RAWANIN TSIYA CHAPTER 4 BY FADEELAH

RAWANIN TSIYA CHAPTER 4 BY FADEELAH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

BUGAJE INDUSTRIES

KANO CENTRAL+

Cikin satin nan Hanifa ta koma aiki a kamfanin mahaifin nata yayinda Hafeez shima ya fara aiki a kamfanin.

Both Hafeez da Hanifa suna aiki tare da Sadiq ne. Kamar yadda office din Hanifa yake kusa da na Sadiq haka shima ofis din Hafeez yana kusa da nasu.

Asali dai tunda Hanifa ta dawo ko sau daya Sadiq bai nemi tayi mishi wani aiki ba.. haka itama bata nemi ya koya mata wani abu ba.. Gashi dama tun ranar da yayi mata fada take ji kamar ta shaqe shi ya mutu ta huta.

Tun da ta dawo tayi dedicating time dinta trying to find out information about him wanda har yanzu babu sa’a.

Hatta HR ta je neman personal info dinshi amma bata samu ba a dalilin komai yana computer din Musbahu (head HR) and she couldn’t get access for now.

Shi kuwa Hafeez tunda ya fara aiki a kamfanin, a ofis din Sadiq yake yini suna aiki tare..

Hafeez dai sossai ya mayar da hankali akan aikin dayake yana da qwalwa tuni yayi picking….

Ya rage ma Sadiq aiki sossai.. A da sai Sadiq ya yini yana aiki, baya samun time din hutawa balle ya dan rage aikin project na Online course dinshi da yake yi amma yanzu he gets enough time to even handle stuffs outside of the company…

☆☆☆☆☆☆☆

A yau Thursday Zaune suke a lounge na ofis din Sadiq wuraren qarfe biyu na rana.. basu dade da dawowa daga Sallar Azahar ba- Sadiq, Hafeez, Yahaya da Musbahu yayinda suke tattaunawa akan Bonus da compensation da za’a biya month-end da kuma production expenses da za’a yi next month (more like a budget)

Paapa ne ya qwanqwaso qofar ya shigo. Cike da girmamawa duk suka miqe yayinda yace “please sit”

Gaba dayan su suka zauna.

“where is Hanifa??” yayi tambaya

“tana ofis dinta” Hafeez ya fada kai tsaye

“Why is she not part of the meeting?”

Gaba dayan su dai shiru sukayi.. he expected that anyway.

“Hafeez je ka kira ta”

“toh Paapa” ya fada yayinda ya miqe da sauri ya fita.

Gani nayi Paapa ya samu kujera ya zauna..

After 2 minutes ne Hafeez ya shigo cikin sallama with Hanifa trailing behind him.

Tun kafin ta daidaita tsayuwarta ta ji Paapan nata yace “Baby meyasa kika zauna a ofis dinki bayan ana meeting anan? are you not a part of the meeting?? aren’t you aware??”2

Hanifa wadda tayi mamakin tone din Paapa da yadda ya daure fuska yana mata magana ne ta bi ta rude.. tabbas idan tace bata sani ba qarya take yi domin kuwa duk wani meeting din da ake yi ana notifying ta Google calendar and anyi this time don haka she cant lie cewar bata gani ba..

Gani nayi ta daga kai ta kalli Sadiq wanda yake duba wani file da yake hannun shi yayinda ta kalli su Musbahu wadanda duk ita suke kallo.

“uhm Paapa dama yanzu zan shigo.. I was tidying up some things ne”

Paapa ya miqe tsaye yace “daga yau idan har ana meeting kuma an gayyace ki duk abinda kike yi ki bar shi kiyi attending meeting.. now join them”

“okay Paapa” ta fada a sanyaye yayinda ta nufi kujera da take nesa da ta Sadiq ta zauna.

STORY CONTINUES BELOW

Paapa ya kalli Sadiq yace “Son, ina da appointment da Mr. Lukman yanzu so I will be stepping out for a while”

“Okay Sir, sai ka dawo.. all the best”

“thank you” Paapa ya fada harda sakin murmushi wanda Hanifa ta kula.

Wato dai Sadiq ya qwace mata faada a wurin Mahaifinta gaba daya.. Yanzu ya daure mata fuska just because she didn’t come for a meeting amma gashi yana ta yi ma Sadiq murmushi.. Like seriously??? lallai dole ne ta tashi tsaye.1

Paapa yana fita suka cigaba da tattaunawa.

Hanifa wadda tayi shiru tana sauraron su sai satar kallon shi takeyi..

Mai karatu Hanifa dai ta tsani Sadiq amma kuma wani ikon Allah bata missing chance na kallon shi a dalilin kyan nan nashi..6

Sanye yake cikin tsadadden off white yadi mai kyan gaske wanda ya sha dinkin zamani very simple… Abinda ta kula da shi yana son sa Native. ko don ya san suna mishi kyau ne.. oho!! but ai ranar da ta fara ganin shi a Airport da qananan kaya da gan shi kuma sun bala’in yi mishi kyau..

Hahaha.. ke dai kika sani!3

Wayar shi ce da tayi ringing ta fargar da ita.. ajiyar zuciya ta saki yayinda ta ji haushin yadda kyan Sadiq yake ruda ta har yake dauke mata hankali..

Gani nayi ya duba fuskar wayar sannan yace “please let me take this call.. its important”

Musbahu ne yace “go ahead Sir”

Ko da ya amsa wayar ne na ji yace “Good day Mr. Kingsley”

Shiru yayi sannan yace “okay I will look for the receipt and bring it to you but it may not be today coz I dont even know where I kept it..”

Murmushi yayi sannan yace “okay then.. thank you bye”

Daga nan ya kashe wayar suka cigaba.

Haka dai Hanifa ta cigaba da sauraron su yayinda take ta satar kallon shi wanda har suka gama bata ce komai ba..

A dan zaman da tayi yanzu ta fahimci lallai Sadiq ya ilimantu.. he is intelligent, smart and from the way he speaks you could tell that he is a very great business man. she definitely can never beat him on that!

Sadiq yayi assigning kowa task dinshi wanda yake expecting feedback from them first thing tomorrow morning amma fa banda Hanifa.. infact he made her look like a ghost a wurin.

Haka kawai ta ji ranta ya baci.. wato ta zo ta zauna a banza kenan. he didn’t acknowledge her presence as usual.. tabbas ba son yi mishi aiki take yi ba amma if she let this go ai ya wulaqanta ta kenan..1

Gaba dayan su sun miqe tsaye ne suka jiyo muryarta tana fadin “Ni meye task dina?? kuna nufin na zo na zauna a banza kenan ko me?? ko ban isa a bani task bane ni da kamfanin mahaifi na”1

Sadiq dai as usual ko kallon ta bai yi ba balle ya amsa ta… Wucewa yayi wurin executive table dinshi ya zauna wanda hakan ya qara bata ma Hanifa rai.

Da sauri Yahaya yace “Ms Hanifa you can handle the compensation and bonus.. idan Mr. Musbahu yayi compiling list of staff din zai baki sai ki fara aiki. I and Hafeez will work on the production expenses for next month”

Hanifa wadda ta cika da bacin rai bata ce komai ba ta dauki wayarta ta wuce ta fita yayinda Yahaya da Musbahu suka girgiza kai suka bi bayanta suka fita.

Hafeez ya dawo gaban table din Sadiq yace “I swear Hanifa case ce”

Sadiq wanda yake kallon mac book dinshi yace “she is no case Hafeez.. people like her suna buqatar discipline ne. she is just a confused spoilt brat wadda ta dauki duniya da fadi”

STORY CONTINUES BELOW

“tunda ka gane irin halin ta kawai Paapa ya baka ita ka aura mana sai ka gyara mana…”6

Bai qarasa magana bane yayi shiru a dalilin wani kallo da Sadiq yayi mishi.

“Sorry sorry.. just kidding” Ya fada tare da surrendering hannuwan shi biyu.

“To change the topic, me zaka ci for lunch??? are you ordering or going out??”

Sadiq wanda ya kalli agogo yace “Now you are talking.. Kamar ka san yunwa nake ji wallahi.. Sakwara nake son ci but bazan iya zuwa ba.. maybe I will just order”

“Kar ka damu I’ll order for both of us..”

“thanks bro, and please dont forget the…”

“…farfesun kayan ciki…” Hafeez ya qarasa mishi yana dariya.

“Yes please.. thanks Bro” ya fada shima yana dariya.

A dan zaman da Sadiq da Hafeez suka yi sun saba da juna sossai. Hafeez ya san duk wani abu da Sadiq yake so da wanda baya so.. dukda Sadiq ya girmi Hafeez da shekara shidda, they still behave like age group dinsu daya.. this alone shows how simple Sadiq is!

☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!!

A yau Friday wuraren qarfe Goma sha biyu na rana ne na ga Hanifa ta fito daga ofis dinta riqe da wani file yayinda ranta yake a bace..

Ji nayi tana fadin “don wulaqanci ma File din sai an kai mishi.. ina matsayin ‘yar mai kamfanin nan amma bani da Secretary sai shi wanda ba kowa ba an bashi babban ofis sannan harda secretary and they are making me work under him.. mtseeew”

A yau dai tun da safe su Hafeez suka yi submitting aikin da Sadiq ya basu amma Hanifa sai yanzu qarfe Goma sha biyu shine ta ga daman submitting nata.. abin mamaki kuma tun jiya ta gama amma saboda Gadara da son nuna ma Sadiq cewar abinda ta ga dama shi zata yi shiyasa ta qi submitting a lokacin da ya buqata.

Haka dai tana tafe tana ta masifa ita kadai.. A lokacin da ta iso ofis din Sadiq ta tarar Suzan bata nan.. da alama she stepped out ne don haka dole ta shiga ta bashi da kanta.

Tsaki ta ja sannan tace “I will have to see his ugly face kenan…”4

Ni kuwa nace kin tabbata ugly ne??!!

As usual shiga tayi kai tsaye ba tare da tayi knocking ba..

Gani nayi ta tsaya cak yayinda ta ja numfashi a dalilin asirtaccen qamshin nan da ya bugi hancinta- Qamshin shi da na office dinshi

Abin mamaki shine duk qamshin da ofis dinta yake yi bai kai sanyin irin wanda na Sadiq yake yi ba.. why??

Gani nayi ta bi ko’ina na ofis din da ido bata gan shi ba..

“ina yake toh?” na ji ta fada

Tsaki tayi ta nufi table dinshi zata ajiye file din.. Aikuwa tana ajiyewa idanuwan ta suka kai kan wani receipt..

Hannu ta sa ta janyo tana dubawa…

Receipt ne na Bristol Palace Hotel.. Ko da tayi scanning receipt din ta ga payment na accommodation har Naira miliyan Goma sha shidda da dubu dari tara da ashirin da takwas.. da sauri ta duba sunan wanda yayi reserving sai ta ga ABUBAKAR SADIQ BUNZA.

Ji nayi tace “aha, I said it. Yau Allah ya kama shi.. ni dama na san cewar there is something off about this guy.. ashe barawo ne! yau kam qarshen zaman ka a kamfanin nan ya zo don wallahi sai nayi exposing dinka”1

toh fa!1

Hannun ta yana rawa na ga tayi snapping receipt din da wayarta tana fadin “kana kwashe kudin mahaifina kana kashewa a banza sannan ni a matsayina na ‘yar shi kana hana mun.. zaka gane baka da wayau”

STORY CONTINUES BELOW

Aikuwa tana rufe bakinta ne ta ji qarar qofa wanda ya sa ta zabura da sauri kamar dai yadda marassa gaskiya suke yi.

Sadiq ne ya fito daga kewayen ofis din nashi yayinda yake gyara sleeves na kaftan dinshi.. da alama alwala yayi don kuwa gashin kanshi, hannuwan shi da fuskar shi sun tabbatar da hakan.

Ba tare da yace mata komai ba ya nufi centre table na qaramin lounge dinshi ya dauki hular shi da key din mota sannan ya juya ya fita..

He didn’t acknowledge her presence again.. even in his office??2

Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “lallai wannan gayen dan wulaqanci ne.. am I invisible to him that he will just walk past me ba tare da yayi mun magana ba?? yana nufin bai gan ni bane ko me??”

Murmushi tayi tace “zaka gane baka da wayau.. bari in je Bristol in binciko ka tukunna.. idan nayi gathering proof dina zamu hadu da kai a Management meeting.. that will be the perfect place to expose you”

A lokacin da ta fito daga ofis dinshi ta tarar da Suzan zaune a workstation dinta yayinda ta hango Sadiq tare da Hafeez zasu shiga lift.. da alama masallaci zasu je.

Suzan tana gaishe ta amma sam bata ji ba.. dama dai ko da ta ji bazata amsa ba saboda kamar yadda ta tsani ogan nata itama haka ta tsane ta.

☆☆☆☆☆☆☆☆

BRISTOL PALACE HOTEL

NASSARAWA-KANO

Bristol hotel ya kasance one of the most expensive hotels a garin Kano.. duk wani mai hannu da shuni nan yake sauka. From the exterior to interior view na hotel din, 100% on point.

Wuraren qarfe biyu saura ne Driver ya kawo Hanifa Hotel din.. As usual driver ne yake kai ta duk inda zata je, Ba wai don bata iya tuqi ba, kawai don bata son yin tuqin.. a cewarta wai a matsayinta bai kamata tana wahalar da kanta tana tuqa mota when she can own a driver that can drive her wherever..

Hanifa wadda take sanye cikin wata plain burgundy material gown tayi masifar kyau.. Tunda ta fito daga mota ake ta kallonta musamman maza.. she shouldn’t be seen in these kinds of places amma kuma ya zata yi??? idan dai tana so tayi exposing Sadiq she has to get the proof that she needs.

1

Glasses dinta na ga ta fiddo ta sanya sannan ta shiga cikin hotel din.

Kai tsaye wurin receptionist ta nufa tare da tamabayarta ofis din Manager. Allah ya taimake ta Manager din was free to see visitors at the moment don haka ne aka yi directing dinta.

Zaune yake a kan kujerar shi yana magana a waya lokacin da Hanifa ta shiga. Gani nayi ya nuna Mata wurin zama da hannun shi yayinda yake qoqarin kammala maganar da yake yi a wayar.

“ah okay, we will have to call a technician to check on it ASAP… thank you”

Bayan ya kashe ne ya kalli Hanifa cike da fara’a yace “Mr. Kingsley, Manager of Bristol Palace Hotel.. how may I help you miss?”

“thank you Mr. Kingsley, My name is Hanifa Aliyu Bugaje”

“you mean the daughter of Alhaji Aliyu the CEO of Bugaje industries??”

Murmushin jin dadi Hanifa tayi tace “Yes, this is she”

“Nice to meet you ma’am.. we had a great business deal with your Dad’s company.. he is a great man I must say. how may I help you?”

Hanifa ta ji dadin jin hakan domin kuwa ta san zata samu information din da take so cikin sauqi tunda dai ta san ba’a disclosing personal details na mutane haka kawai to strangers.

“I am here to enquire about one of your guests… he goes by the name Abubakar Sadiq Bunza”

Tun kafin Hanifa ta rufe baki ta ga Mr. Kingsley yayi murmushi sannan yace “Mr Bunza is a very special guest in this hotel.. is he a relative?”

“uhm yes, I just saw a receipt of over N16.9m for accommodation and wanted to confirm if…”

“Oh the receipt?? actually he already made a six-month payment for accommodation and since there are days he travelled, we had to request and retrieve the initial receipt issued to him so we can start the arrangement to make the necessary deductions and re-fund him, he sent you to bring the receipt??”2

“ah No, not really”

“Okay”

“So he has been staying here for quite a while now??”

“Yes, getting to 5months actually. he stays at a deluxe suite which costs N92,000 per night. it’s just a month left for him now”2

Hanifa wadda ta cika da mamaki kasa magana ma tayi… Ajiyar zuciya ta saki a ranta tace “wato kudin Paapa yake amfani da su yana sharholiyar shi a cikin hotel ko???”

“Ms Bugaje I can’t tell you more because this is highly confidential.. it’s due to the familiarity that I am even telling you this.. so If you don’t mind…”

“Dont worry Mr Kingsley, I wont ask further questions.. thank you very much” Hanifa ta fada yayinda ta miqe tsaye.

Shima miqewa yayi yace “you are most welcome ma’am.. regards to your Dad please”

“Sure”

Ko da Hanifa ta fito daga hotel din gani nayi tana ta murmushi yayinda na ji tace “well, well, well Mr Sadiq.. Your game is over, Finally na gano abinda kake yi and I am sure with what I have, ba korar ka kawai zan sa ayi ba.. you are going straight to jail”8

BUGAJE INDUSTRIES

KANO- CENTRAL+

Zaune suke a conference room wuraren qarfe hudu da rabi na yamma.

Paapa, Hafeez, Hanifa da Unit heads na Comapny din..

Sadiq ne ya shigo yana fadin “sorry for keeping you waiting.. Clients din namu ne sai ahankali”

Hanifa wadda take zaune kusa da Paapa ce da danna mishi harara yayinda sauran heads din suke fadin “it’s okay Sir”

Paapa ya nuna mishi kujera wadda take opposite ta Hanifa yace “ai ni na so kawai ayi forfeiting deal din tunda na ga murdaddun mutane ne.. were you able to convince them in the end???”

“Yes Sir..”

“Well done Son..”

“Thank you Sir” ya fada tare da zama kan kujera

Gyaran murya Paapa yayi sannan ya kalli Hanifa yace “toh Baby, tell us why you called for this emergency meeting”

Cike da mamaki na ga Sadiq ya kalli Paapa sannan ya kalli Hanifa wadda itama shi take kallo..2

Wai dama ita ta kira meeting din? for what??

Hanifa wadda ta miqe tsaye ce tace “dama ina so in fadi muku cewar Sadiq is not who you all think he is..”

Gaba daya aka ce “what??”

Paapa wanda yake kallon Hanifa cike da mamaki yace “Baby me kike fadi haka??”

Gani nayi Sadiq yana ta shafa kanshi da hannuwan shi biyu non-stop.. da alama baya son inda zancen Hanifa yake zuwa.. He knows cewar whatever it is, it has to do with receipt na Bristol da ta gani a ofis dinshi dazu.

hmmmm…

“Yes Paapa.. Sadiq sata yake yi maka a kamfanin nan”

Tun kafin ta rufe baki kowa ya cika da mamaki yayinda na ji wasu suna fadin “subhanalillah” wasu kuma suna fadin “what??” yayinda saura suke ta qus-qus…1

Sadiq dai a wannan karon duqar da kan shi kawai yayi cike da haushi da takaicin abinda Hanifa ta fada..

A ran shi kuwa fadi yake yi “this garl must be very stupid”2

Paapa wanda shima ranshi yake a bace ne yace “Ke Hanifa lafiyar ki kuwa??? akan wane dalili zaki tara mu ki ci ma Sadiq fuska?? how can you accuse him of stealing?? shin kin san ko waye Sadiq kuwa??”

“ofcourse na sani Paapa, Abubakar Sadiq Bunza is a thief” ta fiddo copies da tayi na receipt din Bristol ta miqa ma Paapa sannan ta miqa ma Head of Marketting wanda yake zaune a gefen ta shima ya gani sannan yayi passing round.

“Sadiq ya saci kudi har N16.9m daga kamfanin nan ya biya kudin accomodation a Bristol Palace Hotel.. Shin salary dinshi har ya kai ya mallaki irin wannan kudaden?? what is he doing in a luxurious hotel anyway??? aaaah, No wonder ya karbi position din Finance Manager ya hana komai motsi.. sai da authorisation dinshi za’a iya fitar da kudi meanwhile yana kwasan kudi yana kashewa ba tare da an sani ba plus…..”

“Shut up Hanifa…” Paapa ya dakatar da ita cikin fada yayinda na ga ta kalle shi cike da tsananin mamaki.

“Kina da hankali zaki zo cikin mutane kiyi ma Sadiq cin mutunci irin wannan?? dama kin fara aiki a kamfanin nan saboda ki sa mishi ido ne? da kika gano all these me ya hana ki zuwa wurina direct ki gaya mun?? do you have to come here and defame him??”

STORY CONTINUES BELOW

Tunda Paapa ya fara magana Hanifa ta daskare.. shin me Papa yake fadi?? asiri kenan Sadiq yayi mishi?? how can someone steal money from you sannan ga evidence nan and you still try to defend him??

“Toh yau zan fadi muku asali ko waye Sadiq” Paapa ya fada rai a bace.2

Sadiq ne yayi saurin fadin “Please Sir, you don’t have to.. mu bar maganan haka nan”

“No Son.. I told you tun farko muyi reconciling issue dinnan amma ka qi.. I think lokaci yayi da yakamata kowa ya san abinda yake faruwa”

Gani nayi Sadiq ya dafe kai yayinda yake ji kamar ya tashi ya falle Hanifa da mari..2

Su kuwa Heads din sun natsu suna so su ji… Da alama dai su ma basu san komai game da Sadiq ba.. kawai sun wayi gari sun gan shi a matsayin ma’aikacin kamfanin..

Ni kuwa nace balle kuma ni da masu karatu… ah toh!!

“Abubakar Sadiq Bunza is the son of marigayi Abubakar Muhammad Bunza, Former Minister of petroleum na qasa mamallakin Bunza Oil & Gas wanda ya rasu shekaru kusan biyu da suka wuce”3

Gaba daya dakin taron sai na ga kowa ya cika da mamaki yayinda ake ta kallon shi ana qus-qus.

Hafeez na ga ya sa ma Sadiq idanuwa shima cike da mamaki.. tabbas ya sani cewar Sadiq comes from a rich and sophisticated family domin kuwa yanayin rayuwar shi says it all.. toh amma bai taba sa ran cewar he is this stinking rich ba.. like he is such a simple, kind-hearted and down to earth kinda guy! Ta ya mutum yana da wannan matsayin a qasar nan zai zama this simple??

Hanifa ma zaro idanuwa tayi, qafafuwanta kuwa sun yi sanyi.. a sanyaye ta zauna kan kujerar ta yayinda ta sa ma Sadiq idanuwa..1

Shi kuwa tunda ya dafe kai bai qara dagowa ba saboda takaici.

“da ni da mahaifin shi tare muka yi karatu a Stanford University a qasar America.. dukda a lokacin he was my senior, jinin mu ya hadu and we became best of friends. I studied business administration yayinda shi kuma ya karanci Petroleum Engineering. Bayan ya gama masters dinshi ne ExxonMobil suka bashi aiki and I am sure you all know that it’s one of the best Oil & Gas producing Companies not just in America but in the world at large, Ya zauna a qasar America for over twenty years shi da iyalin shi… dukda ba qasa daya muke ba, abokantakar mu ta cigaba har lokacin da ya dawo Nigeria ya zo ya zama Minister of Petroleum na qasa..”

Girgiza kai na ga yayi sannan ya cigaba da fadin “Mahaifin Sadiq shine mamallakin Bunza Oil & Gas wanda nasan gaba dayan ku babu wanda bai san shi ba.. Kun sani cewar his business is beyond this country.. Ya rasu a sanadiyyar hatsarin mota da suka yi shi da matar shi (mahaifiyar Sadiq) akan hanyar su ta dawowa daga airport..”

Ya dan yi shiru tare da kallon Sadiq wanda kanshi yake a duqe har a lokacin sannan na ga ya dafa kafadarshi yace “Allah ya jiqan su da Rahama”

Gaba daya dakin taron suka amsa da “ameen”

“Me Sadiq yake yi a kamfanin nan?? na san dukkanin ku tambayar da kuke yi ma kanku kenan… idan bazaku manta ba wata goma da suka wuce Bugaje Industries yayi sinking wanda har ya kai mu ga shiga bankrupt.. dayawan ku kun sani cewar saboda haka ne aka kasa biyan salary dinku wanda har ya kai ga anyi downsizing ma’aikata.. We all saw it on the newspaper that I was about to sell the company in order to pay our debts until this gentleman showed up..”2

Sadiq ya dago kai ya kalli Paapa yace “please Sir, is this necessary??”

“Yes it is son… na gaji da jin qananan maganganun da Baby take yi akan ka da yadda take wulaqanta ka… she needs to know cewar kamfanin nan was in a serious problem lokacin da take karatu a qasar waje and I was here struggling to send her pocket money, She needs to know cewar har ciwon zuciya na ya kusa zama ajali na if not for you that came to my rescue, she needs to know cewar kudaden da ake juyawa a kamfanin nan gaba daya da wadanda take spending naka ne… and yes yakamata ta sani cewar accusations dinta a kanka na ka saci kudi ka biya accomodation ba haka bane, she needs to know cewar you actually spent so much money to save her father’s company…”

STORY CONTINUES BELOW

Gani nayi Sadiq ya kalli Heads na Unit din yace “gentlemen I guess this is where you should all take your leave.. it’s close of business already so you can close for the day. See you on tuesday and enjoy your public holiday on Monday.. Happy Independence Day in advance and God bless Nigeria”

Gaba dayan su suka miqe cike da girmamawa suka yi musu sallama.. Duk sun fita suna ta mamakin labarin Sadiq da suka ji.. dukda basu ji qarashin labarin Paapa ba sun gane lallai Sadiq shi ya ceci kamfanin a lokacin da suka fada gwata.. instantly he earned more respect domin kuwa dayawan su sunyi losing aikin su a lokacin.. farfadowar da kamfanin tayi ne aka dawo da su.

Bayan sun fita ne Sadiq ya miqe ya dauki I-pad dinshi da wayoyin shi ya kalli Paapa yace “I am sorry Sir, I will have to take my leave too. Ka san har yanzu ina ta fama da project work dina gashi lokaci yana ta qurewa..”

Paapa wanda yayi murmushi yace “Okay Son..” ya miqe tsaye shima ya cigaba da fadin “..I am so sorry akan abinda Baby tayi maka.. I really am ashamed of everything”

Girgiza kai Sadiq yayi yace “it’s okay Sir.. please dont be”

“but you never told me cewar ka kashe kudi dayawa haka wurin accommodation.. why didn’t you take my offer na hayan gida da nace zan kama maka?”

“I am sorry sir.. for some reasons I prefer not to stay in a rented house”

“dukda haka Son, N16.9m kudade ne dayawa.. zaka iya siyan gida lafiyayye ma da shi ai”

Sadiq ya dan yi murmushi yace “haka ne Sir, but it’s done already”

“toh shikenan Son, Allah yayi maka albarka”

“Ameen Sir, nagode”

Ya kalli Hafeez yace “take care Bro..”

Hafeez yana murmushi yace “You too..”

Ba tare da ya kalli Hanifa ba ya juya ya fita abinshi.

Hanifa wadda gaba daya tayi da-na-sanin dauko wannan zancen duk ta bi ta cika da kunya.. she wasn’t even able to look Sadiq in the eye anymore har ya fita… Gaba daya confidence dinnan nata ya bace.3

Bayan Sadiq ya tafi ne Paapa ya kalli Hafeez da Hanifa ya cigaba da fadin “…Sadiq ya ga newspaper din da aka yi publishing labarin Bugaje industries… Saboda damuwa da na shiga a lokacin har kwanciya asibiti nayi a dalilin ciwon zuciya na da ya tashi.. Immediately yayi contacting dina tare da dakatar da ni daga siyar da kamfanin nan, ya ji haushi sossai na yadda irin wannan matsalar ta same ni amma ban fadi mishi ba tunda we have always been in touch tun bayan rasuwar mahaifin shi.. In taqaice muku zance Sadiq shine ya biya dukkanin bashin da ake bin kamfanin nan sannan yayi investing huge amount of money in order to bring the company back to life.. ba wannan kawai yayi ba, shi ya gano ainihin wanda ya cuci kamfanin from our records. Saifullahi ya dade a kamfanin nan, shine Finance manager tun lokacin da mahaifi na yake raye and ganin cewar he was very good I decided to let him continue ko bayan rasuwar mahaifina. Amma dayake dan adam butulu ne ashe yana ta shuka mana tsiya yana diverting kudin kamfani to his pocket ba’a sani ba. Ko da muka yi discovering cewar shine tuni ya bace.. an neme shi sama da qasa ba’a gan shi ba. Sadiq shi ya sa aka dawo da duk wani wanda aka kora daga kamfanin nan.. ya gyara package na salary, bonus da compensation.. Sadiq shine ya dawo da martabar kamfanin nan har ya qaro mana manyan clients ba a nan qasar ba kawai har daga qasashen qetare. He introduced so many new and unique business strategies to this company and its thanks to him we are doing very well. A yanzu haka Sadiq yana managing both Bugaje industries and Bunza Oil & Gas at thesame time shiyasa lokutta da dama yakan yi tafiye-tafiye. Yana managing Bugaje Industries ne in order to set things straight for a while. we didn’t know who to trust with the finance management na kamfanin, he spared me six months of his time to train Yahaya wanda shine most trusted staff a kamfanin nan.. munyi testing dinshi several times and he came out clean shiyasa aka cigaba da training dinshi kafin ke Hanifa da kai Hafeez ku kammala karatun ku kuyi Joining kamfanin nan, learn everything possible and take over from him together with Yahaya..”

Muryar Hanifa tana rawa tace “kenan Paapa kamfanin nan ba naka bane… nashi ne?”1

Murmushi Paapa yayi yace “the company is still mine baby.. Sadiq ya taimaki kamfanin nan ne don Allah sannan don amintar da take tsakanina da mahaifin shi.. babu wani wurin da ya nuna cewar Sadiq yana da share cikin kudin kamfanin nan.. everything is still in my name.. aiki yake yi ma kamfanin nan amma baya daukar ko sisi a ciki a matsayin salary da makamantan su. His name is not even on our Payroll.. Da qyar ya amince aka yi centralizing account din kamfanin yadda ko ni idan zan kashe kudi sai nayi requesting.. a cewar shi it’s my company and I can spend as much money as I want but i said No. Dayake ya san he is here for just 6months shiyasa ya haqura ya qyale ni tunda we all know cewar after the 6 months, he will be out and kamar yadda yace -for good”2

Paapa ya saki ajiyar zuciya yace “kin ji kadan daga cikin irin abin alkhairin da Sadiq yayi mana don haka instead of wulaqanta shi da kike yi, he deserves some respect from you.. he saved our company”4

Ya kalli agogon hannun shi yace “ku tashi mu tafi gida.. it’s close of business already”

Daga nan ya miqe ya fita abin shi yayinda Hafeez ma ya miqe ya bi bayan shi not without smiling at a confused Hanifa.

Aikuwa suna fita na ga ta fashe da kuka.. tambayoyi kala-kala ta fara jero ma kanta…

Yanzu dama duk kudaden da take kashewa na Sadiq ne?? kenan kamfanin Paapa dukda babu a rubuce, partially nashi ne??? kenan duk gorin da take yi mishi kawai kallonta yake yi a matsayin fool?? wannan abun kunyan har ina??3

Wani littafi da yake kan conference table din ta dauka ta jefar da qarfin gaske tare da fadin “I hate you Sadiq.. I hate you for how you make me feel right now”

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE