RAWANIN TSIYA CHAPTER 9 BY FADEELAH
RAWANIN TSIYA CHAPTER 9 BY FADEELAH
Kamar yadda aka tsara, Abbu (Hanan’s Father) ya zo Nigeria sun hadu da su Big Daddy (Yazeed’s father) da Dad (Faisal’s Father) da Barrister mijin Hafsat, Yazeed da Faisal sun je Kano neman auren Sadiq.. Paapa da abokanen shi sun karbi baqin nasu cikin karramawa. Dayake dai harka ce ta girma komai anyi shi cikin tsari.. A nan suka nemi a sanya ranar biki Sati biyu kacal…2
Paapa ya dan yi mamakin jin sun buqaci ayi bikin so soon amma kuma daga baya sai yayi tunanin qila shi Sadiq din wants to just quickly fulfill his wish ne and send her back kamar yadda ya umurce shi..1
Sun jaddada ma Paapa cewar basu buqatar komai na daga kayan daki da sauran su tunda dama ba addini ya tsara lallai sai anyi haka ba.. All necessary formalities were done and it became official- Auren Sadiq da Hanifa nan da sati biyu!
Hankalin Hanifa ya tashi jin cewar an sa ranar bikinta in 2 weeks- bikinta da maqiyin ta SADIQ. Sossai abun ya dame ta.. gaba daya ma ta zama confused.. Tabbas tana da plan din da zata yi executing a gidan Sadiq amma kuma dukda haka jikin ta yayi sanyi… Ko me yasa???1
Hanifa dai ta gaya ma su Paapa cewar Sadiq ya bata blank cheque na lefen ta da hidimar biki amma kuma ta gaya musu cewar bata son lefen don haka bazatayi amfani da kudin shi ba..
Shi kam Paapa babu abinda ya dame shi da wannan dukda kuwa yayi mamakin ace yadda Hanifa take da son kashe kudi sannan an bata blank cheque amma ta qi amfani da shi? Unbelievable!!
Could it be a sign na cewar Sadiq ya fara gyara ta kenan tunda a dalilin shi for the first time she has uncountable money at her disposal amma kuma she refuse to spend???3
Well, a wurin Paapa dai whatever the case may be, tayi daidai tunda dama auren ba lasting zaiyi ba don haka gwara kar ta kashe mishi kudi a banza (even though deep down within him yana so auren yayi lasting coz he knows Hanifa will never get a good husband kamar Sadiq din)4
Mamy kuwa ta lallabe ta ko da kadan ne ayi lefen amma sam ta qi.. Gyaran jikin ma da za’a yi mata cewa tayi bata so, a cewarta wa zata gyara ma jiki bayan ko hannunta bazata taba bari ya taba ba balle….
toh fa!
Kai gaba daya komai na shirye shiryen bikin Hanifa ta qi tayi participating. Mamy da dangin mahaifiyarta su suke ta kidan su suna rawar su..
A bangaren Sadiq ma babu wani abinda yake yi na shirin bikin.. He was so occupied with work da kwata-kwata ya manta cewar zai yi aure.. kai har tafiya yayi a tsakanin wannan lokacin..
Shima dai kamar yadda ya fadi ma Naana baya son wani event don haka kawai da zarar an daura auren shikenan..
Tuni IV na daurin aure ya fita.. ya bi ko ina a qasar Nigeria. Dukda abin low-key ne sai da aka samu ‘yan nacin da suka zaqulo hotunan Sadiq da Hanifa suka baza a social media.. tuni suka zama talk of the town..
Kowa yana murnar bikin Sadiq a cikin dangi amma banda Asma’u. Gaba daya ko maganar bikin bata so ta ji balle sunan Hanifa… Ita kuwa Hanan ta zama indifferent about it, a part of her is happy for him and a part is not!! Ta sani cewar tunda ba auren shi zata yi ba bai kamata tayi mishi baqin ciki ba dukda shi din ba son auren yake yi ba..2
Ana saura sati daya bikin ne su Jameela da Nana Fatima suka iso Nigeria.
Sossai suka dinga qorafi jin an ce babu event din da za’a yi har a bangaren amarya.. Har kiran Sadiq suka yi suka sanya shi a gaba suna ta masifa amma kuma ya dinga basu haquri..
STORY CONTINUES BELOW
Su kansu Faisal da Yazeed sunyi qorafi har suka gaji.. Babu shiri suka haqura suka qyale shi.. a cewar su tunda dai zai yi auren ai shikenan!
Su Hanan ma tun ana saura sati daya suka iso.. tunda suka iso kuwa tana nan maqale da Sadiq.. hatta ofis tare suke zuwa.. Har yawon shopping suke zuwa tare da Asma’u kamar ba wanda ya rage sauran kwanaki ba bikin shi..
this is to show how very much unimportant he takes the wedding!!!
hmmmmmm!!!!!!
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
*
*
*
*
ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA
A yau Juma’a, Yau ne ranar daurin auren Hanifa da Sadiq wanda za’a yi bayan sallan juma’a a Central Mosque.
Garin Kano ta cika da manyan baqi a wannan safiya domin dai it’s the Union between the Children of two Rich, powerful and sophisticated families.
Amarya Hanifa dai tun jiya da dare da ta shiga dakinta bata qara fitowa ba gashi a yanzu har qarfe Goma sha daya na safe..
Tun kwana biyar da suka wuce gidan ya cika da baqi ‘yan uwa da abokan arziki.. Dangin mahaifiyarta har wadanda suke qasar Morroco duk sun zo..
Tun da safe kowa tambayar whereabouts din amarya yake yi amma babu ita..
Abin mamaki shine duk wanda aka aika ya je ya kira ta sai su dawo su ce tace tana zuwa.. hatta Mamy da ta kira ta a waya cewa tayi tana zuwa amma kuma bata fito din ba. Da Mamy ta kula da take-taken ta ne ta kira Paapa a waya ta sanar da shi.. Shi dai Paapa jin an ce tana responding sai yace a qyale ta, idan ya dawo he will handle her.1
Dangin su Hanifa dai basu yi mamakin wannan al’amari ba tunda sun ji labarin cewar arranged Marriage ne.. su kam sun sani sarai girman kai irin na Hanifa bazai taba bari tayi soyayya da namiji har ta kai su ga yin aure ba don kuwa tun tana qarama babu wanda bai san halinta ba.
Mai karatu, ni kam da na kula kamar babu yadda za’ayi in ga Hanifa sai wata dabara ta fado mun.. ladder na hau na shiga ta window don in gano muku abinda yake wakana a cikin dakin..
Kwance take a kan resting chair na dakinta yayinda idanuwan ta suke a rufe.. Karatun Al-qur’ani na ji yana tashi in a very low volume yadda idan ba kana daf da ita ba bazaka taba ji ba..
Hanifa dai ba wani zurfi tayi a karatun Al-qur’ani ba domin kuwa bata yi sauka ba amma kuma karatun addini is the one thing da Paapa yayi mata tsaye akai tun tana qarama- babu laifi kuma ta samu dukda ba wani mai zurfin gaske ba…
A dalilin ta iya hada baqi shiyasa ko wuraren da ba’a koya mata ba ta iya karantawa.. Hadda ne dai bata iya ba sai ‘yan surorin qasa wadanda basu da tsawo..
A yanzu haka Suratul Maryam take sauraro.. she has been listening to the recitation of the Holy Qur’an tun Safe da ta tashi daga bacci…
A jiya ta kwana cikin wani yanayi- Yanayin da ita kanta bata iya fasalta shi.. she was feeling all sorts of emotions.. Jikinta ne yake qara sanyi wanda bata san dalili ba.. even after ta riga ta shirya karta ma Sadiq rashin mutuncin da ko kwana uku bazata yi ba a gidan shi zata dawo, a part of her is telling her cewar ba abinda zai faru ba kenan.. but why???5
Gaba daya ta farka feeling very weak, she slept on an empty stomach and yanzu haka bata ci komai ba.. tana da fridge danqare da Chocolates dinta da sauran kayan ciye-ciye a dakinta amma hatta su ta kasa ci.. tayi losing appetite completely.
Yanzu haka karatun Al-qur’anin da take sauraro shine ya sanyaya mata rai har ta samu natsuwa.. A haka kuwa har bacci ya sace ta kusan tsawon awa uku..
STORY CONTINUES BELOW
Hayaniyar mata a cikin gidan ne ya farkar da ita.. Aikuwa tana farkawa ta ji guda non-stop.
“toh sarkin iko sai ki fito tunda dai an daura auren ki.. Lallai jan ajin ki ba a banza ba tunda aka biya naira miliyan daya kudin sadakin ki…” ta jiyo muryar Anty Anisa a bakin qofa.
A gigice ta tashi zaune tare da dafe qirjin ta.. zuciyarya ce take ta bugawa kamar wadda tayi gudu na kilometer dari..
“what??? an daura aure na?? Sadaki one million naira??? is he mad?? what does he want to prove??”
Agogo na ga ta kalla sannan ta miqe tsaye tace “Ba dai ni ba Hanifa.. baka isa ka wulaqanta ni ba.. kudin sadakin naka ma mayar maka zanyi don wallahi bana so” ta fada cike da gadara yayinda na ga ta wuce dressing room.. Da alama dai wanka zata yi.3
toh fa…
*********************
Wuraren qarfe Uku na rana tana zaune a kan gadon dakinta sanye cikin wata burgundy jumpsuit mai kyan gaske…
Sossai tayi kyau dukda bata yi kwalliya ba.. abin mamaki ni da nake kallonta sai na ga ban taba ganin tayi kyan da tayi ba a yau.. ko meyasa???5
Fuskar wayarta na ga ta qura ma idanuwa babu ko qyaftawa yayinda zuciyarta take ta bugawa.. Gaba daya ta zama lost.. Ni kuwa da sauri na matsa don in ga abinda take kallo da har ta shiga wannan yanayin..
Mai karatu ba wani abu bane illa hoton SADIQ!! Hotunan daurin aure ne da aka baza a social media..
Sanye yake cikin dinkin babban riga (irin wanda samarin zamani suke yayi) na wani farin yadi mai bala’in kyau wanda ba sai an fada ba ya ja Naira.. Ya sha hularshi Zanna Bukar wadda ta bala’in dacewa da kalar fatar shi.. Ga gashin fuskar shi sun sha gyara sai qyalli suke yi.. A taqaice dai mai karatu Sadiq from head to toe 100% on point..
A yau din Hanifa sai ta ga ya fi kullum yin kyau.. Allah ya sani kyan Sadiq yana masifar ruda Hanifa, har yau ta kasa controlling kanta a duk lokacin da ta kalle shi.. Now that they are going to live together under one roof ya zata yi???6
Next hoton da ta bude kuwa Sadiq din na hango tare da Yazeed, Faisal da kuma Hafeez.. Su kuma anko suka yi na sky blue yadi suma duk dinkin babbar rigar suka sanya iri daya.. they surely made the perfect groomsmen!!
Dukkanin su sunyi kyau amma kuma tabbas Sadiq ya fi su yin kyau nesa ba kusa ba.. ko dama dai ya fi su kyan ne amma kuma ai ko ba don haka ba he is the groom so he has to look more handsome than any other person… Yeah??!!
Ajiyar zuciya ta saki sannan na ji tace “yanzu shikenan na zama matar shi???”3
Muryar Paapa ta jiyo a bakin qofa yana fadin “Baby open the door..”
Da sauri ta miqe ta nufi qofar ta bude.. for the first time today Hanifa ta bude qofar dakinta!!
Ganin Paapa tayi a tsaye tare da Mamy da kuma Anty Anisa suna kallonta..
“meye haka Baby?? yau daurin auren ki and you are not dressed??”
Turo baki tayi tace “toh Paapa wai ba nace ni bana son event ba??”
“toh amma ko don albarkacin baqin da suka zo ai yakamata ace kin shirya..”
“Paapa..”
“Please Baby..”
Ya kalli Mamy da Anty Anisa yace “help her get ready yanzun nan sannan ta fita ta je su gaisa da sirikan ta…”4
Kafin Hanifa tayi magana kuwa ya juya abinshi yayinda su Mamy suka shiga dakinta riqe da wani akwati trolley dan qarami.
STORY CONTINUES BELOW
Akan dole kuwa Hanifa ta zauna Anty Anisa ta fara yi mata make up..
“I swear ban taba ganin yarinya mai taurin kai ba irinki Hanifa.. ace ranar bikin ki ma sai kin yi abinda kika ga dama? which bride turns up without a henna on her wedding day??”
Ta kalli Mamy wadda take fitar da kaya daga akwatin da suka shigo da shi tace “duk laifin ki ne Mamy.. ai da ko maganin bacci kun dura mata ayi lallen. idan ta farka sai mu ga yadda zata goge shi..”3
Mamy dai fashewa tayi da dariya tana mamakin masifar da Anty Anisa take yi when ita da kanta tana nan a gidan for almost a week now and she didnt force her to do the Henna sai ita da bata dauka a bakin komai ba ce zata tilasta mata.. Haka kawai tana zaman ta lafiya ta janyo ma kanta kwasar wulaqancin Hanifa!!
Hanifa dai turo baki take ta yi yayinda ta cika fam da takaici da bacin rai..
“sossai nake tausaya ma angon nan naki don kuwa zai sha wahala da wannan halin banzan naki” Anty Anisa ta fada
“toh idan ba zai iya ba ai sai ya sallamo ni tunda dama ba son auren nake ba..” Hanifa ta fada kai tsaye
“habawa yarinya baki isa ba.. ko zai sallame ki sai ya fanshi nairan shi miliyan daya sannan, banda shashanci irin naki me zai sa kiyi ma kanki mugun fata irin wannan?? do you know how it feels for a woman to become a divorcee??”
Ita dai Mamy tana ta sauraron su yayinda take murmushi.. Sossai ta gode ma Allah da zai raba ta da Hanifa ta huta da wulaqancin da take yi mata, don ma anyi sa’a kwana biyu ta dan yi sanyi..
Mamy dai a zahiri ba wai ta tsani Hanifa bane, On the contrary ma she loves her alot.. Lokacin da ta zo gidan ta yi qoqarin janyo ta a jiki, she wanted to be like a mother to her amma sam Hanifa ta qi instead ma she hated her.. she doesn’t miss the opportunity na ta wulaqanta ta a kullum. Mamy had no choice but to distance herself from her domin kuwa da ta biye ma Hanifa da yanzu an kore ta daga gidan!3
A haka dai Anty Anisa tana ta tsokanar Hanifa har suka gama make up din.. Aikuwa tayi kyau sossai kamar wata professional make up artist tayi mata kwalliyar.
Mamy ta dinga yabawa.. kai hatta ita kanta Hanifa ta yaba. Tabbas kwalliya yana yi mata kyau…
Wasu turaruka Anty Anisa ta fiddo ta dinga shafa mata a jiki wanda nan da nan wani qamshi mai dadin gaske ya cika dakin..
“akwai turaruka da mayyuka dayawa na hado miki su an zuba cikin kayan ki.. kar kiyi wasa da su don kuwa special hadi ne daga Marwa Sa’id, akwai na wanka da na shafawa kuma kowanne yana da directions dinshi”
Marwa Sa’id dai wata shahararriyar mai gyaran jiki ce a qasar Morocco.. sananna ce worldwide domin kuwa tana da customers from different part of the world. the most interesting thing about her is da zarar ta hada maka turaruka da mayyukan ta toh fa shikenan ta gama gyara ki tsab.. as long as you follow the directions an gama..
Hanifa dai dukda bata son hidimar da ake yi mata sossai ta ji dadin qamshin turarukan..1
“ina mai tabbatar miki idan har kika kusanci angon naki sanye cikin wadannan turarukan sossai zaki haukatar da shi.. ki tabbatar kinyi using dinsu when you are ready for action” ta fada tare da kashe mata ido daya sannan ta cigaba da fadin “I hope you understand what I am saying..”
Hanifa wadda ta tabe baki a ranta tace ‘as if I told her I need his attention or want to be intimate with him’
Haka dai Anty Anisa ta cigaba da yi ma Hanifa bayanai iri-iri na yadda zata tafiyar da Sadiq wanda yake shiga ta kunne daya yana fita ta dayan.
Mamy ce tace “ga kayanki nan sai ki tashi ki sanya.. Your in-laws are waiting for you, imagine harda matar gwamna suka zo.. kin ga ko ba komai albarkacin ki mun gan ta, gashi ta biyo mu har gida..”
STORY CONTINUES BELOW
Cike da mamaki Hanifa tace “what?? matar gwamna kuma??”
*****************
Zaune suke a babban falon Mamy suna ta hira kamar wadanda suka san juna tuntuni..
Mummy (mahaifiyar su Yazeed), Mom (mahaifiyar su Faisal), Ammi (Mahaifiyar Hanan), Anty Jameela, Anty Fatima, Anty Hafsat, Nabeeha (matar Yazeed) da kuma matar gwamnan Kano da muqarraban ta guda hudu.. Naana, Asma’u da Hanan ne kawai ban gani ba..
Asali dai tun jiya suka iso garin Kano cikin private Jet din Marigayi mahaifin Sadiq inda suka sauka a gidan gwamnan Kano wanda ya kasance aminin Dad (mahaifin Faisal) sannan ita kuma Matar shi ta kasance aminiyar Mom…
A yau din sun zo gidan su Hanifa ne don ayi yinin biki da su wanda kuma gobe zasu dauki amaryarsu su wuce da ita gida (Abuja).
Asma’u dai da gangan ta qi zuwa don kuwa ita ba son auren take yi ba.. ko da aka tashi tafiya sai cewa tayi zata tsaya tare da Naana don su tarbi amaryar idan ta iso..
Ita kuwa Hanan jikin ta da yake a sanyaye ne ya sa ta kasa zuwa.. itama din sai kawai tace zata tsaya tare da su Naana saboda shirye-shiryen tarbar Hanifa.
Mai karatu a yanzu haka da nake kallon wadannan mutane babu abinda na gani sai dukiya shimfide a jikin su.. da ganin su ka san manyan mutane ne wanda suka fito daga cikin arziki.. Yanayin su zai tabbatar maka da lallai irin mutanen nan ne wadanda aka haifo su cikin kudi (ba ‘yan haye ba)… each and every one of them looked so classy and elegant!
Abin da ya fi birge mutane shine dukda they are very Rich and sophisticated people, they are so down to earth and very friendly, basu da girman kai ko alama..
Suna cikin hirar su ne na jiyo guda yayinda na hango Mamy da Anty Anisa riqe da Hanifa wadda aka rufe mata fuska sai sauran dangin mahaifiyarta biye da su..
Gaba daya hankulan kowa suka dawo kan su..
Hanifa tana sanye cikin wani tsadadden yadi pink color… wannan yadin dai musamman Anty Anisa ta dinko mata shi daga qasar su Morocco… Yadin is so unique and very expensive, it’s one of the traditional attires da brides suke sanyawa a qasar su.. Sarqa, dan kunne da bangles na zinaren da ta sanya kuwa special gift ne from her Paapa.. da ganin su kuwa ka san sun ja kudi… Hanifa dai sai qyalli take yi tana baza qamshi..
1
Kai tsaye su Mamy suka kai ta wurin sirikan nata yayinda suka zaunar da ita a qasa..
Mom ce ta sa hannu ta bude fuskar Hanifa yayinda aka fara rangado guda from all directions..
“Masha Allah” na ji sun fada yayinda suke ta yaba kyanta.
Matar gwamna ce tace “what a beautiful bride.. Allah ya sanya alkhairi ya kawo zuri’a dayyaba”
Gaba daya aka amsa da ‘ameen’
Su Mummy dai ko dama sun ga hotunan Hanifa a Social media wadanda akayi ta posting.. Sun sani cewar kyakyawa ce amma a yanzu da suka gan ta sai suka ga ba kyau ba kawai, ta masifar haduwa.. Ga dan jikinta daidai ‘yar fitted da ita!
Mom dai janyo ta tayi ta zauna a cikin su yayinda suka cigaba da yaba kyanta suna ta yi mata addu’o’i ita da Sadiq..
Ita dai Hanifa bata samu damar kallon su ba sossai amma ta fahimci cewar dangin Sadiq manyan mutane ne kuma ta fahimci suna son mutane.. Tabbas da ace tana son auren da tayi sa’an sirikai toh amma me?? A halin da ake ciki duk wani wanda is related to Sadiq bata qaunar shi don haka dukkanin su bata son su..2
Banda don Paapa ya tilasta mata babu abinda zai sa ta fito..
Jira kawai take yi a gama komai a kai ta gidan Sadiq ta karta mishi rashin mutuncin da ta shirya mishi ya sallameta ta dawo gida ta cigaba da rayuwarta as always..
ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA+
Zaune take a kan gadon dakinta yayinda na ga wasu DVD/CD plates baje a kan gadon tana ta sorting dinsu.. Ko da nayi zooming sai na ga duk plates din waqa ne da kuma na rawa both audio and Video.1
She was taking her time to sort them sannan tana sakawa a cikin wata jaka.
Ni kuwa nace ina zata je da su??? ba dai gidan auren nata ba?? Hanifa is surely not serious!!2
Wayarta ce tayi ringing yayinda na ga ta lalubo ta da sauri a dalilin ringtone din- Ringtone din Paapa..2
Tana answering yace “Baby zo ki same ni a falo na yanzu”
Kai tsaye tace “toh Paapa”
*****************
Zaune yake a bisa one-seater kujera a falon Paapa yayinda suke ta hira kamar ba sirikai ba..
A yau Bayan an gama yinin biki dangin ango dai sun tafi akan washegari zasu dawo su dauki amaryar su..
A daren yau din ne Paapa ya gayyaci Sadiq a dalilin wata muhimmiyar magana da yake so yayi mishi.. well dama dai ko da Paapa bai yi inviting dinshi ba he’d still come don yayi mishi sallama.
A wannan lokacin su Mamy suna can suna hidima da baqin su dukda dai dangi ne..
Hanifa ce ta shigo falon yayinda ta tsaya cak a dalilin qamshin turaren shi da ta ji.. Zuciyarta ce take ta bugawa fiye da na kullum.. jikinta har rawa yake yi wanda ta rasa dalili.2
Paapa wanda ya dago kai ya ganta ne yace “ya kika tsaya a nan?? shigo mana”
A sanyaye ta qarasa shigowa yayinda ta nufi wurin Paapa kai tsaye ba tare da ta kalli Sadiq ba.. Shi kam Sadiq tunda ya ji Paapa ya kira sunanta na ga ya fara latsa wayar shi.. Toh fa!2
Sanye take cikin kayan bacci na T-shirt ‘yar qarama daidai dan jikinta da wandon three quarter.. As usual ta daure gashinta a tsakiyar kai wanda yayi buzu-buzu amma kuma dukda hakan tayi kyau sossai..
Hanifa ta zauna kan kujerar da Paapa yake zaune ta maqale a jikin shi kamar mage tace “Gani Paapa”
“Baki iya gaisuwa bane Baby?? Baki ga mijin ki bane a zaune??”
Turo baki tayi and for the first time ta dago kai ta kalle shi.. Wani irin bugawa zuciyarta tayi a dalilin masifar kyau da Sadiq yayi mata..6
Sanye yake cikin wani Yadi off white wanda aka yi ma dinkin half jumper… a yanzu haka fa ba wai ya dago kanshi bane, kawai side view dinshi take kallo amma she could swear bata taba ganin namiji mai kyan Sadiq ba a rayuwarta… toh amma kuma me?? ta tsane shi!!
Hararar shi tayi sannan tace “ban gan shi bane Paapa”
“tunda kin gan shi greet him then..”
“Ina wuni” ta fada in a low tone yadda ta san ba zai ji ba and to her greatest suprise sai ta ga ya dago kai ya kalle ta har yana murmushi yace “lafiya lau Mrs Bunza”6
Ran Hanifa ne yayi mugun baci jin ya kirata da sunan da bata so.. Wata muguwar harara ta gabza mishi sannan tace “Ba nace ka daina kira na Mrs Bunza ba?” ta kalli Paapa cikin shagwaba tace “Paapa ka gaya mishi ya daina kirana da wannan sunan”
Shi kam Paapa a ranshi dadi ya ji a dalilin yadda Sadiq din yayi addressing dinta.. Allah ya sani da son ranshi auren nasu ya dore don kuwa yana bala’in son Sadiq toh amma from the looks of it all Hanifa bazata yi lasting a wurin shi ba… idan ma ta gyara hali ya gode ma Allah!!
STORY CONTINUES BELOW
“toh me kike so ya kira ki da shi??” Paapa ya tambayeta yayinda yake kallon ta..
Turo baki tayi bata ce komai ba..
“Sauka ki koma ki zauna kusa da mijin ki… magana zanyi muku”
Da sauri ta daga kai ta kalli Paapa zata yi magana amma yanayin yadda ta ga fuskar shi ta canza ne ya sanya kawai ta miqe. Jikinta na rawa ta nufi wurin da Sadiq yake zaune..
Dayake kujerar da yake zaune din One-seater ce sai kawai na ga ta zauna a kan hannun kujerar… the first time da suka fara zama this very close to eachother..
Hakan kuwa sai ya sa Sadiq ya zama so very much uncomfortable!4
“Sauka qasa wurin qafafuwan shi ki zauna” suka jiyo Paapa ya fada..
Zaro idanuwa tayi tace “Paapa??? toh shi kuma fa??”
“ina wasa da ke ne Hanifa?” Paapa ya fada rai a bace yayinda Sadiq yayi murmushi- Murmushin that didn’t go unnoticed by Hanifa.
Hakan kuwa ya qona mata rai…
Ya za’ayi Paapa ya sa ta zauna a qasa kusa da qafafuwan shi??? don kawai a nuna shine da girma??? shikenan ajinta ya gama zubewa kenan??? ita kam she still cant believe Paapa is making her do things against her wish.. what’s going on???
Tana turo baki kamar zata yi kuka ta zauna a qasa kusa da Sadiq…
Paapa yayi gyaran murya yace “there is something important that I need to tell you both”
Hanifa wadda take kallon Paapa sai ta ji zuciyarta ta buga for no reason yayinda take ta wondering abinda yake so ya fadi..
Ita kam ta sani tun ana bikin nan saura sati daya Paapa yake kiranta everyday ya zaunar da ita a gaban Mamy yana yi mata nasiha.. nasihar da batada amfani a wurinta tunda ba zama zata je yi ba.. toh meye ya rage wanda bai fadi mata ba kuma???
“Baby a yau an daura miki aure da Sadiq, a matsayin shi na mijinki duk abinda yace kiyi, ki tabbatar kinyi shi sannan duk abinda ya hana ki, kar ki kuskura kiyi.. ki kasance mai ladabi da biyayya zuwa ga mijin ki domin kuwa kamar yadda na fadi miki Aljannar ki tana qarqashin qafar shi.. ko da wasa kar ki kuskura kiyi abinda zai bata mishi rai…”
Gani nayi Hanifa tana kallon Paapa cike da mamaki yayinda yake ta magana amma sam hankalinta yayi nisa.. kenan yana nufin sai abinda Sadiq yake so tayi shi zata yi??? har wani bin shi zata yi ahankali don kar ta bata mishi rai??? toh ita fa??
Aikuwa bata ankara ba ta ji Paapa yace “kai kuma Sadiq dont hesitate to deal with her idan tayi maka ba daidai ba.. You have my full authorization ka hukunta Hanifa whenever you feel like idan tayi maka ba daidai ba..”
“What???” Hanifa ta fada yayinda na ga ta zaro idanuwa
Paapa wanda yake kallonta yace “Yes Hanifa, kuma ina so in ja miki kunne.. idan kika kuskura kika kashe auren ki da kan ki wanda ba mijin ki ya sake ki don kan shi ba ban yafe miki ba… infact ki nemi wani uban ba ni ba”3
“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..” ta fada yayinda ta miqe tsaye dafe da qirjinta.
Fashewa tayi da kuka tace “Paapa meyasa zaka fadi haka kamar ka daina sona?? Paapa don Allah kayi haquri, this is not fair…” ta kalli Sadiq wanda yake kallonta ta cigaba da fadin “wallahi Paapa he is going to take advantage of abubuwan da ka fada ya bani wahala… I swear mugu ne”
“toh sai kiyi qoqari kiyi abinda yakamata yadda bazai baki wahala ba Baby.. Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya”
Sadiq wanda yake murmushi yace “Ameen Sir.. nagode”
STORY CONTINUES BELOW
Shi dai Sadiq didn’t expect to hear this from Paapa.. it’s as if ya san asalin abinda yake faruwa tsakanin shi da ‘yar tashi for him to say that.. Well, it’s perfect for him tunda dai da wannan sharadin ya tabbatar he will deal with Hanifa kamar yadda yayi niyya ba tare da tunanin zaiyi rashin kyautawa ga mahaifin nata ba..
Hanifa wadda take rusa kuka sai gani nayi ta ruga a guje ta bar falon…1
toh fa!
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Washegari!!
Wuraren qarfe takwas da rabi na safe tana kwance a kan gadon dakinta.. idanuwanta a rufe tana tuno kalaman Paapa a jiya..
…she just couldn’t forget the look on Sadiq’s face lokacin da Paapa ya bata wannan sharadin- sharadin da ya ruguza mata plan dinta gaba daya.
He looked so happy!!
Gaba daya Paapa ya mayar da ita powerless.. gaba daya ya rusa mata plan dinta, Paapa ya kasance the most important person a rayuwarta.. Ko kadan bata iya bijire ma umurni shi toh amma wannan din abu ne mai wuya.. ita da tayi niyyan ko kwana uku bazata yi ba a gidan Sadiq toh yanzu ya kenan??? kenan zama zata yi Sadiq yayi yadda ya ga dama da ita??? zama zata yi ya wulaqanta ta??? shin meyasa Sadiq yake samun nasara akan ta everytime?? why will her Paapa do this to her???
Gani nayi ta fashe da kuka yayinda na ji tana fadin “Paapa why?? meyasa zaka yi mun haka?? I hate you Sadiq, i hate you from the bottom of my heart and i will never forgive you for this”
Ko da ta tashi zaune gani nayi fuskarta ta kumbura.. hakan ya tabbatar mun da lallai ba wani baccin arziki tayi ba kuma babu shakka ta kwana tana kuka..
Gani nayi ta sauka daga kan gadonta ta nufi gaban Vanity mirror dinta ta tsaya tana kallon fuskarta.. she looked so very much disorganized and all because of SADIQ!
Runtse idanuwa yayi ta bude sannan ta saki wata ajiyar zuciya tace “wai meyasa nake kuka na shiga damuwa haka??? saboda Sadiq??? why did I give him the right to trouble my life this much?? why??”
Hawayen fuskarta ta goge.. irin gogewar nan wanda zai tabbatar maka da lallai ta gama kukan kenan sannan ta cigaba da fadin “Paapa only asked me kar in kashe aure na da kaina but amma kuma zan iya tunzira shi ya sake ni da kanshi and willingly, yeah??? it simply means I will carry on with my plan..”3
Murmushi tayi tace “Dear Sadiq, I will trouble you so much that you will send me packing in no time insha Allah… just watch and see”
Daga nan kawai sai na ga ta shiga dressing room dinta..
Da alama dai shirin wanka zata yi..
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Wuraren qarfe Goma sha daya da rabi na safe ne Anty Anisa ta qwanqwaso qofar dakin sannan ta shigo..
Gani nayi ta tsaya turus da baki a sake yayinda take kallon Hanifa..
Mai karatu, ina juyowa na kalle ta nima sai na saki baki..
Zaune take a gaban Vanity mirror dinta yayinda take qarasa kwalliyar fuskarta..
Hanifa dai sanye take cikin wani teal lafaya very simple amma mai shegen kyau.. tana sanye da accessories dinta masu kyan gaske very simple su ma.. abinda ya fi bani mamaki shine kalar make up din da tayi wanda idan ka kalle ta bazaka ce itace take a hargitse ba just a while ago..
5
STORY CONTINUES BELOW
Babu abinda take bazawa sai qamshi…
Gani nayi ta ajiye blush din da yake hannunta ta miqe tsaye tace “Anty har sun zo ne??”
Anty Anisa wadda ta cika da mamaki tace “Hanifa lafiyar ki kuwa??? da kan ki kika shirya and you are even asking ko in-laws dinki sun zo?? wow.. “
Murmushi Hanifa tayi tace “toh ya zanyi? tunda kun yi mun auren ai dole sai dai inyi haquri”
Anty Anisa wadda ta girgiza kai ce tace “for the first time in your life you’ve said something great… I can see aure har ya fara canza ki Babyn Paapa and I am very much happy about it”
Hanifa wadda take murmushi a ranta tace “habawa Anty, if only you know” a zahiri kuwa tace “toh wai tsaya, Baki fadi mun ko nayi kyau ko ban yi ba”
“kin yi kyau sossai Babyn Paapa.. lallai angon nan zai sha kwalliya.. kin ga yadda kika koma kamar wata ‘yar Indiya”
Gani nayi Hanifa ta fashe da dariya.. Mamaki take yi wai Sadiq zai sha kwalliya, How can she waste her make-up for the monster!!
Mamy ce ta shigo tare da Anty Ruqayya, Anty Safeena da kuma Anty Rabi’atu (duk ‘yan uwan mahaifiyarta)
“toh maza ki fito ga dangin mijin ki sun zo.. kar ki bata musu lokaci”
Zuciyar Hanifa ce ta buga yayinda jikinta yayi mugun sanyi.. Finally she is leaving her Paapa’s house amma insha Allah not for good don kuwa zata dawo in a few days’ time…
Hmmmmm….
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
LATE ALHAJI ABUBAKAR MUHAMMAD BUNZA RESIDENCE- ASOKORO ABUJA
Gidan a cike yake da abokanen arziki a lokacin da suka iso.
Naana dai tunda suka yi waya da su Mummy suka sanar da ita zasuyi boarding jirgi ta kasa zama.. sai nan da nan take yi yayinda take ta shirya tarbar amarya Hanifa.. Sirikarta, Matar favorite dinta- SADIQ
Sadiq dai da ‘yan uwan shi Yazeed and Faisal commercial flight suka biyo tun da safe suka shigo Abuja.. Su Big Daddy kuwa dama tun bayan daurin aure jiya suka dawo Abujan!!
Qarar motoci a waje da kuma Guda non-stop ne ya tabbatar min da lallai amarya ta iso..
Dayake dai Hanifa bata da qawa ko daya Mamy, Anty Anisa, Anty Ruqayya, Anty Safeena da Anty Rabi’atu su ne suka rako ta zasu ga gidanta sannan anjima da yamma zasu koma Kano!
Dayake an rufe fuskar Hanifa babu wanda ya samu ganin fuskarta har suka shiga cikin gidan..
Kai tsaye wurin Naana aka kai ta.. Cike da murna da farin ciki Naana ta riqe Hanifa yayinda ta rungume ta tana yi mata addu’a.
Abin mamaki duk yadda Hanifa take jin haushin dangin Sadiq, for the first time dukda bata ga fuskar Naana ba sai ta ji wani sanyi a ranta.. she felt a strong connection between them instantly. Irin grand mother- grand daughter connection dinnan. Bata san lokacin da ta ba Naana wani bone crushing hug ba yayinda take jin son ta har cikin zuciyarta..2
Ita kanta Naana sai da tayi mamakin hug din wanda kuma ta ji dadi har ranta..
“Masha Allah Hanifa.. Allah yayi albarka”
Gaba daya aka ce ‘ameen’
Duk wannan al’amarin da ake yi Hanan da Asma’u suna tsaye suna kallo yayinda ran Asma’u yake a bace, ita kuma Hanan jikinta yake a sanyaye..
A lokacin da aka bude fuskar Hanifa ne aka shiga rangada guda yayinda aka dinga yaba kyan ta..
Zuciyar Hanan ce ta buga ganin wani irin kyau da Hanifa tayi.. dukda ta taba ganinta a Video call briefly sannan ta ga hotunan ta da aka yi posting a social media tabbas ganinta a yanzu ta fahimci Hanifa first class ce wurin kyau.. Mamaki take yi na yadda kyan ta bai taba zuciyar Sadiq ba…2
STORY CONTINUES BELOW
Asma’u wadda take tsaye a gefen Hanan ce tace “just look at how they are all praising her saboda tana da kyau.. su basu san halinta bane?? I swear I hate her”
Hanan ta riqo hannun Asma’u tana murmushi tace “calm down Asmy, kar kiyi mamaki ta gyara hali har ma kuyi getting along”
“what??? never.. I can’t wait for Big B to just teach her a lesson and send her away” ta fada yayinda ta kalli Hanan tace “duk ke kika ja mana Ya Hanan.. if only you accepted his proposal, all these wouldn’t have happened. Please accept his proposal kawai ya sake ta ya aure…” Kafin ta qarasa magana ne wayar Hanan tayi ringing.
Gani nayi ta duba sannan ta kalli Asma’u tace “excuse me please” yayinda tayi answering tare da juyawa..
Naana ce tace “Asma’u, Hanan come and say Hi to your sister in-law”
Asma’u ta turo baki yayinda ta juya ta kalli Hanan wadda take magana a waya tace “Ya Hanan mu je mu ga gimbiya”
Hanan ta dan juyo tare da fadin “Go ahead Asmy, I will be right behind you..”
Hanifa wadda ta hango Asma’u ta tabbatar ita ce qanwar Sadiq don kuwa suna kama.. kawai dai ta fi shi haske ne sai kuma shi din ya fi ta kyau.. Haka kawai kuma sai ta ji yarinyar ta kwanta mata a rai ko me yasa???
Zuciyar Hanifa ce ta buga a dalilin hango wata kyakyawar mace da tayi a bayan Asma’u…
HANAN!!
6
Da sauri ta kauda kai ba tare da ta qara kallonta ba..
“You are welcome to the family In-law” Hanan ta fada cikin muryarta mai dadi a lokacin da suka qaraso wurin su.
the sweet voice that made Hanifa to look at her again.. ‘who is she???’ ta tambayi kanta.
Kamar Naana ta san what’s going on a ran Hanifa sai ta ji tace “this is Hanan, Favorite Cousin din Sadiq da take Egypt.. Na tabbatar kin san ta tunda babu wanda zai zauna tare da Sadiq ace bai san Hanan ba”
Hanifa dai gaba daya ji tayi ranta duk ya baci wanda ta rasa dalili..
Before anyone could say anything ne wayar Hanan ta qara ringing yayinda ta duba.. tana murmushi tayi answering tace “Hey Chocopie, ga amaryarka nan an kawo…” Daga nan ta wuce yayinda Hanifa ta bi ta da kallo tana mamaki…
Sadiq ne take kira Chocopie?? why??? do cousins address each other like that? besides why is she so beautiful???14
Shaking off tunanin tayi yayinda tace ‘me ya ruwan ki Hanifa? you dont even like the guy.. so what idan wata ta kira shi da koma wane irin suna??’
Bata ankara ba ta jiyo muryar Mom tana fadin “wato ya kira don ya ji ko an kawo mishi amaryar shi kenan ko?? yaran zamani babu kunya.. “
Su Mummy ne suke ta dariya..
“Asma’u won’t you greet your sister in-law??” Naana ta fada in a reprimanding tone
Asma’u ta dan saki fuska tace “you are welcome Sis in-law”
Hanifa wadda ta kalli Asma’u tayi murmushi wholeheartedly tace “thank you Asmy” yayinda na ga kuma ta koma ta kalli wani direction..
Ko da na bi direction din da take kallo Hanan na hango tana magana da Sadiq a waya tana ta kwasar dariya.. da alama she is enjoying the conversation da suke yi!
Just like that Hanifa ta ji wani iri a game da Hanan, Haka kawai ta ji bata son ta… but why??7
Hmmmmm…. wahala don be like bicycle!!