SANADIN SONKI CHAPTER 4
SANADIN SONKI CHAPTER 4
Babu wanda yayi k’arfin halin yi mishi magana a tsakanin Baba Adamu tare da Babaa Lantana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai cikin d’akin, lokaci d’aya kuma gaban shi na bugawa da k’arfi sosai.
Aliyu yana sanya k’afar shi cikin d’akin idanun shi suka hango mishi Umman shi kwance an lullu6e da zani, da sauri ya k’arasa wajen gaban shi na tsananta fad’uwa, hannun shi na rawa ya sanya akan zanin ya fara janye shi a hankali, fuskar Fatima ce ta bayyana kamar an kirata ta amsa, sai kace ba matacciya ba, tuni Aliyu ya durkushe tare da sakin wani irin kuka yana cewa
“Umma ki tashi don Allah kada ki tafi ki barmu a wannan duniyar mu kad’ai”
Kuka sosai Aliyu yake yana sumbatu, ganin haka ya sanya Baba Adamu ya janye shi daga gaban gawar Fatima dakyar don shima hawayen yake yi, Babaa Lantana kuwa da Aliyah Suhaima kuka suke yi sosai.
Daga k’arshe Baba Adamu ya fita don sanar wa da jama’ar gari, cikin k’ank’anin lokaci mutuwar Fatima baiwar Allah ta zagaye cikin k’auyen nasu, sosai mutane sun jimanta rasuwar ta tare da yaba kyawawan halayen ta, da irin yanda take hak’uri da jure irin rashin mutunci irin na mijin ta wanda sam kanshi ya sani.
Babu jimawa mutane suka taru akayi wa Fatima wanka aka had’a ta cikin likkafani, sannan daga k’arshe aka sadata da gidan ta na gaskiya, gidan da shi muke jira Allah ya jik’an wad’anda suka mutu mu kuma Allah yasa mu cika da imani Amin.
Aliyu da Suhaima sun sha kuka kuwa, musamman Aliyu don yafi Suhaima hankali sai yafi jin rad’ad’in mutuwar fiye da ita, su Baba Adamu da Babaa Lantana ne suke tausar su tare da yi musu nasihar yarda da k’addara, lokacin Fatima ne yayi don haka Allah ya d’auki abarshi, kowanne mutum da iyakacin lokacin da Allah ya d’ibar mishi yanzu Fatima addu’a tafi buk’ata fiye da komai, Allah yasa mu dace duniya da lahira Amin.
Haka Aliyu da Suhaima suka rungume maraicin su, sun koma abin tausayi, bayan sadakar bakwai ne ‘yan uwan Fatima suka nemi tafiya da Suhaima shi kuma Aliyu ya zauna a wajen ‘yan uwan uban shi, amman k’ememe Aliyu ya yak’i yarda da tafiya da Suhaima, anyi rarrashin sunyi fad’an amman ina yak’i aminta dole suka damk’a amanar su hannun Babaa Lantana da Baba Adamu, tukunna suka tafi bayan su bawa Aliyu wani d’an taimakon da zai nemi wata sana’ar ta domin kula da kansu.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, inda Aliyu da Suhaima suka sake shak’uwa da junan su, komai Aliyu ya samu zaka ji bakin shi na ambatar Suhaima, kulawa sosai yake bata don shi yafi tausayin ta fiye da kanshi, sai dai ita Suhaima ta koma gidan Babaa Lantana da zama sai dai tana shigowa wajen Yayan nata tana tayashi ‘yar hira.
Aliyu ya dage da yin sana’a kowacce iri ce indai zai samu halal d’in shi, aiki yake yi sosai na k’arfi kuma, haka ya dunga tara kud’i har ya sanya Suhaima a makarantar primary tana nan cikin k’auyen nasu tare da islamiya, babu dad’e wa Suhaima ta fara zuwa makaranta hankali kwance, kullum shi zai kai ta a tsohon keken da Baba Adamu ya cika mishi kud’i ya siya, haka idan aka taso su zai zo ya d’auke ta.
Ganin Aliyu ya fi karkata akan son yin noma da kiwo yasa Baba Adamu bashi aron gonar shi guda d’aya don yana yin amfani da ita, shi kuma ya rik’e guda d’aya, da yake gonakin nashi guda biyu ne manya, gashi gonar da ya bawa Aliyu aro a kusa da gidan su Aliyun take, idan ma mutum bai kula ba ya d’auka kamar gidan a tsakiyar gonar yake, sosai Aliyu yayi murna da wannan karamcin da Baba Adamu yayi mishi.
**** **** ****
Haka lokaci ya cigaba da tafiya watanni da shekaru na wuce wa kamar kiftawar ido, Suhaima an fara zama ‘yammata an don har ta kammala makarantar primary sun zana commen interest tana gida ana jiran fitowar result sai makarantar islamiyya da take cigaba da zuwa.
Yayin da Aliyu an zama matashin saurayi, ya zama cikakken manomi a yanzu, don ya rik’e sana’ar noma da kiwo, da wannan gonar da Baba Adamu ya bashi aro yake noman shi and cikin ta har zuwa yanzu da ta zama mallakin shi, don tuni Baba Adamu ya siyar mishi da ita, bayan aikin noma kuma yana yin kiwo irin su kaji, awakai da shanu sai kuma yana siyar da kwan kaji sosai yake samu bud’i a harkar shi, ga taimakawar wani amintaccen yaron shi da Baba Adamu ya sama mishi yana taimaka mishi.
Ya gyara gidan su sosai yayi kyau, inda a lokacin kuma Baba Adamu ya nemi da yayi aure, babu 6ata lokaci ya sanar musu da Aliyah d’iyar shi yake sosai, babu wanda bai yi farinciki da hakan ba don haka babu 6ata Lokaci akayi aure amarya ta tare a gidan ta, nan kusa da gidan su tun da Aliyu a asalin gidan su ya zauna, a lokacin kuma Suhaima ta dawo hannun Yayan ta da zama, zaman su suke cikin kwanciyar hankali da farinciki, Aliyu ya mayar da hankalin shi sosai kan sana’ar tashi, ya dad’a zama wani babban mutum musamm da yanzu yayi aure.
Kamar yau ne ranar laraba ranar da kasuwar garin nasu take ci, tun safe Aliyu ya bar k’auyen nasu ya tafi cikin birni kai wasu kwai masu yawa, wajen mutumin da yake kaiwa ya siya a kan machine d’in shi, don haka gidan ya rage daga Aliyah sai Suhaima a ciki.
Ranar Suhaima cikin farinciki take saboda Yayan ta baya nan, zata je cin kasuwa don haka da wuri tayi wanka ta ci gayun ta cikin wata atampa mai kalar milk da brown a jiki, ta sanya hijab d’in ta k’arami kalar brown, sannan ta fito daga d’akin ta zuwa wajen da Aliyah take.
Aliyah tana zaune tana gyaran kayan miya don tana son gama girki da wuri kafin Aliyu ya dawo, ta hango Suhaima tana tahowa zuwa wajen ta, fuskar ta d’auke da murmishi tace
” Suhaima wannan gayun fa ina zuwa? ”
Cikin dariya Suhaima tace
“Yaya Aliyah nayi kyau ne?”
Itama Aliyah tana dariya tace
“Sosai ma ‘yar k’anwata kinyi kyau, ina zuwa? ”
“Cin kasuwa zan je ”
Zaro ido Aliyah tayi tare da cewa
“Haba Suhaima kin mance Yayan ki baya son kina zuwa koh, yanzu idan ya dawo bakyanan nasan fad’a zai mana ni da ke ”
Shagwa6e fuska Suhaima tayi tare da cewa
“Haba Yayah Aliyah kafin ya dawo fah na dawo, ba dad’e wa zanyi ba ”
“Toh shikenan amman don Allah kada ki dad’e ”
“Yawwa Yayah Aliyah nagode, kuma bazan dad’e ba ”
Murmishi suka yiwa junan su, sannan Aliyah ta d’auko kud’i ta bata, godiya tayi tukunna ta tafi cikin zuciyar ta fal farinciki.
Tana fita waje ta tarar da k’awayen ta suna jiran ta, nan suka tafi kasuwar suna tarar ana tacin kasuwa ga mutane daban daban har da na maraya ma suna zuwa cin kasuwar.
Suhaima bata dad’e ba tace wa k’awayen ta zata tafi gida, don kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata dawo ba yayi mata fad’a, aikuwa suka ce sai dai tayi gaba su ba yanzu ba, haka Suhaima ta kamo hanya tana tafiya ita kad’ai cikin sauri.
Sauri sauri take gaba d’aya hankalin ta yayi gida, tana tsoron kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata nan.
D’ago kan da zatayi ta hango wata kyakkyawar yarinya a tsaye kusan sa’ar ta, sai dai zata ba Suhaima wajen shekara biyu, sai wani dattijo a tsaye shima a gefen ta a tsaye da alama sun k’agu da tsayuwar da suka yi.
A hankali Suhaima ta k’arasa inda suke tsaye har zata wuce su, da sauri yarinyar nan ta k’arasa wurin Suhaima tace
” ‘yar uwa idan baza ki damu ba don Allah muna son ki taimaka mana da ruwa zamu sanya a mota ”
D’ago kanta Suhaima tayi ta kalle ta sannan tace
“Toh ba matsala bari na k’arasa gida na d’ebo muku”
Murmishi yarinyar tayi tare da cewa
“Idan baza ki damu ba zan bi ki don na gaji da tsayuwar ”
“Ba komai mu je ”
“Ngde ‘yar uwa ”
Kallon dattijon nan tayi tare da cewa
“Malam Habu bari mu je gidan su mu kawo ruwan ”
Sai da dattijon nan da yarinyar ta kirawo da Malam Habu yayi d’an jim kad’an kafin yace
“Toh amman kada ki dad’e kinga kada yamma tayi mana a hanya ”
Gid’a kanta tayi sannan ta juya wajen Suhaima tace
“Mu tafi koh? ”
A nutse suka fara tafiya yarinyar tana yiwa Suhaima hira sai dai bata fiye bata amsa ba daga ehh sai a’a, can sai kuma tace
“Ni sunana Hauwaa amman ‘yan gidan mu na kirana da Jiddah saboda sunan kakar mu ne ”
Murmishi Suhaima tayi tare da cewa
“Sunan ki mai dad’i ”
“thank you, ke fah what’s your name? ”
“My name is Suhaima Umar”
“Wow nice name, daman kina jin turaci? ”
“Yeah but kad’an kad’an.”
“Good, kin gama primary ne ”
“Ehh na gama ina jiran result ya fito na cigaba ”
“Amman kin birge ni Suhaima, zamu iya zama friends? ”
“Why not ”
Cewar Suhaima, nan kowacce ta bada d’an yatsan ta suka k’ulla friendship, tukunna suka k’arasa shiga gidan da sallama.
Gaban Suhaima ne ya fad’i ganin Yaya Aliyu a tsaye yana safa da marwa, ga Yaya Aliyah ma a tsaye fuskar ta d’auke da damuwa da alama dai ita ake nema.
Suna ganin ta gaba d’aya sukayo inda take Aliyu ya sanya hannun shi saman kafad’ar ta ya rik’e da d’an k’arfi yace
“Ina kika zauna Suhaima, ba na hana ki fita kasuwa ba ”
Idanun tane yayi raurau kamar zata yi kuka, batason ganin damuwar Yayan nata ko kad’an, don haka sai tace
“Kayi hak’uri Yaya bazan sake ba ”
Kallon ta kawai yake bayason wani abu ya samu tilon k’anwar tashi.
“I’m so sorry Yayah bazata sake ba ”
Aliyu da Aliyah suka ji saukar muryar Jiddah, da sauri suka kallo inda take don sam basu kula da ita ba hankalin su gaba d’aya yana kan Suhaima.
Kallon Suhaima Aliyu yayi irin na neman k’arin bayanin ina ta samu wannan yarinyar, fahimtar hakan da Suhaima tayi ne ya sanya ta bud’e baki tayi mishi bayanin had’uwar su.
Ba wanda yayi magana sai da Jiddah ta gaida su sannan suka amsa, kallo d’aya zaka yiwa Jiddah kasan ta samu tarbiyya mai kyau a wajen manyanta.
Babu 6ata lokaci Aliyu ya samu jarka ya zuba ruwa taf a ciki, sannan ya d’auko ta Suhaima da Jiddah na bin shi a baya har zuwa wajen da motar su tayi parking.
Bayan sun k’arasa ne Aiyu suka gaisa da Malam Habu sannan ya kar6i ruwan ya zuba a mota yana godiya, mik’a wa Aliyu jarkar ruwan yayi yana sake godiya, girgiza kai Aliyu yayi tare da cewa
“A’a ka barshi a wurin ka idan buk’atar hakan ya taso muku a gaba kwayi amfani dashi ”
Malam Habu cikin girmama karamcin Aliyu yace
“Mun gode d’an samari Allah ya saka da alkhairi ”
Daga haka Malam Habu ya shiga cikin mota yayi mata key ya tasar da ita, sannan ya d’ago kanshi ya kalli Jiddah da bata da alamun shigo wa motar yace
“Jiddah taho mu tafi yamma nayi ”
Maimakon ta bawa Malam Habu amsa, sai ta juya wajen Aiyu ta rik’e hannayen shi duk biyun tace
“Don Allah Yaya Aliyu zan na zuwa nan ganin Suhaima, Allah tun da na ganta naji ina sonta sosai, gashi mun k’ulla k’awance da ita, kuma ina son ka zama Yaya nah ”
D’an murmishi Aliyu yayi shi duk wanda yake k’aunar ‘yar k’anwar shi, to shima yana son shi, dafa kan Jiddah yayi tare da cewa
“Kada ki damu Jiddah na d’auke matsayin k’anwa, kuma duk lokacin da kike son zuwa wajen Suhaima ki zo ki ganta ”
Dariya Jiddah ta sanya ita da Suhaima kafin tace
“Nagode sosai Yaya Aliyu ”
Sannan ta jiyo wajen Suhaima suka rungume junan su, dakyar ta iya sakin Suhaima ta shiga mota har da d’an hawayen ta, don ji tayi kamar ta zauna a wurin su, suna tsaye Aliyu da Suhaima suna d’aga musu hannu har suka daina hango motar su.
Sannan Aliyu da Suhaima suka juya zuwa gida, sosai Suhaima ta fara jin kewar Jiddah kamar wad’anda suka shekara da sanin junan su, ita haka kawai taji Allah ya sanya mata son Jiddah kamar irin ‘yar uwar nan ta jini…