RIKICIN KAUNA CHAPTER 6 BY MARYAM SALISU MAI DALA
ko abu mai Karfi sannan zai shigo don lokuta da dama ya kan gayawa kaka shi gani yake idan ya shiga gidan tamkar zai ga Bilya, to a haka ma makaranta don har babansu Nana ya kira shi daga baya ya yi masa fadan ya yi hakuri ya dinga zuwa, don shi yana son su yi karatun na boko, da har ya koma daga baya kuma ya daina zuwa, a shekarar da ta zagayo kuwa Innar su Nana ta haihu kowa ya miyi tunanin Bilya Malam Mado zai maida sai aka ji yaro ya karbi Sama’ilansa suke kiransa da , sai daga baya Tafida ke gayawa kaka gara ma da ba a maida Bilya ba don zai dinga yawan tuna masa abokinsa.
Haka rayuwar Tafida ta tashi shi da kakar shi, kaka na sonshi shima yana sonta sai dai duk wannan abun bai hanasu haurawa ba wataran, musamman idan Tafida ya, yi ba daidai din ba don kaka na da zafi don tafi Tafida sosai, sannan kaka bata da fiyalewa in dai kai mata ta rama ne kawai, gata bata son munafunci ko a dinga rufa-rufar abu, a’a ita komai kai tsayen ta ke fadarsa ko da kuwa. zai maka zafi ta dai fadi gaskiyar abin, sai dai duk wannan abu kaka tana sane da maiyi mata ta ko kuma san mutuncin kayi mata tana kuma son mai son nata, shi yasa suke qimanta juna tsakaninta da gidan Malam Mado (baban su Nana). Haka shima birni yana kuma sha’awar mutanen ciki don har tallan gonarsa ya taba kaiwa wani Alhaji Dalla anan Kauyen a tun lokacin kaka batasa kin tafiyarsa ba ya ce yana son Alhaji ya bashi kudin rabin gonar ko ya siyi ramfarsa ta kasuwa.
Da gudu Alhaji Dalha ya taso zai biya, ai sa’adda kaka taji har kuka ta yi ta kuma hada shi da Malam Mado baban su Nania, dole aka bar batun don fur taki don a lokacin tana cewa, kuma ka rasa wa zaka kai wa ya siya din sai Alhaji Dalha mutumin da sai dai idan ya san shi zai ci riba da kai sa’annan zai yarda, da abu, wai su nan mai kudi a garin nan, amma bai san taimako ba, bai san tausayi ba amma shi Trafida duk bai damu* da wannan ba tunda bai taba nema a gunsa ba wannan din ma hakkinsa zai biyashi idanya siya, don a karshe Alhaji Dalha har aike ya yowa kaka amma taki a saida komai dole ya hakura. Shi Tafida ya ajiye maganar tunda, ya ga kaka ranta bai kwanta ba.
Alhaji Dalha shima yake kuma kusan, shine me kudi. a kauyen kamar yadda kaka ta fada din kuwa haka halinsa yake, a dan dama,war da akayin na ba’tun
‘yar kadarar Tafida kuwa yaga nana aiko yace malam Mado shi in dai bai yiwa Nana ma’auri ba shi ya yiwa dansa Shehu Kamu dake birni yana karatu da fari kamar zai yarda don shima ya san yaron amma daga baya ya yiwa Alhaji Dalha maganar sai a jira ya dawo idan yana sonta itama kuma Nanan tana sonshi sai a hadasun to a haka aka bar abin to mutanen kauyen sun camfa Alhaji Dalha da asiri don ko wani abu naka ya nema ka saida masa gonar ka ko wani abun idan baka siyar ba to kuma daga baya da kanka zaka je ka nemi da ya siya din to hakan da suka dauka ko da baya yin komai su dai sun barshi a hakan yakeyi, don ko kaka ma sai da ta sa aka yi mata addu’a a kansu da gonarsu don har tafida yana cewa kai kaka duk fa camfin mutane ne babu wani abu da yake yi ta ce, kai tafican sanda zai yin fada maka zai yi, to irin wannan ce ya jawo akwai masu son Nana (Aisha) da yawa a kauye sosai amma kowa yana tsoron ya fito ya ce yana sonta ka da Alhaji Dalha ya ji ya yi masa wani abun don an san ya ce ya yiwa dan sa rikon Nana, shi kuwa’ Malam Mado hakan bai dameshi ba don ko ya zo din idan Nana ta ce bata so yana ganin ba zai takura ta ba, wannan ne ya ja Nana ke dan karatun ta na boko da na arabi ba tare da an ta gudidin ba ta yi aure ba, duk da duka Nana tana cikin shekara ta sha hudu, amma a kauyen ta kai minzalin aure ko tana hanya don duka budurwa bata fin sha biyar zuwa sha shida an aura da ita, Nana na san karatun na boko don har wasu suna cewa wai ko don zata auri dan boko ne har akwai masu kiranta Nana ‘yar boko, don himmarta da tafiya bokon, amma duk da camfin mutane Habu ya dage akan Nana yana kuma son ta sosai a yayin da Nana kuwa gata nan ne tamkar har yanzun bata san menene shi kansa son ba sai dai nutsuwar ta da yawan shirunta da kan birge mutane to hakan ne ya ki rabuwa da Habu kullum yana kan hanyar ta ta boko.
Dubu itama itace wadda suka shirya da Tafida ta na son Tafida kamar tai yaya don sau tari ita ce take zuwar masa zance amma ta wayance kamar ba haka ta je ba, ko kuma da ta ga sun zauna a mahadarsu da yammaci sai tai ta shigewa har sai ya tashi ya bita, ko kuma jikin wani mangoro da suke zama da rana idan zafi yayi yawa, haka shima Tafida yana son Dubu sai dai ‘yar rawar kanta ce wata rana ke bashi haushi, har su dan bata, ko su yi rikici akan wani abun da yaga tayin wanda baya so, to a haka rayuwar kaka da Tafida take suyi fada wataran wataran kuma a yi dadi. To har a washegari kaka lallabar Tafida take da safen yana fitowa kofar dakinsa da karamar rigar ciki a jikinsa (singileti) zafi yasa har ya fito, yana ciki mika da salati ya hangi Nana ta katanga itama daga Kofar dakin su ta fito tayi shirin boko tsaf da itan, suna hada ido ya sauke hannaye yana kebe baki alamar bata yi ba, Nana ita ma ta kalle shi ta juya ta janyo kofar dakin ta sanya dan itace don kada ta bude tana waigowa yana sake kede mata baki ta kwala masa harara ta wuce abinta har ta wuce gidansu Laure ta biya mata tana kiyasta jiya har ana wani tatarradin ya bar gari amma da ga tashinsa yanzu har ya fara tsokanar mutane.
Kaka ta ce “To yanzu Tafida yini gudan jiya inaka samu ka ci abinci.”
•Tafida ya ce “Ka ji ma kaka da wani irin zance sai in kasa cin abinci ko na siye ne ai mutum baya tarkar abu sai ya san yana da tudun da ya dafa.”
Kaka ta dan kalle shi ta ce “Shi kenan Allah ya kyauta.”
Ya ce “Amin dai.” Yana ‘yar dariya ya ce
“Kaka dan sammin ruwa nayi wanka mana “
Ta dubeshi kadan ta ce “Sai raguwar wanda
Nana ta zuba min jiya gashi can.” Tana nunowa da baki “Idan bai isheka ba sai dai ka ja wani.” Ya ce “Kaka da sassafen nan mutum bai karya da komai ba sai ya karya da jan ruwa.”
Ta ce “Ai ka karya da wanka kai ba iyali ba ba komai ba.”
Tafida bai gano da yadda ta yi masa maganar. ba don itan ma sai bayan ta fada din take dan kallon idonsa don kada ya kuma bore mata irin na jiya to shi din bai kula ba ya ce “Wallahi zafi ne ya hanani bacci kaka ai da yanzu ban tashi ba, ni dai don Allah ki bani duka idan na fita zan turo almajiri ya ja miki.”
Kaka ta dan harari inda ta rufe ragowar ruwa. ta ce “Ai gashi can amma da ka fara cin tuwonka da na dumama ga kokon shima da zafinsa.”
Ya mike ya ce “Ina dai zuwa.”
Ya juye ruwan ya shiga wankansa bai dade da shiga din ba sai ga Dubu ta shigo tamkar wacce aka jehota yadda ta shigo firgai-firgai har ya sa kaka ta zubo mata ido tana kallonta gashi kuma ta bugo sammako akan yadda ta saba shigowa Dubu ta fahimci hakan, sai ta dan wayance ta gaida kaka, kaka na amsawa ta ce “Hala wani abu ya faru Dubu na ganki a hargitsen.”
Dubu har ta danji nauyi sannan a hankali ta ce
“Dama kaka naga jiya kwata-kwata banga Tafida ba, sai yanzun dana tambayi Da’u yake ce min ai
ya bar gari.”Kaka ta ganota ta ce “E jiyan dai baya nan
amma dai a gida ya kwanan shine ma yanzu a bayi
yake wanka.”
Daidai lokacin da Tafida ya budo kofa ya fito
amma ganin Dubu ya sa shi saurin komawa ya
sako ‘yar rigar da ya shiga da itan ya fito ya shige
dakinsa kawai ba tare da ko magana ya yi masu
ba, kaka ma ta san titsiyen da Dubu tayi masa
bashi da cikakken kaya a jiki yasa ba. zai yi
magana ba, sai da taga ya ziro doguwar riga ya fito
yana shirin fita ta ce “Tafida, Dubu fa kai ta zo
dubawa wunin jiya ba ta ga gilmawarka ba.”
Ba tare da ya kallosu ba ya ce “Ina zuwa.”
Kawai ya fice tamkar wanda zai leka wajen ya
dawo amma Tafida shiru-shiru har rana ta fara
lekowa, sai ga yaro da kosan kaka ya kawo mata
kaka ta ce “Uhum! Yayi
karyawarsa a waje,
Tafida na rasa irinsa ya san fa kina nan kina
tsimansa.”Dubu tayi dan murmushi ta ce “Ai kwana
biyun ma ko kulani ba ya yi.”
Kaka ta dan kalle ta ta ce “Dama kuwa ya ce
kun yi fada ko me ya farun.” Tana kallon dubu: Dubu da ta dan kallo ta da a tsoracen don ta dauka ko Tafida ya fada mata abinda ya farun, sai da ta ji tana tambayar me ya farun sannan ta dan Sauke fuska kawai tayi shirun kaka tayi dan nazarinta, ta fahimto ko meye bai rasa nasaba daga gareta, ta ce “To Allah dai ya kyauta, ko ma dai meye ku yi ku sasanta din don ko jiya munyi maganar zuwa baikon ku.”
Dubu ta dafe Kirji tana zazzaro ido kamar ba daidai ta ji ba, sai kuma ta dan dauke kai don ta tuna a gaban kaka ne, kakar ma ta gano ta, ta kuma cewa “Cikin satin nan komin abinsa dai a haka zai ajiye aje a yi baiko a tsaida muku lokaci kamar kowa.”
Dubu ta shiga murmushi tana sosa kai, kaka ta ce “Kuma duk abin Tafida nasan na kafin aure ne idan anyi auren sai kin ji yayi shirunsa yana lallabarki.”
Dubu ta shiga sosa kai, kaka ta ci gaba “Don har addu’a nakewa Tafida Allah ya rabashi da irin halin su magaji.”Dubu da kanta ke a sunkuye a hankali ta ce
“Kaka alamu ma ba daya ba don dama shi
Tafida bai cika kalle-kallen mata ba shi kuwa dama dan megari da yammar nan inda yake zama ana dan taruwa dama zaman kallan mata ne a ga wacce zata wuce me kyau da mara kyau, budurwa ko bazawar.”
Kaka tana kallonta ta rike baki yadda duk ta san haka, a ranta tana kiyasta ko da yake su
‘yammata ne zasu fahimta ita ko ina take kula, ta ce “Allah dai ya kyauta ya rufawa ‘yan baya asiri.”
Dubu ta ce “Amin.” Sannan ta mike ta yiwa kaka ‘yan kaye-kaye da shara ta dauraye mata kwanoni har kaka ta ce mata ga tuwan Tafida nan tunda kuwa ya kai iyanzu ba zai ci ba, ko zata cin, a hakan tana dan jin nauyi ta saka guda ta ci ta tafi.
A washegari kuwa labari har ya bazu Magaji ya kai kudin aurensa gidan Nalamin Tudu gurin Atine ita kuma ya gano, anan kowa ya gane dama don ya aureta ne ya rabu da Furera da ciki, shi ne zai maida gurbin nata da Atine don Atinen ma bata so sosai don ance sai gursheken kuka take amma ance yayi bajinta don kudin aurenta kadai jaka biyar ya bade kafin sadaki da kayan lefe (naira dubu) su Tafida na tattauna wannan abin takaici a mahadarsu da yammaci, salon Baffa (Malama Bello) ya iske shi yana nemansa nan ya saka takalmansa ya fita ya sanarwa kaka, da Manbila zashin Baffa ya turo sunyi baki daga birni Kano zai je ya taya bakon kwana, can din ko ya kwana har a washegari suna tare dasu Captain Tabir,
Hmmmm