RANA DAYA CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA CHAPTER 9 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
suka amsa ya yi addu’a ga mamacin ya kuma ba Innar tasu magana sosai.
Salma ta ce, “Inna wannan shi ne Alhajin nan da ya taimake mu.” Nan suka yi godiya. Ya mike
ya fito tære da ce ma Salma “Zo mu je.” Ta taho haka. Yace “Ki saka hijabinki.”
Duk da tsufan da kayan jikinta ke da su, da mataccen hijabin da ke jikinta bai ji kyamar bude mata gidan gaba ya ce ta shiga ba.
Ita ma bata ji tsoron shiga ba, don sai take kallon shi kamar wani daga danginsu. Ya harba motar kan titi, sannan ya dube ta.
“Kayan abinci zamu siyo, nasan su aka fi bukata yanzun ko?” Ta dube shi idanunta suka kawo ruwa. Ya ce “A’a kar ki min haka. Ba na ce ki daina kuka ba?”
Ta runtse ido sannan ta sauke ajiyar zuciya. Ya kai hannu gefenshi ya dauko ruwan gora ya mika mata, “Amsa ki sha.” Ta amsa ta bude murfin roba ruwan ta daga tana sha, bata san tana jin kishi ba sai lokacin.
Tas! Ta shanye ta sauke goran tana rufe murfin. Ya dube ta “Kiyi hakuri kin ji?” Ta ce, “Na gode Alhaji.” Ya ce, “Sunana Muhammad Ja’afar amma an fi kirana Shatima. Cikin uku sai ki ke kirana da daya a ciki, na kuma tambaye ki an fi bukatar abinci ko?” Ta ce, “Eh.”
Wani shagon kayan abinci suka tsaya, ya sai
buhun shinkafa, Gero, da Taliya, da su mai da
Magi. Ya biya suka koma. Lokacin an dawo daga Makabarta. Yaya Auwal Www.bankinhausanovels.com.ng
ne suka kama suka shiga da kayan suna ta godiya. Ya ciro dubu biyar ya ba Salma ya ce, “Ki ba Inna wannan saboda cefane. In na dawo aiki gobe zan
zo ko da dare ne. Ta ce, “To Alhaji mun gode.” Ya ce, “Bana ce bana son alhj ba.” Ta ce, “To in ce maka ya ya?”Yanda tayi maganar cikin muryar tausayi duk sai
ya ji tausayinta ya karu a zuciyarshi. Ya ce, “Ki ce min haka to. Kada ki manta na ce, addu’a za ki masa ba kuka ba.” Ta ce, “To.” Ya shiga mota ya wuce.
Salma tabi motar da kallo har ya bace. Sannan ta ce, “Allah Ya biya ka da gidan Aljanna.” Ta shiga gidan ta samu har an soma wanke tukunya za a dora girki. Ta kira Yaya Hadiza ta bata kudin ta kuma fada mata yanda suka yi.
Tunda ya gama al’adun shi da ya saba yi kafin ya kwanta, bacci yake ji sosai. Amma yana kwanciya sai ya ji baccin ya kama gabanshi. Tunanin gidan su yarinyar nan Ummu Salma
ya tuna yanda gidan yake a rube, kowane lokaci
gidan zai iya fadowa a kansu. Yarinyar nan ya
tabbata bata kai sa ar Badi’atu kanwarsa ba, kuma
bai ga alamun tana zuwa Makaranta ba..
Sannan kai gaskıya yana bukatar taimakawa yarinyar nan sosai. Ya rumtse ido a cikin zuciyarshi, ya ce ya dauki alkawari tsakaninshi da Mahaliccinshi zai taimaki Umma Salma
Zai inganta rayuwarta ta hanyar bata ilimi. domin daga ganinta. Ya tabbatar tana bukatar ilimi, tana son karatu. Gaskiya gobe zai mata tambayoyi. Www.bankinhausanovels.com.ng
sai dai a rin wannan lokacin da yake tsakiyar hidimar auransa
ba shi da halin yi musu wani gyara domin aiki ne ba karami ba. Haka lamarin yarinyar yayi ta damun sa ya kasa bacci har kusan Asubahi..
Washegari ya dawo aiki ya yi wanka ya saka
farar jallabiya kar!, takalmi ma silifa yasa mai dan
tudu ya kwashi wayoyinshi da makullin mota ya
nufi kasa
Da motar ya nufi Masallaci, da suka idar da Magriba ya nufi gidan su Munnir. Bayan sun gaisa ya ce, ya zo su shiga su ci abinci.
Shatima ya ce, “Bana jin yunwa. Muje ka raka ni muyi gaisuwa.” Munnir ya ce, “Waye ya rasu?” Shatima ya ce, “Baban yarinyar nan da suke kwance a asibiti.” Ya kwatanta mishi.
Munnir ya gane ya ce, “Allah Sarki! To bari in
fada ma Fatima.” Ya shiga ya ce da matarshi sun
fita sannan ya zo suka wuce Sai da suka yi Isha’i
sannan suka karasa gidan.
Da suka yi fakin suka tsallaka gurin ‘yan zaman makoki suka gaisa. Yaya Auwal ya tashi ya zo yana sake fadin “Sannun ku da zuwa Alhaji.
Shatima ya ce, “Na kawo abokina zai yi musu gaisuwa. Shi ne ya yi musu jagora zuwa dakin Innarsu. Daga waje suka tsugunna suka gaisar da ‘yan ciki.
Innar ta leko bakin kofa. Yaya Hadiza ta kwala ma Salma kira. Idar da sallarta kenan a dakin Baito, ta fito ko takalmi babu, ta ce “Yaya Hadiza gani.”
Ta ce, “Dama su Alhaji ne suka zo.” Tayi saurin karasawa kusa da su, ta tsugunna. “Yaya sannun ku da zuwa.” Ya dube ta.
“Salma ya karin hakuri?”
“Da godiya.” Ta gaida Munnir shima yayi mata gaisuwa. Suka mike suka soma tafiya, Inna tana musu godiya. Ya waiwayo yaga Salma a tsaye, dama gidan da duhu, kila ma ba a taba saka wutar lantarki a gidan ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da wayar Munnir suka haska don su ga hanya. Shatima ya ce “Zo mana Salma.
Munnir ya bude motar ya shiga, Shatima ya jingina da motar. Tazo ta tsugunna a gabanshi cikin ladabi. Ta ce. “Gani Yaya.” Ya ce, “Tashi Salma.” Ta mike.
Ya ce, “Dama zan tambaye ki ne kina zuwa Makaranta? Ta ce. “Eh, ina zuwa Islamiyya.” Ya ce. “Boko fa?” Ta ce, “Tun da na gama J.S.3 ban samu damar wucewa ba.”
“Saboda me?” Ya tambaye ta.”Saboda lokacin Babanmu ya soma rashin lafiya, ba ya fita neman abinci, ni ce ni ke nemo mana abin da zamu ci. In yi talla ko in soya awara a waje.”
Ya ce, “Ba ku da wani Yayan? Wancan ba wanku ba ne?” Ta ce, “Yaya Auwal shi ne ke aikin gidan biredi ana biyanshi dubu tara a wata. Lokacin kudin maganin Baba yake biya, ba sa isa ma.”
Shatima ya ce, “Yanzun ke ce ki ke ciyar da ku? Shekarunki nawa ne ma?” Ta ce, “Shekaruna goma sha shida, idan wannan Azumin yazo.”
Ya ce, “Sha biyar da watanni.” Ta ce, “Eh.” Ya lumshe ido cikin tsananin tausayin ta. Can ya ce, “Salma!” Ta ce, “Na’am!” Ya ce, “Fada min taimakon da ki ke son in yi miki?” Ta ce, “Kamar ya ya? Ai kayi mana duk wani taimako, abinci muka fi bukata kuma ka ba mu.”
Ya ce, “Ban da wancan, ke kanki ni ke son in taimake ki, taimakon da ba za ki manta ba, ina son ki nutsu zan bar ki zuwa ranar sadakar uku, yaushe ne?” Ta ce, “Juma’a.” Ya ce, “In nazo sai ki fada min, kiyi shawara da Innarku da Yayanki, ki dubi mene ne burinki sai in taimake ki a kai, kin ji ko?”Ta ce, “To Yaya, Allah Ya saka da alkairi, Ya baka duk abin da ka ke so duniya da lahira.” Ya ce, “Babu komai, ki koma gida.”
Yana shiga mota Munnir ya ce “Gaskiya mutanan nan suna cikin tsananin bukata, dubi irin gidan da ‘yan Adam ke rayuwa, kuma suna da makota masu hali sun sani amma ba za su iya taimakonsu ba.
Shatima ya ce, “Ai ba ka sani ba, su fa masu
hali in za su yi taimakon nan sai dai su taimaki
masu karfi ‘yan uwansu.” Haka suke tattaunawa har suka zo layin su Kaka. Ya ce, “Yauwa, bari mu shiga in fada ma su Kaka a rinka kawo abin sadaka gidan mutuwar nan.
Munnir ya ce, “Haka ne. Allah Ya taimake
mu.” shi kanshi Shatima yana mamakin irin yanda
lamarin yarinyar nan ya hana shi sukuni. Har yaje
yake ba wa Hajiyar shi labarin yarinyar da Www.bankinhausanovels.com.ng
iyayenta. Hajiya ta tausaya, ta ce “Akwai masara a store, ko za ka sa a kai musu buhu biyu?” Ya ji dadin haka sosai. Ya ce “Gobe ne zan je, in na dawo aiki. Tunda gobe rabin rana ce zan dawo da wuri.
Wani abu da ya yi ta bai wa Shatima mamaki yanda har sakon Aliya da ya shigo na Juma’ar yau bai sami damar budewa ba, kowane lokaci zuciyarshi tana can gurin tunanin yarinya Salma. Abin da yafi tsaya mishi a rai, ‘yar shekaru sha biyar ke rike da gida.
Salma da ke kwance a tsakar dakin Baito kan yar tabarma, ta rufe kafafunta da hijabinta, nan take kwana kasancewar Baito bata da miji.
Juyi kawai take yi tana tunanin maganganun Shatima, dole tayi nazari sosai a kan kanta kafin ta tunkari su Yaya Hadiza, burinta da yake magana a kai shi ne take tufka da warwara a kai. Ta sani tun da ta taso fatanta Allah Ya bata
ilimi mai albarka, ta zama ‘yar Jarida ma aikaciya
a gidan TV ko Radiyo. Tun lokacin da Mahaifinta ya farka. Duk da cewa makarantar Gwamnati take kullum sai ya bata Naira talatin zuwa Naira talatin dawowa, in da kudi har Naira dari yana bata don ta samu dan na kashi.
Mamansu tana aikin gida, a gidan wasu masu hali, itama dole aikin ya tsaya saboda jinya. Tun daga lokacin Mahaifinta ya soma zancen aurar da ita, kullum sai ya fadawa Innarsu cewa shi ya tabbata ciwon shi ba na tashi ba ne amma yanason don Allah su aurar da Salma don ta daina wannan wahalar ta talla, za su ci abinci daga abin da Yaya Auwal yake samu.
Tunda in an aurar da ita sai Umar da Sani kannenta su ko maza ne. Ko ranar da zai mutu sai da ya yi zancen aurar da ita, abin da ya tsaya mata a rai har da kuka ya yi lokacin da ya ke maganar.
Tana wannan tunanin ne sakamakon zancen da Shatiman ya zo mata da shi. Dole ta aje burinta na karatu, saboda in ya dauki nauyin biya mata kudin Makaranta da takardu da komai, kudin mota na yau da kullum zata dora masa ne?
Ita dai kawai zata ce abu dayan da ya ce ta zaba ta zabi ya aurar da ita ga Basiru saurayin da ya nuna kaunarsa gareta, ya yi mata kayan daki tunda shi ne burin mahaifinta.
Washegari da safe kula guda katuwa aka kawo cike da waina daga gidan su Kaka. Www.bankinhausanovels.com.ng
Salma tana jin mutane na ta yabon Hajiya Kakar su Shatima, suka ce duk in da aka yi rasuwa ko basu sanka ba sai sun kai.
Salma ta ce ma Yaya Hadiza “Ai Hajiyar Kakar wannan Alhaji ce da ya ke taimakonmu, kila ma shine ya sa a kawo.” Bayan yan addu’a sun watse ta ce Amira ‘yar gidan Yaya Hadiza ta leka ta kira Yaya Auwal.
Inna ta ce, “Mene ne?” Salma ta ce, “Alhaji ya bani wani zabi ne, shi ne ni ke so muyi shawara da ku.” Bayan sun hadu, Salma ta fada musu yanda suka yi da Shatima. Yaya Auwal ya
cc, “Mc zai hana ki ce ya sai mana gida?” Ta ce. “Burina ya ce wai in zaɓi abu daya, ba wai namu ba. Kowa yasan bani da burin da ya wuce in yi karatu in zama ‘yar jarida. Sannan kuma burin Baba shi ne ayi min aure
To ina son ku duba ku gani a cikin nan wanne zan zaba?” Yaya Hadiza da Yaya Auwal suka ce, “Ki zabi karatun.” Inna ta ce, “A’a in ba ku manta ba, zancen
aurar da ita yana daya daga cikin kalaman
Malam na karshe. A nawa tunanin tunda ga
Basiru yana sonta, kuma yana da dan abin yin sa,sai a ce ya fito.
Shi kuma sai ya taimaka ya yi mata kayan aure. Hadiza tace, “Haka ne, to ayi hakan. Yaya Auwal ne dai shi bai gamsu ba, amma ganin ita Salma ta yarda sai ya mika wuya shima.Salma tasan ita bata son wani Basiru, bata ma san kowa don ba hakan a gabanta.
Tana bacci taji ana cewa ga buhun nan masara ana shigowa da su. Duk da ba ta fito ba tasan shakka babu Shatima ne. Yaya Hadiza ta leko dakin Baito.
“Salma ki zo ga Alhaji ya aiko da buhun Masara guda biyu.” Ta fito ta samu su Inna suna tsaye bakin kofa suna godiya. Hadiza ta ce “Kai wannan bawan Allah Yana taimakonmu, Allah dai ya saka mishi da alkairi.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Salma ta ce “Ya tafi ne?” Yaya Auwal ya ce, “Yana waje cikin motarsa.” Ta saka takalmi ta fita. Gaban motar ta gani a bude, daga gani ta samu matsala ne, shi kuma yana tsaye yana waya.
Ta tsaya daga inda take, tana iya sauraron abin da yake fadi. Ta fahimci da Bakanike (mai gyara) ya ke magana. Don taji yana cewa “Zafi take yi, kazo ka same ni a nan Tudun Wada…” Ya ci gaba da yi masa kwatance.
Da ya gama ya tsallako suka tsaya a inuwa inda “yan zaman makoki suka watse. Ya ce. “Salma! Tace. “Na’am! Yaya.”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG