RANA DAYA CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 8 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya
dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman da za’a zuba musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai
mata, dama oder take yi.
Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da safiya lokaci zuwa lokaci.

Amna kuwa ba ta mantawa da tura masa sakon murna da shiga sabon wata a duk lokacin da aka shiga. Tsarin kowaccensu ya birge shi
Shatima yana da kaifin basira, da hikimar zama
da jama’a, don haka yake ganin kamar cin tuwo ne
ko shan ruwa zama cikin mata hudu ma bare uku. Shagali ake shiryawa a kowane bangare musamman gidan su Amna wadda ta kasance ita ce mace ta farko da za’a soma aurar wa a gurin Mahaifinta.
Itama Nafisa ana ta shiri don ita ce ‘yar fari gurin Babanta, ga kuma dangi kowa na cin buri, Aliya kuwa suma suna shiri daidai karfinsu, bata shagali suke yi ba su, suna ta kayan daki ne a samu a yi mata gado seti biyu, ga kuma gara tunda sun san yana da hali da kyar in ba daki biyu za’a kai ta ba. Sannan gefen kayan gyara jikin Amare ko ina suna ta yin daidai karfinsu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Alhaji Isa Baban Shatima cewa ya yi ba zai ba Shatima komai ba ‘yarshi zai wa kayan Gado da kayan gara. Ya fadi haka ne lokacin da Shatima ya samu Babanshi da Hajiyar su a daki Baban nashi yana tambayar wace gudunmawa zai ba shi?

Shatima ya ce, “Alhaji nima a dan duba min, Allah asusuna babu kudin kirki, gashi ko akwatuna ban siya ba.”
Hajiya ta ce, “Amma jiya ka ce min Alhaji Murtala ya turo maka da dubu dari biyu ko? Yanzun ma nike fadawa Babanku.”
Shatima ya ce, “To duk kowace ta min magana ashobe da za su fitar, Amna ce kawai bata min ba, itama nasan zata yi, shi ne zan raba musu wannan dari biyun.”
Alhaji ya ce, “Ai kai dan dangi ne za ka samu gudunmawa, Murtala da duk cikin ‘ya’yan Mahaifinmu yafi kowa mako, amma shi ya fara baka gudunmawa har dari biyu.”
Hajiya ta ce, “Ba dole kowa ya motsa ba tunda Babansu zai yi aure har mata uku rana daya. Shatima ya ce, “Alhaji ka min daí wani abu koda canza min mota ne.”
Ya ce, “Au! Ka ma tuna min, Alhaji Nadabo ya
ce kaje gidan motocinsa ka zabi wadda ka ke so.”Murna ta cika Shatima. Ya ce, “Amma gaskiya Www.bankinhausanovels.com.ng
Baba Alhaji Nadabo ya yi min komai.”  Hajiya ta ce, “Kuma fa ya ce duk ruwan da za a sha a biki na gora aje kamfaninsa na ruwa a debo. Allah ya saka mishi da alkhairi.” Suka ce
“Ameen.”Shatima ya ce, “Allah Yasa mu ma abotarmu da Munir tayi kamar taku, shima yana da irin halin Babanshi.” Ya cc, “To ke Hajiya har yau ba ki fadi naki ba.”
Ta ce, “Kai uban masu kudi da gata ka ke, nan da wata mai kamawa asusunka sai yayi kamar zai fashe. Don haka ni yanzun ba zan yi alkawarin komai ba sai nan gaba tukunna.”
Ya mike “Shi kenan, bari in je in shirya yau Kano zani gurin Amna.” Hajiya ta ce, “Ka fa yi ma Badi’atu alkawarin zuwa da ita tun shekaran jiya take min zancen.” Ya ce “To ta shirya har da Munnir zamu je ni na ma manta da mun yi haka da ita.”
Karfe biyu sun isa birnin Kano sun samu tarba sosai musamman Badi’atu wadda tayi kyau cikin riga da wando da mayafinsu ‘yan Dubai.
Amna tayi murna da zuwan Badi’atu, ta hada ta da kanwarta Sumy don za su yi sa’annin juna. Tunda suka kebe ta shagulgulan da za su shirya. soma mishi zancen
Ta ce “Mu fa tun ranar Laraba zamu fara biki.” Ta tashi ta dauko mishi katin wanda aka tsara shi da ruwan zaiba, jikinshi kuma ruwan jibi. Karamine kwarai katin sai shegen kyau kamar ka lika a jiki kayi ado.
Ya karanta a ranshi ya ce tab! In ko shi zai ba da kudin shagalin nan za a samu matsala, don ba shi da su, amma dai bari ya jira ya ji abin da zata ce. Ta dube shi.
“Katin yayi kyau kuwa?” Ya ce, “Sosai ma.” Ta ce, “Kamar guda nawa zan baka?” Ya ce “Tun da yanzu saura kusan wata biyu har da kwanaki, ki bari sai abin ya kara matsowa, kar in zuba a wani guri in manta.Kin san kaina kullum kara daukan hayaki yake yi, mata uku fa!” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta taba baki, “Ni ina mantawa da cewa bani daya ba ce, ko su Mom dina ba su fada ma kowa ba sune kawai suka sani. Zan ajiye maka amma za ka zo min dai duka ko?”
Ya ce Zan dai zo amma ba duka ba, kuma mu da abokanmu zamu shirya Dinner wadda za ku zo ku duka amma sai an kai ku.” Ta ce, “In lokacin mutane na sun watse zan je mana, amma in suna nan sai dai kayi hakuri don ba su sani ba.”
To babu matsala, Allah Ya kai mu.” Munnir ma da ya ga katin sai ya ce, “Ni dai bari in rike wannan yayi min kyau.”Sumayya da suka je dakin su da Badi’atu, ta nuna mata ashobensu kala shida. Duk masu tsada ne kowane shagali da kalar da za a sa.
Badi’atu ta ce, “Lallai ku kam har kun fitar, mu dai sai cikin watan nan da zamu shiga sannan za a
fitar, Kanwar Babanmu ce zata fitar da su.”
Sumayya ta ce “Mutum yaushe har ma an kusan gama bada wa. Yayar Babanmu tayo odar ba saidawa ake yi ba, har kawayenta duk an basu ne tare da katin biki.”
Badi’atu ta ce “Tab! Duk wannan kuma za a ba mutum daya?” Sumayya ta ce, “Eh mana. Ita kuwa Amarya kin ga kayan da zata sa da biki? Akwati uku ne aka je Dubai aka dinko su, na biki ne kawai har ma da irin rigar aure dinnan zata sa.Tare aka siyo da kayan da shima ango zai sa a
ranar da takalmi da komai. Badi’atu ta saki baki,
har ta soma tunani tsarata kawai Summy ke yi
Har suka soma shirin tafiya Shatima bai ji tayi masa zancen kudin komai ba, kamar yanda Aliya da Nafisa suka mishi da ya ziyarce su a ranakun Juma’a da Asabar.
Kowace ta tambayi kudin ashobe, da kuma sauran shagulgulan tata zata yi da kawayenta Ya kalli Amna, “Ke ba za ki yi ashobe ba ne?”Ta lumishe ido, “Ai tuni sun cire abinsu, ni ai ba zan sa ba, sun kusan gama raba shi ma.” Ya ce, “To yanzun me ki ke bukata daga gare ni don shagali ko wani abu? Gara in sani tunda wuri kin san abin da yawa.”
Ta ce “Ban gane ba.” Ya ce, “Kudin siyan ashobe da shagalin da zaku yi.” Ta girgiza kai tare da tabe baki.
“Babu fa. Ni ban sani ba ko ana bada wani kudi
na shagali ba.” Ya ce, “Shi kenan, in dai da wani
abu sai muyi magana ko?” ta ce “To, babu matsala.” Ta ce, “Bari in je in kira Badi’atu din ko.” Ta samu Mom dinsu ta hada ma Badi’atu sha tara ta arziki, irin su kayan kwalliya, da na ci, kayan zaki, sai ko ashoben su kala shidan nan da
na kai, sannan Amna ta ba da turare a kai ma Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya Hajiya kuwa tayi murma har taji cewa Amna ta kwanta mata a zuciya, a fili ta ce, “Harkar arziki da me arziki ake yin shi.” Badi’atu kuwa sai labari a ke baiwa Hajiya na abubuwan da ta gano, da kuma wanda taji. Hajiya ta ce, “Ai familyn Baita Nasiri sun fi da haka, masu kudi ne na wuce tunani.”Kamar yanda iyayen Shatima suka ce, hakan ce
ta kasance. Ana shiga watan sha daya, iyayensa maza da mata wadanda suke uba daya da wadanda suke da dangantaka ta dan nesa. Sai kira suke Shatima ya turo da lambarshi ta account.
Bayan haka suna kaiwa Kaka tata. Shatima ranar yaje gurin Kaka yana alfahari da sunan da suka sa masa. Ya ce “Kaka ‘ya’yanki sun yi mini komai, sun cika asusuna da kudi gaskiya na yarda da kalmar Hajiya ni ne dan masu kudi, kuma uban masu kudi.”
Kaka tayi dariya, “Tun daga haihuwarka goshinka kazo, uwarka bata baka labari ba? Ran da aka haife ka Kakanka ya samu Sarauta, kuma ranar ne Sarkin Zazzau na wancan lokacin ya bai wa Kakan naka kujerun Makka har uku.
Dama shi da matarshi ta fari sun je, don hakan sai ya bar mana muka je mu uku.”
Shatima ya yi dariya, “Ki ce da arzikina aka haife ni?” Ta ce, “Sha Allahu…” wayarshi tayi kira, da ya duba Munnir ne. Ya ce, “Aboki ya ya ne?” Ya ce, “Na zo gida ba ka nan, gani tare da Telan da muka yi magana da kai.” Ya ce, “To ku jira ni gani nan gidan Kaka nazo yanzu zan fito.”Ta ce, “In kuma kuna sauri ka shiga ciki, Badi’atu ta dauko maka kaya a cikin Ghana most go a kusa da durowata sai mu sake haduwa.”
Ya ce, “To, haka ma za a yi. Sai mun yi waya kenan.” Suna sallama ya mike, “Kaka bari in je.” Ta ce, “Kayi baki ne?” Ya ce, “Tela ne wani da aka ce ya iya dinki ga rikon alkawari, a Abuja yake aiki.” Ta ce, “To ka gaida mutanan gidan.”
Daidai kwanar gidan su Salma Shatima ya rage tafiya, yayi fakin gefe sakamakon ganin gidan su yarinyar nan in da ta nuna mishi.
Yaga mutane sun taru, wasu na alwala wasu na tsaye. Da ya kai duba kofar shiga gidan sai ya hangi wasu suna kici-kicin shiga da Makara. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya fito ya jingina da motarsa, sannan ya harde
hannuwansa a kirji, jikinshi a mace. So yake ya
sani ko wane ne ya rasu a gidan.
Duk da zuciyar shi ta raya masa cewa Baban ne ya rasu tunda shi ne ba shi da lafiya, amma wata zuciyar ta ce masa ba dole ba ne ya zama sai shi, tunda dukkan mai rai maniaci ne, haka kuma cuta ba mutuwa ba ce.
Kusan minti talatin sannan aka fito da gawar, shima ya shiga sahun sallah. Da aka idar ya koma jikin motar ana ta wucewa ya hango mata sun fito Kofar gidan suna kuka, ga wata can ana ta rike ta tamkar zata bi gawar.
Ya gano Salma ce, don haka ya tsallaka, bai damu da dinbin matan da ke gurin ba, yaje kusa da ita da kuma wadanda ke rike da ita. Ya ce, “Kanwata!”
Ta dago ido ta dube shi. Ya ce, “Wane ne ya rasu?” Ta ce, “Babanmu ne.” Ta sake rushewa da sabon kuka. Ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Jikin ne ya tashi?”
Ta ce, “Ai dama bai samu sauki ba muka dawo gida, saboda bamu da kudin da za a ci gaba da yi mishi gashi, da kuma siyan magani.
Ya ce, “Me yasa ba ki neme ni ba?” Ta ce, “To
ni ban san in da zan same ka ba, ko da ma na ce
zan neme ka sannan naga kayi mana taimako
daidai gwargwado. Ya ce, “Ina Mamanku fa?” Ta nuna cikin gidan, “Tana ciki.” Ya ce, “Muje in gaishe ta.” Ya dubi matan, “Ku sake ta.” Ya ce, “Kiyi hakuri kin ji? Yaya sunanki?” Ta ce, “Ummu Salma.”
Ya ce, “Kiyi masa addu’a, ita yafi bukata ba kuka ba. Share hawayen ki Ummu Salma kin ji?” Tasa bayan hannunta ta share, sannan ya ce “Muje.Mutanen cikin dakin suka ragu, aka shimfida mishi wata tsohuwar dardumar sallah ya zauna. Ya bi dakin da kallo. Wani dan tsohon gado ne na karfe da ‘yar feleliyar katifa, sai gidan sauro da ke daure daga saman gadon.
Tsakar dakin duk simintin ya fashe. Gefe kuma ga tebur mai dauke da kwanuka, da sauran tarkace. Salma ta katse shi da cewa, “Alhaji ga Innarmu din nan.” Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya kai duba gurin Salma, sannan ya kalli wadda ta ce Innarsu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga gani ba wai tsohuwa ba ce, amma wahala tasa ta zama tsohuwa. Ya ce, “Ina yini? Ya ya hakuri?” suka amsa ya yi addu’a ga mamacin ya kuma ba Innar tasu magana sosai.
Salma ta ce, “Inna wannan shi ne Alhajin nan da ya taimake mu.” Nan suka yi godiya. Ya mike
ya fito tære da ce ma Salma “Zo mu je.” Ta taho haka. Yace “Ki saka hijabinki.”
Duk da tsufan da kayan jikinta ke da su, da mataccen hijabin da ke jikinta bai ji kyamar bude mata gidan gaba ya ce ta shiga ba.
Ita ma bata ji tsoron shiga ba, don sai take kallon shi kamar wani daga danginsu. Ya harba motar kan titi, sannan ya dube ta.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE