RAWANIN TSIYA CHAPTER 3 BY FADEELAH

RAWANIN TSIYA CHAPTER 3 BY FADEELAH

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Days later!!

BUGAJE INDUSTRIES

KANO-CENTRAL

A yau kwana uku kenan da Hanifa ta fara aiki a kamfanin mahaifinta.

Kamar dai yadda ta tsara, kwana biyu kawai tayi a Dubai. Sai da Paapa ya qara mata 1million naira saboda qorafin da ta dinga yi. Tayi shopping na kayan sawa masu kyau dukda babu yawa tunda kudin babu yawa.. Hanifa duk yawan kayan da take da su a closet dinta basu ishe ta ba.. kullum burin ta shine ta sa sabon kaya don haka ne kullum tana kan shopping.3

Hanifa ta so a bata ofis din Sadiq amma sam Paapa ya qi. Asali dai an bata wani ofis ne a kusa da na Sadiq din tunda dai she will be working in his department.

Paapa ya sa an gyara mata ofis din to her taste dukda dan qarami ne babu laifi an qawata shi da kayan zamani na gani na fada.

Hanifa dai tayi qorafi sossai wanda dai as usual da lallashi Paapan nata ya shawo kanta.

Kamar yadda Paapa ya buqata tayi aiki tare da Sadiq, ta amince. For now ta ajiye dream dinta a gefe, her immediate buri a yanzu shine ta wulaqanta Sadiq din.. she made it her personal mission to screw him a kamfanin.. ta tabbatar babu wanda baya da skeleton a closet dinshi don haka ta qudiri niyyan gano wani abu negative about him that she can use against him and finally idan ta kore shi then she can start working properly in ‘her Paapa’s Company’1

toh fa…

A kwana ukun da ta fara aiki a kamfanin sau daya ta ga Sadiq.. shima tana tsaye a floor dinsu ta hango shi yana fita daga kamfanin.. according to yadda ta ji ana production ne shiyasa almost all important heads na departments din kamfanin suka zama very busy… don haka shi da ita basu hadu one on one ba.

A cikin kwanaki ukun nan da ta fara aiki a kamfanin kuwa ta takura ma ma’aikatan kamfanin.. Hanifa dai komin tsufan mutum idan kayi mata ba daidai ba sai ta wulaqanta ka.. tunda ta zo kowa yake qoqarin yin taka tsan-tsan domin kuwa babu wanda ya shirya barin aiki a sanadiyyar ta.

A yau din dai bata shigo ofis ba sai wuraren qarfe Goma. Tana sane cewar lokacin zuwa aiki a kamfanin qarfe takwas ne kuma ta sani cewar akwai punishment for late coming.. infact babu wani rules and regulations na kamfanin da bata sani ba tunda an bata terms and condition of service na Kamfanin kuma ta karanta.

As usual dai tunda ta shigo ma’aikatan kamfanin suka dinga gaishe ta wanda ko kallo basu ishe ta ba.. tana tafe cikin isa da gadara (wai ita ‘yar mai kamfani)

Sanye take cikin wata Black stylish jumpsuit.. tayi masifar kyau a cikin kayan.. sai baza qamshi take yi. Bayan tayi signing-in ta wani e-machine ne tayi proceeding.

5

STORY CONTINUES BELOW

Sai kallonta ake yi saboda kyau da tayi.

Tana tsaye tana jiran elevator ya sauko qasa.. aikuwa ko da ya sauko ya bude Sadiq ta gani ya fito.. As usual sai da kyan nan nashi ya taba zuciyarta.

Yana ganinta kuwa ya kalli agogon hannun shi..

Past 10..

Hanifa ta danna mishi harara zata ratsa ta gefen shi ne ta ji yace “meyasa kika zo ofis late??”

“excuse me?” ta fada tare da tsayawa tana kallon shi a wulaqance.

“the next time da zaki zo ofis late ba tare da kin dauki excuse ba the HR will act accordingly.. be warned”1

Bai tsaya jiran abinda zata ce ba yayi tafiyar shi.

Hanifa wadda ta cika da haushi ne ta bi bayan shi da sauri.. A lokacin da ya kai tsakiyar hall din ne ya jiyo muryarta tana fadin “who do you think you are to tell me what not to do a kamfanin babana??”

Gaba daya kowa yayi tsit yayinda hankulan su suka dawo kansu.

Dama dai gaba dayan su ma’aikatan kamfanin sun san duk ranar da rigima ta shiga tsakanin Hanifa da Sadiq akwai matsala.. Sun sani cewar mutum ne wanda baya tolerating shit, sun sani cewar bazai yi tolerating wulaqancin Hanifa ba.. for the first time suna sa ran an samu wanda zai saita mata hankali without fear..

Nikuwa nace how so??? bayan dagaske dai kamafanin baban ta ne…2

“….Ni da kamfanin babana zaka zo ka fi ni iko? me ya ruwanka da lokacin da nake zuwa aiki.. kai nake yi ma aiki??? A total stranger ka zo kawai ka shishige ma Paapa, who knows ma qila jazz kayi mishi…” ta fada da qarfi yadda kowa zai ji.1

Gaba daya tension ya cika ma’aikatan ganin abinda yake faruwa.

Sadiq wanda ya juyo yana kallon ta ya jira har ta gama magana ne yace “are you done??”

“yes, akwai abinda zaka iya yi mun ne??”

Ji nayi yace “where is the Head HR??”

Musbahu wanda shine yake matsayin head HR na kamfanin ne yace “I am here Sir” Ya qaraso wurin Sadiq da sauri. Dama dai ya sauko qasa verifying wani report ne shine ya tarar da cakwakiyar Hanifa da Sadiq.

“According to the terms and condition of service, what’s the sanction for insubordination??”

“two weeks suspension Sir”

“Go ahead and issue the lady a two weeks Suspension”5

Tun kafin ya rufe baki ma’aikatan kamfanin suka zaro idanuwa cike da mamaki yayinda suke ta qus-qus.. su kam sun sani cewar Paapa yana ji da Sadiq a kamfanin toh amma kuma matsayin shi har ya kai ya ba ‘yarshi suspension???

Hanifa wadda ta ji abinda yace gani nayi fuskarta tayi displaying shock yayinda ta kasa magana.

“So yes… you are suspended for two weeks” ya fada yayinda ya kalle ta cikin ido.

Daga nan ya kalli kowa yace “everyone get back to work” ya juya ya nufi customer service office wanda dama can zai je.

Nan da nan kowa ya watse yayinda suke ta murna na yadda Sadiq yayi ma Hanifa.. ko banza ya rama musu wulaqancin da take yi musu.. but still dai suna jiye mishi abinda zai biyo baya knowing yadda Paapa yake ji da ‘yar tashi.

Hanifa wadda take tsaye still in shock gaba daya ta kasa motsi.. Gani nayi hawaye sun fara bin fuskar ta wanda tayi saurin gogewa.. Da sauri ta juya ta nufi hanyar ofis din Paapa wanda yake topmost floor.

A lokacin da ta shiga elevator ne na ga ta duqe qasa ta fashe da kuka.. the first time da wani yake wulaqanta ta a gaban mutane, the first time da wani unimportant person ya sanya ta zubar da hawaye.. how could she let that happen??1

STORY CONTINUES BELOW

Gani nayi ta miqe tsaye ta share hawayen ta sannan tace “yau sai dai Paapa ya zaba, ko ni ko shi”

**********************

Paapa wanda yake zaune a ofis dinshi yana waya da wani client dinshi daga qasar Uganda ne ya ganta ta shigo office dinshi a yamutse..

Ji nayi yace “I’ll call you back Mr. David”

Bayan ya kashe wayar ne na ga ya miqe tsaye da sauri ya zagayo yayinda ta rugo tare da rungume shi ta qara fashewa da kuka.

“Baby what happened?? meyasa kike kuka??? wani abu ya faru ne???” ya fada hankalin shi a tashe.

Cikin kuka tace “Paapa Sadiq ne..”

Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “me yayi miki??? zo mu zauna ki fadi mun abinda yayi miki..”

Daga nan ya ja ta zuwa mini lounge dinshi ya zaunar da ita sannan shima ya zauna a gefenta yace “I’m listening”

Daga nan kuwa ta fara bashi labarin dukkanin abinda ya faru tun daga farko har qarshe ba tare da ta qara ko ta rage a zancen ba..

One thing da Hanifa shine a rayuwarta bata qarya.. ko da ita ce batada gaskiya she always says the truth domin kuwa a cewarta tunda ta fi qarfin kowa babu amfani tayi qarya.. she will always get what she wants dukda sometimes she doesn’t idan har mahaifin nata ya bata rashin gaskiya.

Bayan ta gama ba Paapa labarin abinda ya faru ne na ga ya girgiza kai cike da disappointment..

Gyaran murya yayi yace “Baby”

tace “na’am Paapa”

“what you did was very wrong.. Sadiq ya fadi miki gaskiya ne ba wani abu ba.. coming late to work is very wrong kuma kin sani tunda kin karanta a terms and conditions of service. Again, da ya gyara miki me zai sa ki gaya mishi irin wadannan maganganun??? that was rude and disrespectful.. a tsarin kamfanin nan tabbas duk wanda yayi disrespecting superior dinshi dole ne a hukunta shi and kin ga yanzu a matsayin ki na ‘ya ta if you dont go on these 2 weeks suspension ma’aikatan kamfanin nan zasu ga kamar an nuna musu bambanci..”

“Yanzu Paapa kana supporting dinshi kenan?? yanzu shikenan duk abinda Sadiq yace ayi a kamfanin nan shi za’a yi?? why do I have a feeling kamar ka fi sonshi akai na??” ta fada tana kuka.

Paapa ya rungume ta tare da fadin “kiyi haquri Baby.. ba komai bane amma ina so ki sani babu abinda Sadiq yayi da zai sa in yi reprimanding dinshi.. kiyi haquri please kin ji, kiyi qoqari idan kin dawo kiyi adjusting saboda ku daina samun matsala.. ina so ki koyi aiki a wurin Sadiq ne because lokaci yana tafiya..”

Ni kuwa nace lokacin me???🤔

“and yes, matsayin ki ya fi na kowa a zuciya ta.. I just want you to be a good person please”

Hanifa dai a yanzu ta fara shawarar ko dai kawai tayi tendering resignation letter ta bar kamfanin ta huta tunda dai ta tsani ta bude idanuwa ta ga Sadiq and from the looks of it as long as tana aiki a kamfanin dole zata ganshi tunda dai da alamu Paapa baya da niyyan korar shi.. infact fadi yake yi ma he wants them to work together. Sai kuma ta ga lallai idan tayi resigning kamar ta ji tsoro ne ta kasa. it will be like tayi accepting defeat ne don haka she has to go and come back strong.. dole ne ta gano wani negative side din Sadiq tayi using dinshi against him… he definitely is not as perfect as he looks!6

Gani nayi ta share hawayen fuskar ta yayinda tace “shikenan Paapa..”

***************

Tun ma’aikatan kamfanin suna sa ran ganin Paapa yayi interfering a rigima Hanifa da Sadiq har suka gaji… the next thing dai sai ji suka yi ta karbi takardar suspension din kuma ta tafi… kenan Sadiq yayi winning.

For the first time an samu wanda yayi defeating Hanifa and for the first time an qara ganin Girma da muhimmancin Sadiq a kamfanin ya tabbatar ma mutane lallai yana da muhimmanci a wurin mamallakin kamfanin. Su kam har ga Allah sunyi farin cikin tafiyar Hanifa domin kuwa ko banza zasu huta har tsawon sati biyu. Dan kwana uku kawai da tayi a kamfanin sun ji jiki..

Abin mamaki shine lokacin da aka zauna Management meeting later in the day, Paapa da kanshi yayi commending Sadiq for a job well done akan suspension din da ya ba Hanifa a dalilin rashin kunyar da tayi mishi a matsayin shi na superior dinta… ya qara jaddada ma ma’aikatan kamfanin da suyi abiding by rules and regulations kamar yadda condition of service na kamfanin ya tsara domin kuwa tunda har za’a iya daukar mataki akan ‘yar mai kamfanin toh lallai babu wanda za’a barDays later+

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE

NASSARAWA GRA

A yau da daddare suna zaune a main dinning na gidan- Paapa, Mamy, Hafeez da Sadiq..

Tun bayan sallan Isha’i Sadiq ya zo gidan yayi dropping ma Paapa wani file a dalilin zai je Abuja washegari don haka bazai je ofis ba.

Paapa ne yayi insisting akan lallai ya zauna yayi dinner kafin ya tafi tunda dai ba mata gareshi ba balle ya sa ran idan ya koma gida zai tarar an dafa mishi abinci.

Da farko Sadiq ya dage akan bazai tsaya ba amma Paapa wasn’t ready to accept No for an answer don haka ne ya haqura ya zauna.

Luckily enough dama Hafeez ya dawo tun shekaran jiya and they had the opportunity to meet for the first time.. Kun san halin maza babu ruwansu.. tuni sunyi blending da juna.

A yanzu haka idan ka kalle su yadda suke cin abinci suna ta hira zaka rantse dama sun san juna.. though they share some things in common- personality, Harvard University, MBA- probably shiyasa sukayi saurin fahimtar juna.

Paapa da Mamy sun ji dadi sossai yadda suke hira suna sharing experiences dinsu..

“Kana nufin Professor Wilson yana nan???” Sadiq ya tambaya cike da mamaki

“wallahi yana nan” Hafeez ya fada yana dariya.

“I swear mutuminnan yana son boko.. dukda ya tsufa bazai je ya huta ba? na tuno lokacin fa da qyar yake tafiya.. that was 6 years ago”

“aikuwa yana nan.. a hakan yake lectures”

“But he is very good.. gaskiya duk wadanda suka samu privilege na zama students dinshi should consider themselves lucky.. he is a great mentor”

“Oh yes i agree with you.. I think shiyasa ma Harvard suka riqe shi” Hafeez ya fada yana murmushi.

“So tell me, yanzu da ka gama meye plans dinka??” Sadiq ya tambaye shi.

“For now gaskiya nothing saboda ina so qwalwata ta huta…”

Tun kafin Hafeez ya qarasa magana ne Sadiq ya kalli Paapa yace “Sir, I disagree with this. ina ganin yakamata ya fara aiki a Bugaje Industries ASAP.. shine perfect mutumin da yakamata yayi replacing dina..”

ni kuwa nace what?? replacing kuma??

Paapa yace “ai dama wannan yana daga cikin burina.. Hafeez da Hanifa suyi aiki a kamfani na. But tunda ka kusa tafiya I think Hafeez should still join and idan ka gama coaching Yahaya shi kuma sai yayi coaching dinsu”

“Okay Sir”

Hafeez wanda yake sauraron su ne yace “ikon Allah… You people are deciding for me when I am seated right here..”

Paapa wanda yake murmushi yace “ai tun kana qarami na sani cewar duk decisions din da nayi taking akanka baka bijirewa and I am sure this won’t be an exception.. one of the reasons why I so much like you Son. Burina dama shine da kai da Hanifa kuyi taking over idan kun gama karatu.. it’s good kun dawo kafin Sadiq ya tafi atleast zaku koyi one or two things and afterwards Yahya zai qarasa muku so it’s a yes from me” ya kalli Mamy yace “You?”

Murmushi tayi sannan tace “Yes from me too.. Allah ya saka da alkhairi”

“A big YES from me too..” Sadiq ya fada yana murmushi harda kashe ma Hafeez ido daya.

STORY CONTINUES BELOW

Hafeez dai murmushi kawai yayi yace “toh ya zanyi.. Allah ya bani ikon riqe kujerar da za’a bani cikin amana”

Gaba daya suka amsa da ‘ameen’

Qamshin turarenta ne ya bugi hancin su..

2

Hanifa ce take saukowa daga stairs din yayinda take jiyo hirar su.. baquwar muryar da ta ji in-between ne ya sa tayi pause tana sauraron hirar tasu.

Ta gane cewar Sadiq ne.. Dukda ta tsane shi bazata taba jin muryarshi ta kasa ganewa ba- muryar shi mai bala’in tsada da dadin sauraro.

Ko da ta qaraso Dinning din gaba dayan su kallonta suke yi banda Sadiq wanda tun tana shigowa da ya san ita ce ya kawar da kanshi… wayarshi ma ya dauka yana latsawa.

Allah ya sani rashin acknowledging presence dinta da Sadiq yake yi yana bata mata rai sossai.. ita kanta ta rasa dalili. Yanzu haka da ta shigo dinning din ta san cewar ya sani sarai ita ce amma ko ya dago ya kalle ta.. wato yana nufin bata kai matsayin da zai kalle ta ba kenan???4

“Baby ina zaki je ne haka na ga kin ci gayu?”

Cikin shagwaba tace “Paapa wallahi Chocolates dina ne suka qare shine nake so in je Shoprite in siya”

“Da daren nan Baby?? ki rubuta ki ba driver kawai ya siyo miki mana”

“No Paapa.. ina so in dan sha iska ne tunda ‘yan baqin ciki sun hana ni watayawa” ta qarasa fada tare da hararar Sadiq wanda ko gani bai yi ba balle ya dame shi. Kai infact bai ma san me take fadi ba tunda dai da zarar ta fara magana yake dauke hankalin shi gaba daya daga kanta.. Kai shi fa her presence disgusts him completely. Yanzu haka banda don kar abin ya zama obvious he would have been on his way out of the house.5

Paapa ya sani sarai da Sadiq take yi kuma bai ji dadin hakan ba..

“Baki ga Sadiq bane Baby??? won’t you greet him?”

“Na gan shi Paapa.. ko na gaishe shi baya amsawa..”

“and where did you get the idea na cewar bazai amsa ba?? this is very bad baby..”

“sorry Paapa” ta fada still ba tare da ta gaida Sadiq ba.

Hafeez wanda yake mamakin halin Hanifa ne ya kalli Sadiq wanda yake latsa wayar shi sannan ya dan yi leaning towards him yace “it’s like you guys already have something going on kenan..”

Sadiq wanda bai fahimce shi bane yace “sorry??”

Kafin Hafeez yayi magana ne suka ji tace “Oh my God.. na manta da waya na da hand bag dina a sama kuma wallahi I can’t go back”

STORY CONTINUES BELOW

A wannan lokacin ne na ga Sadiq ya daga kai ya kalle ta… da alama dai ya ji abinda ta fada this time.

Bell din da ke kan dinning din ta danna wanda ko seconds ashirin ba’a yi ba daya daga cikin masu aikin ta shigo da sauri.

“Je ki dauko mun waya na da hand bag dina a dakina”

“toh Anty..” ta fada.

Gani nayi Hanifa ta nufi empty seat wadda take nesa da ta Sadiq ta zauna. da alama dai zaman jiran mai aikin take yi.

A daidai lokacin ne wayar Paapa tayi ringing yayinda ya miqe yace “excuse me please”

Hafeez ne yace “go ahead Paapa”

Bayan Paapa ya fita ne mai aikin ta dawo.. Har qasa ta russuna ta miqa ma Hanifa Jakarta da wayarta.. As usual dai a wulaqance Hanifa ta miqa hannu zata karba and unfortunately for the maid kuma ashe Hanifa bata kai ga riqe handle na jakar ba kawai sai jakar ta fadi a qasa.

Da sauri mai aikin ta duqa ta dauki jakar tare da fadin “yi haquri Anty…”

Kafin ta rufe bakinta kuwa ta ji saukar wani mugun mari wanda har ya sanya ta saki ihu tare da zubewa qasa.1

“dan uban ki jaka ta kika yar a qasa??? kin san nawa take?? kin kuwa sani cewar jakar nan ta fi ki daraja…”

“hey” ta jiyo muryar shi cikin fada wanda har ta razana yayinda ta dago kai ta gan shi yana approaching wurinsu.

Sadiq!!!

“are you stupid???” ya fada yayinda ya qaraso wurin su.2

Mamy da Hafeez were shocked for few seconds and daga baya sai na ga fuskokin su sunyi displaying farin ciki.. da alama dai sun ji dadin tsawar da Sadiq yayi mata… ko banza for the first time za’a samu wanda zai taka ma Hanifa birki akan rashin mutuncin da take yi.2

Paapa wanda yake tsaye kan hanyar shigowa dinning din ya ga komai da ya faru.. Sossai hankalin shi yake a tashe ganin yadda Hanifa ta mari Maid din.. ba sai an fada ba, He is so disappointed at what he just saw. Dama dagaske rashin mutuncin da take yi kenan a bayan idanuwan shi?? a yadda ta mari mai aikin ya tabbatar it’s not the first time da hakan yake faruwa because she did it confidently. Kenan abinda Mamy take fadi tun tuni akan Hanifa dagaske ne???

Ita dai mai aikin hankalinta a matuqar tashe yake ganin anyi ma Hanifa tsawa saboda ita.. ta sani cewar lallai zamanta a gidan ya qare..

“akan wane dalili zaki mare ta saboda wata jakar ki ta banza that mistakenly fell thanks to you?? akan wane dalili zaki bude baki ki ce your stupid handbag ta fi dan adam daraja??? saboda ‘yar aiki ce?? Banda rashin hankali irin naki ba Allah ne ya halicce mu gaba daya ba?? is it her fault that she was born into a poor family da har ya sanya ta zo qarqashin ki tana aiki?? You are lucky cewar ke ba qanwa ta bace.. da sai na zabga miki marin da ya fi wanda kika yi mata, that way you will feel what she is feeling right now…”5

Ya nuna ta da yatsa ya cigaba da fadin “…let me tell you this for the very first and last time.. idan kika kuskura kika qara wulaqanta wani in my presence I swear you will regret it for the rest of your life..”

Paapa wanda yake tsaye yana sauraron kalaman Sadiq ne na ga yana girgiza kai alamar he is impressed by how Sadiq just handled the issue..

STORY CONTINUES BELOW

Hanifa wadda take kallon Sadiq hawaye na bin fuskarta gaba daya mamaki ne ya cika ta yayinda ta kasa motsi.. the first time da wani ya daga mata murya ta kasa yin komai shima a dalilin ‘yar aiki wadda bata dauka a bakin komai ba… Kalaman Sadiq sune suke yawo a cikin qwalwarta yayinda jikinta yake ta rawa. She could only stand there and watch him like a statue.

Ran shi a bace ya kalli mai aikin yace “tashi ki koma workstation dinki… kiyi haquri”

Jiki a sanyaye ta miqe ta fita abinta.

Gani nayi ya dawo wurin dinning table ya kwashe wayoyin shi da makullin motar shi wanda a nan ya ga Paapa a tsaye yana kallon su.

Without any remorse na abinda yayi ne yace “Sir, Ni zan tafi… good night. Idan na isa Abuja zan kira ka”

Paapa yayi murmushi yace “toh Son, thank you very much for everything.. Allah ya kiyaye hanya”

“Ameen” ya fada tare da kallon Mamy yace “Good night Ma”

Mamy wadda tayi murmushi ce tace “sai da safe Sadiq, Allah ya kiyaye hanya”

“Ameen nagode”

Hafeez ne ya miqe yace “bari in raka ka..”

“Thanks Hafeez”

Bayan Hafeez da Sadiq sun fita ne Hanifa wadda take ta zubar da hawaye ta kalli Paapa cike da mamaki.. Ya za’ayi wani ya gaya mata maganganu a gaban shi amma bai ce komai ba??

“Paapa???” ta kira sunan shi tana kuka.

Paapa wanda ya nufi kujerar shi ya zauna ne yace “Yes Baby”

“Baka ga abinda Sadiq yayi mun ba?? ihu yayi mun fa kuma baka yi interfering ba”

“Na gani Baby… Sadiq is just like an older brother to you kuma don yayi miki fada akan laifin da kika yi it’s not a big deal.. i am shocked and disappointed at what you did. Ni ban yi miki tarbiyar da zaki dinga wulaqanta mutane ba. I still cant believe what you did…”

Cike da mamaki Hanifa take kallon Paapa.. what is wrong with him??? kenan Sadiq asiri yayi mishi ko me???

Fashewa tayi da kuka tace “Paapa ka daina sona ne?? ka fi son Sadiq a kaina???”

Mamy dai shiru tayi ta zuba musu idanuwa as usual.. ita kam komai ma da ya faru yayi mata dadi.3

Gani nayi Paapa ya miqe ya nufi wurin Hanifa ya janyo ta jikin shi ya rungume ta yace “I love you very much Baby kuma na san kin san wannan amma it’s high time ki girma ki natsu sannan ki fahimci rayuwa.. what you did was absolutely wrong.. I never trained you to belittle anyone in this life, please and please ki daina wulaqanta mutane. Let this be last time da zan ga kin yi abu makamancin hakan. Please let this not happen again.. and if it does, I am afraid ni da ke bazamu shirya ba…”

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Tsaye suke a jikin motar Sadiq yayinda suke exchanging numbers.

Bayan sun gama ne Hafeez yace “what you did back there inside the house na rantse maka da Allah babu wanda ya taba yi.. ka kyauta da kayi mata hakan. I swear idan ka ga yadda take treating mutane sai ka riqe baki”

Sadiq wanda yayi murmushi yace “I am a living witness to that Hafeez..”

“Ya salaam, kenan dai ta karta maka rashin mutuncin nata”

“sossai…”

“please tell me.. me tayi maka??”

Da farko Sadiq yayi hesitating bashi labari don kuwa hakan is not in his character infact shi magana ma wahala take yi mishi.. but da Hafeez ya nace sai ya bashi labarin last encounter dinsu briefly.. encounter dinsu wanda ya janyo har ya sa aka bata suspension.

Hafeez yana kwasar dariya yace “da kyau bro, kayi mun daidai. Na ga alama kai ne zaka iya yi mana maganin ta plus na ga kamar Paapa ya ji dadin yadda kayi handling dinta.. I am sure you will do well wurin saita mana ita”2

Sadiq ya girgiza kai yana murmushi yace “I dont have her time bro.. ko alama bana so in bude idanuwa na ma in ganta a kusa da ni balle har wani abu ya hada ni da ita. I hate girls like her. I just can’t wait to finish what I am doing here and go far away from her drama..”

“ka je ina?? na ji kai da Paapa kuna maganar ayi training dinmu saboda kai zaka tafi.. ban gane ba, kana nufin kai ba permanent employee bane???” Hafeez ya tambayeshi confusedly.

Murmushi Sadiq yayi yace “let’s leave this for another day bro, yanzu dai dare yana yi.. bari in je in qarasa packing kayana.. flight dina da sassafe ne”

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Hanifa wadda ta shiga daki ranta a bace straight bisa gadonta ta fada yayinda ta shiga rera kuka kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa.

Cikin kukan ne na ji tace “wallahi bazan qyale ka ba… Sadiq, You will pay for what you did to me. Tun da ka shigo rayuwa ta kasa Paapa yana ganin laifi na akan komai. Gaba daya ya daina bani upper hand. Nobody ever came close to doing what you are doing to me right now and it has to stop. Allah ya kai mu in koma ofis sai na takura ma rayuwarka, sai na fitine ka in such a way that da kanka idan ka gaji zaka yi resigning.. I promise to find out about your darkest secret don kuwa na san kana da shi.. I will use it against you. Sai na wulaqanta ka yadda har abada bazaka so ka qara haduwa da mai suna Hanifa ba..”7

toh fa!!

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE