri ki ke
min?” Ta ce, “Ta kara karfin soyayya har gidan
Aljanna.” Ya ce, “Kin kyauta, amma ina son kiyi min wata tawa ta musamman. “Kamar wacce ke nan?” Ta tambaye shi.
“Ki min addu’a in kin dawo duk abin da na zo miki da shi za ki amshe shi.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ban gane ba?” Ta fada da sauri.”Za ki gane in kin dawo, ni dai ina son ki daga hannu ki ce Ya Allah Kasa duk abin da Muhammad Ja’afar ya zo min da shi in amshe shi. Tayi dariya, “In ka zo da abin da ya sha kan tunanina fa?”
“Ba zai sha ba in sha Allah.””Nayi alkawarin zan yi maka.” Ya ce, “Na gode. Yaushe za ki dawo? Na kosa
in gan ki.”Saura kwana biyar mu dawo.””To ni in zo yaushe?” Ya tambayeta.”Ban da ranar da muka dawo, amma ka iya zuwa koyaushe.” Ya ce, “To washegarin ranar zan zo.” Ta ce, “Na gode da kulawa, kaje kayi bacci.” Ya ce, “Ranki ya dade.” Tayi ‘yar dariya sukayi sallama.
Ta shiga kicin ta samu Mama tana girkin abincin rana, taje tá jingina da (Freezer) din da ke bayanta. Ta ce, “Mama da zan tafi Makaranta kin ce min za ku yi magana da Babanmu, wallahi ni fa yau ko a aji ban iya gane komai ba.
Ina son in san gaskiyar abin da Yaya Shatima ya fada, tun ranar da ya kira Baba Alhaji ya ce masa yaje gurin Kaka a can zai ji gaskiyar magana, to wai bai je ba ne?” Mama ta kalli yarta cikin tausayi, “Bari
Babanku ya dawo sai kuje gurin Kaka tare don kiji da kunnenki.”
Ta ce, “Amma dai zance mafi inganci shi ne mu ukun kenan?” Ta ce, “A’a, ni na fada miki ban san komai ba sam-sam!”
Ta ce, “Ai ko yau da dare zan je tare da Baba
din.” Ya zuba ido yana kallon gurin zaman Nafisa, “Ina me wannan kujerar?” Mama ta ce, “Tana dakinta tana kunci.” Ya
tsura ma Mama ido.Wane kunci kuma?”
Ta ce, “Zancan auransu da Shatima mana, bad na fada maka tace ya fada mata su uku ne rana daya ba, ka kira Alhaji ya ce maka kaje gurin Kaka ka ji cikakken zance.”
Ya aje cokalin hannunshi ya kurbi ruwa sannan ya mike. Dakin Nafisa ya nufa saboda duk cikin ‘ya’yansa babu kamar ta a zuciyarshi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kwance ya same ta tana wasa da rigar wayarta, amma ga dukkan alamu tunaninta ba ya tare da rigar wayar, hankalinta yana can wani gurin.Ya tsaya a gabanta, sannan ya maida hannuwansa baya. Ya ce, “Nafisa!” Ta dago ta dube shi. Ya ce, “Me yasa ba ki zo cin abinci ba?” Ta ce, “Na koshi Babanmu.” Ya ce, “Ina son ki fada min damuwarki.” Ta dago ta kalle shi.
“Babanmu ina son ka binciko min gaske ne Yaya Shatima mu uku zai aura rana daya?” Ya kalli ‘yarshi cikin tausayi, duk da kunya irin ta Nafisa amma sai da ta iya yi masa wannan magana. Ya ce, “Tashi muje gidan Hajiyar yanzun.
Cikin sauri ta saka hijabinta.
Kaka ta idar da sallar Isha’i tana jan carbi kafin tayi shafa’i da wutiri. Sallamar su ta jiyo, duk da bata san ko wane ne ba, ta raya a ranta ba za ta fito ba sai dai in na gida ne su shigo cikin dakin nata.
Maryama ta shigo ta ce, “Kaka ga Kawu Alhaji nan.” Ta ce, “Kamar murya biyu naji.” Ta ce, “Eh, shi da Nafisa ne.” Ta ce, “Su shigo ciki.”
Gabanta suka zauna suka gaisheta. Ta kalli Nafisa, “Dama kina nan?” Ta sunkuyar da kai. Kaka ta ci gaba da yuwa Nafisa fadan rashin son shiga jama’a, da rashin zumunci. Hakuri tayi ta baiwa Kaka.Alhaji Musa ya ce, “Hajiya kiyi hakuri, wannan halinta ne rashin son shiga mutane, kullum tana gida in dai ba Makaranta taje ba.”
Kaka ta ce “Ita dai ta sani, ga shi nan za ki yi aure da kishiyoyi, zama ne za ku yi na wanda ya iya allonsa ya wanke ya sha…”
Nafisa ta dafa kirji. “Dama gaske ne Kaka ba ni kadai Yaya Shatima zai aura ba?” Kaka ta ce, “Au! Dama bai fada miki ba?”
Nafisa ta soma kuka. Alhaji ya ce, “Hajiya bai kamata a bar Shatima yana dan karamin shi ya auri mace sama da daya ba, zai hada ma kanshi damuwar da zata sa shi yayi da na sani.”
Kaka ta ce, “Allah Ya raba shi da aikata da na sani, sunna fa zai yi, ibada ka ke fada min da na sani? Yanzun dai a takaice ka taso ‘yarka ne ka fada min cewa ya fasa auran ‘ya’yan wasu ya auri ‘yarka?”
Ya sunkuyar da kai, sannan ya shiga ba Hajiya hakuri don ba a son ɓacin ranta saboda tana da hawan jini. Duk da haka Hajiya ba ta yi shiru ba sai da tayi masu tatas!
Ta ce, “Ku kun kasa zama jarumai, kun amince ku mutu da mata dai-dai shi yasa kowanne zai zo yana fadin bai kamata ba, amma ba wanda ya kawo min aya ko hadisi da ta haramta masa auran.Ke kuma ko da dayar zai zaba ai ba ki ciki, saboda akwai yarinya Aliya ‘yar makotanmu ce, sama da shekaru uku tana jiransa. Don haka kin ga kema cikin ‘yan kari ki ke.Nafisa ta mike fuuu! Cikin kuka ta ce, “Kaka
sai anjima.” Alhaji ya ce, “Bari mu tafi Hajiya.”Ta ce, “Ku gaida gida.”A mota yana ta lallashinta. Ta ce, “Baba ni dai kawai na fasa, na hakura.” Ya ce, “A ‘a Nafisa, kar ki ce haka, ki bari dai muje gida.
Iyayen sun tasa ta a dakin Maman suna lallashinta, kan cewa tayi hakuri kar ta ce ta fasa, domin Kaka za ta yi fushi.
“Kin san dai fushinta zai janyo babbar matsala.” Mama ta ce, “Ke da yake dan uwanki, Hajiyarsu ke tafi so, kuma kema kin san dole zai fi sonki saboda dangantaka.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka dai suka yi ta lallashinta har taje ta kwanta, amma ba don ta gamsu da maganar mahaifinta ba.
Tun da ya isa kofar gidan gabanshi ya fadi, duk yanda yake zaton kudin su Amna daga ka kalli gidan kasan ya wüce yanda ya zata.
Dama tun da ya taso daga Zariya waya suke yi har ya iso tangamemiyar kofar gidan tasu mai kama da kofar gari.
Maigadi ya bude masa ya shiga. ‘Yan matasan samari ne suka tare shi. Ya fito cikin shiga ta alfarma, shadda ce gizna mai kalar kwai. Yayi matukar kyau da bakar hular da ya dora.Su ne
suka jagorance shi zuwa wani
kasaitaccen falo. Duk da suna da kudi ya tabbata
su Amna sun fi su nesa ba kusa ba.
Amna ta fito cikin doguwar riga English wears, sai dan mayafi karami da ta yafa. Tayi kyau matuka. ‘Yan gidan suna ta zuwa suna gaishe shi (kannenta). Dama ta fada masa ita ce mace babba a gidan,
sai wanta namiji babba yana zaune a Ingila da
matarshi da yara biyu. Amaryar Babansu ta zo
suka gaisa, itama yarinya ce danta daya.
Tayi masa jagora zuwa gurin Mahaifiyarta ya gaishe ta. An shirya mishi abubuwan ci da sha na zamani. Sannan sun yi hira sosai irin ta masoya, amma ya matsu ya fada mata cewa su uku ne.Ita ma a nata ran ta matsu ta san abin da zai zo mata da shi, wanda ya ce ta yi masa addu’a a kai.Ya kalleta da niyar maganar, sai ta riga shi da cewa, “Ban ji kayi maganar da ka sani in yi maka addu’a ba?”
Ya cire hula ya ajiye, yasa hankici ya share zufar da ta ratso goshinsa a nan take. Sannan ya ce, “Ki min alkawari abin da zan fada ba zai raba mu ba?”
Ta lumshe ido, muryarta can kasa. Ta ce, “Nayi
maka alkawari ba zan barka ba.” Ya ce, “Na taba
baki labarin Aliya budurwar da na fara yi nace
ba za ta jira ni ba ko?”
Ta daga kai tare da fadin “Na tuna. Ya ce, “To ashe tana nan tana jirana.” Ya tsura mata ido yaga yanda zata dauki maganar. Tabbas fuskarta ta canza, sannan tayi shiru ta
kasa magana. Ya ce, “Kin yi shiru honey.” Ta
dube shi “Me zan ce maka? Na fahimci ka sani in yi addu’a a kan cewa zaka min kishiya, haka ne?” Ya ce, “Kishiyoyi za ki ce dai, domin gida sun cire min Nafisa baya-bayan nan. Yanzun dai ku uku ne za a yi rana daya.”
Ta tura kanta cikin cinyarta. Ya tausasa murya.”Kar ki damu Amna, wallahi ina matukar sonki.”
Ta dago ta dube shi.”Nafisar ba ta dame ni ba amma na tuna yanda kayi ta bani labarin Aliya da soyayyarku. Nasan kafi sonta.”
Ya ce, “Ni nafi sonki, saboda kin fi sona.” Haka ya yi ta lallabata har ta hakura, sannan ta ce ya yi shiru yanzun tukunna kada Mom suji ba za Su yarda ba. Ya ce, “Shi kenan na gode da hadin kanki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Da zai tafi ya ba kannenta dubu goma sabbin ‘yan dari biyar-biyar, ya ce su sha alawa babu yawa. Ita kuma ta kawo mishi wasu ledoji guda biyu ta ce ga tsarabarsa, suka rako shi har mota, ta zuba ledojin a kujerar baya.
Ya nufi dakin Hajiyar shi don ya gaisheta tare da yi mata sallama, ya kuma kwashi albarkar safiya ya nufi Kaduna gurin aiki.
Ba ta falon ba ta dakin, don haka ya nufi falon Alhajin su. Ya same su har Badi’atu suna karin kumallo ita da kayan Makaranta a jikinta. Ya tsuguna ya gaida su. Alhajin yasa mishi
albarka tare da masa fatan ya dawo lafiya. Ya kalli
Hajiya ya ce, “Hajiya zan je aiki.”
Ta ce, “Kafin nan wai kai ‘yammatan naka wadanne iri ne? ni dai ‘yata Nafisa na sani, kasan dai sai mun bincika asali.”Ya ce, “Hajiya Aliya ce wadda dai ki ka sani asalin budurwata, ko Kaka dai za ta ba ki labarin asalinsu.
Ta ce, “To dayar fa?” Ya ce, “Amna ‘yar family din Alhaji Baita Nasidi ce.” Ga mamakinsa sai yaga Hajiyarsa ta dago daga kashingidar da tayi. Ta ce, “Wane Alhaji Baitan? Na Kano babban dan kasuwar nan?” Ya ce, “Eh.”
Ta ce, ‘Yar kareren dangi ce ko?” Ya ce, “Hajiya ba karere ba ce, jikarsa ce, shi ya Babanta Alhaji Ibrahim Baita Nasidi.” haifi
Tayi dan murmushi, “Lallai ka tabo babban gida.” Ya kalli Badi ‘atu “Je dakina a kan gado za ki ga wasu ledoji guda biyu ki kawo min, yi sauri. Ya kai karshen maganar yana kallon agogon hannunshi gudun yin latti (makara). Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Yaya bari in bi ka ka sauke ni.” Ya ce, “A’a ina Dircbanki? Ta tafi tana cewa, “Wai sai ya kai Yaya Mustapha wani guri sannan zai kai ni. Bai ce komai ba ta fita zuwa dakinsa.
Ta dawo dauke da ledojin. Ya ce, “Ba Hajiya nata tsarabar da Amna tayo min daga Umra.”
Badi’atu ta soma zazzage kayan iyayen suna kallo. Ledar farko riguna ne masu kyau, dogon hannu da gajeren hannu. Sai gajerun wanduna irin na ciki guda biyu.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG