SARAUTA TAH CE CHAPTER 2 BY NUCEELUV

SARAUTA TAH CE CHAPTER 2 BY NUCEELUV

 

 

A hankali Samantha ta Dora hannayen ta a kafadar yareema yaseer hade da matsa Masa shi a hankali, Yareema yaseer dake duke ya cije lips dakyar Yana lumshe ido be dago ba bare tasa ran yaji tabin ta dukda kuwa cewar Wannan salon Yana tafiya dashi wato massage ta wajen kafada zuwa wuyansa.Samantha tasan halin prince yaseer miskili ne na karshe ko Yana jin tabi da wuya kaga ya nuna Kai tsaye d wuri sai ya gama Jan ajin nasa na izza kafin ya biye maka ayi harka.
“I missed you prince, I missed everything about you”
Samantha ta furta Hakan a daidai saitin kunnen sa tana me lasar saman kunnen a hankali cike da salo na kwarewa…,
Numfashi kadan yaja still beyi mgn ba, Sam taci gaba da kissing dinsa kota Ina a haka ta samu damar juyo dashi tana me hayewa kan cinyar shi gaba1 hade da cire Masa rigar sa daga Nan salon abun nasu ya canja domin izuwa yanzu ta Karasa kunna prince yaseer gaba1, dama can a kunne yake Jan aji ne kawai irin nasa yake ta Shan kamshi tun dazu.
Hannun sa yakai kan Albarkatun kirjin ta Yana shafawa a hankali domin tuni Sam ta cire tata rigar itama, daga karshe yakai bakinsa Yana tsotar su tamkar ya Sami sweet.
A Wannan lkcn dai a parlo aka baje koli shi da Samantha. Ya Kuma samu yadda yakeso domin 100% ya samu duk Abubuwan da yakeso dama yafi son wayayyiyar mace wacce zata baje ayi harka sosai bawai kidahuma ba.
******
*KAUYEN JIRAGO*
*”Bilqees,* Bilqees….Ke Bilqees”
cewar wata mata dake tsakar gida a zaune ta baje da tire a gabanta shake da doyar rogo tana kasawa.
Bilqees da yanzu ta gama shafa Addu’ar da take tun bayan data gama sallar azahar ta mike a nutse ta fito a hankali tace,
“Na’am dagowa matar tayi tana banko mata harara hade da Jan tsaki tace,
“Ishashiya sai yanzu kikaga damar Amsa kiran da nake maki tun dazu?”
“Sallah nake Baaba zabba.”
“Ke dallah tafi can dauki kason ki keda uwarki Kiyi gaba”
ta Ida mgnr tana nuna mata doya kwaya biyu kacal kananu wai shine kason su na abincin Rana ita da mahaifiyar ta, sauran kason ta duba sai taga Duk an shake shi a cike kowanne yanada doyar rogo manya masu kyau da gari ba irin tasu ba me cike da jijiya….,
“Bazaki dauka bane kika min tsaye akai kamar wacce zata dokeni?”
“Bilqees dauko Mana”
Cewar Inna habi mahaifiyar ta da fitowar ta a bayan gida kenan rike da buta zatayi Alwala taji Inna zabba na yiwa bilqees mgn.
Dukawa Bilqees tayi ta dauko doyar tana juya Baya Inna zabba tace,
“eh ba shakka uwarki ai tayi mgn dole kiji Amma dake ni kin maida ni er Tasha tun dazu nake kwarara maki Kira baki zoba saida kikaga dama sannan kika fito Toh Wlh ki kiyayeni dake da uwar taki duk Idan iskanci na ya motsa sai abincin gidan Nan ya gagareku gaba1.”
“Kai…kaii hayaniyar me nake ji ne tun daga kofar gida?”
Wani dattijo ya fado gidan hannun sa rike da iccen bishiya karami Yana aswaki. Inna zabba’u tace,
“ni da waccar ishashiyar yarinyar taka Mana mlm Musa”
mlm Musa ya dakata da aswakin da yake yana bin bayan bilqees data kusa shigewa daki yanzu da harara yace, me ta miki?”
Inna zabba’u ta karkace baki tana gyara daurin dan kwalin ta tace,
“akan abinci ne mlm wai kamar bilqees ta dubi doyar gabana tace tafi karfin cinta nikuma nace duk tsiya dai ai gidan mahaifin ta ne, idan tanaso ta nuna Wannan isar saita bari idan tayi aure sai tayi Wannan mulkin a gidan mijinta.”
Mmki ne ya kama Bilqees dake zaune tsakiyar dakinsu tana jiyo karyar da inna zabba’u take shirgawa mahaifinsu. innarta na sallah Dan itama barin cikin gidan tayi tun bayan mlm Mus Daya shigo.
Zama yyi a dakalin kofarsa dake dab da fita ya shiga zabgawa Inna habi Kira, Gyaran murya Inna habi tayi saidai ba lalle yaji ba Dan haka bilqees ta mike tana fitowa waje tace,
“sallah take ba!a”
“zo Nan ai harda ke nake nema”
kirjinta ne ya fadi Amma ta dake ta isa gareshi tana dukawa a gabansa tace,
“gani ba!a.”
Kallo yake binta dashi kallo na tsana tamkar ba ‘yar daya Haifa ba yace,
“ke bilqees ni Zaki wulakanta akan tukunyar gidana?”
Da sauri bilqees ta girgiza kai tana fadin,
“ba!a Wlh ba Abinda nace akan abincin gidan Nan…”
salati Inna Zabba ta saki ta doka tace,
“ni zan maki Karya bilqees? Koda yake ai idan ma zagina kikayi bazanyi mmki ba Wlh.”
Kasa cewa komai, bilqees tayi domin tun ba yau ba ta dade da sanin makircin inna Zabba kishiryar mahaifiyar su.
“Toh ki jini dakyau na fara gajiya…na fara gajiya da dawainiyar ki bilqees”
a razane bilqees ta dago tana duban mahaifin nata fuskar sa a daure yace,
“kedin Nan kaya ce a gareni hakurina ya fara gazawa na gaji da daukar nauyin cin ki da Shan ki Kuma ke ba namiji da zan mora ba ke Kuma ba aure ba abin yamin yawa Wlh.”
Inna habi ce ta iso wajen da sauri jin furucin mlm Musa tayi saurin katse shi da fadin,
“Ina sallah naji ka kirani gani, ke Kuma bilqees koma tunda nazo.”
“Toh ai tare nake neman ku uwar son ‘ya’ya, ‘ya’yan da basu da amfani ko kadan sai afkin wahala tun daga haihuwa har tsufansu wahala ce.”
“Dan Allah kayi hakuri ka daina furta irin Wannan kalaman malam maza da mata ai duka Allah ke yinsu.”
“Dallah tafi can, matsalar Nan daga gareki ne, baki da kwari baki da gwabi, ace yara dai…dai har guda shida duk mata baki iya haufo namji ba? Wannan wacce irin bakar masifa ce…”
_Wa’iyazubillah._
Inna habi ta furta Hakan a ranta tana girgiza kai cike da takaicin halin mlm Musa. Yaci gaba da fadin,
“Saida nace karki haifo ‘yarnan Amma dake ke jarababbiya ce Saida kika nace ni nasan za’a rina ai nasan cewa bazaki iya haifo Abinda nakeso ba wato namiji Toh ki jini da kyau gaki ga erki Nan, katotuwar budurwa me shekara 16, ace har yanzu batayi aure ba abin kunya ne a gareni ni mlm Musa Dan haka na baku wata uku zuwa hudu idan har Bata fitar da mijin aure ba Wlh sadaka zan bayar da ita.”
Hankalin inna habi da bilqees ne ya tashi Wannan wacce irin jarrabawa ce ace mahaifin daya haifi yaransa ya dinga jin kamar Wani nauyi ne a kansa?
“Kunji Abinda nace??”
Ya maimaita Hakan cike da tsawa, girgiza Kai inna habi tayi tana kallon bilqees data dukar da kanta tace,
“tashi muje” mikewa bilkees tayi suka bar wajen zuciyoyin su babu dadi.
Inna Zabba ta saki murmushin jin dadi tana turo tiren gaban mlm Musa tace,
“kwantar da hankalin ka mlm yanzu dai fadamin doya da Manja zakaci? Ko kuwa mandako?”
Ta furta Hakan ranta fari tasss, sauke ajiyar zuciya yyi yana mikewa tsaye yyi cikin dakinsa batare da yyi mgn ba.
dariya sosai inna Zabba ta kwashe da ita tana fadin,
“Saini me ‘ya’ya maza bari na leka idan su ilu na kofar gida suzo su kwashi nasu rabon”
ta furta Hakan tana kwadawa sabitu Kira data hango wulgawar sa.
*WACECE BILQEES?*
Bilqees Musa direba, ‘ya ta shida kenan a dakinsu itace Nan Auta tanada yayunta duka mata sunyi aure Rabi, Sa’a, Atika, Shema’u, maimuna, sai ita Auta Bilqees, Mahaifiyar su Habiba da ake Kira da inna habi itace Nan uwargidan mlm Musa tun farkon haihuwa ta mlm Musa ya fito kiri-kiri ya nuna cewar bayason ‘ya mace saidai namiji, domin mlm Musa Yana daya daga cikin irin mutanen nan da basason haihuwar ‘ya’ya mata, ita kuwa inna habi Bata damu da kowanne za’a haifo ba fatan ta kawai ace Allah yasa masu Albarka, shikuwa Sam besan da Wannan ba sosai yasa kafa ya take yace matukar Bata haifo mace ba Wlh zai karo aure, inna habi tace ya karo mata uku ma bayanta Bata damu ba kowacce da halinta za’a zauna.
Haihuwa ta gaba sai gashi ta sake haihuwar mace, abin ya Kona ran mlm Musa a satin daya kamata ayi bikin Suna a Wannan satin mlm Musa ya angwance da amaryar sa zabba’u Hakan yasa ko abin Suna ba’ayi yanka ba, Wannan Abu yyiwa inna habi ciwo matuka Amma dai ta danne ta mika lamuranta ga Allah.
Shekara na zagayowa Amarya zabba’u ta haifo danta namiji habawa mlm Musa kamar ya zuba ruwa a kasa yasha dan dadi fadi yake ga Inda ake haihuwa, ga Inda darajar haihuwa take. A daidai Wannan lkcn itama inna habi ta sake haihuwar mace, wayyo Allah kamar an Kara kunnawa mlm Musa tsanar ‘ya’ya mata Sam beyi farinciki da Wannan haihuwar ba Dan haka itama babu abin yanka haka sunan ya tafi lami sikal.
Ta bangaren zabba’u kuwa abin ya mata dadi, domin ta samu miji a hannu sai Abinda takeso kawai akeyi a gidan yaranta biyar duk maza ne, Aminu, sabitu, isa, ilyasu, Lawal. sai ya kasance koda mgn ce anfi daukar mgnr ta sama data inna habi, yaran inna habi sai suka taso tamkar wasu bare a gidan sbd yadda mlm Musa ke nuna kyara da tsangwama a garesu tun Suna shekara sha 14 ya dinga aurar su ko basa so saiya aurar a haka suka hakura badan sunso ba saidai babu yadda zasuyi domin zaman gidan ma ba dadinsa sukeji ba.
Akan haihuwar bilqees kuwa ansha daba sosai, mlm Musa yace sai an zubar da cikin Dan ya gaji da wahala dukda ba Wani abin arziki yake masu ba amma cewa yake yara mata ba komai bane sama da dawainiya d wahala har tsufan su, Inna habi tace Sam baza’a zubar da cikin ba dake Allah yyi da rabon zuwan Bilqees haka dai babu yadda mlm Musa ya iya aka haifota Yana Jan tsaki ko kallon ‘yar ma bayason yi sbd tukukin takaicin mace aka sake Haifa, sai kuma Allah yyi haihuwar ta tsaya daga kan bilqees.
Bilqees ta taso tun tana yarinya ta fahimci mugun halin mahaifinsu dake nunawa a kanta da sauran yayunta da mahaifiyar ta Hakan yasa a koda yaushe fuskar ta take a daure Bata murmushi, sbd yawan tunani da yyi mata yawa da Rashin kwanciyar hankali, ga tsanar maza data taso a ranta tana ganin duk halinsu daya da mahaifin ta ba Abinda sukeso sama da su auri mace kawai suyita wulakantata batare da Wani daraja ko kima ba.shiyasa har gobe babu namijin da zaice yaga fuska a wajen bilqees bare yasa ran zata kulashi gashi Kuma Allah yyi mata sura a dire take irin wacce ake Kira coca cola shaped, gashin ta har gadon baya irin na cikakkun fulanin ga idanuwan ta dara-dara farare Kal tamkar Madara. Kullum Bata da abokin hira sama da radion dake dakinsu kullum tana manne a kunnenta tana sauraron shirye-shiryen da ake gabatarwa tun daga birni, abin na matukar birgeta har sha’awa yake Bata idan ana Wani shiri na ilimin yaran mu a yau, a yadda ake kwadaitar da ilimi ji take inama tanada Wannan damar na zuwa makaranta? Iyakar su ilimin Muhammadiya, na bokon kuwa primary ce kawai waccce a sati befi mlmi daya yazo ba dake Suna cikin lungu sosai shiyasa ba’a cika samun malamai ba gsky, sannan ba kowa ke kaunar shigowa Yankin ba sbd yadda yake da manyan jeji da Rafi zuwan mutanen birni wajen sai Wanda ya daure.
Mahaifin ta mlm Musa direba ne, dake diban mutane a motar sa a Kori kura zuwa can gaban kauyen su cin kasuwa ko wata Rana su shiga birni sannan su dawo gida shine sana’ar sa.
*CIGABAN LABARI*
*MASARAUTAR MANARAS*
Maimartaba sarki Abdallah ya dubi Gimbiya Falmata duba na tsanaki kafin ya dauke kai beyi mgn ba, dagowa Falmata tayi a sanyaye tace,
“Allah ya baka yawan rai maimartaba hannun ka baya rubewa ka yanke shi, har gobe dai yareema yaseer Dane a garemu idan mukace zamuci gaba da fushi dashi abin bazaiyi Masa kyau ba Dan Allah a duba.”
Falmata ta Ida mgnr tana Kara dukar da kanta kasa.
Shiru na ‘yan dakiku Maimartaba yyi kafin ya nisa a nutse yace,
“zanyi tunani akai”
kasa motsawa Falmata tayi lalle ba karamin fushi maimartaba keyi da Dan nasu ba yareema yaseer, musamman yadda yake nuna halin ko in kula akan mgnr sa yasa ta fahimci irin Girman fushin da yakeyi dashi… Gsky bazata so abin ya tafi a haka ba dole tasan yadda zata daidaita komai. Girgiza Kai tayi a sanyaye tana aro murmushin jarumta ta yaba a fuskar ta Tace,
“shikenan duk Abinda ka yanke a gareshi daidai ne domin kaidin mahaifin sa ne Kai kke da ikon komai a kansa, na barka lpy.”
Ta Ida mgnr tana mikewa a sanyaye tayi hanyar fita. “Dakata.”
Cewar maimartaba daya juyo a tsanake yana dubanta yace,
“dukda nasan cewa ya dade da kammala degree dinsa na biyu be dawo gida ba Hakan na nufin baya bukatar a takura Masa game da kazamar halayyar sa…..”
Ya cije lips cike da takaici kafin yaci gaba da fadin,
“Zan neme shi, zansa ayi Masa mgn ya dawo, Amma ki sani daga ranar daya dawo bazai wuce wata biyu ba zan hadashi aure da duk yarinyar Dana gadama…..”
Juyowa Falmata tayi a firgice Dan tun dazun dama Bata juyo ba kawai ta dakata ne tana sauraron sa, girgiza Kai yyi cike da Tabbatar wa yace,
“Abinda yake bukata kenan, nikuma zan Masa batare Dana ji ra’ayin sa akan yanada wacce yakeso ko akasin Hakan ba Wannan Kuma umarni ne daga maimartaba na masarautar MANARAS bawai daga mahaifi ba Dan bazan lamunci ya zubar min da kima da Daraja a idon Mutanen gari da kewaye ba Ina fatan kin fahimta???”
Hankali tashe Falmata ta girgiza kai cike da karbar umarni daga maimartaba babu damar musu bare ta samu abin fada haka tanaji tana gani ta shanye maganganun da taso furtawa a bisa yaken dole tayi Masa sallama sannan ta tafi sashen ta hankalin ta a matukar tashe.MASARAUTAR MANARAS*
Bayi ne jere a layi Suna duka mata wasu na zubewa idan sun ganta sbd girmamawa saidai Sam hankalin ta bekai garesu ba sbd tashin hankalin da take ciki na mgnr da sukayi da maimartaba akan yareema yaseer, shigewa sashen ta tayi tana me wucewa can kuryar dakinta batare data kula bayin kofar tata dake mata sannu ba.
Zama tayi a gefen lallausan gadon ta Wanda yaji ado da tarin mayafai irin na sarauta ta cire alkyabbar dake jikinta tana gyara zama sosai hade da fadawa duniyar tunani…
Ba komai yasa Gimbiya Falmata shiga Wannan yanayin ba saidan kawai tasan waye yareema yaseer, tasan yadda ya tsani Aure da duk Abinda zai danganta shi da Hakan bayaso, sbd Bata mantawa kwanani tayi Masa mgnr cewa yaje ya nemi duk yarinyar da yakeso a aura Masa domin ya daina Wannan kazamar halayyar tasa tashi guda ya nuna tsantsar tsanar auren a Fili yace bayaso, yace Kuma idan har akan Wannan dalilin ne ma takeson ya dawo Nigeria Toh ya fasa gwara yyi zamansa acan America domin babu plan din aure a ransa yanzu sam-sam.
A yadda ta fahimta har cikin zuciyar sa yake fada mata Hakan, Wannan dalilin yasa Gimbiya Falmata ke fushi dashi Bata karayi Masa mgnr ba saidai abinka ga uwa, gaba1 ta damu da yadda Al’amuran yareema yaseer ke dagulewa nisantar sa da masarauta na Kara yawaita sunan sa a matsayin babban da namiji Kuma Wanda ake sa ran ya haye karagar MULKI na Kara kokarin dushewa Hakan ya Kara daga mata hankali sosai,
Shiyasa ta yanke shawarar yiwa Maimartaba mgnr Dan ta lura kamar yyi watsi da lamarin sa a gefe…Toh Kuma sai Wannan ta kunno, batason ta Rasa danta Kuma idan ya fahimci za’ayi Masa aure batare da zabin sa ba tohm batasan mezai biyo Baya ba kuma dukda a kasan zuciyar ta tafi kowa son ayi Hakan ko Allah zaisa yareema yaseer ya shiryu ya daina mu’amala da matan banza.
Gwauron numfashi sosai Gimbiya Falmata taja bayan ta gama Wannan tunanin ta kwanta a hankali hade da lumshe ido tana fatan ace komai ya daidaita.
*AMERICA*
“You’re very sweet prince…”
Sam ta furta Hakan a daidai lkcn da take maida kayanta bayan sun gama masha’ar su.
lumshe ido yareema yaseer yyi beyi mata mgn ba ya kawar da Kai Yana dauko wayarsa dake kan center table ya latsa kiran Musa, Musa na can waje ya mike da sauri ganin kiran yallabai ya Kara a kunne cike da girmamawa yace,
“barka ranka shi dade” “tura mata kudi.”
Cewar yareema yaseer da yyi mgnr a takaice Yana kashe wayar.
Ko ba’a fada ba bafaden Musa yasan wa yake nufi Samantha a tura mata kudin harkar da sukayi, take kuwa yyi mata transfer din 1mil a kudin su na can, domin dama yanada account number yawan cinsu Already.
Sam na daukar pos dinta zata tafi domin tasan ba mgn zaiyi mata ba taji wayarta tayi Kara, murmushi tayi ko Bata duba ba tasan sakon yareema ne, Gsky tanason Wannan gayen ya hadu ta kowanne fanni maida wayar tayi ta iso gabansa lkcn idonsa a lumshe kamar me bcci ta duka daidai kan fuskar sa takai Masa peck kiss a goshi tana murmushi Tace,
“Thanks you…till we meet next time.”
Ta furta Hakan tana barin wajen cike da karairaya tana karkada bom-bom.
Yatsina fuska prince yyi yana Dan Jan tsaki a hankali ya Kara gyara kwanciyar sa akan kujerar d yake kafin ya lumshe ido ba’a dauki Wani lkci me tsawo ba kuwa bcci yyi awon gaba dashi. KAUYEN JIRAGO*
“Bilqees Kin gama hada wankin?”
Cewar Inna habi data shigo dakin yanzu tana miko mata Omo tace,
“Kiyi sauri kada Rana tayi maki a bakin Rafi”
karbar omon bilqees tayi tana cusawa cikin kullin wankin data hada tace,
“zan biya gidansu Ramatu ne domin tace min zataje” Inna habi tace,
“toh ku kula da hanya yauwa ga Wannan sakon na kukar miya ki bawa innar Ramatu kinji?”
Karbar kullin ledar kukar bilqees tayi tace, “tohm inna saina dawo.”
“Allah ya tsare.”
“Ameen”
Bilqees ta Amsa tana daukar kayan wankin akai zata Dora sai kuma ta dawo dashi tana kallon inna habi tace,
“Na manta inna anjima zanje kasuwar *GWAB’E* na saro kayan marmari na wajena sun kusa karewa.”
Inna habi tace,
“kayya Toh ai d kinyi mgn tun jiya gashi zakije wanki ko hakura zakiyi? Don kamata yyi kije kasuwar da wuri.”
Girgiza Kai bilqees tayi tace,
“zanyi kokari na dawo akan lkci kafin a fara lodin zuwa kasuwar tunda sai bayan azahar ake tafiya.”
“Toh shikenan Allah ya kaimu anjimar.”
Nan bilqees tayi mata sallama ta fito turus tayi ganin mahaifin ta a tsakar gida tsaye da inna zabba’u Yana shirin fita. Dukawa tayi har kasa tace,
“Ina kwana ba!a.”
Tsaki yaja Yana dauke kai beyi mgn ba, bilqees ta sake fadin,
“barka da safiya inna Zabba.”
Tabe baki inna zabba’u tayi dakyar tace,
“Lpy.”
Mikewa bilqees tayi zata wuce inna Zabba ta dakatar da ita,
“Tsaya bilqees.”
Inna Zabba ta furta Hakan tana kallon mlm Musa tace,
“kamar naga ka Tara wanki koh?” Mlm Musa yace,
“hakane”
inna Zabba tace,
“toh bari na debo mata su tunda itama wankin zataje.”
Harara mlm Musa ya dankarawa Bilqees yace,
“Ai da kin barni naga gudun ruwanta ‘yar jakar uba zataje wanke na uwarta batasan da nawa ba.”
Yyi mgnr kamar ya maketa, inna Zabba tace,
“Rashin hankali fa laifin duk na uwar ne tana Koya mata raina uba, bari dai na kwaso.”
Tayi mgnr tana shigewa dakinsa cike da dariyar keta.
Kasa dagowa bilqees tayi tana mmkin idan wajen wahala ne Toh ubanta ne, idan kuwa shine zaiyi mata wahalar ji yake tamkar tsintar ta yyi ba shine uban ba, ga tunanin yadda omon zai isheta ne ko a’a? Ga kuma kayan baba Wanda tasan ba lalle ya bata kudin sabulu ba toh duk Wannan be dameta ba matsalar kawai omon wajenta bazai ishesu bane.
Watso mata kayan inna Zabba tayi masu yawa kusan kala shida tace,
“A wanke su tass.”
Girgiza Kai bilqees tayi ta duka tana kwashewa kafin ta zuba cikin abin wankinta tayi waje.A kofar gida ta tarar da ilu Suna buga kwallon leda da abokan sa ga sauran yayunta can maza kwance kasan bishiya anata musu kan Wani kansilan dake wakiltar Yankin su, ta girgiza kai kawai tanajin takaicin gasu nan dai sun Dan tasa Amma har yanzu bata ga amfanin da mahaifin su ke cewa sunada dashi ba, domin duk ruwan gidansu itace Nan ke debowa haka zalika itacen girki ita ke siyowa da Duk Wani aike,
mazan gidan ba Abinda suka sani sama da suci sai kuma ayita hira kasan bishiya Ana musu daga Nan Kuma ayita bin daji Ana Harbin Naman dawa tamkar wasu mafarauta aikin su kenan.
Ta gefen su ta wuce fuskar ta a daure harta shiga layin su Ramatu a tsakar gida ta tarar da Ramatu na shirin fitowa ganin bilqees tace,
“kaga er halaq yanzu nake cewa duk yadda akayi kina hanya domin bakya Bata lkci”
Murmushi bilqees tayi tana gaishe da innarta dake zaune kan kujerar tsakar gida tace,
“ga sakon ki inji innata.”
Karba innar Ramatu tayi da fara’a tace,
“Kai Amma Nagode Wlh kice mata Ina godiya.”
Bilqees ta girgiza kai kafin sukayi sallama sannan suka bar gidan gaba1.
*AMERICA*
“Yallabai dama munada baki ne yau?”
Cewar Musa dake driving motar da prince yaseer ke ciki Yana Kara kallon gaban gidan da suke dawowar su daga Wani waje kenan sun Dan fita tun safe.
Dagowa prince yyi a nutse yana kallon fadawan dake tsaye gaban gidan sa kowanne yasha rawani Ana jiran isowar sa. Mmki ne ya kama shi, saidai be nuna Hakan a Fili ba kawai dai ya tabe baki Yana me maida kansa jikin laptop dinsa dake gabansa yaci gaba da latsawa hankali kwance.
“An gaishe da yarima me jiran gado, sarkin gobe da yardar Allah, gaba salamun baya salamun….”
Cewar fadawan dake tsaye a wajen suka fara yi Masa kirari cikin girmamawa da nuna soyayyar su gareshi.
Lumshe ido yareema yaseer yyi yanajin Wani irin yanayi haka na daban a jikinsa beyi masu mgn ba har lkcn da Musa yyi parking a cikin gidan daya daga cikinsu ya iso da sauri yana bude Masa kofa wasu na baza babbar rigar su yareema zai fito.
Yafi minti 10 zaune a cikin motar be taso ba en mulkin sun motsa kansa ya Kara zafi haka ya shanya su sai can ya fito cike da kasaita Yana gyara tsayuwar sa kafin suka sauke babbar rigar su.
Nan sukaci gaba dayi Masa kirari Suna binsa a Baya lkcn da yake tafiya izuwa parlon sa.
Tsayawa duk sukayi a bakin kofar parlon basu shiga ciki ba daya daga cikin ya dubi bafaden yareema Musa yace,
“Ka sanarwa yareema Sako ne daga maimartaba sarkin MANARAS Yana bukatar ganinsa daga yau zuwa gobe.”
Girgiza Kai Musa yyi ya shige cikin parlon lkcn yareema na hakimce kan kujerar sa, Musa ya fadi cike da girmamawa yace,
“Allah ya baka yawan rai Sako ne daga masarautar MANARAS maimartaba na son ganin ka daga yau zuwa gobe.”
Shiru yareema yaseer yyi bece u!an ba, har Musa ya cire tsammani dajin Amsa can dai yaji yareema yaseer yace,
“ohk.”
Sake dukawa bafaden Musa yyi yace,
“Zan isar da sakon ka domin kowa ya zama cikin shiri.”
Yana Ida mgnr ya mike yayo waje har yanzu Suna yadda suke Ana jiran aji ta bakin yareema Musa ya sanar dasu cewar yareema ya Amsa gayyatar sarki cike da girmamawa Dan haka kowa ya zama cikin shiri zamu wuce Nigeria.
Suma cike da girmamawa sukace, “Allah ya kaimu da Alkhairi Ameen.”
*MASARAUTAR MANARAS*
sad’af-sad’af ya karaso sashen nata Yana waiwaye fuskar sa lullube da jan mayafi, Kai tsaye ya shige ciki batare daya nemi iso ba domin ta boyayyiyar hanyar da zata sadaka da cikin dakin nata ya biyo kamar yadda ya saba a koda yaushe.
Kwarkwara sa’adiyya na kishingide wata baiwa na mata tausa sukaga shigowar mutumin fuskar daure da Jan kyalle, Tana ganinsa ta gane waye Dan haka ta dubi baiwar tata tana mata alamar ta fita ta basu waje,
Mikewa baiwar tayi kafin shikuma ya warware mayafin sa Yana dan waiwaye na Rashin gsky.
Mikewa zaune sa’adiyya tayi tana kallon sa a tsanake tace,
*”Sarkin gida* zuwan ka bana banza ba dole akwai muhimmin labari tattare dakai”
Dukawa yyi cike da girmamawa yace,
“Allah yaja kwana ranki shi dade akwai Wani muhimmin Abu da nake tafe dashi”
yyi mgnr kasa-kasa Yana Kara waiwaye. Girgiza Kai tayi tace,
“ni nasan da haka bayyanar ka anan Saida dalili”
sake risinawa yyi sosai Yana Kara kasa da muryar sa yace,
“ranki shi dade Abinda nake tafe dashi mummunan labari ne……”

 

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE