RAYUWAR ASMAU CHAPTER 1
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 1
Da sunan Allah mai rahama da jin kai duk kan yabo ya tabbata ga Allah da kuma annabin sa Muhammad (SAW).
Ina godiya da Allah da ya bani ikon kammala *Koma kan mashekiya* Ya bani damar fara wani sabon littafi *ASMA’U HUSNAH*
To Alhamdulillah ina godiya ga rabbil samati wal ardi. Kuma ina rokan Allah ya bani ikon farawa lafiya tare da kammalawa lafiya
*Ameen*
Ya Allah ka jagorance ni wajen mika sakon da nake son mikawa. Allah ka shigen gaba.
Allah ka sa mu gama lafiya.
*Ameen!*
Wannan labarin kagage ne, ni na kirkire shi in kag yayi dai dai da rayuwar ki/ka akasi aka samu.
Da fatan zzai nishandar ya kuma fadakar da masu karatu.
*Nagode*
*Asma’u Husnah* littafinne da ya shafi soyayya, akwai abubuwan tausayi, da zalunci da yan matan suke da yawan yin sa nabin wajen malamai.*
*Banyi alkawarin baku posting kullun ba amman in lokaci ya samu zaku samu da yaddar Allah.*
Bari dai mu shiga daga ciki dan jin abinda ke ciki.
*THE WHOLE BOOK*
*DEDICATED TO MY LOVELLY MOMY*
Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana. Ameen Ya Allah.
Kwance take akan gadon ta. Katone, dakin ma kasan abin kalla ne.
Komai na ciki ruwan hoda ne. Gefen gadon durowa ce katuwa, sai mudubi, sai wani table dake gefe.
Littafai ne a cike akai. Gefen dama littafan isilamiyya daya gefen kuma na boko. Sai wata sofa dake gefe guda.
Sai wajen takalman ta, da jakun kuna, dakin sai kamshi yake ko ina a gyara tsab.
Sanyin AC ya ratsa shi, ga dadadan kamshi. Gefe wata kofa ce guda biyu daya wacce zata sada ka da cikin gidan ce. Daya kuma ta bandakin ta ne.
Idon ta a lumshe sai zuba murmushi take.
Baka ce, amman bakin ta me kyau ne irin sune black beauty. tana da hanci da idanu, da yar haba, sai kumatun ta dake a lubawa sanadin murmushin da take.
Girar ta cike take da gashi wanda yake a kwance ke kace gyara ta akayi ko zane akayi ma. Gashin kanta har gadon baya. Leben ta me kyau da taushi. Pink colour.
Magana take kasa kasa cikin zagin muryar ta mai dadin sauraro wacce duk wandan ya saurare ta sai yaso kara saurara ta.
Kunne na kasa dan jin me take cewa.
Muryar ya me sanyi da zaki naji tana cewa,
“Haba Yayana ai nima ka riga da ka dauken tawa zuciyar dan ban da wani abinda nake so da kauna da ya wuce kai.”
Fulon dake gefen ta, shi ta ja jikin ta, ta rumgume shi. Tana sauraron maganar da ake fadi daga can ban garen.
Murmushi ta sake saki wanda ya har sai da hakoran ta farare masu kyau, wanda yake dauke da wushirya ya bayyana.
Magana ta fara cikin shagwaba kamar zatayi kuka.
“Wallahi, nima haka.”
STORY CONTINUES BELOW

Shiru ta kuma yi tana sauke ajiyar zuciya.
Mikewa tayi daga kwancen da take, wayar ta cire a kunne tana sa ta a spearker.
Gyara zama tayi, tana gyaran gashin kanta da ya barbaje a bayan ta.
Murmushin fuskar ta be dauke ba.
Muryar sa me dadi ta cikaken namiji ta fito ras sai kace a dakin yake.
“Baby na kin fiya shagwaba fa. banda burin da ya wuce na ganmu tare a matsayin ma’aurata. Kece farinciki na. Dake nake son na rayu na kuma mutu dake.”
Murmushi da take yi ne ya nin ku. Dan na yanzu har da sauti.
“Nima haka, na maka alkawarin bazan taba barin ka ba har sai in kai ka bukaci haka.”
Ta fada tana daure kanta da ribon.
“Wayoo Allah baby nah! Tayaya zan bukaci rabuwa da rayuwa ta. ai Bazan iya ba.”
“Yayana ina son ka.”
“Baby na son da nake miki bazai taba misaltuwa ba.”
Ido ta lumshe lokacin da ya fara fado mata wasu dada dan kalamai.
Ji tayi kamar duk duniya ba wanda yafita dace da masoyi, ba kuma wanda yake cikin farin cikin da take ciki.
Ya dade yana sanyaya mata zuciyar ta da sata nishadi sannan sukai sallama badan sun so ba sai dan kiran magariba da sukaji ana yi.
“Baby nah! je kiyi sallah!”
“To Yayana.”
“Ayi mana addu’a”
“Insha Allahu.”
Kiss ya blowing ta cikin wayar, wanda taji kamar a fili yayi dan yadda tsigar jikin ta ta tashi.
Murmushi tayi, ta mike a hankali ta fada ban dakin dakin ta.
Masha Allah ban dakin ma kasan sa abin kallo ne. Komai na ciki shima ruwan hoda ne. Wato pink colour.
Wanka ta farayi sannan ta dauro alwala ta fito. Sai da ta goge jikin ta sannan ta dauki wata doguwar riga ta zuro ta dauki hijab ta, tada sallah.
Tana idar wa ta jawo kur’anin ta, ta fara muraja’a sai da akayi isha’i sannan ta dire shi ta mike ta tada sallah.
Ko da ta idar sai da tayi shafa’i da wuturi sannan ta dauko mannta cocoa butter, ta fara murje jikin ta dashi.
Ko powder bata shafa ba, sai man lebe da ta murza akan tatausan leben ta.
Riga da wando ta saka, rigar ta wuce gwiwar ta sai dogon wando.
Turare ta bade jikin ta dashi sannan, ta nufi kofar da zata sada ta da cikin gidan.
Katuwar barander ta fita. wacce take dauke da falo da aka saka mata kujeru masu kyau da tsari.
Ko ina tsab dashi, sai tashin kamshi yake, ido ta lumshe sannan ta bude su. Tare da sakin murmushi.
Matattakala ta nufa Wacce zata sada ta da babban falon gidan.
Tana sauka, Murmushi dake kan fuskar ta ya fadada. ganin yan gidan nasu duk sun halarta a falon.
Katon falo ne, da yasha kujeru masu kyau manya manya. Dakin sai tashin kamshi yake.
Cikin tafiya me daukar hankali ta nufi wajen Dadyn ta.
“Oyoyo Dady nah sannu da zuwa.”
Ta fada tana karasa wa wajen sa.
Hannun ta ya kamo,
“Oyoyo *Husnah* ya gidan?”
Murmushin fuskar ta be bace ba, idon ta akan Mahaifin nata. Ta amsa masa da.
“Lafiya lou Dady nah.”
Kallon ta yayi cikin kulawa, yace,
“Makarantar fa. Ince ba matsala.”
Wani murmushi ta kuma sakar masa.
“Dady komai lafiya Alhamdulillah.”
Shima murmushi yayi, yana kallon ‘yar tasa,
“Masha Allah! Allah kara dafawa.”
“Ameen ya Allah. Dady na taso kaci abinci kaji.”
Ta fada tana kamo Hannun sa.
Yayan ta da ke gefe yayi tsaki ya mike ya kamo hannun Mamin su.
Ya fara magana cikin kishi.
“Mami na taso muje kici abinci.”
Dariya Dady yayi. Ya girgiza kan sa.
*Asma’u* tace,
“Wai dan na kula da Dady na ko?”
“Ina ruwan ki badai Dady kika gani a falon ba kawai.”
Dariya tayi, Haka ma Dady har da Mami.
“Haba Yayana sorry!”
Ta fada da sigar tsokana,
“Muje Dady na.”
Suka nufi daining gaba dayan su.
Dady ta fara zubawa abincin sa, sannan ta hadawa Mami tana me murmushi.
Ita da yayan ta, ta hada musu.
“Yayana muci ko?”
Hararar ta yayi ya dauki cokali, suka fara cin abincin.
Sai da suka gama sannan ta kwashe kwanu kan tayi kitchen dasu ta wanke.
A falo ta same su. Gefen Dady ta koma.
“Dady Nah ya gajiyar aiki.”
“Gajiya babu.”
“Sannu toh! Allah kara budi da daukaka yasa ka gama lafiya ya jikan iyayen ka.”
“Ameen! Ameen! *Husnah tah.* “
“Mami sannu da hutawa.”
Ta fada tana daga gefen Dadyn ta.
“Sai da kika gama da Dadyn naki.”
Dady dariya yayi.
“To kar ta kula da nine. Wai duk kishi kuke da ni bayan kunsan yadda nake da *Husnah* “
“A’ah Dadyn *Asma’u* ni bance ba.”
Dariya ya kuma yi.
“Naji baku fada ba amman kun nuna a fuskar ku ko?”
*Asma’u* ce ta fara magana cikin shagwaba,
“Uhmm Dadyn in fa baka nan dasu nake kula.”
“To yanzu na dawo kuma sai a kula dani ko?”
“Eh man Dady nah.” Ta fada tana dariya.
Dariya sukai duka suka cigaba da hirar su.
Tara da kwata *Asma’u* ta mike.
“Dady nah sai da safe,”
“Allah tashe mu lafiya.”
Ya sumbace goshin ta murmushi ta sakar masa. Sannan ta wuce gun Mami.
“Mami nah sai da safe.”
“Allah kaimu.”
“Ameen Mami nah.”
itama a kumatu ta sumbace ta.
Murmushi tayi mata ta wuce gun Yayan ta.
“Yayanah!”
Banza yayi mata.
“Haba Yaya nah.”
Hararar ta yayi
“Shikenan. Yayana sai da safe.”
Ta shagwabe fuska tayi gaba. Janyo ta yayi, ta fado jikin sa.
“Haba *Asmy nah* “
Fuska ta hade idon ta na kawo ruwa.
“A’ah dan Allah, kada kiyi. yi hakuri. Please Baby Asmy.”
Dariya ta saki tai masa gwalo ta mike daga kan cinyar sa.
“Sai na fada wa Anty Zee nah.”
Ido ya zaro dan bai son su Mami suji.
Yatsan sa ya daura akan leben sa.
“Dan Allah man,”
Murmushi tayi. tana kada kai, Tayi hanyar benen.
“Yayana Swt dreams of Ur Zee.”
Ta fada da karfi, ido ya zaro. Ya mike ya bita a guje.
“Wayoo Dady night!”
Ta diba a guje tayi daki ta rufe kofar ta.
“Wallahi zan kamaki ne.”
“Naji din”
Mami da Dady kuwa dariya suke dan *Asma’u* indai batai tsokana ba bata jin dadi indai tana waje sai anyi dariya.
+
************
Tana shiga dakinta! Ta shige bandaki tayo alwala. Kayan jikin ta ta cire ta saka kayan bacci.
Sky blue din riga da wando ne, wanda suke hade da hular su.
Kan gadonta, ta haye tana me yin Bismillah.
Wayarta ta sa hannu ta zaro daga karkashi filon ta.
Kunna ta tayi, Ido ta zaro, tare da daura hannun ta akan bakin ta, missed call din shi ta gani guda biyar.
Murmushi tayi tana girgiza kanta.
Tana kokarin kira sai ga kiran sa nan ya shigo.
Murmushi tayi, ta dauka.
Shiru sukayi ba wanda yace kala. Sun dauki wajen minti goma a haka, Sai numfashin su dake tashi kawai.
Ido ta lumshe, Tana me tunanin kyakyawar fuskar sa.
“Baby nah!”
Yayi maganar da wata irin murya. Dan numfashin ta dake tashi ji yake kamar a jikin sa dumin sa ke sauka.
Kiran sunan ta da yayi shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
“Na’am!”
Ta amsa da wata murya me rikita me sauraron ta.
“Baby na ina kika shiga, duk na rikice. Gashi number su Mami na kira duk sunki shiga.”
Numfashi ta sauke,
“Ayyah Yayana Dan Allah kayi hakuri, ina wajen Dady nah ne.”
Ajiyar zuciya ya sauke,
“Dady ya dawo kenan.”
Itama ajiyar zuciyar ta sauke, tare da yin murmushi.
“Eh!”
“Ki gaishe shi.”
Ido ta lumshe,
“Zai ji.”
Murya ya kara yin kasa da ita,
“Baby na son ki zai haukatar dani fa.”
Ido ta bude da sauri, tare da zaro su ta mike zaune.
“Ya Salam Yayana tayaya?”
Wata ajiyar zuciyar ya sauke dan duk lokacin da *Asma’u* na magana tana kashe masa jiki ne.
” *Husnah* son ki yayi mun kamu sosai. Baki ji yadda naji dana kira bakya nan ba. wallahi *Husnah* nasan bazan taba daina son ki ba.”
Murmushi tayi, tare da sauke ajiyar zuciya.
“Shine kuma zai haukatar da kai.”
Tayi maganar cikin shagwaba.
“Baki ji yadda naji a time din bane.”
Kai ta girgiza tana murmushi.
“To am sorry Yayana Banyi dan na bata maka ba.”
“Kar ki damu nasan da haka. Nasan yanzu kuma ana gun Dady mantawa nayi na neme ki.”
Murmushi tayi. Ta lumshe idon ta, dan yana da saurin fahimta da bawa mutum uzuri.
“Nagode da fahimta ta da kayi.”
“Nagode da son da kike min.”
Sukayi murmushi a tare.
“To Baby kije kiyi
alwala kiyi addua ki kwanta.”
“Toh!”
ta fada tana tashi daga zaune da take. A speaker ta saka wayar ta wuce ban daki.
STORY CONTINUES BELOW

Sai da tayi, addu’ar shiga sannan ta shiga.
Alwalar tayi, sannan ta dawo Dakin.
“Nayi Yayana.”
“To maza yi Addu’a naji muryar ki.”
“Toh!” Tace, ta bude tafukan hannayen ta ta fara karantowa.
Falaki da Nas da Kul huwallahu Ahad
Kafa uku uku sannan ta tofa a hannun ta ta shafe jikin ta dashi.
Sai ta karanto Ayatul Kursiyu, sannan ta daura da amana Rasuli,
*Bismika rabi wa da’atu. Janni wa bika arufa’uhu fa ina amusakutu nafsi daru jamha wa ina aru salutaha fa hufazuha bima tahufazu bihi ibadakal salihina*
*Allahumma fina axabaka yauma tabu’asu ibadaka ×3*
*Bismikallahumma Amutu wa ahaya.*
*Subhanallah ×33*
*walhamdililah ×33*
*wallahu akbar ×34*
*Allahuma Fadiri samaqati qal’ard raba kulli sha’in wa malikatu. Ashadu al la’illa anta a’uzu bika min sharri nafsi wa min sharri shaidanu wa shirukihi. Wa an aftalihu ala nafsi au adillahu illa muslim*
“Shafe jikin ki ki kwanta da dama.”
Yin yadda ya umarce ta yayi sannan ya karanto mata shima.
“Rufe idon ki.”
Rufewa tayi,
“to kiyi bacci me dadi tare dani.”
Murmushi tayi tana gyara kwanciyar ta.
Kissoshi ya dinga karanto mata. Tin tana ji har bacci ya dauke ta.
Sai da ya tabbatar tayi bacci sannan ya kashe wayar sa.
Alwala yayi yai addu’a ya kwanta da tunanin Babyn sa a ransa.
Karfe sha daya Mami ta leko dakin nata, bacci ta same ta tana yi.
A gefen ta ta zauna, kanta take shafawa ta zuba mata ido. Ido ta lumshe sannan ta bude.
Addu’a ta kara tofa mata ta ja mata bargo ta fita tare da rufe mata kofa.
Karfe biyar da kwata, ta mike, ban daki ta shiga tayo alwala.
Tana fitowa, taji karar wayar ta.
Murmushi tayi da taga me kiran nata.
“Asssalamu Alaikum!”
“Wa’alaikum salam My Ra’isul khalbi.”
“Kin tashi kenan.”
“Eh na tashi.”
“Masha Allah kije kiyi ibada kiyi mana addu’a.”
“Insha Allah!”
Kan sallaya ta zauna sallah tayi raka’a biyu sannan ta dauko alkur’ani.
A dai dai lokacin Mami ta shigo dakin nata.
Akan sallaya ta ganta tana rairo karatun al kur’ani.
Ganin tana karatun yasa ta juya ta fita.
Jin za’a fara kiran sa yasa ta mike tayi raka’atanil fijir.
Tana idar wa ta mike tayo sallah. Ta jima tana addu’ar sannan tajawo kur’anin ta ta cigaba da karanta wa.
Sai da takai izifi biyu sannan ta mike ta dauko littafin makarantar boko tayi bitar karatun ta.
Tana son karatun bayan magariba dana asuba dan in ta karanta ji take, kamar an bude kan ta an zuba mata dan sauki da yadda take fahimtar sa.
Sai shida da rabi ta sauka kasa. Ko ina tsab sai tashin kamshi yake yi.
Murmushi tayi, Mamin ta akwai tsafta da son kamshi.
Kitchen ta shiga, Mami ta gani tana gyara nama.
Murmushi tayi, ta karasa. Durkusawa tayi sannan tace,
“Mami ina kwana?.”
Juyowa Mami tayi, ta kalle ta tare da yin fara’a
“Kin tashi lafiya?”
“Lafiya lou.”
STORY CONTINUES BELOW

“Kawo na taya ki.”
“A’ah jeki wajen Jamila, ki amso dankalin dana bata ta feraye.”
“Toh” ta amsa,
Fita tayi wajen masu aikin gidan ta karbo ta dawo.
kara wanke shi tayi sannan ta soya shi sama sama. Ta tsame shi ta kada kwai ta zuba kayan hadi ta dinga dibar soyayen dankalin tana zubawa cikin kwan tana soyawa.
Tana gamawa ta hadawa Dadyn ta kunun gyada da yaji madara yai fari tas da shi.
Tana gamawa ta gyare kitchen din sannan ta wuce sama.
Dakin ta kara gyara wa ta saka room freshner da turare da dadi sanyin AC dakin nata.
Kayyan jikin ta ta cire, ta shige ban daki danyin wanka. Sai da ta fara wanke bandakin ta sannan shima ta bade shin da kamshi. Sannan tayo wankan.
Tana fitowa ta tsane jikin ta, mai ta shafa, sannan ta hade jikin ta da kamshi. Body spary ta dauko na Alharaman da na man sa ta shafe jikin ta dasu.
Hoda kawai ta shafa sai kwalli da ta saka ya kara fito mata da manyan idanun ta. Sai man lebe da ta saka shima, ya amshi leben ta.
shirya wa tayi, cikin wata, bakar doguwar riga da akai mata ado da ruwan hoda.
Ruwan hodar mayafi da takalmi ta dauko, sai bakar jakar ta.
Dakin Dady tayi,
“Dady ina kwana,”
Ta fada tana karasawa wajen sa.
“Lafiya lou *Husnah tah* “
Tea da yake hadawa ta karba ta karasa hada masa.
Fulas ta bude ta zuba masa soyayen dankalin da tayi sai, farfesun duk ta hada masa.
Dankali ta dauka guda daya taci.
“Dady na tafi.”
“Ina zaki?”
“Makaranta.”
“Kin karya ne?”
“In naje naci a makaranta.”
Fuska ya bata. Dawo wa tayi,
“Menene Dady?”
“Zauna kici kinji ko?”
“Toh,”
Ta fada tana daukar kofi zata hada tea.
“Karbi wannan.”
Murmushi tayi,
“A’ah! Dady gashi ma zan hada.”
“Toh!”
Tana gama hadawa ta saka hannu suna karyawa. Kadan taci ta zare hannun ta.
“Dady na koshi.”
“Haba *Husnah* wai meyasa bakya son cin abinci ne.”
Murmushi tayi
“Dady duk abincin da naci.”
“Kina cin abinci kinji yar gidan Dady.”
“Insha Allah Dady nah.”
Mami ce ta fito daga daki.
“Iyye wai meyasa kike son kina deben ladan nawa, kici nawa kije kici naki.”
Murmushi *Asma’u* tayi,
“Mami duk abinda nayi na bar miki ladan.”
“Toh kinji dai.”
Dady ya fada.
“Naji amman tana bari na ina yin aikina.”
“Da kika samu me son yin aikin ma.”
“Rabu da ita dai Dady, haka take cewa in nayi aure bata san ya zatayi ba duk ta sangar ce fa.”
” ‘Ka niyar ki. Yaushe na ke fadan haka.”
“Haba Mami kin manta ne.”
“Ina ji dai!”
Ta fita. Tana dariya,
“Dady bari naje kar na makara.”
“To *Husnah* a dawo lafiya.”
“Allah yasa,”
“Karbi wannan.”
Juyowa tayi,
“Dady ka barshi da kudi a hannuna.”
“Haba *Husnah* ki karba, kika san wanda zai nemi taimakon ki kuma kika san abinda zai taso miki na kudi.”
“Toh Dady nagode Allah kara budi ya jikan mahaifa.”
“Ameen! Ameen! *Husnah* “
“Na tafi Dady nah.”
“Allah kiyaye hanya. Ayi karatu da kyau.”
“Insha Allah.”
Dakin ta ta wuce, ta dauki jakar ta. ta dauki waya tayi. ta dauki hoton kanta.
Dakin yayan ta, ta wuce.
Yana kwance akan gado ya rufa da bargo. Murmushi tayi ta karasa kan gadon nasa.
Yaye masa rufar tayi,
“Yaya nah!”
Ta kwala masa kira a kunnen sa. A gigice ya mike. Kallon ta ya tsaya yi.
Baya taja. Tana murmushi.
“Ina kwana Yayana.”
Hararar ta yayi,
“Allah *Husnah* ki shiga hankalin ki, ina bacci kizo ki tashe ni.”
“Yi hakuri Yayanah, makaranta fa zan tafi shiysa naxo na gaishe ka.”
“Wai ke tin yaushe na fada miki bana son kina tadani ina bacci.”
Wayar tace tayi kara, tana dubawa taga Zainab ce.
Murmushi tayi ta dauka.
“Besty ya aka yine.”
“Kin tsaya tsokanar taki ko? Bayan kinsa Yau Sir Sabir ne damu kuma kinsan baya bari a shiga in an makara, ki kalli agogo karfe tara saura minti goma fa.”
Ido ta zaro,
“Wayyo Sis gani nan.”
Ta fice a dakin da sauri. Mami taje taiwa sallama sannan ta dawo dakin Ya Buhari.
“Ya please! Kazo ka kaini wallahi Baba baya sauri.”
“Naki.”
“Dan Allah!”
Ta fara masa magiya. Har da su zubewa a kasa.
“Tashi muje.”
yai gaba tabi shi a baya.
Suna shiga mota, Aka kira ta. Dagawa tayi, da fara’a akan fuskar ta.
“Assalamu Alaikum!”
Ta fada dauke da murmushi.
“Wa’alaikum salam!”
Aka amsa mata daga can bangaren
“Ina kwana Yaya nah!”
“Lafiya lou. Kin fita dai ko.”
“Gani a hanya.”
ta amsa masa”Ina hoto nah?”
y
a tambaya.
“Bari na turo maka. Ina nawa?”
Ta fada tana lumshe ido.
“Naki yana can yana jiran ki.”
ya bata amsa.+
“Masha Allah ganawa nan zuwa.”
Ta kashe wayar. whatsapp ta hau tayi masa sending pics din da ta dauka.
Nasa ta fara budewa, kallon wayar ta zubawa idanu.
Wani hoto ne ya bayyana, akan wayar ta.
Wani hadaden Balarabe ya bayyana, yana sanye cikin bakar suit, idon sa sanye da farin gilashi.
“Masha Allah! Yayanah kayi kyau.”
Ta tura masa.
Amsa ya turo mata.
“Tabarakallah! Allah nagode maka da ka bani wannan kyakyawar yarinyar Allah ka mallaka min ita.”
“Ameen Ya Allah Yaya na. Ka fita ne.”
“Gani a hanya.”
“To kaje ka duba mutane sai anjima.”
Ta fada.
“Toh ki kular min da kanki kar ki bari kowa ya kalli fuskar ki.”
“Hmm ka kular min da kanka nima.”
Ta sauka a online. Titi ta kalla.
“Haba Yaya.”
“Mene?”
Ya tambaya yana kallon ta. Fuska ta dan bata ta ce,
“Baka sauri fa.”
Murmushi yayi ya ce,
“Karbi tukun.”
STORY CONTINUES BELOW

“A’ah yi hakuri. Amman dan Allah ka dada sauri kaga har tara tayi.”
ta fada tana marairaice masa fuska.
Sauri ya dada sukayi gaba, yana direta ta bude kofar da sauri.
“Nagode Yayana ka bada sako ga Besty nah.”
Ta fada tana murmushi
Hararar ta yayi.
“Ban da wayar ta ne ko baki.”
“Allah sarki Yayanah ji zanyi ko da gyaran da zan maka ne dan nasan na fika iya love.”
ta fada tana kanne masa ido daya.
Kokarin bude kofa yake ya fito.
“Yi hakuri!”
Ta fada tana yin gaba da sauri.
Kofar ajin ta karasa. Wani kyakyawan saurayi ne a ciki baki ne amman yana da kyau ba kadan ba.
Sai kayi tsamanin irin black american nan ne.
Sanye yake da farar shadda kansa ba kula sai gashi da ya kwanta luf luf akan sa.
Lekawa take yi jifa jifa. Ganin sun hada ido yasa tai saurin dauke kan ta.
Fita yayi ya zuba mata ido. Kai ta dukar kasa. Kallon ta ya cigaba dayi.
“Wa kike nema.”
Ya tambaye ta da turanci.
“Uhmm daman yanzu nazo ne.”
ta bashi amsa tana in ina.
“Shine kuma me?”
Ya tambaye ya.
“Ba komai.”
Ta fada jiki a sanyaye
“Karfe nawa kuke da lecture?”
Magana yake cikin turancin da ya kware a bakin sa.
“Sir karfe tara.”
ta fada masa kan ta a kasa.
“What say’s d time now (Karfe nawa yanzun).”
“Ban sani ba.”
Kallon ta ya tsaya yi. Sannan ya duba agogon hannun sa. Karfe tara da rabi.
“9:30am yanzu ne lokacin zuwan ki.”
“I am sorry Sir.”
“Naji daga yau kika makara kar ki kara dosan kofar ajina kinji ko?”
Kai ta gyada masa.
Kanta a kasa taki yadda su hada ido dan wani kwarjini yayi mata.
“Shigo ciki.”
Ya fada yana yin gaba
A gaban allo ya tsaya tayi hanya zata shige ciki.
“Come here (zo nan),”
Ya fada yana nuna mata wajen da zata zauna. A gaban sa.
Komawa tayi ta zauna, duk dagowar da zatayi idon sa na kanta. Kuma duk tambayar da zaiyi ita yake jefawa.
Sosai take bashi amsa dan *Asma’u* akwai kokari.
Sai karfe sha daya yabar ajin nasu. Tana zaune a inda take zaune sai ga Zainab ta karaso wajen ta.
” *Asma’u* amman fa kinyi sa’a har malamin nan ya bar ki kika shigo.”
“Nima nayi mamaki dan kinsan haka yan wacan shekara suka sha fama dashi.”
“Dan Allah kina dai kula.”
zainab ta fada cikin damuwa dan bata son kawar tata ta rasa aji.
“Kar ki damu yau ma akasi aka samu ne.”
Wani malamin ne ya shigo musu, yai musu lectures dan sai karfe daya ya fita.
Yana fita suka shige, masallaci. Sai karfe daya sukai sallah sannan sukayo cafeteria.
Lemo kawai ta karba, sannan ta tambayi Zainab me take so. Ta siya mata.
Suka samu wajen zama.
“Sis wannan gayen fa ya dame ni da maganar ki.”
Murmushi *Asma’u* tayi,
“Wane gaye fa.”
STORY CONTINUES BELOW

Hararar ta Zee tayi,
“Wai har kin manta.”
Asma’u ta ce,
“Wallahi na manta.”
Zee ta ce,
“Wannan Nasir din dan unguwar mu.”
Murmuahi Asma’u tayi ta ce,
“Oh na tina. Ya akayi.”
Dan hararar ta zee tayi ta ce,
“Wallahi ya dame ni ne.”
Kallon Zainab Asma’u tayi ta dan saki murmushi ta ce,
“Ki bashi hakuri kinsan dai irin karatun da muke ciki ko?”
Zainab ta ce,
“Haka ne, amman ai karatu mun gama tinda asibiti zamu tafi, ya kamata ki maka ma miji da mun kammala sai mu shige gidan mu ko.”
“Haka ne Zee amman nifa nayi karama da yawa!”
Hararar ta Zee tayi.
“Shekara sha tara din shine kike karama. Da da akewa yan shekara goma aure fa suce me.”
“Haka ne, Sis ina tsoron aure ne, kuma dai bari kinji na fada miki. Nayiwa kai na miji kuma nasan shi zai fahimce ni ya kuma gatan tani.”
Murmushi Zee tayi,
“Masha Allah wane wannan.”
“Ya Aslam mana.”
Asma’u ta bata amsa tana lumshe ido.
Dariya Zainab ttayi ta ce,
“Wane ma Ya Aslam.”
“Ke Zee har kin manta shi. Dan gidan Yayar Mami nah fa. Ta Abujar nan.”
“Oh nagane shi. Abinda har gida sun zo tare da Love dina.”
Murmushi *Asma’u* tayi.
“Dan haka ki bashi hakuri. Nasan Nasir nada hankali da ilimi komai dai ya hada. Amman ki bashi hakuri.”
“Ba komai zan san yadda zan sanar masa insha Allahu.”
“Nagode.”
“kar ki damu.”
Wayar tace tayi kara,
Tana dubawa ta saki murmushi ta dauka.
“Assalamu Alaikum Baby “
aka dada daga can bangaren
“Wa’alaikum Salam.”
Ta amsa masa murmushi dauke a fuskar ta.
“Kina lafiya dai ko?”
Ya tambaya.
“Lafiya kai fa?”
“Lafiya Alhamdulilah da fatan kinyi sallah kinci abinci.”
“Yaya duk nayi biyu nake jira tayi mu shiga aji.”
“Masha Allah abinda na kira naji kenan.”
“Nagode da kulawar ka.”
“Ba komai.”
“To kai kaci abincin da sallah “
Na dai yi Sallah abinci kuma sai na gama aiki zan ci.”
“Kai Yaya!”
ta fada a shagwabe
“Yi hakuri befi mutum uku ba kinji “
“Da gaske.”
“Eh!”
“To dan Allah kana gamawa kaci.”
“Insha Allahu!”
“Yauwah nagode.”
“To sai ajima ko.”
“Aha bye.”
Ta katse wayar.
Zainab ce ta kalleta.
“Kece kuwa *Asma’u* “
“Me nayi?”
“Soyayya “
“Haba Aunty Zee ina wata soyayya anan. In ma soyayya ce ke kika koya min ai.”
“Ni kuma?”
“Eh man yadda ko da yaushe kike yi a gabana.”
Dariya tayi,
“Tashi mu tafi.”
“Toh!”
Suka tafi hall din da zasuyi lectures.
Tinda suka shiga sai bayan hudu suka fito. Suna fitowa sallah sukayi su.
Lokacin har anzo daukar Zainab dan haka ta tafi ta bar *Asma’u* tana jiran azo daukar ta.
Ba tayi minti biyar da zama ba, aka zo daukar ta.
Tana mota Ya Aslam ya kira ta.
“Baby nah ya makaranta.”
“Gani a hanyar komawa gida.”
“Sannu kin gaji ko?”
“Wallahi, na gaji jikina sai ciwo yake min”
“Sannu kinji ai da ina kusa da nayi miki tausa ko.”
Murmushi kawai tayi.
“Yaya nah kai fa ka tashi.”
“Ina fa, aiki ma zan fita yanxu.”
“To Allah bada nasara.”
“Ameen! Sai anjima.”
Ta kashe wayar. Idon ta ta lumshe, gaskiya tayi sa’a samun Yayan ta a matsayin me sonta, wanda tasan tin kafin ya fara son ta yake kula da ita da riritata bare yanzu kuma.
A rana sayi waya sau nawa banda text din safe na rana da na dare. Yayanta na son ta sosai da duk tafiyar da zaiyi tsarabar ta daban ce.
Haka nan Ga soyayyar Dadyn ta da itama take kara sa mata nutsuwa.
Tana shiga gida ta tadda Mami a kitchen dan haka kitchen ta shige ta fara taya ta aiki. Sai gab da magariba suka gama sannan ta mike ta hau sama.
Wanka tayi ta saka kaya mara sa nauyi. Turare ta feshe jikin ta sanna ta hau kan sallaya tayi sallah.
Tana idar wa ta dauko kur’ani ta fara bita sai da ta kai ixifi daya sanna taji kiran sallah isha’i mikewa tayi, tayi sannan ta fita zuwa falo.