SALON SO CHAPTER 9
SALON SO CHAPTER 9
Faruk ya ce, “Ba ruwana babu inda za ni bare ta
zo ka ci mata mutunci ta zo ta rinka ganin h rashin
kirkina.
Haidar ya ce, “To ni ka kai ni wajen ta na ganta,
Faruk ya yi murmushi, Haidar ko dai ka so ma
son ta ne?”
Haidar ya rintse ido ya ce, “Wallahi ban san
lokacin da son yarinyar nan ya yi min dirar mikiya
ba, ya shige ni.
Inna kwanta da daddare Allah Allah nake gari ya
waye don na ga kyakkyawar fuskar matata kuma
kanwata, wallahi ni kadai na san yanda tsananin
son jawahir yake raina, kai abin da na yi wa
Kausar a gananta ma na yi ne don na auna na ga
tana so na kuwa ko ni kadai nake shirme na.
Faruk ya ce, Ka ga irin abin da na so ka gane
tuntuni ka ki, to yanzu kuwa in ta ji halin da kake
ciki sai ta ce don ka ga ba za iya kwanciya da ita
ba ne, shi yasa ka nemi shiri da ita.
Haidar ya ce, “Ai likita ya ce zan warke fa”. Ko da
yake yanzu ne lokacin tantance wanda take
sonka don Allah da wadda a kayi auren sha awa.
“Haidar ya ce, Ni dai don Allah ka je ka taho min
da sahibata ko don na ga halin da take ciki.
Faruk ya ce, “Zan je ai yanxu
Kausar ta turo kofar ta shiga fuskarta a murtuke
babu alamar fara’a, ta je gefe daya ta zauna ba
tare da ta kula wani a cikinsu ba. Faruk ya mike
Haidar bari na je in dawo ko? Duk yanda muka yi
zan zo ka ji.
Ya ce, “Don Allah ka je fa yanzu kada ka ki zuwa
ka ji. Faruk ya ce Insha Allahu kuwa yanzu zan
je.
Faruk ya fita ya bar su Haidar ya juya ya kalli
Kausar ya ce, “Me ya same ki ne na ga kamar
ranki a ba ce? Ko cikinne yake ciwo?”
Ta zumbura baki, “Kai yanzu har ka manta da
barnar da Jawahir ta yi maka a jikinka har kake
cewa a je a taho da ita? To wallahi ni ba zan
yarda ba don ta ga ita ba ta da amfani a wajenka
shine za ta nakasta min kai, wato ka zamo marar
amfani, to wallahi ba zan yarda ba don ita ma sai
na nakasta ta, sai dai duk abin da za a yi a yi.”
Haidar ya daka mata tsawa ya ce, “Ke ki shiga
hankalinki kina ganin duk da son da nake wa
jawahir da ta yi miki abu sai da na yi mata marin
da ta gigice, to wallahi ki shiga hankalinki idan
kika sake kika taba min mata wallahi sai kin yi
mugun raina kanki, don sai kin yi mamakin abin
da zan yi miki.” Ta mike ta yi waje tana kunkuni
ta zari mota ta nufi gidan Yakumbon Haidar wato
kakarsa ta wajen uba, ta je ta zayyane mata
maganganun karya da gaskiya ta gaya mata,
Yakumbo ta hau sababi ka ji mu da tsinanniyar
yarinya don ba ta son sa shine take neman
hanyar kashe shi, to wallahi bi ba yarda zan yi
ba, tashi ki koma asibitin gani nan zuwa yanzun
nan, “Kausar ta koma asibiti ta tarar su Anti da
Momy da su Yaya Abba sun cika asibitin taf, ana
ta jajen abin da ya faru.
Shi kuwa Faruk da ya je gidan Haidar yayi
sallama falon, su jawahir suna daga kicin suka
amsa sallamar suka fito falon, Faruk ya nemi
waje ya zauna jawahir da Bilkisu suka gaishe shi,
faruk ya ce, Haidar ne ya turo ni na zo na ga
halin da kike ciki in kuma da hali ki zo mu je yana
son ganinki. “Jawahir ta sunkuyar da kai ta ce,
“Gaskiya Yaya Faruk ba zan je inda yaya yake ba,
don in na je ban san irin wulakancin da zai yi min
ba, ka ga kuwa da na je ya bata min rai ai gwara
ban je ba.
Faruk ya ce, “Wallahi Haidar yana wani hali na
mutuwar sonki kin san miskilancinsa ya rasa ta
hanyar da zai bi ya nuna miki Kaunar da yake
miki don yanzu da kin ga irin magiyar da lallamin
da ya rinka yi min sai na zo gare ki dakin
tausaya masa.
Kafin ta yi magana Bilki ta ce, “Faruk bari mu
karasa girkin da za mu kai masa sai mu fito mu
je.” Faruk ya ce, to shi kenan bari na je na dawo.
Bilki ta zuzzuba komai a fulas ita kuma jawahir
ta je ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin atamfa
ja! Super Holland dinkin filet ne ya kama jikinta
sai zani da dankwali da ta daura, farar hoda
kawai ta shafa a fuskarta sai dan man leben da
ta shafa ta dauko jan mayafi da jan takalmi ta
saka, kunnanta fashon din yari ne me jan dutse a
tsakiya. Bilkisu ta tafa mata “Amma
yarinyar nan kin yi kyau, kwalliyar taki ta burge ni
sai dai kash kin manta a shafa hadin turarukanki.
Jawahir ta yamutsa fuska, “Kin san fa inda za mu
je za ki ce na shafa hadin turare. Bilki ta ce, to
meye ba wajen mijinki za ki ba, ai gwanda ki
shafa turarukan da kamshinsu zai gigitar da shi
kuma ga karin lada a wajen Ubangiji, don duk
sanda mace ta yi abun da zai farantawa mijinta
har ya ji dadi a ransa to Ubangiji zai ba ta ladan
da ba ta san adadin yawansa ba.
Jawahir ta ce, Haka ne bari na shafa don na
fuskace shi yana son kamshi.
Sun jejjera fulas-fulas din a dan kwando me kyau
ta lullube shi da farin yanki me adon bakin les da
fulawoyi a jiki. Faruk ya dawo suka dunguma a
motarsa zuwa asibiti.
A lokacin ba kowa duk sun tafi sai kausar kawai
da take zaune kan kujera tana karanta jarida, ba
ta daga kai ba balle ta kalli wani a cikinsu. Faruk
ya ce, “To ga ta nan na cika alkawari ko, ga ta
na kawo maka
Haidar ya yi murmushi ya ce, “Ai kuwa na gode
Bilkisu ce ta fara gaishe shi tare da yi masa ya
jiki. Cikin fara’a ya ce, “Ai jiki Alhamdullahi.”
Jawahir ta durkusa cikin dari-dari da rawar
murya Kamar
mai shirin kuka ta ce, “Yaya ina wuni? Ya jikin?
Ya ce, “Lafiya lau jawahir ya naki jikin.?
Ya sa hannu ya dago ta daga tsugunnun ya shafi
kuncinta, ya ce, “Wai haka kuncinki ya tashi
hannuna ya fito radau na marin da na yi miki,
sorry Babyna ki gafarce ni, “Kafin tayi magana
aka turo kofar aka shigo tare da sallama,
Yakwalkwal ce ta shigo rike da hannun Sayyid.
Sayyid ya fincike da gudu ya nufi jawahir yana
cewa, “Anti na anti na, shine rannan kika gudu
unguwa kika bar ni ina ta kiran ki ba ki zo kin tafi
da ni ba. “Jawahir ta dauke shi ai yau da kai zan
tafi kai ta kwana a can ko? Jawahir ba ta ankara
ba ta ji saukar mari a kuncinta, Yagwalgwal ce ta
kuma hau fada, “Annamimiya me kuma ya kawo
ki wajen jikana kin so ki kashe shi, Allah bai baki
nasara ba shi ne kika biyo shi nan ki karasa shi
ko?
Haidar kuwa tuni ya diro daga gadon jinyar ya
tare jawahir yana cewa, “Haba Yagwalgwal ya za
ki doke ta ita ma fa ba lafiya ce da ita ba, me ta
yi miki?”
Yagwalgwal ta ce, “Ubanka ta yi min, shege
sallamamme so kake yanda uwarka ta mallake
Alhaji kai ma jikan mallake ka za ayi,
“Yagwalgwal ta ci gaba da nuna jawahir da dan
yatsa tana yi mata sababi, daga yau na gaya miki
ba ke ba Haidar in ke mayya ce ki ci kanki da
kanki, haka kawai hankalinsa ya kwanta yana
zaune da matarsa lafiya za ki zo ki bata musu
zama.
Jawahir ta mike jikinta ba kwari za ta fita Haidar
ya yi saurin riko hannunta yana cewa, “Haba
Yagwalgwal ya za ki zo ki korar min matata ki ce
sai ta tafi? Ai ba ita ta kawo kanta ba ni na sa a
je a dauko ta in ta tafi waye zai yi jiyya ta?
Kawai mutum da matarsa a nemi raba su. Kan ya
rufe baki bakinsa Yagwalgwal ta ba shi nasa
marin ya dafe kunci ita kuma ta ci gaba da
sababi tana nuna shi da dan yatsa, “Ka shiga
hankalinka ka san da wacce kake magana, idan
ba ka san ciwon kanka ba ai ni na san ciwonka,
yarinya ta nakasa ka ka zamo marar amfani
amma ba za ka guje ta ba, wata rana ma ranka
za ta raba ka da shi.
Jawahir ta fincike hannunta ta yi waje cikin sauri
Haidar ya yunkura zai bi ta Yagwalgwal ta rike
shi, Bilkisu ta bi bayan jawahir yayin da Faruk ya
rufa musu baya. Da kyar da ban hakuri ya shawo
kan jawahir ta shiga motarsa don ya mayar da su
gida. Faruk ya ce, “Don Allah don Annabi jawahir
ki yi hakuri da abin da tsuhowar nan ta yi miki.
Jawahir ta yi saurin katse shi, “Haba yaya Faruk
ka fi kowa sanin ta yanda a ka yi aurenmu da
yaya, ba son sa nake yi ba na aure shi don
biyayyar iyayena na zo nake zaman hakuri da shi,
ya tashi ya dankaro min kishiya ni duk hakurin da
na yi a kansa ba a gani ba kenan.
Fashe da kuka Faruk ya ci gaba da rarrashinta ki
yi hakuri jawahir ki tuna aure kike, aure kuwa
bautar Ubangiji ne kada bacin ran wasu ya sa ki
sabawa megidanki kin ji?”
Yanda na san ki da hakuri da ladabi da biyayya ki
ci gaba da yi komai me wucewa ne wata rana sai
labari kin ji?”.
Ta daga kai ya ce, “Yauwa ko ke fa gobe ku
shirya da wuri sai na zo na kai ku ta ce to. Ya
sauke su a gidan shi kuma ya koma asibitin shi
kuwa Haidar tun bayan fitarsu jawahir da
Yagwalgwal ta rike shi don kar ya bi su gado ya
koma ya kwanta ya yi rigingine ya rufe idonsa.
Maganar duniya babu wadda ba a yi masa ba
amma ya yi musu shiru ko motsi bai yi ba dole
suka gaji suka hakura suka bar masa dakin.
Faruk ya shigo ya dinga lallaminsa yana ba shi
baki tare da va shi hakuri sannan ya tashi ya
jawo kwandon da jawahir ta jero masa kayan
abinci.
Dakakkiyar sakwara ce lukui da miyar agushi mai
wadataccen nama, sai jalof din taliya da lemon
kwakwa. Haidar ya ce, “Ka ga yarinyar nan da
zan bata mata rai ba za ta ki yin abinci ba don
gudun kada ta bar ni da yunwa.” Faruk ya ce, ai
haka ake so ka ga yanzu sai ka rike ta da kyau
ka nuna mata garanci wanda ba ta samu ba a
baya. Haidar ya ce, “Allah dai ya ba ni lafiya amin
in ji Faruk yayin da ya zuba musu abincin a filet
din da ta zubo suka ci sosai dan shi kansa Faruk
ya yaba da dadin girkin nata.
Can kuwa Bilki ta mike don tafiya gida, “To ni zan
tafi jawahir sai dai gobe zan zo da wuri na raka
ki mu sake dubo shi. Jawahir ta hangame baki ta
ce, “Don kin ji Faruk ya fada ba kya tsoron mu je
a yi mana wani sabon wulakancin da ya fi na
yau.?
Bilkisu ta ce, “Insha Allahu hakan ba za ta faru
ba gwanda ki je, kada su samu kafar raba ki da
mijinki ga shi kuma yanzu kuna son juna. Jawahir
ta ce, “Shi kenan Allah ya kai mu goben na gode
Bilki da kaunar da kike min, da ba ni shawarwari
masu kyau da kike yi, Allah ya kara mana dankon
zumunci a tsakaninmu amin. Da haka suka yi
sallama ta tafi.
Jawahir ta shiga dakinta ta kwanta tana tunanin
abin da ya faru yau da ita.
Faruk ya fita ya yi sallar insha Haidar ya kalli
Kausar ya ce ke ba za ki yi sallar ba ne na ga ko
magariba ba kiyiba?
Ta ce, “A’a ina ruwanka a yin sallah ta ka ga
malam kawai ka ji da abin da ya dame ka. Faruk
ya turo kofar ya shigo Kausar ta zuba masa
harara tare da jan tsaki ta mike ta bar dakin.
Faruk ya taimakawa Haidar ya yi Sallah, Haidar
ya daga hannu sama ya dade yana addu’a
sannan ya shafa ya xuba tagumi.
Faruk ya cire hannun tagumin ya ce, “Haba
malam menene kuma? Ka yi hakuri a kan larurae
da ta same ka, ka yarda da kaddara ko?
Haidar ya ce, wallahi ba wannan ne ya dame ni
ba halin da jawahir rake ciki nake tunani kada fa
ta Gudu
gidan Inna ta kuma boye ta ka san ranta ya ba ci
dazu da abin da Yagwalgwal ta yi mata. Faruk ya
ce, “Ba na jin za ta fita har gida na kai ta kuma
na babbata hakuri ka san yarinyar akwai biyayya”
To don Allah ka je ka taho min da ita ta kwana a
wajena ka ga gidan ba kowa sai masu aiki.
“Faruk ya ce, “Ka yi hakuri da safe ai za ta zo ka
ga yanzu dare ya yi yanxu haka ma ta kwanta.
Haidar ya ce, “Haba Faruk don Allah ka taimaka
min ka je ka taho min da jawahir yanzu duk
girman gidan nan ta kwana ita kadai sai masu
aiki? Faruk ya ce, “Shikenan bari na je amma sai
na biya na dau Hafsa don ita ma ta zo ganin
likita.”
Haidar ya ce, “Ko dai ta harbu ne.? Faruk ya yi
murmushi ya ce, “To ga mu dai ga Allah don mun
sa rai.
Ya fita yana dariya ya biya ya dauki matarsa
Hafsa suka tafi. Ya ce, Ya ku ka yi da likitan? Ta
ce, “Gwaje gwaje ya yi min ya kuma dauki
fitsarina ya ce da safe a zo a karbi result din.
Faruk ya ce, “To Allah ya taimaka mana ya sa
abin da muke nema ne, ta ce Amin. Suka yi wa
juna murmushi.
Suka yi fakin a harabar gidan Hafsa ce a gaba
don ita take buga kofar falon nasu da yake kulle.
Jawahir da take takure a falo don zuciyarta cike
take da tsoro da fargaba ka sancewar ta ita kadai
a sashen ta yi tunanin ko ta kirawo ‘yan aikin
Kausar su taya ta kwana sai kuma ta fasa, to jin
bugun sai ya dada tsoratar
da ita. A tsorace ta je gaban kofar cikin rawar
murya ta ce, “Wanene?” Faruk ya ce, “Bude mu
ne, ta kalli agogo karfe tara gabanta ya fadi,
Allah ya sa dai lafiya? Ta bude kofar ta ba su
hanya suka shigo Faruk ya ce, “Sarkin tsoro da
kin zata barayi ne suka zo sa ce ki?” Ta yi dariya
ta kamo hannun Hafsa ta ce, “Wai yaushe rabon
ki da gidan nan? Ko da yake ban sani ba ko kina
zuwa wajen amaryarku Kausar, “Hafsa ta yi
dariya ta ce, Ni ina zan zo gidan nan mutuniyata
ba ta nan ta gudu ta bar min abokin miji ya zamo
abin tausayi a gari?” Ga ba daya suka yi dariya.
Faruk ya ce, “Kar dai a gaji da mu dan mun kuma
zuwa da kokon bararmu da karin ban hakuri
megida ya ce, a zo a tafi dake don Allah ki kwana
a wajensa. Ta yi shiru can ta ce gaskiya ni ba
zan je wajensa na kwana ba. Faruk ya ce,
“Subhanallahi, kin san hukuncin matar da mijinta
ya yi kiranta ta ki zuwa kuwa? Ko kina so ki
hadu da fushin ubangiji ne?
Jawahir ta ce, “Gaskiya Yaya faruk ba zan je ba,
ba Kausar tana can ba?
Ai ita ta saba kwanciya da shi ni in na je ina da
abin da zan yi masa ne? Faruk ya ce, “Haba
jawahir kada ki yi haka mana da iliminki da komai
ki yi hakuri ki amsa kiran mijinki mana.
Ta ce, “Haba yaya Faruk har ka manta irin
zaman da na yi da yaya Haidar a gidan nan ni
bani da hakki a kansa sai shi yanzu yake da
hakki a kaina har zai neme ni?” Ta sa kuka ta
mike tayi daki, “Wallahi ba inda zan je”. Ta turo
kofar dakinta ta kulle.
Hafsa ta ce, “Gaskiya fa ni fa ban ga laifin jawahir
ba, don gaskiya an zalinceta” Faruk ya dakawa
Hafsa tsawa tare da cewa, “Yi min shiru ana
neman sasanta magana kina dada tunzurata. Ya
jawo wayarsa ya yi danne-danne. Haidar ya
dauka, “Hello” Yauwa Haidar ka kwantar da
hankalinka kayi hakuri mun zo mun tarar jawahir
tayi bacci amma don Allah kada ka tsayar da
hankalinka da safe kafin na tafi office zan biya na
dauko maka ita. Haidar kafin ya ce, wani abu tuni
Faruk ya katse wayar ya kuma kasheta gaba
daya don ya san halin Haidar ba kyale shi zai yi
ba.
Haidar kuwa tun daga lokacin wata zuffa ta rinka
tsiyayo masa, hankalinsa ya yi mummunan tashi,
jikinsa sai rawar sanyi yake yi. Ba jimawa zazzabi
mai zafi ya rufe shi. Nan da nan jiki ya rikice a
ranar da sai Abbansa ne da yaya Abba suka
kwana a wajensa. Ba shi da wata magana sai ta
ambaton an bar jawahir ita kadai a gidan nan sai
masu aiki kada wani abu ya samar masa ita.
Yaya Abba ne yake dan karfafa masa gwiwa yana
tunasarsa. Yawan ambaton jawahir da Haidar
yake yi ya sa Kausar ta yi fushi ta baro asibitin
ta dawo gida. Jiyya ta koma hannun yaya Abba
da Faruk, amma asibitin kullum cike yake da yan
uwa da abokan arziki sai dai rashin matansa a
wajen. Duk da haka Yagwalgwal ba ta fasa yada
habaici da kananan maganganu ba don haka Anti
ba ta son yawan zuwa don ita take yiwa
habaicin.
Kamar ita ta haifa mata Haidar din
Yau kwanan Haidar hudu kenan a asibiti suna zaune a
dakin jinyar, Faruk da yaya Abba Haidar ya ce da
su, Faruk da yaya Abba ku fara hada kaya ku
karbo min takardar sallama.” Yaya Abba ya ce,
Ah sabo da me? Cikin raunanniyar murya Haidar
ya ce, “To kun ki zuwa ku rarraso min jawahir ta
zo gareni na ganta ko hankalina ya kwanta. Tun
da haka ne gwanda na koma gidan na yi jinyata a
can inda zan samu kulawarta.
Shi dai yaya Abba ba ya son jawahir ta zo wajen
nan ko don sabo da kananan maganganun da
Yagwalgwal take yi, don haka ya yi shiru bai ce
komai ba. Haidar kawai ya fara hada kaya Faruk
ya tausaya masa, ya ce, “Bari Haidar yi hakuri
bari na je yanzu na shawo kanta insha Allahu za
ta zo.
Jawahir tana zaune tana bitar karatun Alkur’ani
wayarta ta yi kara. Ta tsagaita da karatun ta
dauka, “Hello wa ke magana? Faruk ya ce, “Ni ne
daman na bugo na gaya miki Haidar yana cikin
dayan biyu ko mutuwa ko rayuwa, don ya rikice
an rasa gane kansa sai kiran sunanki kawai yake
yi”
Jawahir ta gigice, “Na shiga uku yaya faruk
yanzu ina yayan yake?
“Yana can asibiti a rikice.”
“Wayyo yaya faruk! Don Allah ka kwantar masa
da hankali yanzu zan zo.” Ya ce, “Ina harabar
gidanku ina jiranki ki fito da hanzari.
Kafin ya rufe bakinsa ya ganta ta fito da wayar
kange a kunnenta. Ya bude mata bayan motar ta
fada, shi kuma ya shiga gaba ya tuka suka yi
gaba. Yana tsayar da motar jawahir ta bude ta
fito a guje ta shiga dakin da yake tana danna kai
ta tarar da shi a gado yana ta faman ihu.
“Wayyo Allah! Ya dafe cikinsa yana ta juyi.” Ga
shi dakin sai shi kadai ba kowa, nan da nan
hankalin jawahir ya tashi, tausayinsa ya kama ta
sai kawai hawaye taji yana zubowa daga
idannuwanta ta zauna a gefen gadon ta dago
kansa ta dora a cinyarta tana rike da shi sai
sannan take yi masa, gani take da tana da ikon
cire ciwon nan ta dawo da shi jikinta da ta yi
domin kawai ya huta a abin da yake damunsa.
“Sannu yaya na kirawo likita ya ba ka magani.
Wayyo yaya cikinka ne yake ciwo? Yaya ko ina
ciwon yake yi?
Sannu yaya, bari na hada maka tea ka sha ko?
Ko za ka iya cin abincin? Don Allah yaya ka
tashi.
A hankali nishi ya lafa sai kadan kadan daga can
ya yi shiru ciwon ya tafi kenan. Jawahir ta
rankwafa kansa, “Sannu yaya”. Ya lalubi
hannunta ya danke a nasa cikin magana sanyi-
sanyi irin wanda yake jin jiki ya ce, “Yaushe kika
zo? Ta ce, “Ban dade da zuwa ba. Ina yaya
Abban ya tafi ya barka kai kadai?”
“Yanzu nan kafin ciwon ya tashi ya tafi gida
amma yanzu zai dawo.”Ta ce “Amma dai bai
kamata su rinka barin ka kai kadai ba kana cikin
wannan hali.”
“To ya zan yi jawahir ke ma da kike ‘yar uwata
matata kin guje ni kin ki jiyyata waye zai jura?”
Jawahir ta ce, “Ka yi hakuri yaya ba wai na ki
zama a wajenka bane ka san halin Yagwalgwal
kar ta zo tana tsinka na a asibiti shi ya sa.
Haidar ya ce, “To shi kenan ba komai zan nemi
likita ya ba ni sallama sai mu koma gida na yi
jinyar a can ko?”
Ta ce, “Haba yaya gwanda ka zauna a nan din ka
ga sun fi kulawa.”
To jawahir ai ba zan juri rashin ganinki ba
gwanda dai na koma gidan.”
Daidai nan likita ya shigo ya dubi Haidar ya ce,
yanxu ina ganin za mu sallameka ka koma gida
tun da Abbanka ya ce kasar waje zai futa da kai.
Don haka ga takardar sallama.
Jawahir ta ce, “To likita yawan ciwon cikin da
yake fa? Likitan ya ce ba komai wannan mun
bashi magunguna sai dai a dinga kula wajen ba
shi ya sha.”
Anan yaya Abba ya shigo ya kalli jawahir ya ce
wato sai yau kika ga damar xuwa wajen mijinki
ko? Kina sane da ba shi da lafiya yana kwance a
asibiti amma ba za ki zauna kusa da shi ba, don
taimaka ma sa ba ko.?
Jawahir cikin biyayya jawahir ta ce, “Kayi hakuri
yaya insha Allahu ba zan sake ba, “Faruk ya
shigo suka kwashi kaya da Haidar suka yi
gidansa.
Dakinsa suka wuce da shi suna budewa kamshi
ya bige su ko ina a gyare fes kamar yana nan.
Jawahir ta hado
musu abubuwan ci da na sha suka ci suka sha
suka yi kat, sannan suka yi musu sallama tare da
kara yi musu addu’ar samun sauki. Jawahir ta
shige tolet dinsa ta hada masa ruwan wanka a
baho ta zuba turaren wanka a cikin ruwan nan da
nan turirin kamshi ya rinka tashi. Ta fito daga
tolet din ta durkusa Yaya ga ruwan wanka can na
hada maka, ya ce yauwa Babyna na gode.
Ya mike ya shige tolet dinshi kansa kamshin da
tolet din yake yi dabanne. Yana shiga cikin ruwan
ya ji wani dadin ni’ima ya ratsa shi ya fara
wankan.
Jawahir kuwa ta fito masa da wasu kananan
kaya, wando je three Quarter (tiri kwata) da rigar
50 Cent marar hannu ta kara feshe su da turare.
Ta debo masa mayukan da zai yi amfani da su
da turarukan. Ta ja masa kofar dakin ta sauka
zuwa kasa nata dakin. A lokacin kuma Kausar ta
dawo ko daga ina take oho ita ta sani.
Jawahir ta shiga wanka ta fito ta gyara jikinta
sai zuba kamshi take yi kamar wadda aka yi barin
turare a jikinta. Riga da wando ta saka da hula
mai harafin sunanta. Fuskar nan tata sai sheki
take yi, jikinta sumul-sumul gwanin sha’awa
kirjinta ya cika fam, da na shanu.
Ta bude kofar ta fito Haidar yana kwance a
doguwar kujera da karamin kur’ani a hannunsa
yana karatu. Kausar tana kujera me zaman
mutum daya tana zaune da jarida a hannunta
tana dubawa, kamshin da suka ji ne ya sa su
saurin dago kai Kausar ta saki tsaki ta mai da
kanta ga karatunta.
Jawahir ta wuce kicin ta dauko kofin gilas me
kyau ta bude firji ta dauko robar ruwa ta
Highland ta iso gaban kuherar da Haidar yake
kwance ta zauna a kasa kan kafet ta balle bakin
robar ruwan ta tsiyayo ta fiffito da magungunan
ta mika masa, “Yaya ga magungunan.
Ya dan mike zaune ya karbi magungunan ta
watsa bakinsa ta kafa masa kofin a baki ya sha
ruwan ya ce ta dan danna masa kafafuwansa don
ciwo suke yi masa. Ta mike sannu a hankali ta
rinka mamnatsa masa tana yi masa tausa. Jin
dadin tausar da ya jine ya sa shi fadin wash,
wash a hankali tare da lumshe ido.
Ita kuwa Allah sarki sai ce masa take yi sannu
sannu yaya cikin alamun ban tausayi, shi kuwa
taushin fatar hannunta mai kama da atafa shi
yake neman dimautar da shi, har yana neman sa
shi ya fita daga hayyacinsa, ba dan yana gudun
kada girma ya fadi ba ai da ya rungumota.
A ka kwankwasa kofar falon jawahir ta kalli
Haidar da yake kwance yana lumshe ido don jin
dadin tausa ta ce, “Yaya na je na bude kofar.?
Kai kawai ya iya daga mata don maganar ta ki
fita kanta bude kofar ta ja da baya don ganin
Yagwalgwal ce. Jawahir ta durkusa kasa ta
gaishe ta, ta ce “Munafuka ba zan amsa gaisuwar
taki ba, me kike jira a gidan da baki tafi ba tun da
kiyayyar da kike yi masa har ta kai ki sabauta
masa lafiyarsa ai za ki iya kashe shi ma, don
haka ni gaskiya ban yarda da wannan auren naku
ba ka sake ta kawai na gaya maka ba na son
gayyar tsiya gayyar jarabawa.
Jawahir ta fashe da kuka ta kalli Haidar ta ce,
wallahi ba don na riga na yi wa Dadyna alkawarin
ba zan kuma fita daga gidan nan ba, ba tare da
izininka ba wallahi yau da na bar zaman gidanka.
Ta durkusa a gabansa tana kuka, “Yaya don Allah
don Annabi yaya ka taimake ni ka sake ni ko ni
ma na samu sukuni a zuciyata.
Haidar ya sunkuya ya dago jawahir ya hada ta da
kirjinsa ya rungumeta yana shafa bayanta alamar
rarrashi, ransa a bace zuciyarsa ta yi bakikkirin
sai fat-fat take yi kamar ta fasa kirjinsa ta fito
waje. Ya kalli Yagwalgwal ya ce, “Yagwalgwal ina
ganin girmanki kada ki bari kimarki ta zube a
idona, jawahir ‘yar uwata ce ko ba aure a
tsakaninmu ni me rike ta ne ballantana matata ta
sunna ki rika aibata ta a gabana, ai aurena da
jawahir mutu ka raba takalmin kaza.
Yagwalgwal ta kama salati tana tafa hannu,
“Yanzu dan nan ni kake gayawa haka a kan
wannan mai kama da sadakar yallan kake neman
zagina, to bari na je wajen uban naka in kai ban
isa da kai ba ai shi ba zai ki jin maganata ba, tun
da ni na haifeshi ko. Jawahir ta zame jikinta daga
jikin Haidar ta nufi dakinta tana kuka ta rufe
kofarta. Haidar ya kamo hannun Yagwalgwal ya
ce, “Yi hakuri matar ta karfen na san du kishi ne
yake dawainiya da ke, Ta doke hannunsa ni sake
ni me kuma za ka gaya min bayan ka gama yi
min rashin kunya. Ya dada kamo hannunta yi
hakuri zo mu je sama dakina na gaya miki komai
don ki ji yanda abin yake. Da kyar ya shawo
kanta suka hau samansa suka zauna a falonsa,
duk wannan abin da ake yi Kausar tana zaune a
kujerar da take tana kallonsu kawai ba tare da ta
tofa komai ba.
Haidar ya ce da Yagwalgwal “Wallahi yarinyar nan
jawahir tana da mutukar hakuri ga ladabi da
biyayya ga sanin ya kamata da hangen nesa, tana
aiki da ilimin da Ubangiji ya ba ta, idan aka ce za
a yi ta tafiya a yanda a ke yi yanzu, to hakika
hakurin jawahir zai iya kai ni wuta.”
Yagwalgwal ta ce, “Dakata! Don na ce ka rabu da
ita kake kawo min wannan bayanin, ka je kada ka
sake ta ran da ta kashe ka ai ma zo mu dauki
gawarka ko?
Haidar ya ce, “Dole dai sai na fasa miki tarihinmu
za ki yarda da zancena. Haidar ya faro mata irin
tsanar da ya yi wa jawahir tun daga farko da
yanda har a ka yi auren da irin zaman da suka yi
da dalilin da ya sa jawahir barin gidansa har
kawo yau.
Yagwalgwal ta saka salati tana cewa, “Ashe ni
balokokon vanza nake yi kai ne marar gaskiya?
To wallahi ka kula ka rike ‘yar uwarka da kyau
don tana yi maka son gaskiya. Da haka dai suka
yi sallama ya debo kudi me yawa ya bata ta yi
masa godiya tare da sa masa albarka ta ce kuma
za ta zo ta bawa jawahir hakuri idan ta wuce.
Haidar ya juyo daga rakiyar Yagwalgwal ya
murda kofar dakin jawahir ya shiga, kamshin dadi
ne suka buge shi ya sheka ya karasa cikin dakin.
Tana zaune a gefen gadonta hada kai da gwiwa
tana shasshekar kuka, ya zauna a gefen gadon ya
dago ta ya kara ta da jikinsa ya rungume ta,
“Subhanallahi wannan jiki haka mai taushi da
dadin kamshi kamar atufa, Ubangiji ka nuna min
ranar da zan mallaki komai na yarinyar nan da na
nuna mata tsantsar soyayya da kaunar da ba a
taba nunawa wata ‘ya mace ba.
Duk zancen nan a zuciyarsa yake yi wanda har
ya so ya shagala cikin tunanin kyan kirar jawahir.
Sautin kukanta ne ya dawo da shi hayyacinsa.
Cikin taushin murya da magana kasa-kasa kamar
mai rada yake rarrashinta yana dan bubbuga
bayanta, “Sorry Babyna yi shiru haka kada kanki
ya zo yana ciwo kin ji baby na yi hakuri, ta dada
shagwabewa tare da langabewa a jikinsa tana
kuka kasa-kasa cikin sigar kissa da shagwaba
kukan nata me shiga rai da tsayawa masoyi a
zuciya.
Tuni kirjin Haidar ya fara bugawa fat fat,
“Subhanallahi ya salam wai yaushe zan mallaki
wannan tsantaararren jikin mai kama da robar
balo-balo?
Muryarta ya tsinkaya cikin rauni da taushi da
dadin murya tana cewa, “Yaya ka sake ni na
koma gida tun da kakarka ba ta son na zauna da
kai.”
Haidar ya ce, “A’ uxubillahi kada na kuma jin kin
furta wannan kalmar kin ji ko, don ubangiji yana
tsinewa duk matar da ta nemi mijinta da ya sake
ta, kada bacin rai ya sa ki rinka jawowa kanki
fadawa cikin fushin ubangiji kin ji ko? Yi saurin
yin istigifari.”
A hankali ta bude baki ta rinka nanata istigifari,
ya ce, “Yauwa Babyna Yagwalgwal ta ce a ba ki
hakuri. Zumbur ta mike ta shiga tolet don ba ta
son maganar don ita a zatonta tanda Yagwalgwal
take tsanarta da nuna mata kiyayya ba za ta taba
son ta ba.
Haidar kuwa binta ya yi da kallo komai nata sha
awa yake ba shi komai na jikinta burge shi ya ke
yi, wai shi ya zai yi da wannan zazzafar kaunar
da yake yi wa jawahir ne? Ta yaya zai yi ya
shawo kanta su kwanta gado daya ne da shi?
Duk dai da tanxu ba shi da karfin gaban da zai
tabuka mata wani abu to amma ko wasanni da
sun yi shi da ya ji ta kwance kan kirjinsa yana
wasa da wadannan tantsa-tantsan na shanun
nata(nono).
Duk dai da shi ya yi wasa da damar da ya samu
tun farko.
Ya dade a zaune yana zaman jira shiru-shiru
jawahir ba ta fito ba dole ya mike ya fita, tana jin
fitarsa ta fito ta sawa kofarta mukulli. .
Abu wasa-wasa jawahir ta kwana ta wuni ba tare
da ta fito Haidar ya ganta ba ko ta yi saken
kofarta a bude ya shigo. Sai dai wani abin
mamaki da safe za ta hada masa lafiyayyen
break a kicin din wajenta sai ta leko falon ta ga
ba kowa sannan ta jere masa kayan break din ta
kuma ajiye masa maganin da zai sha na lokacin
da robar ruwan Highland ta koma bangarenta ta
kulle kofarta, sai dai in Haidar ya gama shirnsa
ya sauko kasa ya hau tebir ya yi break ya dauki
magani ya sha ya jira ko jawahir za ta bude ya ji
shiru ya taba kofarta ya ji ta a kulle. A lokacin ya
juya ya koma sama sannan ya tashi ‘yar mulkin
tasa wato kausar sarkin ‘yan hutu, to wani abin
mamakin duk da yau kusan a falo ya wuni amma
be ga jawahir ta fito ba bare ya kalli idonta ya ga
yanda ta kwana. Sai da ya ji an yi kiran sallar
azahar ya daura alwalla ya fita masallaci amma
kafin ya dawo jawahir ta fito ta jere masa kayan
abinci, tuwon farar shinkafa ya tuku ya yi mulmul
da shi da miyar agushi, wadda don dahuwa kazar
da take ciki duk ta narke ta dagargaje a ciki.
Ta gasa masa naman rago mai ruwa ruwa ya sha
kayan kamshi ga tumatir da albasa kai dai
kamshi yake tashi. Sai lemon aya da ta hadawa
kanta ta zuba masa a jek ta cilla kankara ya sha
kayan kamshi, ta jere komai cikin kayatattun fulas
masu kyau ta sa farin kyalle mai dauke da
falawoyi a jiki ta rufe ta yi saurin juyawa ta koma
dakinta ta rufe sashenta ta shiga kicin dinta duk
ta gyara kayan data bata, ta wanke komai ta
goge ta mai da shi inda yake, sannan ta shige
tolet dinta ta saki shaya a kanta ta fara wanka. Karfe
biyu da rabi Haidar ya shigo gidan da carbi a
hannunsa, “Yan matan kausar ya ga daya a bakin
kofar falon tana gadin falon ta yi masa sannu da
zuwa ya wuce. Ya shiga falon ya taba kofar
jawahir a bame kamar yanda ta kwana. Ya
girgiza kansa kawai, shi jin kansa ya hana shi
kwankwasawa ya nufi bangaren kausar tana
zaune a kan kujera ‘yan matanta biyu suna
gefenta daya tana yanka mata tufa a kan filet
dayar kuma tana zuba mata abinci a daya filet
din, wanda ya kasa banbancewa da kuskus ne ko
burabusko. Yanda ya gan shi a dundunkule ya
sha ruwa ya yi sharkaf.
Ya zauna gefen ta ‘yan matan suka yi saurin
nikewa suka yi waje. Kausar ta dauki filet din
abincinta za ta fara ci ta kalle shi ta ce,
“Bismillah.” Ya ce, “Wa! Ni?
Allah ya sauwake na ci wannan abincin, ai sai na
yi amai.” Ta tabe baki ta ce, “Au kai fa ba ka cin
abincin masu aiki ko? Ka sa kanka a wahala don
yau na ga abin da za ka ci tun da na ga
Sarauniyar taka fushi take yi bare ta zo ta girka
maka.
Wai ni kuwa yau ka yi break? Don ban ji motsinta
ba bare na ji ko ta girka maka
Ya ce, “Ke za a tambaya ba tare muka kwana ba,
tsakanin ke da ita wa ya kamata ya yimin girki?
Ta tabe baki, “Ka san ni ban tashi a cikin wahala
ba don haka ba zan iya wani aikin komai ba.
Da kake maganar da ni ka kwana ai tausaya
maka na yi nake taya ka kwanciya don kada ka
kwana kai kadai, me kake iya tabuka min? Ka
riga ka zama nakasasshe, in ban da ka ishe ni da
tabe-tabe ka tayar min da hankali babu biyan
bukata.”
Ya daka mata tsawa tare da nuna ta da dan
yatsa, ke saurara kada ki sake ki kawo min
maganar banza a nan, da haka nake? Ko don
lalura ta same ni za ki gaya min maganar banza,
daure ki na yi ko cewa na yi dole ki zauna idan
kin gaji ba dole, ba zan danne miki hakki ba ga
hanya nan sai ki san inda dare ya yi miki.
A ranta ta ce, “Ba inda zan je gwarzon namiji
kamar ka ina zan iya barin ka, idan na yi sake ka
subuce min ta yaya zan yi na mayar da kamar ka
bare yanda na dandani zumarka ai sai dai na ga
ba ka samu lafiya ba tukunna zan ki zama da kai.
Ya gama banbamin fadansa ya fice yana tunanin
tsananin hakurin jawahir da kawaicinta. Ya ji
sallamar Hafsan faruk ya amsa mata cikin fara’a
yau ina megidan naki na gan ki ke kadai? Wallahi
yana office ka san bai taso ba, yanxu ma gidan
yini zan je ya ce na fara biyo wa na ga jikin naka.
Haidar ya ce, “Jiki Alhamdullahi.” Ta zauna a
falon suka gaisa ta ce, “Ina matan gidan ne? Ya
ce, “Bari na kirawo miki su. Ya kwankwasa kofar
jawahir ya ce, “Ki fito kin yi bakuwa, Hafsa ce ta
zo.
Ya juya ya nufi dakin kausar ya ce ki zo kun yi
bakuwa, “Tace, “Wacece?”
Ya ce, “In kin zo kya gani, “Ya juya ya fita. Jawahir
ta bude falonta ta fito cikin dammamiyar riga
body hook da jeans din wando da ya dame mata
cinyoyi daga kasa kuma yake da fadi, kanta ba
dankwali sai kananan kalba da ta tufka ta a
bayanta ta kwanto guda biyar gaba. Ta yi kyau
sai zuba kamshi take yi ta taho da dan gudunta
ta fada jikin Hafsa tana dariya. Haidar kuwa ya
zuba mata ido kallon ta yake yi yana hadiyar
yawu, yarinyar nan kuwa ta san yanda take rikitar
masa da hankali? Ta san yanda kirjin nan nata
yake dauke masa hankali kuwa?
Kausar ta shigo tana yatsina kujerar da Haidar
yake kai ta nufa ta zauna masa kan cinya ya ce,
“A’a ke me ye haka? Ta ce, Haba Darling kai ma
ka san nan ne wajen zamana don ka riga ka
sabar min.
Ya ce, “Amma kina ganin bakuwa a wajen ko? Ko
dan rashin kamun kai.” Ya zame ta takaici da
tsantsar kishi suka tokare zuciyar jawahir kamar
ta yi kuka ta dan daure ta ce, “Hafsa tashi mu
koma daki. Hafsa ta mike yayin da take gaisar da
Kausar. Suka shiga dakin jawahir Hafsa ta ce, tab
amma kina shan kallo, haka Kausar din take ba ta
da kunya? Jawahir ta ce, “Ina ruwana da ita? Me
ya dame ni da ita? Tun da ba zamanta nake yi
ba.
“Yanzu haka za ki zuba mata ido tana iskanci? In
ni ce ai sai na nuna mata cewar ita karamar ‘yar
iska ce, bare yanda na ga hankalinsa da
tunaninsa duk ya raja’a a kanki me ya sa ba za
ki sakar masa jiki ku rinka farantawa juna rai
ba.?
Jawahir ta ce, “Kyale ni Hafsa ni na san halin da
zuciyata take ciki a kan son Haidar, to kin san
wani abu da yake damuna? Na tsani na bude ido
na ga Kausar tana yi masa magana ko tana
kallonsa bare ta hada jikinta da shi wallahi sai na
ji kamar na je na shake ta ta mutu ko na huta.
Hafsa ta ce, to bari na ba ki shawara wallahi
yanzu yanda na fuskarki mijinki yana tsananin
sonki mai zai hana ki fito masa da taki irin kissar
kin san Allah nan gaba sai kin dinga tausaya
masa don bin ki zai dinka yi kamar rakumi da
akala saboda ‘yar uwa ba dama ce fa ke, dole ne
ki rikita Haidar, irin wannan cika haka komai ya ji,
me zai hana hankalin Haidar tashi da gigicewa a
kan ki.?
Jawahir ta ce, “To ai ni ba ki sani ba kunyar hada
jiki nake yi da shi sabo da sai na ga kamar zai ce
min ba ni da kunya.
Hafsa ta ce, “Tabdi jan zauna a barki a baya, au
na gaya miki cikin dabara da hikima za ki rinka
sakin jiki da shi kina yawan zama a duk inda
yake ki rinka yawaita kwalliyar da za ta rikitar da
shi kamar irin wannan sai kin zo kina ba ni labari
da bakinki, “Hafsa ta yi zumbur ta mike bari na yi
sauri na leka gidan wunin nan na koma gida kada
Oga ya dawo daga office ba na nan.
Jawahir ta yo mata rakiya Haidar yana falon tayi
masa sallama Hafsa tana gaba jawahir tana biye
da ita Hafsa ta fita daga falon jawahir za ta fita
ke nan Haidar ya yi magana kasa kasa, “Kada ki
fita harabar gidan nan da direba suka xo kada ya
ganki. “Jawahir ta ja tunga suka karasa sallama
da Hafsa tare da yi mata alkawarin zuwa in an
kwana biyu, ita kuma ta tafi.
Ta juyo daga rakiyarta har ta isa kofar dakinta
ya kirawo ta. Jawahir ta tsaya kam, a wajen ba
tare da ta juyo ba ta ce na’am, ya lankwasa
murya ya a raunane ya ce, “Yanzu haka za ki bar
ni na wuni da yunwa bayan kin san ba cikakkiyar
lafiya ce da ni ba, ga shi lokacin shan maganina
har yana kokarin wucewa, ta juyo a raunane cikin
tausayawa ta ce, yanzu ba kaci abinci ba.?
Ya dada langabewa to wa zai ba ni? Ke da kika
san ciwona kike girka min yanzu gashi ba ki yi
min ba. Ta ce, yaya na girka maka mana ta nufi
tebir din ya biyo bayanta yanda ta ajiye haka
yake ba wanda ya taba. “Ta bude komai ta jawo
filet ta fito da tuwo malmala biyu ta cire su daga
cikin ledar da ta zuba a filet din, ta zuba masa
miyar a daya filet din ta tura masa gabansa
kamar mai jira ya fara ci ta tsiyaya masa kunun
aya, ya yi sanyi kuwa karara a gilas kof ta ajiye
masa a gefe. Ta dan langabe kai ganin ya ture
filet din tuwon ta ce, duk yunwar da kake ji dan
wannan za ka ci? Ni jira nake fa ka cinye na kara
maka wani. Ya ce, “Haba Babyna na cinye
malmala daya da rabi ai dole na ji na koshi.
Ta dan marairaice cikin shagwaba ta ce, to ci
naman.” Ta bude masa kamshinsa ya bige shi
har na ji yawuna ya tsinke, ya kamo ta ya zaunar
da ita a cinyarsa to zauna mu ci tare don na ga
alamar ba ki ci komai ba.
Ta langwabe a jikinsa ta ce, “Uhm Yaya na ci
abinci fa a koshe nake.”
Ya ce, to gaya min me kika ci?
“Yaya na sha yogourt da nama na kuma sha
wannan. Ta nuna kunun ayar, da yake kofin. Ta
dauko ta sa masa a bakinsa yaya kai ma dan sha
ka ji akwai dadi. Ya kwankwada, “Uhm akwai
dadi, dan karamin, ta noke tana yi masa dariya
kasa-kasa ta ce, “Yaya ka ci naman tukunna
kada ka cika cikinka da ruwan kunun aya.
Ta yago naman ta sa masa abaki ya kama
taunawa yana lumshe ido um carkwai wannan
dadin haka kada ya tsinken kunne, “Ta kama
shasshekar dariya tana langabewa a kirjinshi tana
yago naman tana ba shi a baki.
Duk abin nan da ake yi dauriya kawai yake yi don
halin da jawahir ta tsunduma shi gaba daya ba
shi da wani kuzari ta dada rikita shi da kaunarta
da sha’awarta ta mamaye kowacce gaba ta
jikinsa, ta mike yaya ka ji ana kiran sallar la’asar
mu je mu yi sallah. Ya ce, to babyna na gode
Allah ya saka da Alkhairi Ubangiji ya yi miki
tukuici da gidan aljanna. Mu je na raka ki dakinki
ko babyna ta langabe a gefensa yaya kada a
tayar da sallah a masallaci ka je ka yi alwalar.
Ya ce, “A’a yau a tolet dinki zan yi alwalar ta yi
dariya to Yayana mu je.
Yau dai a dakinta ya yi sallah don shi ya ja musu
jam’i, ya dade yana kwararo musu addu’a sannan
suka shafa. Yau dai wuni guda cikin farin ciki da
annushuwa suka yi shi, gaba dayan su kokarin
farantawa junansu rai suke yi bugun kofar da ake
yi musu ne kamar za a balla ya sa Haidar saurin
mikewa cikin fushi ya je ya bude, Kausar ce a
tsaye tana girgiza kugu tana taunar cingam tare
da yamutsar fuska, “Lafiya.?
Abin da ya ce mata kenan.
Cikin tsiwa ta ce, “To me za ka yi min ko ka
manta cewar yanzu kai ba cikakken namiji ba ne
ka zama miskini? Ai ni ba ka da amfani a wajena
ita ma da ka ga tana rawar kafa don duk haka
kuke ne ita ma ba me lafiyar ba ce don haka ta
nakasta ka
Ya daka mata tsawa, “Ke kausar ki shiga
taitayinki ni ba sakaran namiji ba ne, ba ki isa ki
wulakanta ni ba.
Ita ma ta hau shi da ma sifa to ka sake ni mana
haka kawai don zalinci ka ajiye ni ka san ba iya
biya Min
bukatata za ka yi ba, kana so da aurena ne na
rinka bin maza kome kake nufi?”
Ya ce, “To shi ke nan na ji ki yi hakuri zan yi
shawara.
Ta ce, “Ina son zuwa gidan kawata. Ya ce, “A
dawo lafiya amma ki dawo da wuri tafi da direba
can sai ya kai ki. Ta juya ba tare da ta ce masa
komai ba.
Kausar tana daukar mota ba ta wani tafi da
direba ita kadai ta yi tafiyarta ta nufi gidan wata
kawarta, ita ma ‘yar Abuja ce aure ne ya kawo ta
nan kano.
Saddika ta tare ta da murna kausar amare yau
nake zancen mun kwana biyu ba mu hadu ba, ina
so in je gidanki ashe kina tafe. Ina angon naki ya
barki kika taho ke kadai.?
Kausar ta dauki lemon da ta ajiye mata ta kurba
ta ajiye ta ce, kyale angon nan nawa ai ni na
kusa barin gidansa. Saddika ta dafe kirji, “Haba
kausar me ya yi zafi haka? Ki tuna irin wahalar
da kika sha kafin ki samu Haidar ya amince ya
aure ki, yanzu idan kika rabu da shi ta yaya za ki
maye gurbin gayen yaro mai jini a jika da naira
kamar Haidar?” Kausar ta tabe baki tare da yin tsaki ta ce, “Ai
wadannan abubuwa da kika lissafa duk sun tashi
a banza don yanzu ya zama solobiyon namiji ba
abin da yake iya yi wa mace.
Saddika ta ce cikin razana, “Ban fahimce ki ba,
me kike nufi?
Kausar ta ce, lokacin da na auri Haidar na same
shi gwarzon namiji me cikakkiyar hallita wanda
ya iya jiyar da mace dadi ko ta ina ban taba
zaton zan iya rabuwa da Haidar ba don ta ko ina
ya yi min
Zamzam ga shi hadadden miji na nunawa sa’a, to
dan bakin cikin matarsa ganin ba ta da lafiya
komai bai taba gudanuwa a tsakaninsu ba shi ne
ta yi min bakin ciki ta kwada masa abu a
gabansa ta nakasta shi har kwanciya ya yi a
asibiti amma likita ya ce ai ya riga ya nakasta.
To yanzu ya dawo gida sai dai in mun kwanta
waje daya da shi ya ruda min jiki da wasanni ba
ya iya aikata komai wallahi ni na gaji gwanda ya
sake ni na huta.
Saddika ta ce, “Gaskiya yarinyar kamar ki da
kuruciyarki da komai zaman hakuri bai kama ki
ba, to amma ba kya tunanin wata rana zai samu
lafiya ki zo kina takaici?
Kausar ta ce, “Ke kuma kin ji ki da wata magana,
likita fa ya ce min ba shi da wata ranar samun
lafiya kina so na shiga yawon bin maza da
aurena ne?
Kinsan ko musulunci ya zama dole ya sake ni.
Saddika ta ce, “Gaskiya ne da ki cilla kanki a
halaka gwanda ku rabu kawai ki auri Bomboy ………… to amma ba kwanaki na ji kin ce
kina da ciki ba.”?
“Ba ciki ba ne ashe batan wata na yi daga baya
na ga al’adata ta zo. A nan ta yi sallar magariba
suka ci abinci ta yi sallar insha sannan ta tafi
gida.27