SARAUTA TAH CE CHAPTER 5
SARAUTA TAH CE CHAPTER 5
YAREEMA YASEER
Daren ashrin da bakwai lkci ne da yawanci yake zuwa cikin duhu a dukkan dararen wata, dukda dogarai da bayi dake shawagi a dukkan sassan masarautar Hakan be hana mutane biyar dinnan samun aiwatar da shirin su ba, da alama ba karamin shiryawa Hakan akayi ba.
Cikin Wani katon buhu suka saka yareema yaseer da izuwa yanzu ya zama tamkar gawa domin baya koda motsin kirki bare yasan a duniya yake ko akasin haka? Ta Inda suka shigo tanan suka fice da yareema yaseer Sunyi kama-kama Suna tafe dashi tamkar kayan wanki ko Wani Abu marar galihu, a haka suka fice daga masarautar gaba1 Wannan nasara sun sake samunta ne daga wasu maboyan makiyan da Sam ba’asan dasu ba domin kuwa kwarkwara sa’adiyya da danta yareema Yazeed sunyi kadan su iya gudanar da Wannan babban aiki a masarauta irinta MANARAS.
Firgigit ta farka daga lallausan gadon nasu da take bcci kirjinta na bugawa da karfi, salati Gimbiya Falmata ta saki tana kama kijrinta Wanda Hakan ya jawo farkawar maimartaba daga barci.
Dan kunna wutar gefensu sukayi Sannan ya kamo hannun ta a tsanake yace,
“Lpy Gimbiya?”
Haka kurum taji jikinta na Bata babu lpy da sauri ta girgiza kai Tace,
“inajin kamar akwai mummunan Abu dake faruwa.” “SUBHANALLAH”
Maimartaba ya furta Hakan yana mikewa da sauri yace, “kodai mafarki kikayi?”
Gimbiya Falmata tayi tsam da ranta tana tunanin mafarki ne ko kuwa haka kurum ta farka? Girgiza ta yyi domin yaga ta shiga tunani, mikewa tayi da sauri lkcn da kunnuwan ta suke jiyo mata muryar yareema yaseer _ummii…ummmiii…_ cikin Wani irin yanayi. Jiki na rawa Tace,
“Yaseer… maimartaba mafarkin yaseer nayi.”
Dafe goshi maimartaba yyi yana kokarin kwantar da hankalin ta yace,
“Yaseer Kuma? Duk Abinda kika gani ai mafarki ne ba gske ba, pls ki kwantar da hankalin Ki.”
Kasa nutsuwa Falmata tayi ta jawo alkyabbar ta saka tana shirin fita, maimartaba ya dauko nasa kayan ya dora akan na bccin sa suka fito waje.
Gidan yyi tsitt Banda ruwan sama da ake shekawa ba Abinda kkeji ga haske tarauu tamkar Rana, maimartaba ya kamo hannun ta yace,
“Ina Zaki a cikin ruwan Nan?” Gimbiya Falmata tace, “wajen yareema yaseer.” Maimartaba yace,
“haba sai kace yaro? Kin daga hankalin ki dayawa, baki ga ruwa ake ba? Ina yareema zaije yanzu? Yanzu haka ma bcci yake bare Kuma da Girman sa zai iya ji da komai ya kamata mu kasance masu kyakkyawan zato.”
Sauke ajiyar zuciya Falmata tayi tana girgiza kai haka tabi bayansa suka koma Amma zuciyar ta na sanar mata kamar akwai yareema yaseer a wajen.
Wata wawiyar ajiyar zuciya suka sake mutane biyar din da suke dauke da yareema yaseer wajen da suka boye, da ace su Gimbiya Falmata sun sake taku biyu kwakkwara Daga Inda suke da kuwa babu Abinda zai hana su gansu domin basu gama ficewa daga wajen ba.
Cikin sassarfa suka Kara saurin tafiyar su ta boyayyiyar hanyar da suke bi daga nan ne suka Karasa ficewa daga masarautar gaba1.
Can gaban motar da tayi parking daga nesa ne suka nufa Suna zuwa wajen suka sashi a booth din mota dama akwai driver a ciki Suna shigewa ciki ya fisgi motar a tamanin.
STORY CONTINUES BELOW
Sunyi tafiya me tsawo wacce ta fitar dasu daga birnin na Adamawa daga nan suka saki hanya Suna fadawa kauyika dake kewayen, basu tsaya anan ba domin sunfi so a jefar dashi can kauyen da zai Karasa rayuwar sa a can wanda shi da masarautar MANARAS sai a lahira idan anayi.
Hakan kuwa ta kasance har yanzu babu me mgn a cikinsu motar kuwa irin me shiga ko Ina dinnan suka Samo Hakan yasa take hayewa duk Wani kwazazzabo da ramuka idan sun fada. Sunyi tafiya me yawa kafin suka gangara Wani kauyen da su kansu basu san Ina suke nufa ba yanzu. Gargadin da boka Markus ya bayar suke tunawa wato a shiga ta yamma da gari sannan a aje shi a kofar makabarta.
Sunsha wahala sosai domin har sun debe tsammanin samun Wani kauyen Kuma can suka hango gidaje tsilla- tsilla daga nesa sun manta ma a bangaren yamma suka biyo ko kuwa gabar? Wani Kaho da suke tafe dashi na tsafi me Jan Ragamar tafiyar ya dauko Yana hurawa a hankali take Wani farin hayaki ya fito ya fice daga motar yana tafiya a hankali Wannan shine makamin da zai nuna masu makabarta idan sunje kamar yadda boka Markus ya fada musu Dan bazasu iya Samo makabarta da kansu haka Nan ba.
Hakan kuwa ta kasance Suna binshi a Baya a hankali Harya jefa su Wani dajin dake nesa sosai Yana zuwa wajen ya kama da wuta ya Kona kurmus.
Sun tsorata Amma sbd dakewar zuciya ta zalunci haka suka tsaya da motar Suna fitowa daga motar gaba1. Bayan booth din suka bude anan suka fiddo da yareema da har yanzu yyi doguwar suman da Baya cikin hayyacin sa. Daga Inda suke zuwa Inda suka ga hayakin ya kone suka dagashi sama sannan suka wurgashi da iyakar karfin su, ji kke timmmm tamkar ba mutum suka jefar ba, tamkar ba yareema yaseer suka wullar ba, yareema yaseer dinnan Dan wanka, Dan kwalisa, me ji da kansa, Wanda tacaccen jinin sarauta ke yawo a jikinsa marar gauraye shine dai yanzu aka watsar tamkar dabbar da tayi mushe a cikin daji.
Sunyi Hakan da gayya ne domin sunfi bukatar mutuwar sa sama da rayuwar sa Kuma. Haka suka shige motocin ba tausayi bare Imani a tamanin suka fisgi motar Suna sauri su isa gida kan lkci kafin wayewar safiya tayi.
*KAUYEN JIRAGO*
Dakyar inna habi ta samu bilqees tayi shiru sannan ta lallabata da kalamai masu dadi da kwantar da hankali, bilqees dai batace komai ba domin zuciyar ta a daure take da bacin rai dakyar ta iya bcci a ranar sai washe gari da safe taji zuciyar ta ta sake saidai ba duka ba.
“Wai Ana sallama da mlm Musa”
malam Musa dake kurbar Koko yace,
“uban waye yakemin sallama da sassafen Nan?”
Yaron yace,
“lauwali ne ba!a.”
Ko Karasa mgnr beyi ba ba!a ya mike da sauri jiki na rawa yace,
“jeka kace Ina zuwa.”
Ya furta Hakan yana jawo silifas dinsa ya zura. Lauwali na tsaye saiga mlm Musa, lauwali yace,
“Baaba Ashe ka tashi, barka da safiya.”
Mlm Musa yace,
“dan samari mu da zamu fita nema? Ai dole mu tashi”
“Lauwali yace,
“dama inaso na sanar dakai ne za’a turo manya domin a tsaida mgn”
Mlm Musa yace,
“Ai daka turosu Kai tsaye domin tuni na dade da baka bilqees”
Lauwali yace,
“godiya nake Baba zan wuce daji ne idan na dawo zakaji lbri.”
Mlm Musa yace, “toh a dawo lpy.” Lauwali yace,
STORY CONTINUES BELOW
“A gaishe min da Baalkiii Ina sauri ne dana tsaya mun gaisa.”
Mlm Musa yace,
“ba damuwa saika dawo.”
~~~
Tana cikin bccinta me dadi taji mlm Musa na zabga mata Kira,
“bilqees ke bilqees”
a razane ta mike tana yowa waje kanta ko Dan kwali babu tace,
“ba!a gani…”
Ransa a mugun bace yace,
“Duk Abinda kikasan naki ne ki fara shiryawa Nan da jibi zan aurar dake.”
Gwalo ido bilqees tayi hade da fashewa da kuka Tace, “ba!a ni bana son shi, ni ban taba sonshi ba.”
“Ke dallah tafi can ‘yar gwafar uba ba kece duk kika jawo min Wannan tsiyar ba? Shegen ji da kanki yasa kika hadu da Wannan Dan iskan lauwali Wanda besan kima da darajar mutane ba Kuma Wallahi saina bashi ke ai hutu ne a gareni.”
“Haba mlm…haba malam…”
Cewar inna habi data shigo gidan dama ta fita ne.
“Toh uwar tsugudidi marina Zaki?”
Janye bilqees dake duke gabansa tayi tace,
“gsky Abinda kkeyi baka kyautawa Wlh…”
“Iyeee?? Lalle ma habiba yanzu akan Yana yiwa ‘yarsa fada shine kike mgn kamar Zaki dokeshi?”
Cewar inna Zabba data fito a daki tana gyara daurin kwali.
“Yoh na nawa Kuma? Ai ban taba ganin me son ‘ya’ya irin habiba ba, yaran da haryau basu taba tsinana mata komai ba sai tsiya.”
Inna habi tace,
“kinga zabba’u bada ke nake mgn ba, Kai Kuma mlm Musa ka dinga Sara kana duban gatari domin hausawa kan ce baki kan yanka wuya Ina guje maka ranar da zakazo kana kunyar kalaman ka da kke furtawa akan ‘ya’ya mata.”
Tana gama fadin haka taja bilqees suka wuce daki. Ita kam bilqees gaba1 ranta ne ya sake baci tanajin tsanar lauwali na Kara tasiri a ranta gashi ta Rasa Inda zata sa kanta taji dadi, sai yamma taje gidansu Shema’u lkcn ta Dan samu saukin zuciyar ta.
Tana share tsakar gidansu ta hango bilqees na tahowa. Aje tsintsiyar tayi tace,
“oyoyo bilqees.”
Hararar ta bilqees tayi tana gaiswa da innarta. Dariya Shema’u tayi tana tunowa da jiya tun a mota da suka rabu Bata Kara waiwayar Inda suke ba tayo gida a guje tana haki kayan bilqees din ma a wajenta yake Bata tsaya batun Bata nata bama.
“Afuwan bilqees”
ta furta Hakan lkcn da suke zama. Bilqees tace, “kin cika tsoro Shema’u.”
Shema’u tace,
“kema Dan babu yadda kika iya ne wlh. Dukda dai na sanki da dakiyar zuciya Amma akan lauwali kowaye dole ya girgiza sbd illar sa, Amma dai ya kuka kare?”
Dan tsaki bilqees taja yanayin ta na canjawa ta sanarwa da Shema’u duk Abinda ya faru.
“Na shigenge..”
Cewar Shema’u data dafe kirji tana gwalo ido tace,
“Nan da kwana uku? Keda lauwali? Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un…, Mun shiga uku.”
Ta sake furta Hakan a tsorace tamkar ita akace za’a aurawa lauwali. Cije lips bilqees tayi a hankali tana kokarin saita kanta tace,
“Ina kayana?”
Tayi mgnr domin kawar da mgnr lauwali Dan ranta baci yake idan ana mgnr sa. Shema’u ta mike tana jawo mata ledar kayan marmarin ta tace,
“gashi nan.”
Karba bilqees tayi tana mikewa tace, “sai mun hadu a dandali.”
Shema’u tace,
“Tohm shikenan.”
Maimakon bilqees ta wuce gida sai kawai ta kama hanyar dajin su wajen wasu bishiyoyi data saba zuwa a Duk lkcn da ranta ya baci Bata da wajen zuwa sai wajen takan Bata lkci a wajen tana kallon ruwan dake gefe yana kwarara a hankali dake bulbulowa ta wasu Tsakanin duwatsu masu haske. Wajen akwai Ni’ima ba laifi.
Tayi tafiya sosai me nisa kafin ta isa wajen tana aje ledar hannun ta a wajen ta cire Dan kwalin ta dake kanta ta shimfida a kasa tana zama akai.
Jawo ledar tayi tana duba siyayyar da tayi a kasuwa cirosu tayi baga1 tana ware Lemo da ayaba gefe guda sai kuma kankana da gwanda Suma duk ta dinga ware su dasu goba kayan marmari dai kusan kala bakwai a ciki.
Tashi tayi ta Debo ruwa a cikin Wani Koko data makale a jikin bishiya tun kwanaki akan duk sanda tazo tana bukatar diban ruwa saidai ta dibo dashi ta huta amfani da zallar hannunta.
Fruit din ta tsaya wankewa Dan sun danyi datti cikinta ne ya Murda take ta tuna rabonta da abinci tun jiya har kawo yanzu ayabar ta ballo ta tsaya barewa a hankali ta cusa a bakinta tana taunawa a hankali hade da lumshe ido…
Ji tayi kamar motsi a bayanta Hakan yasa ta bude ido da sauri. Sake wara ido tayi a mugun tsorace tana duban mutumin dake gabanta ya harde hannayen sa a kirji hade da zuba mata na mujiya.
Kalle-kalle ta farayi tana ja Baya. Har lkcn be motsa ba fuskar sa ta baci da jini ga alamar ciwo Nan yaji a jikinsa Mikewa tayi a hankali tana ja Baya sai taga ya fara takowa Inda take…a mugun firgice ta juya zata gudu taji ta fadi Tim….
kafarta ta harde da Wani itace, kokarin tashi taso yi Amma ta kasa sake juyowa tayi sai kuma ta ganshi tsaye a kanta yana miko mata hannu, firgita ta Sake yi, baki na rawa Tace,
“Dan Allah waye Kai?Mutum ne ko Aljani? Idan sbd zaman da nake anan ne wlh na daina bazan sake ba”
Ta Karasa mgnr a rude tana kallon yadda ya sunkuyo a hankali Yana miko mata hannu alamar zai taimaka mata. Kin bashi hannun tayi tana jan kafa dakyar da alama ma kashin ta ya goce Dan ba karamar buguwa tayi ba.
Gani tayi ya tsugunna a nutse yana kamo kafar tata tayi kokarin kwacewa ta kasa domin ya rike, a nutse ya fara gyara mata kafar Yana yi a hankali sai taji bass..kashin yyi Kara alamar ya daidaita mata shi, karar azaba ta saki tana rintse ido shikuma ya matsa gefe yana komawa Inda ta tashi ya zauna.
Gani tayi ya dauko fruit din data bari Yana kaiwa bakinsa ya gatsa guava din daya dauko.
Mikewa tayi da sauri tana cije lips fuskar ta a hade Tace,
“Kai aje min kayana naka ne? Waikai waye Kai? Daga Ina kke? Dallah ni tashi ka tafi.”
Ta furta Hakan tana kokarin janye Dan kwalin ta daya zauna a kasa sai haki take tana cije lips.
Kamar bada shi take ba haka yyi banza da ita Yana tauna guava din a hankali tamkar Wanda yake cin mgni har yanzu beyi tari ba bare tasa ran Yana mgn ne ko akasin haka?Yadda taga jinin har yanzu be daina zuba akan fuskar sa ba yasa ta hadiye masifar data so yi Masa tana kallon sa cike da tausayawa ta rarrafa gabansa a hankali tana kallon fuskar tashi da kyau.
Idonsa na kallon Wani side din Dan be Wani kalleta ba dukda ta matso wajen Kuma yasan ta zauna kusa dashi.
“A Ina kaji ciwo haka? Su waye suka dake ka?”
Tayi mgnr da tausayi tana wara ido sai kallon wajen take harda keyarsa ma Abinda ya daure mata Kai har yanzu be damu d zubar jinin ba tamkar ba daga jikinsa yake fitowa ba.
Kallon Dan kwalinta tayi taga har yanzu Yana Kai bare ta goge Mai dashi. Numfashi taja kafin tasa hannunta tana kadawa a gefen idonsa tace,
“bawan Allah…kodai Kai kurma ne? Baka ji??” Tayi mgnr tana Masa alama d si!ar kurame.
Kyawawan idanunsa ya zube mata a nata take taji Wani irin faduwar gaba ta sameta Dan haka ta kawar dakai da sauri shi Kuma a lkcn yake mikewa zai tafi.
Da sauri ta kamo hannun sa batare data shirya Hakan ba. Ji tayi hannun da laushi sosai tamkar audiga.
Tsayawa yyi Amma be juyo ba Sbd ta rike masa hannu. Jan hannun nasa tayi zuwa bakin rafin dake gabansu tana kallon idonsa tayi Masa alamar ya zauna kan Wani dakalin Dutse.
Zama yyi kamar yadda tace ita kuma tasa Wannan kokon tana Debo ruwa ta dawo gabansa alama tayi Masa da hannu tace,
“wanke fuskar ka.”
Gani tayi ya zubawa ruwan ido Yana kallo. Dan girgiza shi tayi ta sake yi Masa alamar kurame Dan izuwa yanzu ta fara tunanin kurma ne tace,
“wanke fuskar ka”
Dauke kai yyi beyi Abinda tace ba Dan haka ta Dora hannunta kan lallausan gashin kansa da tun dazu take mmkin ganinsa ta Debo ruwan tana zubawa a fuskar sa. Take ya lumshe ido a hankali Yana sauke ajiyar zuciya. Ci gaba tayi da wanke Masa ciwon har lkcn idonsa a rufe Yana jinta. Hatta gashin kansa daya yamutse da keyar sa Duk Saida ta wanke Masa Sannan ta dawo kan kafarsa daya tutturje Nan ma.
Dagowa tayi da niyyar yi Masa mgn sai taga Ashe ita yake kallo. Kawar da Kai tayi tana mikewa ta kamo hannun sa suka koma wajen daya zauna dazu. Zama yyi sannan ta zauna tana dubansa a tsanake tace,
“waye Kai? Daga Ina kke? Daga wacce nahiyar ka bullo? Dan babu me irin kamar ka akaf fadin kauyikam mu. Kodai ka samu batan hanya ne? Da alama ma barayi ne sukai maka fashi koh???”
Duk ita kadai take ta jera wa’annan tambayoyin batare daya kalli side dinta ba bare tasa ran amsar Sa. Ya fara Bata haushi ta mike a zuciye tace,
“Ko Kai waye ma Kaci kanka”
Tana gama fadin haka ta zari ledar fruit dinta tabar wajen tana mgn ita kadai,
“haka kurum mutum ayita Masa mgn yyi banza dakai nayi alamar kurame ma duk a banza tamkar da Dutse kke mgn mwsss.”
Da Wannan maganganun tabar jejin gaba1 batare data sake waiwaiyar Inda yake ba.
*MASARAUTAR MANARAS*
Ba karamin tashin hankali aka fuskanta ba a wayewar ranar da aka nemi yareema yaseer aka Rasa sama ko kasa ba’a fahimci cewar baya masarautar ba Sai wajen karfe 11am anje Kai masa Karin kumallo suhaima taga baya Nan.
STORY CONTINUES BELOW
Da farko sunyi zaton ya fita ne Saida sukaci karo da wayarsa da system dinsa da komai daya saba fita dashi kafin suka farga da Wannan mummunan Al’amari.
Sun tmbyi duk masu tsaron sashen sa da sauran sassan waje kowa yace bega yareema yaseer ba.
Yadda yareema Yazeed ya daga hankalin sa sosai akai zaka dauka daki daya suka fito.
Soyayyar da maimartaba ke yiwa yareema yaseer Bata bayyana sosai ba Saida aka Rasa shi gaba1 anan hankalin sarki ya tashi Harya so bawa mutane tsoro sbd yadda hawan jini tashi guda ya kama shi.
A bangaren ummi kuwa tamkar mahaukaciya haka ta haukace da dimuwar Rasa yareema yaseer dukka dai masarautar yanzu cikin tashin hankali ake. Take kuwa aka bada umarnin kama dukkan masu tsaron sashen sa aka jefasu gidan sauya hali na masarautar basu zasu fito ba har sai randa yareema yaseer ya bayyana.
A rude ta karaso sashen bayi na mata gaisuwa Bata kulasu ba. Mama sarauniya uwargidan sarki itace Nan ta shigo sashen ummi hankalin ta a mugun tashe kwana biyu bata cikin masarautar sai lbrin batan yareema yaseer taji.
Ummi na cikin daki tana zubda hawaye aka sanar mata da isowar mama sarauniya. Batayi mgn ba saidai gyada Kai kawai da tayi alamar ta bada izini a shigo. Mama sarauniya ta Karasa dakin fuskar ta da alamun tashin hankali tace,
“garin yaya yareema yaseer ya bace a cikin masarauta? Ina masu kula dashi suke?”
Matse hawaye ummi tayi tana girgiza kai Tace,
“Allah shine mafi sani har yanzu babu Wani Wanda ya Amsa cewar yaga lkcn da aka sace yareema yaseer.”
“SUBHANALLAH”
mama sarauniya ta furta Hakan tana dafe goshi tace,
“dole akwai maciya Amana a ciki zansa ayi duk Wani bincike da za’ayi domin gani Inda bakin zaren yake.”
Ummi ta gyada Kai kawai batace komai ba. Sallama mama sarauniya tayi mata tace,
“bari naje wajen maimartaba ance yana kwance.” Ummi tace,
“Nagode.”
Fita mama sarauniya tayi. Yyinda ummi ta bita da kallo tana jin kaunar ta a ranta duk cikin matan sarkin wato kishiyoyin ta babu wacce tafi damuwa da lamarin ‘ya’yanta sama da mama sarauniya har kunyar Abinda yareema yaseer keyi mata take, idan ba itace ta turashi ya gaishe ta ba sai suyi satuka basu hadu ba batasan meyasa baya sakewa da itaba mace me kirki tamkar ba kishiya ba Dan har yau Bata taba ganin ta nuna kishinta koda a ido ba.
Sauran matan sarkin da aka karo bisa kanta Suma dai zaman gashi nan dai basa haihuwa shiyasa kowa harkar gabansa kurum yake tunda kowacce da sashen ta.
Saida aka Bata izni Kafin ta shiga sashen sarki cike da girmamawa ta fara gaishe shi. Yana kwance ya mike dakyar Yana kallon ta yace,
“Aisha kin dawo?” Mama sarauniya tace,
“hankali na ya Gaza kwanciya tunda naji wanann mummunan lbrn daya faru ga danmu yareema yaseer, shiyasa na taho ba tare Dana Ida Abinda ya kaini ba.”
Maimartaba yace,
“Nagode Aisha. Kinada kirki kina son Abinda nakeso Wannan kadai ya isa ki samu gurbi a zuciya ta.”
Dan murmushi kawai tayi tana dukar da kanta kafin tace,
“ya zama wajibi nayi biyayya akan duk Abinda kkeso Nima na kaunace shi matukar be take shari’ar musulunci ba.”
Sosai maimartaba yaji dadin kalamanta. Kafin yace,
“kina ganin wanne me tsaurin idon ne ya samu damar dauke yareema yaseer a masarauta? Kuma wanne irin karfi da madafan iko ne dashi haka daya iya aikata irin Wannan aikin me matukar hatsari?”
STORY CONTINUES BELOW
Dakyar mama sarauniya ta jawo ajiyar zuciya ta dire tana sake sauke wata ajiyar zuciyar ta dire a jere kafin ta lullube fuskar ta da murmushi Tace,
“tabbas baza’a Rasa makiyan boyen da muke dasu a cikin Wannan fadar ba, sannan bazan iya sanin waye yyi Hakan ba sai dai an bani izinin na Nemo Hakan.”
“Na baki wuka da nama sarauniya ta, Zaki iya kula da Wannan binciken….”
Tari ya fara yi a hankali Yana haki. Mama sarauniya ta dubeshi a rude tace,
“ciwon Harya kai haka ne??”
Murmushi yyi cikin kwantar da zuciya yace,
“a’a ba komai…”
Sannan yaci gaba da fadin,
“Amma Dan Allah kisa ayi binciken Nan da wuri Ina bukatar yareema yaseer a kusa dani, shine kadai magajin da nake da burin mallakawa Wannan kujerar da nake Kai domin nasan zai kula da komai bisa tsari sannan Kuma zai kula da lamuran ku inada yakinin yareema yaseer zai zame maku Alkhairi a cikin wannan masarauta kiyi iyakar bakin kokarin ki kinji?”
Yanayin ta ne ya canja tana kokarin yin murmushi dakyar tace,
“Kana dagamin Hankali da wannan maganganun naka maimartaba kada rudewar Rashin yareema yasa ka fara tunanin karshen ka ne yazo, Insha ALLAH baza’a dau lkci ba za’a ganshi so ka kwantar da hankalin ka please.”
Murmushi maimartaba yyi yana Gyara kwanciyar sa kawai. Hakan yasa mama sarauniya ta fito bayan tayi Masa sallama.
A waje ta hango jakadiya. Kallon ta tayi a tsanake kafin tace, “Ina neman ki anjima.”
Jakadiya tace,
“an gana ranki shi dade.”
Tana gama fadin haka itama ta wuce sashen ta bayin dake biye da ita Suna binta a Baya.
~~~~
Music ne ke tashi a hankali acan Sashen yareema Yazeed, kwalbar giyace a hannun sa daga shi sai gajeran wando Yana zaune kan kujera sai babbaka dariya yake tamkar sabon mahaukaci ga ‘yan mata Nan tsala-tsala da aka shigo msa shi daga waje da gani dama karuwai ne sai rawa suke a gabansa Suna turo kirji da mazaunai dama ba kayan kirki ne a jikinsu ba daga su sai bra da pant a haka suke takawa a hankali. Wakar ce ta kare Dan haka yareema Yazeed yayi masu alamar suzo, tahowa sukayi su biyu Yana wara hannun sa kowacce ta fada gefen jikinsa.
Cikin yanayi na maye yace, “saura next step.”
Ya fadi Hakan yana sake rungume su. Kamar jira suke Nan suka fara lashe shi tamkar wasu mayu Suna cire Masa wandon dake jikinsa a haka sukaci gaba da lalume junansu shi Kuma Yana numfashi sama2 hade da kamo duk Inda yyi Masa a jikinsu Cike da Nishadi Yana hango makekiyar kujerar sarautar masarautar MANARAS ta zama tashi domin ba Wani mgji namiji yanzu saishi.
•••••
*KAUYEN JIRAGO*
“Meyake damunki ne wai tun dazu na lura kamar akwai Abinda ke damunki ko duk akan mgnr lauwali ne?”
Shema’u ta tmbyi bilqees lkcn da suka isa dandali da dare yanayin nata yafi na kullum sbd damuwa.
Numfashi taja tana tuno dazu bayan ta barshi a wajen sbd shareta da yyi ita kuma ga zuciya saida tayi nisa sosai sai kuma wata zuciyar take tunatar da ita akan Hakan da tayi Sam bata kyauta ba.
Kuma ga dukkan alamu bako ne a Yankin su, ba mmki kurman ne dgske, kila bayajin Abinda take fada, ko kuma a yanayin yadda take Masa mgnr kurame kila a yaren su ba haka ake kwatanta yadda ta sani ba domin ta fahimci duk yadda akai Wani kabilar ne daga wata nahiyar domin baya kama da irin mutanen data saba gani a wajajen su tamkar dai Wani balarabe dayazo daga Yankin larabawa irin Wanda sukejin lbri a bakin Wanda suka fita wajen kauyikan su ko Kuma idan Ana hira a gidan radio tana iya fahimtar Abinda suke fada koda Bata gani a zahiri ba.
Juyawa tayi tana Kara ganin Rashin kyautawarta ta koma Inda yake cike da dimbin tausayin sa. Saidai me? Lkcn data isa wajen Bata ganshi ba bare me kama dashi.
“Innalillahi”
ta furta Hakan tana waige2 ko kadan babu alamar sa a wajen. Take taji hankalin ta ya tashi Nan ta aje kayan ta fara dudduba kusa da Inda take Nan dai amsar dayace baya wajen.
Ta dade sosai tana zagaye wajen Bata ganshi ba haka dai zuciyar ta babu dadi ta koma gida Toh koda ta koma gida ma hankalin ta kasa kwanciya yyi har izuwa yanzu da suka zo dandali hankalin ta na kansa…..
Girgiza ta Shema’u tayi a karo na biyu tace,
“wai tunanin me kike? Nayi mgn baki bani Amsa ba kin fada tunani Kuma.”
Cije kasan lips dinta tayi a hankali tana girgiza kanta tace, “ba komai.”
Kyaleta tayi kawai ta aje tiren goron hannunta a gefenta tana kallon yadda ‘yan matan kauyen su ke girgiza kugu a gaban meyin kidan kalangu maza na muru Kari Ana shewa.
Itama bilqees ajewa tayi tana kallon wasan da akowanne dare sai me kidan kalangu yazo yyi abinsa Yana Shan ciniki kowa na nishadi ba Arabi bare Boko.
Wani lkcn Kuma masu garaya ne kawai ke abinsu harda masu hawan bori anayi a Wannan kauyen wasa dai kala2 basu san meke faruwa ma a sauran sassan duniya ba kawai rayuwar su sukeyi a haka.
Ji tayi kamar Ana kallon ta, Dan haka ta juya gefenta a hankali da niyar makawa meyin kallon harara Dan haka samarin kauyen keyi mata sai kuma karaf suka hada ido dashi Yana daga can gefe ta cikin daji a bayan wata karamar bishiya Yana kallon ta direct ko kya”awa babu,
karaf suka hada ido dashi da sauri ta mike tana sauke ajiyar zuciya haka kurum taji dadin ganinsa Shema’u ta kalli gefenta tace,
“Ina Kuma Zaki?”
Bilqees tace,
“Dan Allah kulamin da kayana yanzu zan dawo.”
Wasan da ake yasha mata Kai shiyasa kawai ta gyada mata Kai tana Kara juyawa tace,
,”saikin dawo.”
Har bilqees ta tafi sai kuma ta dawo tana diban kankana da sauran fruit din a leda tana kullewa.
Ga mmkin ta tana dagowa Kuma sai taga baya wajen a razane ta fara waige2 tana Dan tafiya a hankali.
Kamar da wasa babu shi babu alamar sa.
“Hasbunallahi wani’imal wakil kodai Gamo nayi ni bilqees?”
Ta furta hakan tana dafe kirji tsoro na fara shigarta a hankali.
Har yanzu bata daddara ba kawai tasa Kai cikin dajin tana nemansa da wata er karamar fitilar ta tana haskawa.
Kusan cin karo tayi da Abu a razane ta bude baki zatayi Kara sai taji lallausan hannun sa a bakin nata Yana rufe mata shi.
Bude ido tayi da sauri tana kokarin kwace kanta hade da jero sakin ajiyar zuciya tace,
“Wai Kai Ina kke tafiya ne? Kayita bacewa saikace Wani Aljani ko tsuntsu???”
Gani tayi yyi murmushi yana riko hannunta alamar su tafi.
Kamar wata sokuwa haka ta bishi cikin dajin a haka suka danyi tafiya kadan sannan ya mata alamar ta zauna kan Wani icce da suka isa wajen.
Zama tayi, shima ya zauna. “Waye Kai???”
Abinda ya fito daga bakinta kenan bayan ta zauna a daidai lkcn da shima ke furta Abinda take fada kenan sukayi Hakan a tare.
Zaro ido tayi tana hade fuska Tace,
“ni namiji ce da zakace waye ni? Saidai kace wacece ke?”
Wani mmkin ne ya sake kamata a daidai lkcn da taji shima ya maimaita exactly Abinda tace babu karawa bare ragewa.
“Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un”
bilqees ta furta Hakan a rude tana kallon yadda bilhakki da gsky kwaikwayon Abinda tace yakeyi batare daya san kalaman dazai furta da kansa ba saikace sabon jaririn da aka haifo duniya ya fara koyon mgn yanzu.