RIKICIN KAUNA CHAPTER 11 BY MARYAM SALISU MAI DALA

wayance da kallon bayanta ya ce “To kuma wa za a ce mata.” Yayi tamkar ma bai san sunanta ba.

Ita kuwa har jikin ta yayi dan sanyi ta ce

“Lamimi ce fa Tafida ni din har ka mance suna

na. Tafida ya ce “An yi haka! Lamimi in sha..

Kawai in ruwa yayi a kansa, Lamimi kuwa an buge farantin goron nata Dubu ce tace “Tafida dama amana ta kake ci ban sani ba.” Ta sake daga ragowar ruwan dabbobi da ta kamfato

a kwatarniya ta sharara masa duka a jiki har fuskarsa bai san sanda ya kwala mata mari ba ta rike fuska yana son yi mata magana bakin ciki ya hana masa tamkar ya fasa kuka don wani wari da ruwa awakan yake, a yayin da ita kuwa Lamimi tunmi ta bar gurin Dubu ta rike fuska tana cewa “Tafida ni ka mara a kan Lamimi da na kama kuna ci min amana! Ni ka mara!?

Don yadda take daga murya matan cikin gidan dake lokon har sun leko yayin da dama tun ruwan da ta zuba masa a jiki yara har sun dan tsattsaya a gurin yana da tsare gida idan bai so ba don duk

wasa da dariyar da ya iya idan ransa ya baci dif zaka ganshi kamar ma bai tada dariyar ba, to haka ne ya hanawa yara ce masa komai. ganin haka jama’a na neman taruwa a kansa ya sa kawai ya yi gaba da sauri ya bar gurin idon sa ya kada ya yi ja.

Kaka na tsakar gida Nana na tufke mata kai ya shiga jikinsa kaca-kaca ya shiga, kaka ma tsorata tayin tana tambayarsa da kyar yake gaya mata Dubu ce tayi masa haka, “Ita ko Dubu me ya. sameta haka.

Ya ce “Kishin bala’i.”

Nana kuwa ta yi tsam ta mike ta ja mishi ruwa a rijiya guga biyu ta zuba a bokitinshi na wanka sannan a hankali ta koma ta zauna amma har lokacin ba ta yi masa magana ba tana dai kallon ikon Allah kadai, sai shi da ya ce ta shiga dakinsa ta miko mishi doguwar riga ta shigan ta mika masa. ya ga sanda ta ja ruwan ya san nasa ne ya dauka ya shige bayi, kaka tana sake sallalallami don taqi bari a karasa tufkar, har ya fito da doguwar rigar a jikinsa tana sake mita da maimaita zancen, ta ce

“Wannan wane irin abu ne Dubu ba

za ta dinga komi na nutsuwa ba.”

Tana daure kanta da Nana ta karasa tufke mata shi ko ya zauna a ‘yar tsugunon da Nana ta tashi yana maidawa kaka yadda akayin tana sake sallallami da rike baki, har Nana zata wuce gida amma ta tsaya ta ja ruwa guga biyu ta zuba akan kayan da Tafida ya cire ya zubo a bokitin da ya fito wanka, tana zubawa din kuwa ta kade gyalenta ta fice har zuwa lokacin ba tayi magana ba, da alama duka sun saba da irin hakan nata ba ta ce masa sannu ba ko Allah ya kiyaye amma ta yi mishi abin da zai gyara sanda ta zuba din kuwa ta fice suka kalli juna kaka da Tafida kaka ta ce “Ina

ruwan Nana miskila ce tun tana yarinyar ta take a haka yayin da shi kuwa Tafida ya ci gaba da bata labarin abin da ya faru.

Tafida ya ce “Ni kaka na rasa wacce iri ce Dubu yanzu a hakan zata zo mu zauna tana irin wannan abu tamkar wata marar hankali, duba fa kaka a yadda na zo dubi irin ruwan kazantar da ta zubamin a jiki don wallahi ko da nayi wankan a yanzun a tsane nake da jikina.” Yana sake sansana jikinsa.

Kaka ta ce “Ai Dubu bata abi na hankali wani lokacin don ta ganka da Lamimi ai ba hauka ya kamata ta yi ba.”

Tafida ya ce “To Kaka ko da ta ganni auren ta nayi da za ta ce kada na yiva wata magana, kuma ko da auren nata nayin ni ba cewa aka yi namiji zai iya auren mace fin daya ba.” Kaka ta ce “Gaskiya fa!”‘

Ya ce “To bare duka baikon mu kawai akayi da dubu, to amma bari zata sani zata gano kurenta.” Kaka ta ce “‘a ka kyaleta ba cewa kayi ka

mareta ba ka rabu da itan, don yanzu abin sawa a

bakin mutane ayi ta yayatawa bashi da yawa, ace

an sa baikon ku kuna ta rikici.”

Tafida ya ce “To kaka sai na bari tai ta yi min cin kashin da ta ga dama kenan.” Yana duban kansa.

Kaka ta ce “Ka dai rabu da ita Tafida ni zan

samu dubun nayi mata fada.”

Kawai girgiza kai yayi yana kwafa, kaka na

kallonshi, ta ce “Nafi son Tafida ya koyi hakuri da

Iyalinsa tun yanzun, ba wai sai anyin ba don ko da

kaga ana yawan rabuwar aure to akwai rashin

hakuri da kawaici.” Ta ce “Yanzu dubi Iliya nan.”

Tana nuna mishi bangaren kudu da bakinta.

Tafida ya kalleta da alamun tambaya, ta ce

“Haba Iliya fa wannan na gidan Malam Audu.”

Tafida yana daga kai alamar ya tuna ta ce “To

shi fa cewa akai matarsa fa ba wata cikakkiyar

mace ba ce, ga masifa amma a haka yake hakuri

da ita.”

Tafida: ya sake kallo ta da tambayar amma har

yanzun bai magana: ba, itama kakan ta fahimto tace “Yo ba cikakkiyar mace ba ce mana! Don bata

da Kirji fayau yake bata kuma da Kugu don ana tunanin ko mata maza ce, tun aurensu a haka ake kallonta kusan wata bakwai kenan.”

Tafida kuwa dafe kai yayi da duka hannu biyun ya ce “Na bani kaka, na bani! Ni yanzu kaka saboda Allah ina ruwana da irin wannan zancen.” Don har yana yi da karfi don ta kyaleshin yana son mikewa

Ta ce “Ba dole na gayawa Tafida ba? Mace ba kirji kwata-kwata ai rabin mace ce, tunda kuwa kai ma auren ya doso ka.”

Tafida kawai mikewa ya yi ya ce “Ni kaka k daina min irin wannan.”

Ta ce “Dole na yi maka Tafida tunda kuwa zaka auri mace.”Ficewarsa: ya yi ‘yana kunkuni ya bar ta tana mita. Washegari kuwa tun Tafida bai fito ba Dubu ta iso don sanda ya fito din ya ganta ko kakan bai yiwa magana ba itama kuwa kakar bata ce mishi ga Dubu ba, sai dubun ce da take labarta wa kaka yadda abin yake, kaka ta ce “To ke ce ma ai dubu, daga Tafida ya tsaya ya amsar min goro sai ki dauki abin da manufa biyu, har kina zuba masa kazamin ruwa a jiki nan ya Karaci fadansa a jiya nace zan sameki, Dubu idan baku shirya a yanzu ba ke da Tafida ban san sai yaushe din ba, amma

Hmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE