SARAUTA TAH CE CHAPTER 3 BY NUCEELUV

 

MASARAUTAR MANARAS*
A zabure ta kalleshi batayi mgn ba saidai kawai tana
jiran taji ta bakinsa ne, sarkin gida dake durkushe
gabanta ya sake waiwayawa kafin ya juyo cikin
magana kasa2 yace,
“daga majiya Mai karfi naji cewar maimartaba sarkin
MANARAS na shirin daurawa yareema yaseer aure
Nan bada jimawa b…”
“Wannan mgnr banza ce”
cewar kwarkwarar sa’adiyya da fuskarta ta fara canja
launin fushi tace,
“yareema yaseer din da baya kasar yaushe aka shirya
Hakan da zaiyi aure? Nifa d kaina na sanya Masa
tsanar auren Nan, na Kuma cusa Masa kaunar Zina a
zuciyar sa, sannan kace min za’ayi Masa aure? Toh
taya? Yaushe ma ya shiryu da har zaiyi tunanin aure?
Kasan irin karfin kafin da nayi a kansa kuwa? Gsky
bakaji daidai ba…”
zafi hankalin ta ya fara tashi. Cike da girmamawa Kwarkwara sa’adiyya ta karashe mgnr zuciyar ta na
sarkin gida yace,
“ai ranki shi dade shi kansa yareeman baisan da
zancen Wannan auren ba, Wannan duk shirin
maimartaba ne.”
Mikewa tsaye kwarkwara sa’adiyya tayi zumbur
hankalin ta a mugun tashe sai dukan hannun ta take
a hankali tana safa da Marwa a Tsakanin Inda suke,
jikinta har Wani rawa yake ta juyo a fusace tamkar ta
fashe da ihun takaici tace,
“yanzu duk kokarin da nake naga na raba Tsakanin
maimartaba da yareema yaseer Ashe Duk aikin banza
ne? So yake ya lalata min shirina? Duk zaman da
yareema Yazeed yakeyi a fada Hakan be wadatar
dashi ba sai hango sa yake acan wata duniyar daya
gama lalacewa a titi?? Kaii bazaiyi yiyu ba Wlh.
Karyane ayimin Wannan kutsen cikin plans dina.”
Ta furta Hakan tana me wucewa cikin can dakinta ko
takan sarkin gida Bata bi ba Hakan yasa shima ya
mike Yana maida Jan kyallen sa ya fice a sace kamar
yadda ya saba.
Tana shiga kuryar dakinta ta kada Wani Shantu take
Wani siririn farin hayaki ya fito ta ciki Yana yin sama
ya bace bat.
Boka Markus dake tsaka da tsafinsa yaga alamun
kiran kwarkwara sa’adiyya sbd bayyanar Wannan
farin hayaki, Hakan ya shaida Masa cewar lalle tana
neman sa, duban lkci yyi yaga har dare ya fara shiga,
Hakan ya Tabbatar Masa da cewar lalle kiran Nan
bana banza bane, take ya mike yana gyara rawanin sa
hade da shiga futuk irinta malaman fada sannan yyi
wuf ya fice Yana bin hanyar da zata sada shi da wajen
haduwar su shi da kwarkwara sa’adiyya.
Zaune ya sameta harta rigashi zuwa kafarta daya kan
daya tana girgiza ta ya karaso a nutse yana zama kan
Dan buzun sa na sihiri yace,
“Ranki shi dade lpy kike nemana a cikin Wannan
daren?”
Juyowa tayi a fusace dama bashi take facing ba, tace,
“boka Markus ya mukayi da Kai?”
“ban fahimci abinda kikeso kice ba ranki shi dade” Cike da daurewar Kai yace,
Tsaki kwarkwara sa’adiyya tayi kafin tace,
“Taya akai ka bari sarki ya fara tunanin daurawa
yareema yaseer Aure? Bayan ka sanar dani babu
Wani lakani dazai Karya sihirin yareema yaseer sama
da ya sadu da matarsa ta Sunna shiyasa ma muka
cusa Masa tsanar aure damma kar Azo da batun
Hakan Amma kwatsam sai naji mummunan lbri cewa
maimartaba na shirin yi Masa Aure????”
STORY CONTINUES BELOW
Shiru boka Markus yyi Harta gama kafin yace,
“Ranki shi dade Inaga Wannan duk Mai sauki ne…”
“ban gane ba”
ta katse shi rai bace, boka Markus ya gyara zamansa
kafin yace,
“Sam Bai kamata ki daga hankalin ki haka ba, kin
manta da kudurin kawar dashi da aka shirya idan ya
dawo ne? Ai kafin a kaiga auren ma an kawar dashi
saidai a maida auren Nan kan yareema Yazeed badai
yareema yaseer ba”
washewa tace,
Numfashi sa’adiyya ta sauke fuskarta na fara
“Kanada tabbacin auren kan Dana zai juye?”
Girgiza Kai boka Markus yyi cike da tabbaci, sa’adiyya
ta mike a tsanake tace,
“lalle kuwa zanje na fara shiri tun yanzu kafin lkci ya
kure.”
Tana gama fadin haka ta fice daga wajen.
*KAUYEN JIRAGO*
“Yau rafin ba mutane da yawa”
cewar Shema’u, bilqees tace,
“ai kinsan dayake yau kasuwa wasu sun tafi tun safe
Nima anjima zanje kasuwar”
Shema’u tace,
“kamar kinsan Nima zanje goron da nake sarowa ya bilqees tace,
kare”
“nikuma saura kadan kawai inaso na karo ne kada yyi
karacin”
“an gaishe da bilqees Mai kayan marmari”
tayi batace komai ba.
cewar Shema’u tana dariya. Dan murmushi bilqees
Sana’ar bilqees kenan Saida kayan marmari irinsu
lemo, ayaba, kankana, gwanda da sauran su. Ta zabi
Hakan ne sbd rufawa kansu Asiri ita da innarta da
sauran yayunta da Suma suke a wahale gidan
mazajen su, tana tausaya masu sosai a dalilin haka
ma ta kyamaci auren gani take duk kanwar ja ce
Kuma ta yarda akan Hakan duba da yadda mahaifin
ta ke gudanar da nasa halayyar a gida sai Hakan be
Wani Bata mmki sosai ba akan Abinda ake yiwa
yayunta.
ko yaushe takan kasa su a tire taje dandali dashi
kullum Inda sauran ke Saida abinsu itama ta jeru
wajensu da kayan marmari tana tallata abinta, Toh
dayake mazan wajen na son yi mata mgn sai kaga
sunata siya ko bada niyya ba…ita Bata San ma sunayi
ba domin har a wajen basa ganin fuska a wajenta
saidai su siya kawai a Hakan Suna kare mata kallo ba
damar mgn.
Saida suka gama wankin tass kafin suka dawo gida, a
gurguje bilqees ta shirya inna habi ta miko mata
abincin Rana da akayi tace,
“ya kamata kici Wani Abun kafin ki tafi”
girgiza Kai bilqees tayi tana shafa man habiba na ‘yar
karamar roba data siyo masu a kasuwar GWAB’E.
Tace,
“banajin cin komai inna”
inna habi ta dubeta a tsanake kafin tace,
“akan mgnr dazu ne?”
Shiru bilqees tayi batace komai ba, inna habi tace, Kara yin hakuri akan halayyar mahaifin ki wata Rana “kamar koyaushe bilqees Ina Mai baki hakuri, da ki
sai lbri bilqees.”
Hawayen da take dannewa ne suka zubo cikin yanayi
na kuka da Jan zuciya Tace,
“Inna mena tarewa ba!a ne a gidan Nan? Meyasa ya
tsane ni haka inna? Dama wai Dan Adam na zabar
Abinda za’a halitta Masa ne?? Ko kuwa mu da muke
‘ya’ya mata ba mutane bane…??”
Ta Ida mgnr tana fashewa da kuka Mai cin rai.
Jawota inna habi tayi tana lallabata a hankali tace,
“Yi hakuri bilqees, komai yyi farko zaiyi karshe,
sannan komai lokaci ne, wata Rana ko ance yyi da
kudi ma bazai iya aibata halittar ‘ya’ya mata ba
bilqees, kisa a ranki haka tamu kaddarar take
Jarrabawa ce daga Ubangi ya kamata mu kasance
masu hakuri a koda yaushe Allah Kuma na son bayin
sa masu hakuri domin mahakurci mawadaci”
Haka dai inna habi ta dinga lallashin bilqees harta
samu bilqees ta yarda ta tsakuri abincin kafin ta mike
ta shirya a nutse sannan tayi mata sallama a lkcn har
Shema’u ta biyo mata suka wuce kasuwar daga Nan.
*MASARAUTAR MANARAS*
“An gaishe da dawisu uban ado, yareema yaseer Mai
jiran gado sarkin gobe da yardar Allah, gaba salamun
baya salamun….”
fadawan masarautar suka fara yiwa yareema yaseer
kirari lkcn da motar data dauko shi daga airport tayi
parking Yana ciki a hakimce jikinsa sanye da Wani irin
tufafi na sarauta yanayin zanen da akayi Hakan zai
bayyana maka asalin waye shi, da kuma tsadar yadin
da akayi amfani dashi Wanda fadar kudin kayan zaisa
ka kafa jari Mai tsokar gske.
Kansa sanye yake da wata irin hula Mai daukar ido
manne da tambarin masarautar MANARAS Hakan ba
karamin Kara tatso da tsantsar kyawunsa yyi ba ko
makiyi saiya yaba.
Yafi minti 30mins zaune a cikin motar ko motsi beyi
ba Kai kace sarkin ne da kansa irin yanayin yadda
yareema yaseer ke gudanar da kasaitar sa na
matukar birge mutane da kuma shayin sa domin
komai nasa cike da kasaita yakeyi, a hankali ya zuro
kafarsa daya zuwa kasa sanye take da Wani irin
takalmi na Alfarma Saida ya bada tazarar lkci kafin ya
sanyo dayar kafar waje a lkcn har wasu fadawan sun
baza babbar rigar su Suna jira ya mike aikuwa Saida
ya Bata lkci kafin ya mike dakyar
wohoho…yareema yaseer kenan da ga Abdallah
Usmanu Yusuf maimartaba sarkin MANARAS. Nan fa
aka ci gaba da zabga kirari,
“takawar ka lfy yareema…fari kke tass Wanda babu
algus a ciki sukari kke fes bakayi farin banza ba yadda
jikin ka yake haka zuciyar ka take fara tass karyar
mahassada suga bayanka Allah ya tsare gabanka da
bayanka yareema yaseer sarkin gobe da yardar
Allah….”
Wanda besan da dawowar yareema yaseer ba Hakan dukkanin daukacin masarautar MANARAS babu
yasa aka shirya gagarumin shagali na tarbar yareema
yaseer babban da namiji ga maimartaba sarki
Abdallah.
Iyakar dannewar kishi yareema Yazeed yyi kafin ya
iya yake yana kokarin maida fuskar shi kamar
koyaushe irinta kamulallun bayi hade da nuna
tsantsar kulawa ga yareema yaseer da bayyana
farincikin dawowar sa. Ya
Isa gaban yareema yaseer lkcn daya shigo fada cike
da murna ya mika Masa hannu yana fadin,
“barka da dawowa Dan uwa”
girgiza kai yareema yaseer yyi alamar amsawa kafin
ya wuce gaban sarki domin kwasar gaisuwa.
Wani irin tukuki ne ya tokare wuyan yareema Yazeed
Amma ya daure yana ci gaba da yake yareema yaseer
ya durkusa cike da biyayya a gaban maimartaba Yana
yi Masa gaisuwa a matsayin sa na maimartaba kafin
su kebe ayi gaisuwa ta Tsakanin da da uba.
“Sarki ya Amsa Kuma Yana godiya hade da nuna
farincikin saukar yareeman masarautar MANARAS
lpy.”
Bafaden sarki Wanda shine bakin sarkin ya bawa
yareema yaseer amsar gaisuwar da yakeyi.
“Godiya muke, Allah ya Karawa sarki Daraja yaja sauran Wanda suka rako yareema yaseer Suma suka kwanan sarki”
furta Hakan cike da girmamawa Suma.
Neman izini yareema yaseer yyi sbd yanason shiga
cikin gida, bafaden sarki yace,
“an baka dama Yareema sarki na maka ban gajiya.”
Mikewa a nutse yareem yaseer yyi ya taho cike da
takun sa na kasaita yabar fadar gaba1.
Kusan mutum biyar ne suka bishi da harara Wani
daga ciki na yiwa na kusa da yareema yaseer inkiya
da wata irin alama ta munafukai wato bafaden sa
Musa….Wani irin jifa yyi da kwalbar dake hannun sa take ta tarwatse a kasa yana tangadi ya zube kan kujera zuciyar sa na turiri…
A sukwane ta isa gabansa tana waiwaye tun daga kofar shigowa dakin nasa ta bawa bayi umarnin duk su matsa can Baya kafin ta samu damar datse kofar tana nufar shi hankali tashe ta riko hannun sa tana fadin,
“Yazeed…”
fauce hannun nasa yyi batare daya jira ta Karasa mgnr data so yi ba ya fara mgn cikin yanayi na bacin rai da kuma maye yace, na gaji dayin Wannan basajar mami, na gaji…”Ya furta Hakan cike da Karaji tuni tasa hannun ta biyu tana rufe shi hade da waiwaye kafin murya kasa2 tace,
“haba yareema na so kke asirin mu ya tonu ne? Ka daina mgn da karfi mana za’a jimu”
tsaki yaja Yana kokarin cire hannunta daga bakinsa yace,
“Har shi ya isa ya dinga nuna min izza?? Dame yake takamawa Wanda ni Banda shi? Duka ma tsirar kwana nawa ya bani? Saikace Wanda ya ban shekara biyar gsky na gaji da dannewa billahillazi zansa a kashe shi….”
dafe goshi kwarkwara sa’adiyya tayi tana tunanin ya kamata lalle tasan abin yi tun kafin asirin su ya tonu, idan akace za’a kashe yareema yaseer yanzu Kai tsaye za’a iya gano waye yyi Hakan cikin gaggawa dole tasan abin yi tasan Kuma babu Abinda zai kwantar da zuciyar yareema Yazeed sama da akawo Masa mace ya kwanta da ita..take ta mike da sauri tana ficewa daga dakin bayan ta datse shi ta waje tayi hanyar da zata sadata ga bangaren bayin gidan,
cike da izza ta isa wajen nasu kowanne na aiyukan daya dace dashi, Kai tsaye tayi pointing wata baiwa alamar tazo, jiki na rawa baiwar ta taso sa’adiyya ta juya baya ita kuma ta biyo bayan nata cike da girmamawa.
Haka halayyar yareema Yazeed yake ta asali, cikakken mashayin giya ne sannan Kuma gawurtaccen Mai lalata da mata musamman bayin masarauta ko kadan babu Wanda ya taba fuskantar Hakan hatta su bayin kansu basa Kara tunawa da Abinda ya faru dasu sbd karfin kafin da sa’adiyya tayi ga duk wacce tsautsayi ya fada kanta zata Kai masa mace da kanta sannan Kuma suyi siddabarun da baiwar zata manta da Duk Abinda ya faru da ita tun bayan lkcn da suka tsunduma kafar su a sashen yareema Yazeed.
Kwarkwara sa’adiyya tayi Hakan ne domin kare mutuncin danta, tunda ta fuskanci Zina tamkar a jinin sa take haka ma Shan giyar a jininsa take bazata iya hanashi ba domin Bata taba hanashi Abinda yakeso ba Dan haka kawai ta yanke shawarar yin Abinda koda yareema Yazeed ya lalata mace babu Wanda zai gane hatta ita wacce akayi lalata da itan.
Baiwar na shiga sashen yareema Yazeed ta manta da kanta da kuma wacece ita, yareema Yazeed daya dauko takobi Yana dab da fitowa waje cikin yanayi na maye kwarkwara sa’adiyya ta turashi ciki da karfi hankalin ta a tashe yanzu idan aka ga yareema Yazeed a halin maye wanne irin kalllo za’ayi Masa? Tunda kowa a fuska yasan cewa kamilin mutum ne me cika ta Kamala Nan kuwa basu san cewar fuska biyu ne shi ba.
Yareema Yazeed daya fadi kasa sbd Rashin karfi a dalilin buguwar da yyi ya yunkuro dakyar zai mike kwarkwara sa’adiyya ta tura Masa baiwar dake bayanta sai gashi ya mike jiki na rawa kamar Wani mayunwacin Zaki ya fara kokarin cirewa baiwar kaya wacce ta zama mutum-mutumi a halin yanzu.
Ficewa daga dakin kwarkwara sa’adiyya tayi ta koma parlon sa bayan ta rufe kofar tasa ta ciki ita kuma ta zauna zaman jiran ya gama shedancin sa kafin ta tafi.
STORY CONTINUES BELOW
••••••
Da murnar ta, ta tare shi tana murmushi Tace,
“welcome back ya yaseer”
suhaima ta furta Hakan zuciyar ta fari tasss yayanta ya dawo, sai yanzu yyi murmushi yana dafa kanta cike da soyaya irinta ‘yan uwan taka yace,
“Tnx u lil sis.”
Ya furta Hakan yana karasawa gaban gimbiya Falmata da take zaune bayi na mata hidima,
dukawa yyi cike da girmamawa yace,
“Barka da hutawa ummi”
batayi mgn ba sai kallon bayin nata da tayi da ido alamar su basu waje take kuwa suka mike kafin ta dawo da hankalin ta kansa tana kallon yanayin sa a tsanake tace,
“da fatan ka iso lpy”
“Alhamdulillah ummi.”
Ya furta Hakan a tsanake yana tankwashe kafafun sa, “I missed you ummi”
ya sake furta Hakan yana kamo hannunta, Janye hannun tayi a hankali, yareema yaseer ya danyi murmushi yasan shi Mai laifi ne a wajen ummi harma da abban su,
“srry ummi”
ya furta Hakan yana kama kunnen sa, Dan sake fuskarta tayi kafin tace,
“meyasa kayi Hakan yareema?” “Ooo…ummi pls sorry kada a tada mgnr.”
Dubansa ta sake yi tana Kara Tuno kalaman Maimartaba da har yanzu take tunanin ya zasu kwashe da yareema yaseer?
“Ummi…”
ya Kira sunan ta a hankali, Yana girgiza hannun ta, Dan numfashi taja tace,
“ya kamata ka huta yareema kana bukatar Hakan”
tashi yyi beyi mgn ba kawai ya fice a dakin ita kuma ta bishi da kallo.
“Ummi ya kike Masa mgn haka?”
Cewar suhaima dake gefensu tun dazu,
“bazaki gane ba suhaima”
cewar Gimbiya Falmata dake Jan numfashi,
“tun ranar na lura kamar akwai Abinda ke damunki ummi ko zaki iya sanar dani meye Wannan abin?”
Murmushi Gimbiya Falmata tayi tana gyara zamanta tace,
“Ba komai suhaima jeki bangaren wajen dafa abinci kisa a hadawa yayanki Abinda yafi so Kiyi masu jagora akai Masa sashen sa.”
Gimbiya Falmata ta bawa suhaima umarnin Hakan cike da kawarwa da tmbyr da take mata.
*****
Saida yareem yaseer ya Bata lkci sosai kafin ya fito daga can cikin dakinsa bayan ya gama watsa ruwa ya kimtsa ya fitowa izuwa parlon sa,
zaune ya tarar da Wani kan kujera yana kallo wanda da alama besan da zuwan yareema yaseer din ba, dauke kai yareema yaseer yyi yana wucewa Inda system dinsa take zai zauna na zaunen ya dago Kai, ganin yareema yaseer yasa shi mikewa Yana isa gaban shi yace,
“Kai Amma Wlh baka da kirki frnd kana ganina Dan wulakanci ka Wani dauke kai..”
cewar Naseer Wanda yake aboki ne ga yareema yaseer Kuma da ga kanin mahaifin sa wamban Adamawa.
“Ban ganka bane”
yareema yaseer ya furta Hakan a takaice Yana bude system dinsa, janyo kujerar gefen nasa Naseer yyi yace,
“ka ganni, baka ganni bama duk amsar daya ce Yareema wulakancin ka ne dai har gobe karuwa yake.”
Dan murmushi kadan yareema yaseer yyi beyi mgn ba yaci gaba da amfani da system dinsa. Naseer yace,
STORY CONTINUES BELOW
“tohm da fatan dai an watsar masu da Abubuwan su acan koh?”
Hade fuska sosai yareema yaseer yyi Dan ya fahimci Inda Naseer din ya dosa ba akan komai bane face tarayyar sa da mata da yakeyi, shiyasa koyaushe basa zama waje daya sbd banbancin ra’ayi domin a koda yaushe Naseer cikin yiwa yareema yaseer fada yake da nasiha dake frnds ne sosai tun Suna yara kafin kowa a kaishi makarantar da yafi so.
“Na tabo maka ruhin ranka ai dole ka Bata rai” Naseer ya sake furta Hakan,
“Enough Naseer”
yareema yaseer ya furta Hakan yana toshe kunnuwan sa, tabe baki Naseer yyi yana mikewa ya koma can kan kujera batare daya Karayi Masa mgn ba yaci gaba da kallon sa.
Suhaima ce ta shigo tare da bayi a bayanta bayan ta nemi izinin Hakan,
“baby da kanki?”
Cewar Naseer daya mike da sauri yana karbar basket din dake hannun ta, murmushi suhaima tayi,
“ya Nas Ashe kana Nan”
“kwarai kuwa tun dazu ma ke nake jira a dalilin ki ma nazo”
ya Ida mgnr yana dire basket din a gaban yareema yaseer da ko dagowa beyi ba, sauran bayin ma ajewa sukayi sannan suka fita.
Suhaima ta dubi yareema tace,
“yaya ga abincin Nan ya kamata Kaci”
girgiza mata Kai yyi be dago ba, suhaima ta janyo Masa basket din dake shake da kayan fruits iri-iri tace,
“nasan kafi son Wannan akan komai”
tayi mgnr da murmushi, dagowa yyi ya kalleta sai kuma ya danyi murmushi yana karbar Apple din data miko Masa yace,
“Tnx u lil sis”
“anytime yaya.”
Juyawa tayi wajen Naseer tace,
“ya Nas wanne kkeso?”
“Kowanne baby indai ta wajen ki ne inaso”
murmushi tayi Masa, sannan ta Debo Masa wasu fruits din a Wani bowl mai kyau sannan ta kawo Masa inda yake zaune kan kujera itama ta zauna. Karba yyi cike da kauna yace,
“Tnx u baby I missed you.”
Yareema yaseer dake can gefe ya tabe baki Yana ganin shirme irin na Naseer wai ‘yar karamar yarinyar Nan da Bata wuce 17yrs ba yakeso koda yake tun Ana goyon ta yake masifar sonta har kawo yau gsky be taba ganin mahaukaci irinsa ba soyayya da jaririya.
Shigowa akayi parlon Kai tsaye batare da neman izini ba, Hakan yasa suka dago gaba1 Banda yareema dake Shan kankana da fork a hannu system dinsa a gabansa Yana latsawa.
“Ashe Duk kuna Nan”
cewar yareema Yazeed daya fado dakin Yana washe baki shi a dole yanaso ya boye haushin su a zuciya…
“ah Yazeed Ashe kana cikin gida” cewar Naseer dake bashi hannu,
“Wlh kuwa kasan babban yaya ya dawo dole Muzo kwasar gaisuwa”
cewar yareema Yazeed,
“Hakan yanada kyau yazeed bismillah zauna.”
Har lkcn yareema yaseer be dago ba kuma bawai Dan bayajin su bane.
“Yaya ya Yazeed na mgn”
Cewar suhaima data taso tana Dan bubbuga table din gabansa, dagowa yyi fuskar sa a hade a tsorace taja Baya tasan ma za’a rina.
STORY CONTINUES BELOW
“Ai da Kaina ma zan iso gareshi”
cewar yareema Yazeed daya taso bayan sun gama gaisawa da Naseer, matsawa tayi batayi mgn ba yareema yaseer ya dauke kai Yana ci gaba da Abinda yake, yareema Yazeed ya cije lips a sace Wani kululun takaici na cinsa a rai sbd Wannan sharewar da yaseer keyi Masa Amma ya maze Yana daukar apple din gabansa yace,
“Dan uwa barka da dawowa da fatan dai ka huta? Nace bari dai na karaso har Inda kke domin gaisuwar sai tafi dadi fiye da ayita cikin fada.”
Dagowa yaseer yyi a tsanake yana kallon sa..yareema Yazeed ya Kawar da ido da sauri alamun Rashin gsky tattare dashi, yareema yaseer yyi murmushi kadan na gefen baki kafin yace,
“I’m fine. Thank you.”
“Masha ALLAH, Wlh naji dadi Toh Dan uwa ya batun aure kuwa? Ya kamata ace kayi yadda muma zamu samu space koya ka gani?”
Ya Ida mgnr da murmushi,
“idan kanaso gobe ma sai ayi maka.” Yareema yaseer ya bashi amsar Kai tsaye.
“A’a ai baza’ayi Hakan ba Wlh, kaine gaba Dani ya kamata ace kayi aure domin shine burin kowa a Wannan masarautar…”
“umarni kke bani ko shawara?”
Yareema yaseer ya furta Hakan fuskar sa a hade Yana kallon Yazeed,
“ah..ni Banda ikon baka umarni ai, shawarar dai” “Toh bazanyi ba, Kuma kada ka sake min mgnr.”
Yareema yaseer ya furta Hakan cikin fada2, dariyar mugunta ce taso kwacewa yareema Yazeed sbd yasan duk a cikin shirin su ne na sawa yareema yaseer kyamatar aure, sai kuma ya cije Yana fadin,
“Haba Mana Dan uwa shifa aure….” “Get out…”
yareema yaseer ya katse shi,
“Dan uwa….”
“i said get outttt…..”
yareema yaseer ya furta Hakan cike da karaji Yana buga table din gabansa da karfi, jiki na rawa yareema Yazeed ya mike Yana kallon yaseer da Ransa yakai kololuwar baci ya tsorata kwarai kadan ya rage ma ya buge da Abu Allah ya tsare ya fice daga parlon gaba1.
Suhaima na ganin haka ta mike da sauri zata fice Naseer ya kamo hannun ta,
“Ina Kuma zakije?”
A tsorace Tace,
“yaya ne, banason yamin tsawa Nima.”
“Idan kowa na gudun shi waye kuma zai tsaya tare dashi?”
Naseer ya furta Hakan yana kallon yadda jikinta ke rawa, girgiza Kai tayi da sauri tace,
“ya Naseer bazaka gane ba pls sakar min hannu”
sakin hannun nata yyi domin yaga alamar lalle ta tsorata, aikuwa ba jimawa ta fice a parlon da sauri.
Sai bayan 15mins Naseer ya mike Yana isa gaban yareema da yanzu hannun sa ke kirji ya dora kafa daya kan daya Yana girgizawa a hankali idonsa a lumshe kamar me bcci,
“meyasa bakason hada inuwa daya da Dan uwanka Yazeed?”
Shiru yareema yaseer yyi dukda ya jishi amma ya share, Naseer yaci gaba da fadin,
“mutumin Nan a koda yaushe jiki na rawa yake tarbar ka, duk Inda kke kaji yazo domin kuyi hira irinta ‘yan uwantaka, koda yaushe Yana fada domin maye gurbin ka kafin ka dawo, Amma Kai a bangaren ka nunawa kke tamkar baka taba sanin sa ba, saikace Wanda yyi maka mugun Abu kamilin mutum dashi me sakin fuska ga jama’a babu ruwanshi Wlh.”
Maimakon ya bashi Amsa sai kawai yaga yyi Masa murmushi yana mikewa tsaye ya dauki laptop dinsa da cup din tacaccen lemon inibi ya wuce can cikin dakinsa dashi batare dayace u!an ba.
Takaice ne ya kama Naseer shima ya fice daga parlon gaba1.
~~~~~
A hanya suka hadu da wazirin Adamawa ya fito daga sashen sarki da alama ganawa sukayi ta sirri da sarkin, cike da girmamawa yareema yaseer ya gaishe shi, wazirin Adamawa ya Amsa fuskar sa a washe Yana miko Masa hannu sukayi musabaha,
“Ya kr2? An kammala koh?”
Waziri ya tmbyi yareema yaseer,
“Alhamdulillah”
ya bashi Amsa a takaice.
“Masha ALLAH ubangiji Allah ya bada sa’a, ya taimaka”
“Ameen.”
Yareema yaseer ya furta Hakan yana kokarin tafiya mgnr da waziri yaso yi Masa ya fasa shima ya wuce kawai abinsa.
Saida sarki ya bashi izinin shiga kafin ya isa cikin parlon nasa daya sha kayan alatu, ya kawatu da ado irin na sarauta, kowa ya shaida a bangaren Arewa babu Wanda yakai Sarkin MANARAS daukar Ado kamar shi, shiyasa yareema yaseer yyi gado domin har yaso ya kere uban nasa a daukar wanka.
Dukawa yyi da ladabi yace,
“Barka da hutawa Abba, da fatan na sameku lpy.” “Lpy Alhamdulillah.”
Maimartaba ya bashi Amsa cike da kulawa Hakan ba karamin mmki yareema yaseer yaji ba domin yasan cewar maimartaba Yana fishi dashi fiye da yadda ma umminsu takeyi,
“zauna daidai mana yaseer”
maimartaba ya sake furta Hakan, cike da kunya yareema yaseer ya gyara zaman nasa a nutse yana dukar da kansa kasa hannun sa cikin dayan Yana tankwasawa a hankali,
“Ya kr2?”
“Alhamdulillah Abba.”
Maimartaba ya girgiza Kai yace,
“Masha Allah, shigowar ka Nan kun hadu da waziri kuwa?”
“Eh Abba” cewar yaseer,
“Good zuwa jibi inaso kaje gidanshi ku gaisa tare da iyalansa Suna ambaton ka a koda yaushe kaine baka zuwa”
Take yanayin yareema yaseer ya canja bawai bayason zuwan bane a’a saidai kawai yadda ‘yarsu ke neman takura Masa a rayuwa ne wato safeenah, tun ba yau ba ya fahimci irin son da take Masa tamkar zata kawo kanta sbd son ya aureta har gudun ma zuwa yake domin yadda yasan waziri da sarki frnds ne komai zai iya faruwa Wanda Sam bayan fatan Hakan ko a mafarki wato a hadasu aure.., Koda ace yanada niyyar aure ma safeenah Bata cikin tsarin matan da yakeso domin Bata da aji kwata2 bazata dace da izzar da yake takama da ita ba sam-sam.
“Why are you silent?”
Maimartaba ya tmby Hakan a nutse yana kare Masa kallo, girgiza Kai yareema yaseer yyi da sauri yana kokarin tashi yace,
“shikenan Abba…zan iya tafiya?”
Ya nemi izini, daga Masa Kai maimartaba yyi batare da yyi mgn ba shima ya dauke kai.
Numfashi kadan yareema yaseer yaja kafin ya sake yin sallama kawai ya tafi.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE