RIKICIN KAUNA CHAPTER 3 BY MARYAM SALISU MAI DALA

kaina, ai ni wallahi Kaka idan ba wata larura ba

• mace kwara guda ta isheni rayuwa, mu haifi yaranmu duka da ita amma har yaushe ka dinga jawa kanka abin magana a unguwa kawai baka san bakin wani ba.”Kaka ta ce “Haka ya ga zai fiye masa shima ko

Allah ba zai bar masa diyoyin haka ba kawai ya dinga mai da yara kananan zawarori.” Tafida na girgiza kai.

Ta ce “Na ji kace kai mace guda ta ishi rayuwar

‘kana nufin daga dubun shi kenan kai.” Tana kallonsa.

Ya ce “Kaka rabu da wannan itama fada mukayi tun jiya.”Kaka ta balalo ido “Fada Tafida! Duk kwakwar ka (naci) da duha take to me ya hada kun?”

Tafida yana wanke hannu ya kuskure bakinsa ya zubar ya ce “Kai Kaka har layar sai an farke miki, kawai dai mun yi fada, kuma wallahi idan bata daina abinda take ba nina hakura gaba daya.” Kaka ta kalleshi da tsoro a fuskarsa ta ce “Zo nan Tafida zauna na ce koma ka zauna!” Tana sake muna masa inda ya tashi.

Tafida ya maida abin wasa da yadda ya ga ta tsoratan sanda ya koma ya zauna ya ce “Ni wallahi

• Kaka da rabuwa kikayi da ni da maganar aure kika

barni na tafi birni na koyi kasuwanci sosai idan na dan tara sai na dawo nayi aure na tafi da matar.”

Kaka ta dan hantare shi sannan ta ce “Ji nake kana zancen zaka hakura da dubu. Tafida wai me yake damunka ne? Dubi “yar gidan Da’u har tayi wayo dubi Kasimu matarsa haihuwa ta biyun zatayi, Balele ma da aka kasashi anyi baikonsa Larabar da ta shige kai kadai ne a baya kake wani zance daban anya kuwa Tafida?” Tana kallonshi,

“Dubi yarinyar nan Dubu yadda take takowa har gida ta zo tayi min wahala da jikinta ta yi min bauta, kuma da kudinta take min wani abun amma Tafida baka gani har kake fadin zaka hakure mata da bakinka kake fadar haka Tafida! Tafida.”

Ya dinga daga mata hannu yana “Ya isa haka

Kaka ya isa, ai ba ki ji ba nace idan ba ta daina ba ita ai ta san abinda ta yi min.”

Kaka ba ta kula ba ta dora a inda ta tsaya, tace

“Yammata nawa ke son aurenka Tafida, goro yanzu na daina siya saboda masu kaunarka Tafida kullum da na hadu da wata zata bani ko a kawomin har gida.” Tana sake kallonshi.

Tafida ya shiga mirgina kai alamar kosawa da zancen, “Amma Tafida duk ka watsar.”Yace “Kaka ni fa ba ce miki nayi bana son.

maceba ko bana son aure. Kaka ta ce “Sai dai kar a kuma…

Maganar ta bawa Tafida haushi kawai ya mike

– yana “Ni kar, ki kuma, yi min irin, wannan kaka br bana so ni a kyaleni idan nayi aure

Bad page bad page bad page

“To kai ko Tafida me yasa zakayi hakan?”

Da’u yake fada don har yana dafe hularsa daga keya don dama shi haka sa hularsa take kullum zaka ganta a keya a haka zaka tarar ya saka gashi kuma da son saka hular don ko a ‘yar fitowar lokacin da Tafida yayi sallama da shi sai da ya sako hula.

Tafida ya ce “Ka kyaleta fada mukayin jiya wai har tana ta daina tuka tuwo ta bani na ci.

Da’u ya yi dan tunani ya ce “Nufi kaki aure kenan to kai ne ma dai Tafida ai.

Tafida ya katse shi Kai dai ya isa ni na wuce sai zuwa dare.”

Ya fito daga lokon su Da’u don har yana waiwayen kofar gidan nasu, yayin da Da’u ya bishi da kallo yana ‘yar dariya wai fada sukayin da kakarshi.

Ai kuwa karfe goma safiya bata karasa din ba sai ga kaka a gidansu Da’u ta tambaya ina Da’ un har ya fita sai matar Da’un ke cewa ya tafi wajen me kosan kusa da Alto mai faskare, kaka ma tayi tunanin haka Tafidan ma yana yawan zuwa can ya siyo kosai ko ya ci a can sai ya aiko mata da nata, to amma tana zuwa Da°u kadai ta tarar sai Balele, da sauri Balele ya mike “Kaka, kece anan tun yanzu.”

Hmmm

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE