RIKICIN KAUNA CHAPTER 5 BY MARYAM SALISU MAI DALA

RIKICIN KAUNA CHAPTER 5 BY MARYAM SALISU MAI DALA

yanzu ka dawo nufi ya ji .” Yana

kallonsa.

Tafida baiyi magana bai yi magana ba, ya ce

“To kaka na kuka dan ta dauka ma da garin kwata-kwata ka bari ashe kana nan, kana nan tun yinin yau baka tako kafarka ka zo ta ganka ka ganta ba, haba Tafida bana yi maka kallon haka, Tafida.” Ya shiga shafa kai kawai, babansu Nana ya ce

“Idan ma wani abu ya farun ai baka yi fushi da gida ba.”

Tafida dai duk ya takura a gurin, kaka ta karba ta ce “Ni ko da yake son tafiyarsa birni ni ba hanawa nayi ba, amma ya fara ajiye iyalin kansa yanda duk inda yaje yana tuna ya ajiye sun zai waiwayo da wuri.”

Baban su Nana ya ce “Ai kaka ke ma abar ya waiwayo kice ba wai iyali kadai ba.”

Ta ce “Wai ma dai ko kuma ya yi ya wuce da matarsa amma a haka yake son ya tafi sikam dinsa babu aure ga rayuwar birni da hure kunne.”

A ran Tafida yana kiyasta ka ji wai kaka cetake cewa ita ba hana shi tafiya birni tayi ba, yana sake kiyasta a kalla abinda ba ta son ta ji ya ce zai yin

“kenan a rayuwarsa kawai ta fadi hakan don ta jono da zancen rashin aurensa da bai yi ba, Babansu Nana ya ce “Aure kam insha Allahu zai yi, Tafida

zai yin kamar kowa, kin san aure shi yana zuwa babu wani jinkiri sai an yin, yanzu don bai zo din ba ne, amma ki barni ni da kaina zan sami babansu dubun don mu san yadda za a yin a zo a yi baiko.”

Kaka ta ce “Shi kenan.”

Shima babansu Nana ya cewa Tafida “Shi kenan Tafida, amma kada in kuma jin irin hakan daga bakin kaka ka ji ko.”.

Tafida ya amsa ya tashi ya fita, sannan suka ci gaba da magana da kaka, itama kuma Nana tana makure a dakinsu tana jiyo komai don ma kusa da dakin nasu suke kuma sun dage labule saboda zafi.

Tafida maraya ne gaba da baya bashi da kowa sai kakar nan tasa wacce ta haifi ubansa sai ‘yan tsirarun dangin mahaifiyarsa dake dan nan gaba da kauyen nasu kakkara dake cikin Manbila anan jahar Adamawa, mahaifinsa Malam Sale ya rasu tun Tafida na da shekaru goma sha biyu a duniya, a lokacin kuwa ana tsaka da jegon Nana, ko wanka basu ajiye ba, don sa’adda labarin mutuwar mahaifin Tafida ta taddasu Malam Mado abokinsa (mahaifin su Nana) shi ya shige gaba aka je har can birni aka taho da gawarsa anan kauyen nasu aka rufe shi, mutuwar tasa kuwa ta girgiza kaka sosai dama duk yawanci nasa na jiki, don haka dama nan gidan shi take zaune da sirikarta babar

Tafida, tun mutuwar tasa kuwa Malam Mado (Babansu Nana) ya sa aka sanya musu kwano a gidanshi duk dare har kawo wannan lokaci, dama kaka Malam Sale kadai ta haifa, shima kuma sai gashi Tafida kadai ya haifa ya tafi sai dai shi din ya binne uku a kasa biyu yayyen Tafida sai guda kuma kanwa ce ga Tafida.

Rayuwar gidan su Tafida ta mike Malam Mado na agaza wani abu, wani abu kuma dama dolen ayi hakuri tunda dama ko da ran Malam Sale watarana baya gari dolen hakurin ake yi, bayan *yan shekaru kadan kuwa dangin mahaifiyar Tafida suka nemi ta koma inda suke ko aure ta samu tayin, da farin ki tayi sai da kaka ta nuna mata babu wani abun ta barsu ita da Tafida tunda dama ko da suke a tare Tafida na manne a jikinta, ta dinge nuna ko ina ta tafin kuma Tafida zai tako har inda take ya zo ya sameta, to Allah ya kaddarama uban Tafida ne kadai ita ta na duniya don kafin yiwuwar auren da zatayi wani dare ciwon cikinta ya tashi kafin safiya kuwa ta rasu, abinda ya sake janyowa Tafida tausayi kenan da shiga ran mutane musamman dama shi ba mai rashin kunya bane, maraicin Tafida ya Karasawa kaka ta dage da lallabarsa da yi masa abinda yake so don Tafida ya shiga ran kaka kowa kuma ya san haka in bacin

girma a yanzun da Tafida yayin amma da daki guda suke kwana, Tafida na da aboki Bilya dan gidan Malam Mado yayan Nana kenan duk kuma tsara suke da juna, watarana Bilya ya shiga yana son su fita da Tafida, Tafida kuwa ranar yini yayi yana hararwa (amai) ga zazzabi don haka kaka ta hana su fitan don har ya zura riga da kaka ta tisa shi ya koma daki, yana bacin rai, da ikon Allah* kwana da wuni ana neman Bilya ba a ganshi ba hankalin kowa ya tashi kowa kuwa cewa yake a tambayi Tafida, sai a tarar shi Tafidan ma gaba dayan jiyan bai leka kofar gida ba bashi da lafiya, sai ma yamamci wanda duka gari ya dauka da neman da ake yiwa Bilya sai baban Da’°u ke cewa shi kuwa ajiyan kamar yaso yaga Bilya a tare da Magaji dan gidan maigari, dama tunda yaji neman da ake yiwa Bilya a tun daren ya tuna haka to amma yana dan shakkar megari kada ya yi masa kwakwazon ya lakawa Magaji a yadda ya ke jin magaji a ransa, sai da tura ta kai bango sannan ya sanar da hakan, ai kuwa ana bincikar magaji yayi wuki-wuki ya ce sunje da shi ruwa amma shi bai fitan ba, anan ya yi jagora har rafin, abin tausayi ana dubawa sai ga Bilya har ya taso saman ruwan, asheya mutu tun a jiyan, jikin magaji har rawa yake don toro a take ya dinga kuka yace shi tun a

jiyan yayi-yayi ya taimake shi ya kasa, wanda daukacin mutanen gurin suka gano tsorata yayin tun a jiyan yaki fade don har a lokacin a cikin tsoron yake, aka gano shi kansa magajin da kyar ya sha, don haka ya kasa taimakon Bilya, shi

Malam Mado ma don zullumi abin ko da aka ce ruwa suka tafi bai bisu rafin ba gida ya dawo, ya hada kai, sai ga tashin hankalin da yake gudu ya gani ya biyoshi har gida don Bilya har ya kumbura ya sha ruwa yayi fam da shi wai don ma an matse masa wani kafin a zo wanda da kyar mutum biyu suka iya dagashi.

•Mutuwar Bilya kuwa ba karamin dukan Tafida tayi ba dama ba shi da lafiya sanda abin ya faru to kuma alhinin haka ya jawo ya Kara rafkewa don yafi wata kusan biyu a kwance daga baya ya ware amma ko bayan tashin rasa Tafida ya fi makaranta a saboda tare suke da Bilya ajin su daya hAtta gurin zama haka ko makarantar arabiya a karatu daya har jiran daya yake yi, bacci kadai yake rabasun, don watarana ma a taren suke kwana duka a daki guda har kaka, amma idan Malam Mado ya fahimta sai ya ce a’a don ita kaka a lokacinko bacci ba zai raba ta da Tafida ba, to wannan shakuwa ce ta janyo Tafida ko shiga gidan su Nana ya daina sai da wani kwakkwaran dalili

Hmmm

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE