RAWANIN TSIYA CHAPTER 2 BY FADEELAH

RAWANIN TSIYA CHAPTER 2 BY FADEELAH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

ALIYU BUGAJE (PAAPA)??+

Alhaji Muhammad Bugaje ya kasance mutumin qaramar hukumar Bugaje ne a cikin garin Katsina. Da shi da mai dakin shi Hajiya Aminatu sun haifi yaro daya kacal, Aliyu.

Aliyu ya taso cikin gata domin kuwa mahaifin shi yana da arziki.. Sana’a ita ta kai mahaifin shi garin Kano wanda a nan garin Kano aka haife shi. Alhaji Muhammad ya kasance yana da kamfani na siyar da Rodi.. a wannan lokacin duk fadin arewa babu kamfanin da suke sayar da rodi mai kyau kamar nashi.. Yayi fice sossai a wannan sana’ar domin kuwa daga qasashen turai yake shigowa da su don haka akwai guarantee na lallai kayan shi masu quality ne.

Aliyu dai tunda ya taso yake son harkar business kamar yadda ya ga mahaifin shi yana yi.. don haka ne ko da ya kammala secondary school dinshi a nan cikin garin Kano sai kawai mahaifin shi ya tura shi qasar America inda ya karanci Business administration a Stanford University.

Aliyu dai bai bar qasar America ba har sai da yayi masters dinshi.. A lokacin da ya dawo ne ya fada kamfanin mahaifin shi.. Sossai ya kawo musu canji a kamfanin tun daga administration na kamfanin har zuwa marketing and customer service. Kasuwan su ta qara budewa sossai domin kuwa ya shigo musu da tsare-tsare da hanyoyin da suka bunqasa yanayin hada-hadar su da customers dinsu.

Har a wannan lokacin siyo Rodi suke yi daga qasashen qetare sannan su siyar… dukda suna samun riba, Aliyu ya zauna yayi analysis ya ga idan suka fara qera rodin da kan su a nan gida Nigeria lallai zasu fi samun riba fiye da yadda suke samu idan sun shigo dasu daga qasashen waje don haka ne ya duqufa research akan how to make this possible.. ya gano qasar China sun fi kowa iya harkar steel Rods don haka ne yayi proposing ma mahaifin shi plan dinshi wanda nan da nan ya amince.

Aikuwa ba tare da bata lokaci ba Aliyu yayi consulting daya daga cikin distributors dinsu na can qasar China din yayinda suka yi mishi marhabun… sun gayyace shi zuwa qasar inda zai shiga wata makaranta da zai samu qarin ilimi- it was more like an engineering school.. Aliyu dai sai da yayi tsawon shekara uku da rabi yana wannan makarantar. Dayake yana da bala’in qwalwa, nan da nan ya shanye komai.

Dayake duk harka ce ta kudi, bayan ya kammala karatun ya samu knowledge akan manufacturing process din ne suka bashi ma’aikata wadanda zasu koma Nigeria tare suyi training ma’aikatan su amma da sharadin zasu dinga biyan su salary da allowances kamar yadda suka buqata..

It was a bit expensive and big capital project toh amma kuma idan suka jure zasu mori abun a nan gaba..

Nan da nan aka zuba ma’aikata graduates wadanda suka samu training mai kyau daga wurin Chinese din.. cikin ikon Allah kafin shekara ta zagayo tuni aiki ya fara with full force. Sai sukayi renaming sunan kamfanin to Bugaje welding rod Manufacturing industry.

A haka dai suka cigaba da kasuwancin su yayinda kamfani yake ta bunqasa.

Aliyu dai tun yana Secondary school yake son wata yarinya a layin su. Aisha ta kasance ‘yar gidan Alhaji Malik Zayyad. Asalin shi dai dan qasar Morocco ne wanda aiki ne ya kawo iyayen shi Nigeria har yayi aure a qasar ya haifi yara.2

Aisha dai kyakyawar yarinya ce fara sol.. duk gidan ita ta biyo kamarnin mahaifinta don haka ita ce tayi kama da larabawa Morocco sossai saidai tun tana yarinya take fama da ciwon asthma- irin mai qarfin nan. idan ta tashi mata sai tayi kamar zata mutu.. a haka dai ta cigaba da rayuwa under special care har ta girma.

STORY CONTINUES BELOW

Tun ranar da Aliyu ya fara ganin ta ya dage ma mahaifin shi yayi ma mahaifinta magana akan idan ya girma shi zai aureta… abu dai kamar wasa tun mahaifin nashi bai dauki maganar shi serious ba har dai ya dauka.. Dayake suna mutunci da mahaifin yarinyar sai yayi mishi maganar.. Gashi dai mahaifinta dama yana bala’in son Aliyu toh amma a dalilin ciwon asthma da yarinyar take fama da ita sai ya qi amincewa tunda dai bai kamata ya dauki yarinya mai fama da ciwo ya basu ba.. Ko da aka yi ma Aliyu bayani cewa yayi ya ji gani.. shi kam ko wacce irin cuta take fama da ita yana son ta. Da wannan ne aka yi ma Aliyu alqawari idan sun girma suna raye zai auri Aisha..

Tun kafin ya tafi qasar America kuwa suka qulla soyayya mai qarfi da Aisha… wani mugun so Aliyu yake yi mata, a duk lokacin da ciwonta ya tashi kuwa zaka tausaya mishi matuqa domin kuwa ji yake yi kamar zai mutu.. ba’a taba gane kanshi har sai ta farfado. Shiyasa ko da ya tafi America idan ta samu attack ba’a gaya mishi..

A lokacin da ya dawo kuwa bayan yayi settling business din mahaifin shi sai ya shigo da maganar son yin aure.. dama dai babban burin shi a rayuwa su ne yayi expanding business din mahaifin shi sannan ya mallaki Aishatu a matsayin matarshi.

Dayake dai harka ce wadda kowa a shirye yake kuma tun dama dai an yi magana sai kawai aka sa ranar bikin su. Lokacin dama Aisha ta kammala karatunta a BUK kano.

An sha biki mai rai da lafiya an kashe kudade.. Mahaifin shi ya bashi kyautar gida qaton gaske a Bompai GRA.

Aishatu dai yarinya ce shiru-shiru, ga riqon addini, ga ladabi da biyayya.. Sossai sirikarta (mahaifiyar Aliyu) take ji da ita. Gata dai dukda ba issasar lafiya gareta ba akwai ta da son yin hidima iri-iri… kama daga girki zuwa tsabtace gida da sauran su.. Sai ya zamanto duk tarin masu aikin gidan basu yin komai duk ita take yi.

Sai da Aliyu yayi dagaske sannan ya raba ta da aikace-aikacen gida amma fa dukda haka idan masu aiki suna yi zaka ganta tsaye a gaban su tana supervising.

A haka dai har shekara ta zagayo ta samu ciki.. tunda ta samu cikin kuwa a kullum addu’ar Aliyu ita ce Allah ya basu ‘ya mace mai kama da Aishatu. Aikuwa dai Allah ya karbi addu’ar shi don kuwa Aishatu ta haihu ta samu yarinya fara sol kyakyawa mai kama da ita sak. Yarinya dai ta ci suna HANIFA.

A lokacin da Hanifa tayi wata bakwai a duniya ne wani al’amari ya faru… wata rana Aishatu ta samu attack wanda hatta inhaler da take shaqa ta qi yi mata amfani don haka ne aka garzaya da ita asibiti… a wannan ranar ko kafin a isa asibiti Allah ya karbi ranta..

Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un!!

Aliyu bazai taba manta wannan ranar ba.. Kanta a bisa cinyar shi cikin mota, yana kallonta ta tafi ta barshi da Hanifa! Mai karatu ba sai na fadi maka kalan tashin hankalin da Aliyu ya shiga ba a lokacin da ya rasa Aishatu.

Har hawan jini ya kama shi wanda yayi sanadiyyar ciwon zuciya, ya dade kwance yana jinya. Har qasar waje aka fitar da shi wanda da qyar aka samo kan shi… Likitoci sun bada shawara akan a kiyaye duk wani abinda zai tayar mishi da hankali saboda it will be dangerous to his health.

A kullum zaka ganshi rungume da Hanifa yana zubar da hawaye… hawayen da baya sanin lokacin da yake yi.. Zamu iya cewa iyayen Aishatu haifan ta kawai suka yi amma tabbas Aliyu ya fi su sonta.

Mahaifiyar shi ita ta karbi Hanifa ta cigaba da rainon ta. dayake Aliyu baya son yin nisa da Hanifa shima dole ya koma gidan su ya cigaba da zama. A haka dai rayuwar shi ta cigaba.. tun yana isolating kanshi har gradually ya fara komawa normal.. A matsayin shi na musulmi dole ne yayi tawakkali ya rungumi qaddara.

Bayan shekara daya da rasuwar Aishatu ne iyayen ta suka yi shawara da iyayen Aliyu akan zasu bashi qanwar Aishatu mai suna Anisa idan yana so. Aikuwa kai tsaye yace baya so, she will only be there to remind him of Aishatu plus bazai iya bata irin kulawar da take buqata ba don haka bazai iya aurenta ba .. a cewar shi bazai iya qara aure ba har abada.. a wannan lokacin dai an qyale shi saboda ana tunanin ko maybe he needs more time ne amma inaaa… Aliyu dai haka ya cigaba da rayuwa ba tare da ya qara kallon wata mace da da idon SO ba.

STORY CONTINUES BELOW

Sai da Hanifa ta kai shekaru Goma sha hudu sannan yayi aure. A wannan lokacin ma mahaifin shi ne ya sa shi a gaba. Aliyu dai ganin cewar mahaifin nashi ya tsufa ya bar mishi kamfanin ya cigaba da running, the only thing da zai yi mishi wanda zai ji dadi shine ya cika mishi burin shi. Don haka ne ya sa Mahaifiyarshi ta nema mishi mata.

Aikuwa nan da nan ta hada shi da Binta wadda itama ta taba yin aure Allah yayi ma mijinta rasuwa.. ya rasu ya barta da da daya namiji mai suna- Hafeez. Hafeez dai ya girmi Hanifa da shekara daya.

Ko da ya auri Binta ya dauki nauyin dan ta wanda ya riqe shi a cikin gidan shi tamkar dan da ya Haifa.

Da farkon zaman auren nasu kuwa Binta ta sha wahala don kuwa kasa fahimtar Aliyu tayi.. amma dayake tana da haquri sannan kuma tana iya qoqarinta wurin kyautata mishi nan da nan ahankali ya sake da ita… Soyayya dai daya ce kuma ya riga ya ba Aishatu amma tabbas Binta holds a special place in his heart too.

Bayan auren Aliyu da wata biyar ne mahaifin shi ya rasu sannan bayan shekaru biyu da rabi da rasuwar Mahaifin Aliyu itama mahaifiyar shi ta rasu. Sai dai mu ce Allah ya jiqan su gaba daya.

☆☆☆☆☆☆☆☆

HANIFA ALIYU BUGAJE??

Kamar yadda na fadi muku Hanifa fara ce sol sannan kyakyawar gaske mai dogon gashi kamar na mahaifiyarta… Daga gashin kanta har zuwa yatsar qafafuwan ta irin na mahaifiyarta ne.. Babu shakka kamarnin ta da mahaifiyarta yana daga cikin abinda ya sanya Mahaifinta yake bala’in sonta.2

Tun tana jaririyarta take cikin gata gaba da baya da kuma tsantsan soyayya. Mahaifinta da Kakannin ta sun dauki soyayyar duniya sun dora akanta.. in taqaice muku zance Hanifa lived and is still living the life of a princess.

A rayuwarta gaba daya babu abinda take yi.. komai yi mata ake yi. Wanka ne kawai take yi da kanta shima very lazily domin kuwa sai tayi sama da awa daya a zaune cikin Jaccuzzi bath tana wasa da ruwan bubbles… da alama dai idan da hali har shi din yi mata za’a yi. The only thing da na san Hanifa take yi babu laziness shine karatu.. when it comes to school she is very active, Sossai take da qwalwa.. tunda ta fara karatu bata taba yin anything other than 1st position ba.. infact she comes first and best in everything.

Hanifa ta taso kowa yana tausayin ta a dalilin rasa mahaifiyarta da tayi tana wata bakwai.. Zamu iya cewa Soyayya da tayi mata yawa ita ta shagwaba ta take yin abinda ta ga dama.. tun tana yarinya duk abinda take so shi ake yi mata.. tun tana yarinya ba’a ce mata NO don haka har ta girma babu No a dictionary dinta.

Tun tana qarama masu aikin gidan kakaninta suke fama da ita.. a dalilin Hanifa an kori masu aiki ya fi a qirga kuma yawanci ba don sunyi laifin komai ba.. kawai saboda Hanifa bata son su ko kuma bata son irin aikin da suke yi mata. Ko da Paapa yayi aure ta dawo gidan su bata canza zani ba.. kullum dai sai ta samu matsala da masu aiki sannan a qarshe ta sa a kore su.

Hanifa tayi primary da secondary school dinta a Lufaloy Group of schools da ke cikin GRA kusa da gidan gwamna a cikin garin Kano. It’s the best school in Kano. Tunda ta shiga makarantar kowa ya san ta for her good and bad side. her good side was tana da qwalwa and her bad was ko kai waye baka isa ka sa ta yin abinda bata so ba.. hatta malaman makarantar kuwa. A dalilin matsayin mahaifinta a cikin garin Kano da kuma qwalwar da take da shi wanda suke alfahari da ita dole aka haqura aka bi ta yadda take.2

Hanifa dai ta taso bata shakkan kowa a duniyan nan sai Kakannin ta and most importantly Paapa dinta. Babu wanda ya isa ya ta yin abu sai su.. shima wani lokaci na kakkanin tana tirjewa amma fa Paapa ko da against her wish ne tana kuka tana yi.. bata taba tsallake maganar shi. Kai hatta rashin mutuncin da take yi ma mutane bata yi a gaban shi don haka zamu iya cewa most of the bad things she does he is not aware.

STORY CONTINUES BELOW

Hanifa’s Paapa is definately her weakness!!

Lokacin da Paapa ya auri Binta wadda suke kira Mamy sossai ta ji haushi.. bata son Mamy a dalilin Paapa yayi sharing soyayyar da yake yi mata da ita.. Da lallashi Paapa ya shawo kanta ta haqura amma fa dukda haka nan babu ruwanta da Mamy.. Sai suyi Sati biyu suna zaune a cikin gida amma basu hadu ba balle suyi ma juna magana.

Da farko Mamy tayi qoqarin janyo ta a jiki amma ganin halinta na wulaqanci, rashin kunya da yadda Paapa baya ganin most of laifin da take yi, sai ta ja baya abinta… after all bazata so Hanifa tayi sanadin mutuwar aurenta ba. Shi dama Hafeez ba mai hayaniya bane musamman tunda ya San ba gidan uban shi bane don haka shima yayi maintaining distance dinshi. Karatun shi kawai ya sa a gaba tunda dai ya samu opportunity Paapa ya bashi damar ya zabi duk qasar da yake so ya je yayi karatu after secondary school.

Shima lufaloy din Paapa ya mayar da shi lokacin da ya auri Mamy.. A lokacin Hanifa tana JSS3 yayinda shi kuma yake SS1. Dukda makaranta daya suke zuwa ba tare ake kai su ba.. kowa da driver dinshi a dalilin rigima irin ta Hanifa.. wai ita ala dole yadda ta saba zuwa school tun kafin Hafeez ya zo haka zata cigaba. Aikuwa her wish is her Paapa’s command, what she wants she gets!

A lokacin da Hanifa ta kammala Secondary school ne ta zabi zuwa Oxford university a qasar England inda zata karanci accounting. Zamu iya cewa tafiyar Hanifa yayi ma kowa dadi.. daga Mamy har zuwa securities na gidan.. an samu sauqi sossai sannan abin mamaki tunda ta tafi ba’a qara korar wani mai aiki ba a gidan saidai idan ta zo hutu sun taki rashin sa’a.

Hanifa dai gwana ce wurin iya gayu.. ma’abociya son designer abu ce. Hatta brush na wanke bakinta designer ne.. Another thing is komai nata unique ne.. zai yi wuya ka ga abu a wurinta sannan ka gan shi a wurin wani.. she always take her time to choose a unique and best stuff. Hanifa dai a rayuwarta tana qaunar English wears.. a cewarta sun fi sauqin sawa amma dukda hakan tana sa native babu laifi.. natives din ma wasu irin unique styles take yi musu don kuwa a kanta fashion designers dinta suke inventing style.

Duk wata take zuwa Dubai da Paris don yin shopping din kaya.. yana wuya ka ga ta maimaita kaya domin kuwa tana da su dayawan gaske.. Idan kuka ga closet dinta zaku rantse boutique ne.

A duk wata kuwa Paapa yake tura musu kudin pocket money masu yawan gaske ita da Hafeez wanda a dalilin high taste da yawan expenses din Hanifa sai da ta buqaci more money.. As usual duk abinda take so shi ake yi mata, Abba yayi increasing pocket money din kamar yadda ta buqata.. ko da ya qara ma Hafeez sai yace baya so don kuwa wanda ake bashi ma sunyi yawa.2

Hanifa dai a rayuwarta tana da bala’in kashe kudi.. ko kadan kudi basu zama a account dinta. Shin ko saboda high taste dinta na abubuwa ne??? oho!!

One thing about Hanifa is bata associating kanta da kowa.. Gani take yi kamar ta fi kowa don haka me zai sa tayi associating da wasu?? kyau, ilimi, iya gayu da wayewa bata ga wadda ta fi ta ba then why will she stoop low for people? Samari masu kyau, aji da kudi sun neme ta amma tayi turning dinsu down.. infact only few of them were able to approach her don kuwa wulaqancin Hanifa is out of this world.. A dalilin bala’in girman kanta kuwa ko qawa batada shi.. Paapa dai shine komai nata. Duk wani abinta na rayuwa she shares only with her Paapa.

And yes ban fadi muku ba, Hanifa gwanar rawa ce.. She can dance for Africa. A dalilin bala’in son rawa da take yi har register tayi a wani dancing school lokacin da take England.. she can dance to all kinds of music. At her leisure time, takan kunna sauti tayi ta rawa abinta.

Babban burin Hanifa a rayuwa shine tayi aiki a kamfanin Paapa.. she wants to take the company to greater heights.. Paapa kuwa ya ji dadi sossai domin kuwa burin shi shine Hanifa da Hafeez su yi running Company din idan sun kammala karatun su sannan shi ya huta.

Lokacin da ta kammala degree dinta a Oxford ne ta dawo Nigeria inda tayi serving a kamfanin Paapa.. aikuwa zaman shekara dayan da tayi an sha wahala.. wulaqanci dai an sha shi, gaba daya kamfanin babu mai sonta. Kowa yayi tir da munanan halayen ta.. Hanifa dai ko kafin ta gama serving sai da tayi sanadiyyar koran ma’aikata har uku.. Lokacin da ta gama kuwa ta tafi sai da ma’aikatan suka hada party.2

Bayan ta gama NYSC dinta ne ta koma Oxford don yin karatun Masters dinta wanda a yanzu haka shine ta kammala ta dawo Nigeria ta hadu da Sadiq wanda tun a airport suka fara rikici.

Gashi Paapa zai hada su aiki tare… Ya kenan???2 days later

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE

NASSARAWA-GRA

Paapa da Mamy ne a qayataccen dinning room na gidan suna dinner.

Hanifa ce ta shigo dinning room din sanye cikin wandon jogger na mata da ‘yar qaramar t-shirt. Kanta babu hula don haka ta dunqule gashin kanta a tsakiyar kai.. qafafuwan ta sanye cikin slippers. Tayi kyau sossai, sai zuba qamshi take yi.

“Baby yau kinyi latti”

Tana murmushi ta qarasa kujerar da take kusa da shi wadda take fuskantar ta Mamy ta zauna yayinda take fadin “wallahi Paapa wankan ne yayi mun wahalan yi yau”1

“Lazy girl” ya fada yana murmushi.

Itama murmushin tayi yayinda na ga ta danna wata na’ura akan table din wadda nake kyautata zaton bell ce. Aikuwa nan da nan na ga wata mai aiki ta shigo.

Har qasa ta russuna ta gaida Hanifa. A wulaqance tace “serve me”

Da sauri mai aikin ta shiga zuba mata kalolin abincin da ta san tana so and neatly in the right proportion. Allah dai ya taimaketa har ta gama zubawa bata yi laifi ba..

“Ki je ki gyara mun daki na yanzun”

“Toh Anty” mai aikin ta fada yayinda ta wuce sashen Hanifa.

Mamy dai tana mamakin halin banza irin na Hanifa. Yarinya qatuwa da ita ko girki bata iya ba balle gyaran gida… komai sai dai ayi mata.

She is even wondering idan tayi aure ya zatayi zaman a gidan miji?? da kanta kuma ta ba kanta amsa👉ai dayake namiji mai irin social status dinta zata aura he can afford all the luxuries for her…3

“Munyi waya da Hafeez dazu yace mun he is coming back next week ko???” Paapa ya tambayi Mamy

“eh wallahi.. haka yace”

Masu karatu kar ku manta yaron Mamy mai suna Hafeez.. yayi karatun degree dinshi a Harvard University a qasar America inda ya karanci Economics.. bayan ya dawo yayi NYSC dinshi ne ya koma yayi MBA.. Finally dai yanzu ya gama shine zai dawo gida.

“Toh madallah… Allah ya dawo da shi lafiya”

Hanifa dai tana sauraron su amma fa bata ce komai ba.. ita dama idan har ta ji Paapa yana hira da Mamy bata sa baki.

Abincin ma dan kadan ta ci ta ture plate din yayinda ta dauki ruwa ta sha.

Paapa ne yace “Baby har kin qoshi??”

“Yes Paapa.. abincin bai yi dadi ba”

Mamy wadda take kallonta sossai ta cika da mamaki.. ya za’ayi Hanifa tace abincin nan bai yi dadi ba bayan ita da kanta tayi supervicing masu aiki wurin dafa shi infact kusan ma ita da dafa shi plus she is well known as a great cook.. how dare she?? ita me ya hana ta shiga ta dafa mai dadin???5

“Haba Baby.. wannan abincin ne bai yi dadi ba?? gaskiya we need to question your tastebud because this dish tastes great”

Turo baki tayi tace “Paapa ni gaskiya ba wani dadi yayi ba”

“toh yanzu ya za’ayi?? ko za’a qara dafa miki wani ne… kin san bana so kina bacci on an empty stomach”

“No Paapa, I am okay”

Har ta miqe tsaye sai kuma ta koma ta zauna tace “yauwa Paapa.. dama ina so in fadi maka I need money to go shopping in Dubai and Paris.. ina buqatar new sets of clothes before I start working at the company”

STORY CONTINUES BELOW

“Babu matsala Baby.. zaki iya zuwa office ki samu Sadiq..”

“what???” ta fada tun kafin Paapa ya qarasa maganar shi.

“Yes Baby.. Sadiq shine finance manager remember??? duk wasu kudi da suke fita daga company din dole ne sai yayi authorizing saboda he accounts for every expenses na kamfanin”1

Shiru Hanifa tayi tana mamaki.. toh wai ya akayi Paapa ya sakar ma gayen nan komai na kamfanin shi.. Yanzu hatta kudi shine zai bata?? why???

“toh Paapa kai bazaka iya bani ba dole sai shi ne?? i thought it’s from your personal account that…”

“Hey Baby listen to me.. kamar yadda na fadi miki abubuwa sun canza, duk wani expenses goes through Sadiq yanzu.. he is in charge don haka gobe sai ki shirya ki je ki karba because zai je Abuja da yamma… kuma kwana biyu zai yi”

Hanifa dai bata qara fadin komai ba ta miqe tsaye tace “good night”

Girgiza kai Paapa yayi yace “good night my dear”

Bayan ta tafi ne ya kalli Mamy yace “ni na rasa dalilin da ya sanya Baby bata son Sadiq.. if only zata kwantar da hankalinta ta fahimce shi they would have gotten along very well”

Mamy tayi dan murmushi tace “aikuwa dai yaron yana da sauqin kai sossai.. probably idan sun fara aiki tare qila ta gane”

“for her sake, I hope so” Paapa ya fada yayinda nayi mamakin kalaman nashi

‘for her sake????’🤔3

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!!

BUGAJE INDUSTRIES

KANO- CENTRAL

Wuraren qarfe Goma da rabi na safe yana zaune a qayataccen office dinshi yana aiki a Macbook dinshi.

Hanifa ce ta shigo ofis din babu sallama balle ta qwanqwasa qofa… Gani nayi tayi freezing a tsaye yayinda ta lumshe idanuwanta tare da jan numfashi..2

Tunda take bata taba ganin ofis mai kyan tsarin wannan ba.. Ga wani asirtaccen qamshi da ya gauraye da sanyin AC ya bayar da wani yanayi mai dadin gaske.

Abin mamaki shine office din Sadiq ya fi kowanne ofis a kamfanin kyau.. kai hatta ofis din Paapa bai kai nashi kyau ba sai dai kawai ya fi na Sadiq din girma.. it’s probably because shi Paapa dattijo ne and he doesn’t fancy such things!!

Gaba daya idan ka shiga office din Sadiq atmosphere din daban ne.. settings din ofis din daban ne, haka wani asirtaccen qamshi da yake tashi kadai ya isa ya hana ka son barin ofis din idan ka shiga. Gashi ko ina spotlessly clean just like the owner himself.

Cikin few seconds Hanifa ta gama analyzing ofis din kaf yayinda ta qara cika da mamaki.. How is it possible Paapa zai dauki ofis irin wannan ya ba Sadiq??? ta qudurta a ranta dole ne idan ta fara aiki a kamfanin ya bar mata ofis din ya koma wani don kuwa a matsayin ta na ‘yar mai kamfanin ita ya dace ta zauna a ciki ba shi ba.1

Secretary dinshi ce ta shigo hankali a tashe ta ratsa ta gefen Hanifa ta qarasa wurin shi tana fadin “sorry Sir.. I tried to request that I inform you of her..”

Sadiq dai ya ba secretary dinshi mai suna Suzan strict warning akan tayi notifying dinshi a duk lokacin da wani ya zo ganin shi.. baya son mutane suna shigowa office dinshi anyhow ba tare da an sanar mishi ba.. it’s only the normal office etiquette and nothing else.

Sadiq wanda sai a wannan lokacin ya dago kanshi ne ya kula da Hanifa tsaye a bakin qofa.. har ga Allah banda don Suzan bai ma san ta shigo ba… babu shakka abinda yake yi ya dauke mishi hankali sossai!

STORY CONTINUES BELOW

“it’s okay Suzan, you can go”

Suzan ta wuce ta fita abinta yayinda Hanifa ta jefa mata harara.

Gani nayi ta dawo da kallonta kan shi.. As usual kyan nan nashi sai da ya taba zuciyarta. yau ma sanye yake cikin native na wani yadi Navy blue mai bala’in kyau.. he looked handsome, elegant and classy as usual.

Maimakon Sadiq yayi acknowledging presence din Hanifa sai gani nayi ya koma kan aikin da yake yi a Macbook dinshi.

Hanifa wadda take kallon shi sossai ta cika da mamaki.. Sossai ranta ya baci, ya zai wulaqanta ta haka?? ace ta shigo ofis dinshi amma don wulaqanci ya kasa acknowledging presence dinta.. Lallai ma gayen nan sai ya gane cewar babu mai taka ta ya zauna lafiya.

“Show some respect Sadiq.. incase ka manta, suna na Hanifa Aliyu Bugaje, the daughter of Alhaji Aliyu Bugaje the CEO of Bugaje industries… does that ring a bell to you??…”1

Qarasowa tayi cikin takunta na isa ta cigaba da fadin “…the last time I checked kamfanin nan na mahaifi na ne.. kuma kai ma’aikaci ne a wannan kamfanin don haka ko kana so ko baka so dole ne kayi respecting dina. Idan baka sani ba, I have the right to make Paapa fire you from this company don haka ka kiyaye ni”

Sadiq wanda yake sauraronta dai har a wannan lokacin bai ce komai ba.. he looked as if ma hankalin shi baya tare da ita a zahiri but then, he heard every single word that she uttered.

Gani nayi tana ta kai da komowa a ofis din tana bin ko ina da kallo.

Murmushin takaici tayi tace “I just can’t believe Paapa ya dauki wannan ofis din ya baka.. a common employee. Well, albishirin ka.. duk wannan zai canza as soon as I start working here. Infact ka kusa barin wannan ofis din ka koma wani so help you God idan ban sa an kore ka ba but be rest assured that your Secretary is going tunda batada kunya”

Dawowa tayi gaban executive table dinshi tace “Paapa yace in zo in karbi kudi a wurin ka.. so just give it to me”

For the first time tunda ta fara magana Sadiq ya dago kai ya kalle ta briefly yace “ki je ki rubuta request and forward it through Suzan, my secretary” daga nan ya maida kallon shi kan Macbook dinshi.

“what?? in rubuta request???” ta fashe da dariya sannan tace “a matsayin ka na wa?? lallai ma wuyan ka yayi kauri..”

Ta duqo tare da dafa table din tace “toh bari in fadi maka, wallahi baka isa ba.. baka isa ka sa ni inyi abinda banyi niyya ba don haka zan je inyi reporting dinka wurin Paapa.. I guess you don’t know who you are messing with” daga nan ta ja wani mugun tsaki ta juya ta fita abinta.

toh fa!1

***************

Hanifa ce zaune a ofis din Paapa tana ta cika tana batsewa.. tuni ta sanar da shi kalar wulaqancin da Sadiq yayi mata da kuma request da yace ta rubuta don kawai zata karbi kudi.

“…don wulaqanci Paapa saboda zan karbi kudi ta wurin shi shine zai ce sai na rubuta request?? ni da kudin mahaifina?? kudin shi ne?? ni kam bazan rubuta wani request ba kuma ka sa shi ya bani kudina tunda dai ba na baban shi bane…”

Paapa wanda ya sauke ajiyar zuciya ne yace “calm down Baby and do as he says.. it’s the new policy na kamfanin nan. A matsayin ki ta accountant, ina kika taba jin ana fitar da kudi haka nan ba tare da anyi accounting musu ba? kin fi kowa sanin abinda ake kira statement of account.. idan ana end of the month review ta ya kike so yayi presenting expenses da aka yi?? come on, stop making a mountain out of a mole hill please”

“and his secretary??”

“I cant fire her baby.. secretary din Sadiq ce, idan ba shi yace baya son aiki da ita ba I have no right.. it’s part of the company’s terms and conditions”

Hanifa dai ji tayi kamar ta mutu ganin yadda Paapa yake kwafsa mata.. yanzu kenan dole ne sai ta rubuta request din?? tunda take a rayuwarta bata taba samun wanda ya takura ma rayuwarta cikin qanqanin lokaci ba irin Sadiq.. suprisingly ma encounter dinsu babu yawa amma he seems to be everywhere around her.. tayi alqawarin sai ta wulaqanta shi.. he can’t get away with this!1

Paapa ne ya turo mata A4 paper da pen yace “go ahead Baby”

Zuciyarta tana quna ta rubuta request din.. Bayan ta gama ne Paapa yace “nawa ne kika yi requesting??”

“5million naira Paapa..” ta fada kai tsaye.

Girgiza kai yayi yace “okay then.. bari in kira secretary dina sai ta kai miki ofis dinshi”

Aikuwa hakan dai aka yi… Secretary din Paapa mai suna Tina ta kai request din Hanifa wurin Suzan wadda ta shiga mishi da shi.

Cikin qanqanin lokaci kuwa aka dawo mata da approval.

Hanifa wadda ta karbi approval din daga hannun Tina gani nayi ta kalli takardar yayinda ta zaro idanuwa.

‘2million naira approved’6

abinda ta ga ya rubuta kenan cikin rubutun shi mai bala’in kyau sannan yayi short note zuwa daya daga cikin accountants din kamfanin akan suyi crediting account dinta.

“what the hell..” ta fada tare da buga takardar a kan table din Paapa.

“meye kuma Baby??” Paapa wanda yake duba wasu files ya fada.

“Gaskiya Paapa na gaji.. wallahi bazan iya ba. Kawai ka zaba ko ni ko Sadiq.. ya za’ayi don wulaqanci ni da kudin mahaifina a nuna mun Gadara.. me zanyi da 2million naira Paapa. I clearly stated cewar 5million nake so akan wane dalili zai yi approving 2million.. ni gaskiya ban yarda ba”

Shi kam Paapa dama dai ya sani cewar Sadiq bazai taba approving 5million naira ba.

“Baby kiyi haquri kiyi managing 2million din.. kin san ana facing wasu ‘yan problems with production kuma already an riga anyi budget for the month shiyasa yayi hakan but I promise you next month zan sa yayi miki approving more money sai ki koma ki qarasa shopping din kin ji??”

Hanifa dai banda don Paapa da ya lallaba ta bazata taba amincewa ba.. tabbas Paapa is her weakness!!

Hawaye na bin fuskarta tace “shikenan Paapa.. amma wallahi if not for you I would have..”

“it’s okay Baby.. now go and get ready. kin dai san appointment letter dinki states that zaki fara aiki next week Monday ko??”

“Yes Paapa I know.. yanzu zan je inyi booking flight against tomorrow. I think Dubai kawai zan je inyi 2 days tunda ban samu kudin da nake so ba” ta fada cike da disappointment wanda Paapa ya kula da hakan amma ya basar.4

“okay Baby.. Allah ya kai ki ya dawo da ke lafiya”

tace “ameen”

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE