RIKICIN KAUNA CHAPTER 8 BY MARYAM SALISU MAI DALA

tana dan hadawa da gudu-gudu saur-sauri, suna dariya ita da Laure, yayin da Tafida ya mike da sauri yana kiranta ina sunyi nisa su ma su Balele suka hau mishi dariya, Tafida ya shiga kurarin lallai babu wanda zai hana mishi bugun Nana Kanwar bayansa.

Da’u ya sake kecewa da dariya ya ce “Ai ni

Nana birgeni take yi cikin kwancivar rai take

“Rama tsokanar da kake mata, kai kuma ka hau fúffuka tamkar ba kai din kake farawa ba.”

Yayin da Tafida kawai shiru yayi yanaci gaba da kwafa yana girgiza kai, a maimakon shi ke fara tashi yau sai shi aka bari a karshe saboda rashin takalmin da zai baro gurin Da’u ya ce bari idan ya karasa gida Zai turo a kawo masa in yaso sai ya sanya ya, taho a haka suka barshi yana sake kufula yayin da suke dariya.

Amma gab da Da’u zai karasa gidan kaka ya badu da ila da tsofaffun takalman Tafida ya ce wai

Nana ta bashi ta ce ya kaiwa Tafida yana can jikin man goro, yace Yawwa Ila maza Tafida na can yana jira.”

Da’u ya zarce gidan su yayo alwala don la’asar tayi, shima Tafidan lallabawa ya yi jikin masallaci, ya yi alwalwa ya shige don kada ma

wani ya zo ya ganshi kafa ba takalmi don haka sa’adda Ila yazo bai tadda shi ba, ya shiga nemansa Tafida ya duba ko Da°u ya aiko masa bai hango kowa ba don haka ya gaji da jira dole ya ture kunya ya dake ya tako a kufule ya iso gida, tunda ya shigo din kuwa yake cewa “Wallahi kaka

Idan na kama Nana kada ma ki bani hakuri.”

Kaka ta kalleshi sosai tana tambayarsa ya shiga gaya mata, a ‘karshe ya ce “Yanzu kaka duba fa a yadda ta bari na tako duk girmana haka na dinga boyon hanya.”

Kaka ta yi ‘yar dariya ta ce “Akwai abinda kayi matan amma haka nan kawai Nana ba zata kwaso takalma ta barka ba.”

Tafida ya ce “Kin ji ki ko kaka! Kin ji ko! Zan kamata don sai na bugeta tasan ni ba sa’anta bane.”

Kaka ta ce “Ai sai ka shirya, yo ni ai Nana ta yi min kyan kai da ta kwaso mini abina akan idonta na siye shin, don jiya iyanzu ma ban siya ba, kuma tasan muddin wani zai kyaleka cikin su Balele to zai zare ne ya bar maka nashi kai kwa ba za kai wani magana ba wai kai mai kara.” Tana kallon Tafida yana yin kamar ba haka bane.

Kaka ta ce “Na nawa sai nayi magana kace zaka siya min wani to ko zaka siya din amma 

yana da kyau ace mutum shi ke kashewa da kansa, don ran nan takalmi na ne na gani a kafar matar Kasimu ba ta ji nauyi ba kuwa sai ni din cema nayi kamar ban gani din ba don me yiwa itan bata san nawa bane na kuwa san ba kowa ne ya yi silar zuwa kafarta ba sai mijinta Kasimu wanda ya ke kai ne ka fita da su to kana fita da shi din kuwa da zarar sun ganshi sabo za su zira su ma.”

Nana da ke gidan su duk tana jiyowa don ma tana shirin dora musa sanwa, Tafida ya ce “Duk da hakan kaka yanzu kamar ni Nana ta kwaso takalmin ta kawo miki ta bari na tako da sawayena.”

Kaka ta ce “Ba ta ba wa lla wani ya kai maka ba.”

Ni ba wanda ya kai min.” yana sake girgiza kai yana kwafa.

Ilan ne ya katse shi da ya shiga dakin da zai yi. yayi sallama da gare-garensa a hannu yace

“Yawwa Tafida ga takalmin inji Nana ina ta nemanka duk na zaga ko ina.”

Kaka ta ce “Af to ka gani sabani kukayi da Ila nima naga sanda ta diba ta fita da su.”

Tafida ya karba ya ce “Ni duk wannan ba zai hanani bugun Nana ba idan na kamata.” Don yana bakin kofar dakinsa har yana karawa da farfi don

ta jiyo shi, itan kuwa tana jinsa yana cewa “Duka duka nawa Nanar take da zata dinga yi min haka.”

Kaka ta yi dariya don yadda yake yi din da yadda ya raina girman Nana, ya jiyo muryar Nanar

ni.” Yana sake kwafa yana girgiza kai.

Kaka ta ce “Babu dadi shiga ta hanci, duk

Ila ne ya katse ta yana miko mata itatuwan da

Kaka ta ce “Nana kuma? Na meye?”

Ila ya ce “Ta dai ce no kawai in kawo mikin.”

Kaka ta dan daga murya ta ce “Ko Nana na

kusa ne?”

Daga can gidan su Nana ta ce “Na’ am kaka.”

Ta ce “Naga Ila da itace.”

Nana ta ce “E kaka na Tafida ne ajiyewa za ki yi tunda akwai me gari akwai ‘yan doka randa duk

Tafida ya bugeni shima idan an bugeshi sai ki yi masa ruwan zafi da su.”

Ba kaka ba hatta Inmarsu Nana dake daki sai da ta sa dariya, tana girgiza kai da wannan rikici na Tafida da Nana ita ko Nana ta ci gaba da abin da

yake gabanta don koma a jikinta ba ta damun ba da abinda ta fadan, nan shima Tafida ya bar kaka na dariya ya shige dalinsa yana kwafa.

Da dare Malam Mado ya riske Kaka a gidan bayan fitar Tafida da kadan don ya gama cin abincinsa kenan, Malam Mado ya ce sun yanke magana da baban Dubu cewa ranar lahadin sama za a je baikon Tafida don haka ta gayawa duk wanda ya kamata ya sani ya sani, musamman bangaren mahaifiyarsa dake nan gaba da su, Baban su Nana ya ce kada ta wani damu duk dan abin yin baikon zai ba da, gara a sa din don idan nasa

Tafidan kan shi zai fi maida hankali

Kaka ta shiga godiya don har tana kwalla tana tuna Malam Sale mahaifin Tafida tana fadoshi, Malam Mado yana nuna mata a ba wani abun, yanza gidanshi da giden nan duk kusan daya ya dauka, a hakan ya barta tana lissafi duka kwanaki takwas kenan ta rage daga ranar tana nan tana jiran.

Tafida, ya shigo bai shigo din ba har ta kwanta, don shima babansu Nana yana shigowar da neman

Tafiden ya fara.

Sai ma da safen kaka take labartawa Tafida yadda sukayin da Bahansu Nana, da ranar da aka tsaida ta zuwan baikon da duba, Tafida ya kalleta kawai amma ya yi shiru yana ji tunda har

Hmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE