SARAUTA TAH CE CHAPTER 4 BY NUCEELUV
SARAUTA TAH CE CHAPTER 4 BY NUCEELUV
KAUYEN JIRAGO*
“Bilqees habu fa yace min zai turo”
Cewar Shema’u da suke kan hanyar su ta shiga kasuwa yanzu bayan sun sauka a motar da suka taho daga kauyen su. cike da murna bilqees tace,
“Dgske?”
Girgiza Kai Shema’u tayi, tace,
“Wlh jiya da muna hira ya furta min Hakan saidai ban kaiga fada a gida bafa”
“Toh meyasa?”
Bilqees ta tmby tana kare mata kallo, fuskar Shema’u ce ta canja cikin Wani irin yanayi tace,
“banaso na barki ke kadai kina yawo ne bilqees bazanji dadi ba”
Ita dariya ma taso Bata Amma ta dake tace,
“Haba Shema’u saikace bakisan komai lkci bane? Ai shi aure da mutuwa lkci ne, duk yadda kaso yin aure idan lkcn beyi ba Wlh bazakayi ba, Dan haka ki daina damun kanki a dalilina Allah ne yyi nufin lkcn auren ki Dan haka ya kamata mu gode Masa Alhamdulillah”
ta Ida mgnr tana murmushi, Shema’u ta numfasa kadan tace,
“toh amma bilqees meyasa kika tsani mazan kauyen ne? Kina jawowa Ana maki kallon me bakin jini alhalin kece Nan bakyason kula samarin da suke da muradin auren ki a kowanne lkci”
Bilqees ta Dan hade fuska kafin tace,
“Shema’u kenan, idan Tani ne gwara na mutu a haka babu aure fiye da ace nayi, domin har ila yau ban taba jin sha’awar aure a rayuwata ba Shema’u, na taso a wata irin rayuwar da har yau ban hango Alfanun yinsa ba,
Domin duka halin mazan dayane, basu da buri sama da su wulakanta mace a kowanne lkci, basu san cinta ba da shanta, duk yawanci matan kauyen mu da kansu suke ciyar da kansu,
mazan da anyi auren bayan wata uku zasu gudu su tafi cirani can kasar kudu da mukejin lbri wasu idan sun tafi sai suyi wata bakwai basu waiwayo gida ba, wasu ko aike babu,
Toh kada na kaiki da nisa mijin yayata Atika da take aure acan gaban kauyen mu gabashi su biyu ne a wajen mijinsu, dayasa kafa ya fice zuwa cirani can wata jiha Kano ko inane? Naji dai Ana ambata a radio, tunda ya tafi babu Aiken fari bare na baki, da kansu suke ci da kansu da ‘ya’yansu, har yyi wata takwas acan Amma abin takaicin daya tashi dawowa duk Wannan watanni wai sai gashi ya taho masu da ‘yan kunne kanana guda biyu da sinkin biredi guda daya shikenan fa tsarabar? Ba batun ‘ya’ya Kuma, ba batun abincin su, Toh ki ganemin Wannan aure ne ko zaman kaddara?
Ni Kuma dana zauna Ana tozarta ni gwara ace na kare rayuwata a haka babu aure Wlh.”
Numfashi Shema’u ta sauke kafin tace,
“Kinada gsky bilqees Toh Amma ya zamuyi? Haka tamu kaddarar take”
tabe baki bilqees tayi tace,
“ai shikenan Allah ya zabar Mana da Abinda yafi zama Alkhairi.”
“Ameen”
Shema’u ta Amsa a daidai lkcn da suka Karasa cikin rumfunan kasuwar zasu zagaya kafin su sayi Abinda ya kawo su.
*YAREEMA YASEER*
Kallon agogon hannun sa yyi, sai kuma Yaja tsaki a hankali yana Bata rai, Kamar daga sama haka yaji karadin muryarta ta fito daga wata kofar ta bayansa cike da murna tace,
STORY CONTINUES BELOW
“OMG! Prince kaine a gidan namu yau?”
Ta furta Hakan da murnar ta tamkar taje tayi hugging dinsa, cije kasan lips dinsa yyi a hankali beyi mgn ba, be Kuma kalli Inda take tahowar ba saima sake kallon agogon hannun sa da yyi yanajin gaba1 ya takura da jira,
zama tayi daga Dan nesa dashi sbd tasan halin nasa tace,
“barka da zuwa prince, da fatan ka dawo lpy? Ya kr2 Ya america I missed you…..”
“Fine.”
Ya katse mgnr nata da sauri a takaice Yana yatsina fuska Dan ta fara isar sa da surutu,
mikewa tayi ta jawo abin motsa bakin da aka kawo Masa dazu tahau tsiyayo Masa lemo sai kwarkwasa take tace,
“Prince sai lbrin zuwan ka naji, ni da kullum nake tmbyr ka a cht yaushe zaka dawo? Baka bude bama bare nasa ran reply idan an Kira ka a waya ma baka dauka tohm nidai banyi fushi ba…”
ta Karasa mgnr tana juyowa hade da cup a hannun ta saita ga wayam ba kowa a wajen, da mmki tahau waige2 can ta hango shi a bakin kofar fita ya saka dayan hannun sa a Aljihu daya Kuma ya Kara waya a kunnen sa yana mgn a hankali…,
Ajiyar zuciya Safeenah ta saki tana aje cup din hannun nata daidai lkcn ya juyo yana kallon ta yace,
“where is mom?”
“Tana zuwa yanzu ma zata zo ku gaisa”
ta bashi Amsa da wuri tana fadin,
“bari nayi mata mgn.”
Ta furta Hakan a jere tana ficewa daga parlon jikinta na rawa.
“Mtwss…”
Yaja tsaki kasa2 yana dauke kai Sam bata da class.
Komawa yyi ya zauna Yana latsa waya mom ta shigo cikin shiga ta Alfarma, zamowa yyi kasa cike da girmamawa yahau gaishe ta, amsawa tayi da fara’a tace,
“ya kr2?”
“Alhamdulillah”
ya Bata Amsa a takaice.
“Masha ALLAH, Allah ya taimaka, an gama ko?” Girgiza Kai yyi beyi mgn ba, mom tace,
“abin naku kamar hadin baki da safeenah satin daya wuce ta gama degree dinta Bata dade da dawowa ba itama.”
“That’s Good.”
Ya furta Hakan a takaice Yana kallon agogon yace, “Dad fa?”
Wato waziri, mom tace,
“kasan yanzu Yana fada saidai ku hadu acan” Girgiza Kai yyi yace,
“Shikenan mom ni zan tafi”
“haba da wurwuri haka yaseer? Inace zuwa kayi mu dade Ana hirar zumunci especially tunda safeenah na Nan ai sai ku gaisa sosai dama tana missing abokin hira tunda yaran Nan suka tafi skul.”
Murmushi yyi a takaice kafin yace,
“Ina kan hanya ne”
ya Ida mgnr yana mikewa tsaye,
“ohk Toh ka gaishe da ummi pls da kuma suhaima.” “Insha ALLAH”
Ya furta Hakan yana ci gaba da fadin,
“bye.”
Yana gama fadin haka ya fice a parlon gaba1.
Bayin dake jiransa a waje ne suka taso cike da girmamawa suka take Masa Baya, bude Masa kofar motar sa akayi bafaden sa Musa yaja motar a nutse suka fice daga gidan gaba1.
STORY CONTINUES BELOW
Zuge labulen window dinta tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali,
“Safeenah”
taji mom ta Kirata, da sauri ta waigo tana washe baki tace,
“mom”
mom tace,
“leken sa kike?”
Girgiza Kai safeenah tayi da sauri tana barin wajen tace,
“Gyarawa nake”
murmushi mom tayi kafin Tace, “biyoni”
bin bayan ta safeenah tayi har Suma koma parlo kafin Nan suka zauna a kujera, mom ta dubeta a tsanake kafin tace,
“zuwa yanzu ya kamata ki kwantar da hankalin ki domin yareema yaseer ya kusa zama naki”
a razane safeenah ta dubi mom d mugun mmki tace, “ni Kuma? How??”
Murmushi mom tayi, kafin tace,
“Bance ki sanarwa da kowa Hakan ba, Amma Ina me Tabbatar maki da auren ki da yareema yaseer bazai wuce 3weeks ba an boye Hakan ne sbd uban gayyar anason bashi surprised ko nace wanna itace kyauta Mai tsoka da za’ayi Masa ta murnar kammala degree dinsa na biyu…”
wayyo dadi safeenah ta Rasa Inda zata dura kanta taji dadi kamar tayi ihu dan murna fadi take
“mom dame zan saka maki da Wannan kyakkyawan Albishirin din? Wayyo ni Allah Ashe zan zama matar yareema yaseer? Wlh ko a mafarki”
dariya mom tayi tana kallon shirmen ‘yartata kafin tace,
“a Wannan wautar taki yareema ke Kara dauke maki Kai haba saikace ba ‘yar MULKI ba? Kema fa jinin sarautar na yawo a jikin ki domin kedin ‘yar wazirin sarkin MANARAS ce.”
Mom ta Ida mgnr da fada. Sunkuyar da Kai safeenah tayi tana wasa da yatsun ta, batasan meyasa ba matukar tana tare da yareema Bata da Wani sukuni, sannan Bata da Wannan kwarin gwiwar da zata iya nuna ita din ‘yar mulki ce saidai kawai taga tana mugun shakkar sa da tsoron sa.
“Ya kamata ki dinga iya takun ki safeenah”
mom ta sake furta Hakan tana mikewa daga wajen gaba1.
Kwanciya safeenah tayi tana bude wayarta murmushi lullube a fuskarta ta shiga folder din da take aje hotunan yareema take ta fara kallo a hankali tana zuba murmushi kamar wacce aka yiwa Albishir da gidan Aljannah.
******
“Baalkii…ke Baalkiii dake nake fah”
cewar lauwali dake masifar son bilqees, shi kadai ne namijin daya iya zuwa Kai tsaye yace Yana sonta Kuma har yau be daina bibiyar ta ba saidai batazo kasuwar ba,
Bata rai tayi sosai batayi mgn ba tana jiran a gama zuba mata lemon ta su tafi ya bantaro rake Yana sha yawu na Dan tsartuwa kadan-kadan yace,
“Kur’ani Baalkiii ranar auren mu mota-mota ta rake za’a dinga jibgewa Ana yiwa ‘yan Taron biki miyar taushe.”
Takaici ne ya sake kulleta, yyinda Mai zuba lemon malam haruna yace,
“haba lauwali ka bari Mana idan ka gama shan rake sai kuyi mgn”
ya Ida mgnr yana dariya Dan da alama santin raken ne ke dibar sa mutanen wajen kuwa dariya suke tayi Masa a sace,
“kaiii kur’ani zan caccake ka, na Huda cikin ka billahillazi ni zaka kawowa iskanci??”
Lauwali ya furta Hakan yana zaro Addar dake rataye a bayan sa…zaro ido bilqees tayi jiki na rawa haruna kuwa yace,
“Allah ya baka hakuri gashi bilqees na bar maki canjin Allah ya kiyaye”
ya furta Hakan a tsorace yana mika mata ledar da sauri burinsa tabar wajen ko Allah zaisa shima ya tafi,
“Toh korar mu kke? Na rantse da Allah zaka sa na sassara ka yanzun Nan…”
“Lauwali…”
bilqees ta furta Hakan da karfi ranta a bace ganin na shirin yin ta’asa dukda cikin ranta a tsorace take ainun Hakan be hanata dakewa ba sosai tace,
“kisan Kai zakayi?”
Dakatawa yyi yana murmushi yace,
“ai kin gama biya Baalkiii furta Sunana daga gareki ya ceci rayuwar sa Wlh, muje mu tafi”
ya furta Hakan yana yin gaba cike da tafiya irinta mafarauta.
Kamar ta fashe Dan haushi haka takeji, Amma da alama idan Bata bishi ba zai iyayin Abinda yayi niyya Hakan yasa ta bishi ranta a mugun bace,
daga can nesa ta hango Shema’u na dago mata hannu, zamewa tayi a sace batare daya lura ba kawai ta tafi wajen Shema’u da gudu suka canja wata rumfar,
“ya kika tafi kika barni a wajen?”
Bilqees ta furtawa Shema’u Hakan, gwalo ido tayi a tsorace tace,
“Baki ga ta’asar da lauwali yaso yi bane? Ai tunda na ganshi ya nufo wajen siyayyar mu Wlh na zame Ina zan iya? Allah Na gani bazan iya tsayawa ba tsoron sa nake”
cije lips bilqees tayi cike da takaici Tace,
“Na Rasa wacce irin jaraba ce da lauwali ya Rasa yarinyar da zaiso Saini? Gsky ya cuceni Allah isa.”
Ta Ida mgnr ranta na mata zafi.
Lauwali shugaban mafarutan duka kauyukan zagayen kenan, Wanda ya gagari kowa, kowa na shakkar sa ba Wanda besan lauwali ba, da kuma muguntar sa, yadda ya saba kashe Naman dawa haka Sara da sukar mutane ba komai bane a wajen shi, ya hadu da bilqees ne a sanadin zuwansu kasuwa sun shigo shawagi cikin gari dake shi yafi zama a daji sosai anan ya kyallo bilqees ya Kuma nace mata a koda yaushe Baalkiii… Baalkii…. Shidai Yana sonta, Hakan ya faru ne tun bayan sati uku da suka hadu a kasuwar GWAB’E.
“Kinfi kowa kyau aduk kauyikan da nake zagawa Baalkiii…”
Ya Ida mgnr yana waiwayowa, wayam… yaga bata wajen,
“burar Karen Nan…Ina kike Baalkiii???”
Ya furta Hakan yana shawagi shi kadai a wajen.
Acan wajen su bilqees kuwa sake hanya sukayi tacan bayan kasuwar suka bi dukda da nisa Amma sun gwammace subi hanyar da ace sun sake gamuwa da lauwali.
“JIRAGO…JIRAGO… JIRAGO…”
kwandastan motar kauyen ya dinga raraka murya Yana neman fasinja, wu!f su bilqees sukayi suka fada motar batare da sunyi mgn ba kwandastan ya juyo,
“ai sai kuce ga fasinja ‘yan mata”
basuyi Masa mgn ba sai sauke ajiyar zuciya da sukayi bilqees kuwa harda lumshe ido…
“Da alama kin gaji sosai koh?…”
lauwali dake zaune gefen da bilqees ta zauna ya furta Hakan yana Sosa gashin bakin sa ta sama…
“Nima na gaji Wlh tun dazu fa ke nake jira, ba Inda ban zaga ba a kasuwar Nan na rasaki karshe dai nace duk tsiya dai Zaki nemi motar kauyen ku shiyasa na yanke shawarar shiga mota yaude har gidanku zan gano Baalkiii.”
Ya Karasa mgnr yana dagaje yalayen hakoran sa.
Tsabar firgita ma bilqees kasa motsi tayi gaba1 ma ta sandare tamkar wacce take cikin firiza.