SARAUTA TAH CE CHAPTER 6 BY NUCEELUV

Ganin yadda yaga hankalin ta ya tashi sosai yasa shi kamo hannun ta a tsanake yana girgiza Kai yace,
“I don’t know who I’m.”
Bilqees ta wara ido d mmki, Tace, “kamar naji kana yaren nasara?” Dan yamutsa fuska yyi yace, “meye yaren nasara?”
Bilqees tayi shiru tana tunanin yadda Wani malamin primary dinsu ke koyar dasu yakan danyi masu turanci daga Baya dayaga basa fahimta sai kawai karatun ya koma da Hausa zallah ko fillanci, dukda ba Wani karatun Azo a gani akeyi a makarantar ba. Tace,
“Ingilishi.”
Gani tayi yyi murmushi kadan Yana kawar dakai yace, “bansan meye Wannan ba.”
Bilqees tace,
“toh yanzu Kai daga Ina kazo?”
Fuskar sa a Dan hade yace,
“nace maki bansan waye ni ba.”
“Oh…”
Bilqees ta furta tana hangame baki tace,
“Ikon Allah, yanzu bakasan waye Kai ba? Amma Toh taya kazo Nan? Kodai fatakai ne sukayi maka fashi? Ko kuwa daga Yankin larabawa ka bullo shine kayi batan hanya? Ba mmki ma kila fadowa kayi ta jirgin sama da yake diban larabawa…..”
“Enough… Enough pls.”
Taji ya furta Hakan da Dan tsawa Yana toshe kunnuwan sa. Fuskar sa a hade yace,
“what’s exactly wrong with you? Kinata min tmby babu coma bare full stop, taya kike tsammanin ni zan iya baki Wannan amsar? I hate noise.”
Ya furta Hakan yana juyowa gareta sai kuma yaga bata wajen. Mikewa yyi da sauri Dan harta fara tafiya.
“Wait..pls wait.”
Ya furta Hakan da sauri yana kamo hannun ta. Kwace hannun tayi tana kokarin ci gaba da tafiya ya sake riko hannun dakyau Yana jawota baya kadan ya rage ta fada jikinsa ta gyara da sauri tana juyowa hade da ballo Masa harara…
Kama baki yyi d mmki yace, “me nayi Kuma?”
Bilqees tace,
“Tmby kke me kayi? Bayan duk irin tsawar daka gama min? Sannan harda Wani na isheka d tmby. Toh sai kayi ta yawo a dajin Kai kadai tunda bakason taimako.”
Dafe goshi yyi yace, “okay srry”
Ya furta Hakan dakyar hade d cije lips dinsa na kasa yanajin kamar Sabon Abu ne a gareshi furta Kalmar hakuri.
Hararar sa tayi tace,
“Soron gidanku.”
Tana gama fadin haka ta juya. Harde hannayen sa yyi a kirji yana binta da kallo batare da yyi kokarin dakatar da itan ba sbd ‘yan mulkin sun motsa…izzar ta taso shiyasa shima ya juya Baya Yana tafiya batare da yasan Inda zaije ba.
Rintse ido tayi tana cije lips a daidai lkcn data tsaya kikam batare data ci gaba da tafiyar da take ba…tanaji a ranta ya kamata ta saurare shi, ta Kuma yi Masa kyakkyawar fahimta, Da Wannan tunanin ta juyo Dan komawa wajensa.
STORY CONTINUES BELOW
Can ta hango shi ya duka kasa Yana taba kafarsa da sauri ta isa wajenshi tana kallon kafar da yake tabawa a hankali.
Haska fitilar wajenta tayi tana karewa wajen kallo har lkcn be dago ba kansa a duke Yana taba kafar. A hankali ta tsugunna gabansa Nan taga Ashe kaya ya taka ya kasa cirewa.
“Ya salam”
Ta furta Hakan a Fili tana Kai hannunta kan kafar taga ya janye d sauri. Dagowa tayi da mmki sai taga fuskar sa a hade Yana shirin barin wajen bilqees tayi kokarin riko shi Amma ya zame Yana ci gaba da tafiya normal tamkar ba kayace a kafar ba.
Binshi da kallo tayi ranta na sosuwa da irin Wannan kyaluwar daya nuna mata daga Dan zaman da tayi dashi ta fahimci Yana da ji da kansa jifa2 sai ya dinga Wani cizewa tamkar Wani basarake.
Tsaki taja kawai ta sake juyowa batare data Kara waiwayar sa ba tayi hanyar dandalin su.
Ana kan yin wasa har yanzu bilqees ta isa wajen zuciyar ta babu dadi. Shema’u data gaji da neman bilqees ta hangota tsaye jikin Wani Dutse ta harde hannu nesa dasu kadan.
Isa wajenta tayi da mugun mmki take binta da kallo tace, “dama kina Nan wajen naketa neman ki ban ganki ba?”
Bilqees tayi mata shiru Bata Amsa ba. Shema’u ta girgiza ta tana sake fadin,
“dake nake mgn fah.”
Dan karamin tsaki bilqees tayi kafin tace, “banajin dadin jikina ne yau.”
“Ai ko baki fada ba Naga alamar haka bilqees, Kuma nasan duk akan zancen lauwali ne. Toh Dan Allah ki daina damuwa Insha Allahu lauwali sai dai Hange daga nesa Amma bazai taba zama mijinki ba kinji?”
Dan numfashi bilqees taja damuwar kam harda ta lauwali dayar damuwa kuwa ta Rasa dalilin dayasa take damuwa akan mutumin da Bata sanshi ba bare asalin sa.
“Muje mu tafi yadda Zaki samu ki kwanta da wuri kinji?”
Shema’u ta furta Hakan tana daukar turen su ta mikowa bilqees kudin hannunta tace,
“gashi anyi ciniki yau saura kadan.”
Godiya bilqees tayi mata sannan suka fara takawa Shema’u na Bata baki akan lamarin lauwali a haka suka isa gidan bilqees dai saidai tace eh ko a’a domin Rabin tunanin ta Yana ga bakon gari.
^^^^
Washe garin ranar da sassafe bilqees ta tashi tana share gidan nasu hade dayin wanka da wuri.
Inna habi dake gaban wuta tana girki ta Kira bilqees data fito wanka yanzu.
“Na’am”
bilqees ta Amsa kiran tana juyawa Inda inna take. Inna habi tace,
“Ina Zaki ne da sassafen Nan naga Duk kinyi ayyukan ki da wuri?”
Bilqees ta danyi murmushi tace,
“yau gidan yaya Atika zan Kai ziyara gabashi.”
Inna habi tace,
“haba koda naji naga ne Duk kin shirya da wuri. Amma bayan Wannan meya hanaki bcci jiya?”
Gwalo ido tayi d mmki tana tuna daren ta na jiya, gaba1 rabi da Rabi tayi bcci jiyan nan bakon gari ya tsaye mata a rai matuka.
Tausayin sa ne ke Kara ruruwa a ranta musamman idan ta tuna cewar ya fada mata wai besan waye shi ba. Besan daga Ina ya fito ba, idan Banda kaddara zabgegen saurayi kamar Wannan ace besan kansa ba?
Ta dade tana tufka da warwara a daren Nan dakyar da sidin goshi bcci barawo yyi awon gaba d ita saidai asubar fari ta farka da tunanin sa ba shiri ta mike tana tunanin mafitar daya dace…..
STORY CONTINUES BELOW
“bilqees”
inna habi ta girgiza ta ganin tayi shiru Bata Bata Amsa ba saima tunani data fada, bilqees ta saki murmushin yake tace,
“ba komai.”
Girgiza Kai kawai inna habi tayi tana tunanin ba komai ke damun bilqees ba sama da zancen mahaifin ta da lauwali.
Mikewa tayi ta wuce daki tana fatan ace ta fice daga gidan batare data ci karo da kowa na gidan nasu ba. Cikin mintuna kalilan sai gashi ta shirya tsaf. Sannan ta Kara wasu fruit din a ledar data Kai masa jiya wacce yaki kulawa bare yaci.
Inna habi tayiwa sallama bayan ta karbi sakon da zata kaiwa yaya atika.
Fitowa tayi a gurguje tana sauri Bata daina Wannan saurin ba kuwa Saida taga tayi nisa da gidansu sosai kafin ta saki hanyar da take kyautata zaton acan zata sameshi.
••
“BILQEES…ke bilqees”
Mlm Musa ya fado gidan Yana rafka mata Kira Jim kadan bayan ficewar bilqees din. Inna habi dake tsakar gidan tace,
“lpy mlm?”
Mlm Musa yace,
“Ina Wannan yarinyar take?”
Inna habi tace,
“Bata Nan.”
“Ban gane ba.”
Cewar mlm Musa Yana hararar inna habi. Inna habi tace,
“na aiketa gidan Atika.”
Wani dogon tsaki mlm Musa yaja tamkar bakinsa zai fice ya juya fuuuuu Yana barin gidan izuwa waje.
Yana tsaye bakin kofar gidan ya iso gareshi. “Ba!a har an Samo ta?”
Lauwali ya furta Hakan yana gyara tsayuwa. Mlm Musa yace,
“uwar yarinyar ta aiketa zuwa wajen yayarta saidai ko anjima sai kazo ku gana.”
Lauwali yace,
“Kassh gsky naso ace mun hadu yanzu Amma babu damuwa indai akan bilqees ne Ina iya hakuri.”
Mlm Musa yace,
“Madallah ya kukayi da magabatan naka jiya?Dan nace kwana uku ma ya wadatar a daura aure.”
Murmushi lauwali yyi yace,
“gsky ba!a kana birgeni saidai akwai Abu daya.” Mlm Musa yace,
“me kenan?”
Lauwali yace,
“na canja tsarin zuwa Nan da wata daya domin inason duk Inda mabiyana suke lungu da Sako, ramuka da kwazazzabo…mutane da Aljanu….kwari da tumakai… kyankyaso da macijzai…zakuna da Aladu duk susan da bikin sarkin dawa lauwali, lauwali uban dawa Wanda ya gagari mutane tsoho da tsohuwa…yaro da yarinya kai hatta Aljanu ma shayina suke Dan haka nakeson na shirya gagarumin bikin da tunda ake ba’a taba yin biki irinsa a Yankin kauyikan Nan ba.”
Zufa ce ta gama jike jikin Mlm Musa tsoro na Kara shigar sa…cikin ransa na Allah Wadai da Wannan haduwar ta lauwali da bilqees.
A Fili kuwa yace,
“Wannan shine asalin kalar uban dawa, Hakan zaisa kowa ya Kara fahimtar jarumtar ka lauwali. Muna maraba da Duk bataliyar daka kwaso Mana hatta tsuntsayen dake shawagi ma Ana gyayyatar su.”
Lauwali yace,
“shiyasa nake yinka ba!a domin kanada matukar fahimta sosai.”
Murmushi yyi cikin ransa kuwa takaici na sake kama shi a haka lauwali yyi masa sallama ya tafi Yana tangadi.
STORY CONTINUES BELOW
MASARAUTAR MANARAS
kallon kallo ne ya afku akan hanyar mama sarauniya tare da amaryar sarki Hajia Mairo, kowacce bayinta na take mata Baya. Kai tsaye kowa ya wuce bayan an gama musayar kallo kafin Nan Hajia Mairo ta wuce sashen Gimbiya Falmata Kai tsaye.
Dan dakatawa mama sarauniya tayi tana juyawa a hankali ta kalli bayanta sai kuma kawai ta juyo gaba tana me ci gaba da tafiya batare data yi yunkurij komai ba.
Tana Dan kishingide akan lallausar kilisar ta aka sake Aiko baiwa a karo na biyu Hajia Mairo na neman izinin shiga wajen Gimbiya Falmata.
Kamar bazata amince ba, saidai ta Amsa dakyar tana gyada Kai kamar dole.
Ita kadai ta shigo parlon nata sauran bayin Suna waje, alama Gimbiya Falmata tayiwa sauran nata bayin dake mata hidima a wajen Suma suka fice.
Zama hjia Mairo tayi tana karewa yanayin parlon kallo duk an canja Masa tsari ba kamar yadda ta barshi ba last zuwan da tayi. Kafin ta dire kallon ta kan Gimbiya Falmata data daure fuska sosai babu alamar fuska a tattare da ita.
Dan numfasawa Hajia Mairo tayi tana gyara Alkybbar ta tace,
“sai kuma mukaji mummunan lbri Dan Lele ya bace?”
Wani irin kallo Gimbiya ta watsa mata tana jin zafi a ranta musamman daga yanayin da tayi mata tmbyr ya Bata haushi akaf matan sarki Abdallah babu wacce sukafi gogawa da ita sama da Hajia Mairo badan komai ba saidan sa mata ido sosai da take akan yaranta especially yarima yaseer duk yabi ya tsole mata ido karara take nuna hasadar ta a Fili shiyasa ko yanzu ma a ranta tana suspecting dasa hannun Hajia Mairo a bacewar yareema yaseer….
“oh.. bafa ni nakar zomon ba Gimbiyar sarki.”
Cewar Hajia Mairo data sake gyara zaman ta tana me ci gaba da fadin,
“har gobe dai bazan daina fadar gsky ba, kuma har gaban abadan saidai kici gaba dajin haushina akan fadar gsky keda maimartaba.”
Daga mata hannu Falmata tayi a fusace tace,
“Fice min daga Nan..”
tayi mata nuni da kofa, murmushi Hajia Mairo tayi tace,
“ko baki fada ba ai zan tafi Amma ki bari na Ida mgnr da nakeson yi….”
“Nace ki fice koh????”
Cewar Gimbiya Falmata da tayi mgnr da tsawa bacin rai karara na sake bayyana akan fuskarta.
Juya idanuwa Hajia Mairo tayi tace,
“ai shikenan bari na tashi kafin ki huce haushin a Kaina.”
Mikewa tayi yyinda Gimbiya Falmata ke aika mata da muguwar harara tamkar idonta zai fice.
A hanya sukaci karo da suhaima zata shigo. “Oh..suhaima kin dawo?”
Hajia Mairo ta furta Hakan tana murmushi, kallon Rashin kunya tayi mata tana dauke kai ta Karasa shigowa ciki.
Tabe baki Hajia Mairo tayi tana barin sashen nasu gaba1. “Ummi me matar Nan takeyi anan?”
Suhaima ta furta ranta a bace, dakuwa ummi tayi mata tana kokarin saita kanta tace,
“respect her.”
Tura baki suhaima tayi tace,
“ummi ya kamata ki dakatar da ita da zuwa sashen Nan naki gaba1 domin ba komai take karawa mutane ba daya wuce ciwon Kai.”
Shiru Gimbiya Falmata tayi tana karajin takaicin Hajia Mairo a ranta.
“Kuma ni Ina suspecting dasa hannunta a bacewar yayana.”
STORY CONTINUES BELOW
Suhaima ta furta Hakan bakinta na rawa. Ita kanta ummi kukan ne yaso kwace mata ta daure dakyar tace,
“I’m suspecting too.”
°°°°°°°
Kallon jakadiya tayi a tsanake tana duban cup din hannunta a tsakiyar parlon maimartaba.
Washe baki jakadiya tayi cike d girmamawa tace,
“a’a Ashe amarya ce da kanta tohm ki jira ai ya samu bcci yanzu na bashi mgni.”
“Mgni Kuma?”
Hajia Mairo ta furta Hakan tana sake kallon cup din hannun nata tace,
“mgnin meye?”
Jakadiya tace,
“eh..toh.. mgnin tari ne na gargajiya.”
Tsuke fuska sosai Hajia Mairo tayi tace,
“ban gane ba? Ina likitan sa yake?”
“Dazun Nan ya tafi yace a dinga bashi tarin zai tsaya.”
Kallon ta tayi na wasu mintuna sai kuma ta tabe baki kawai batare data sake mgn ba kawai ta wuce ciki batare data jira anyi mata iso ba.
Yana zaune ya dafe kirji, da mmki ta kalleshi shi da akace Yana bcci?
Zama tayi kusa dashi ya dago kansa a hankali Yana kallon ta. Hajia Mairo tace,
“Allah ya baka yawan rai, Lfy da Nisan kwana maimartaba sarkin MANARAS da fatan kana lpy?”
Girgiza Kai maimartaba yyi yana lumshe ido a hankali. Hajia Mairo tace,
“madallah. Yanzu Ina aka tsaya da binciken Inda yarima yaseer yake?”
Da mmki ya kalleta sai yaga tayi murmushi Tace,
“Rashin tausayin nawa bekai har haka ba maimartaba, yanzu dai su waye akan binciken nasa?”
“Aisha.”
Ya bata Amsa a takaice.
Gwalo ido tayi da sauri tana dafe kirji tace, “Whattt….?????”
KAUYEN JIRAGO
Duk iya duban da zatayi, tayishi Amma har yanzu bata gano Inda Wannan bakon yake ba. Harta cire tsammani ta juya zata tafi sai kuma taji taku a bayanta, juyowa tayi da sauri tana kare Masa kallo shine dai rungume da hannun a kirjin sa jikinsa duk a jike.
Wara ido tayi tana isa wajenshi d sauri tace, “Wanka kayi?”
Tayi mgnr tana nuna jikinsa daya jike. Murmushi yyi mata Yana gyada Kai.
Bilqees ta kamo hannun sa suka koma kasan bishiya tace, “Allah sarki inata neman ka Wlh”
ta Ida mgnr Suna zama. Shima zama yyi kamar yadda yaga tayi ta dauko ledar gefenta tana ajewa a tsakiya tace,
“Dan Allah kayi hakuri ni bansan Abinda zakaci ba kaji? Ga Wannan kasha”
ta bude Masa ledar tana Ciro lemon zagin data yanka gani tayi ya karba da murnar sa Yana kaiwa baki.
Hakan yasa ta zuba Masa ido cike da tausayawa tana kallon sa.
Sosai yasha duk ywancin fruit din data kawo Masa fuskar sa wasai tamkar Wanda yakecin dawisu.
Haka kawai taji dadi ya kamata musamman data ga Yana farinciki sai cin fruits din yake a fuskar sa zaka gane yaji dadi.
Saida ya koshi Sannan ya Daina ci. Kallon sauran tayi yafi Rabi tace,
“bakaso ne?”
Tayi mgnr da damuwa. Girgiza Kai yyi, tace, “Ka koshi?”
Sai taga ya gyada mata Kai. Murmushi tayi har hakwaron ta na fitowa ta dauki ayaba daya tana barewa takai bakinta zuciyar ta fari tasss.
Gani tayi ya zuba mata ido kamar ya samu tv tana masa yanayi da Wani Abinda ya Rasa Ina ya taba sani? Dauke idonta tayi daga gareshi domin ji tayi ya mata nauyi. Kafin tace,
“Sunana bilqees. Fadi muji.” Shiru yyi Hakan yasa ta dago. “BILQEES…”
taji ya furta a hankali. Dummm….taji Wani irin Abu ya bugi kirjinta ya soke tashi guda tayi saurin dafe kirjin tana lumshe ido har yanzu Abinda taji be daina yawo a Tsakanin kirjin nata ba, batajin tunda take a rayuwar ta akwai Wani mutum ko ace Wani bil’adama daya iya furta sunan ta cike da sauti me dadi da kayatarwa sama da sautin daya fito daga Wannan bakon garin da Bata San koshi waye ba.
Bude idon tayi a hankali tana sauke numfashi bayan ta daidaita nutsuwar ta, saita tafa a hankali tana murmushi Tace,
“dakyau ka iya furtawa daidai.”
Murmushi yyi yana dauke kai, bilqees Kuma tace,
“tohm tunda Kai baka San waye Kai ba wanne Suna ya kamata a kiraka dashi….???”
Karshen mgnr ta ce ta makale a tsorace lkcn data jiyo muryar su lauwali na dosowa Inda suke da karnukan su Suna ihu irin na mafarauta………..

Tsurawa pink lips dinta ido yyi tamkar Wanda ya samu hoto. Yadda take motsa shi a hankali ya sake Jan hankalin sa sai kawai ya fara murmushi a hankali batare daya san dalilin Hakan ba.
Idonta a rufe besan me takeyi ba hatta numfashin su sarkewa yake da juna sbd matsin wajen da suka fake kwakkwaran motsi sukayi Ana iya jinsu ko a gansu.
Bilqees kenan da tun bayan jiyowar tahowar su lauwali ta mike a sukwane tana Jan yareema yaseer cikin Wani kogon Dutse dake gefen su, shigarsu keda wuya kenan su lauwali auka karaso wajen Suna zagawa domin neman Naman daji.
Kogon bashi da Wani fadi bare girma Hakan yasa suka takure waje daya gaba1 a baganren ta a tsorace take musamman data hango tahowar lauwali dake mgn Yana kokarin tsayawa a gefen kogon da suke Hakan ya Kara sata rudewa ta lumshe ido da sauri jikinta na rawa tana yin Addu’a a hankali tare da fatan ace basu gansu ba domin kwakkwaran motsi sukayi babu Abinda zai hanasu ganin su.
Karen lauwali ne yake ta tsalle a wajen yaki tafiya kamar yadda lauwalin ya Kora shi kin tafiya yyi yana kokarin shigewa kogon bilqees ta kankame yarima yaseer da har yanzu be daina kallonta ba yaji ta Masa wata irin wawiyar runguma ba shiri ya saki numfashin da be shirya ba.
Juyowa lauwali yyi kamar numfashi yaji a gefen sa Yana shirin leka kogon abokin sa sale yace,
“Lauwali babu me iya kama dilar Nan Yasin sai Kai, Dan Allah taho mu samu na karyawar safe.”
Lauwali ya dawo da hankalin sa kan sale yace,
“haba salele me akai akayi Wani dila Kuma?”
Sale yace,
“Wannan saiku manyan dawa ku kuke ji da komai.”
Murmushi lauwali yyi kansa na bugawa yace,
“muje mutumina Yasin saidai uwarsa ta haifi Wani Amma kam sai Munci naman dilar Nan yau.”
Sale yana hada hannayen sa cike da kirarai yace,
“Sai ogaaaa… Ina gwanin Wani ga nawa? Lauwali ikon Allah wanda ya gagari dabbobi da Aljanu.”
Ihu sauran matafiyan suka saka Suna maganganun irin na mafarauta a haka suka bar Wannan sararin Inda su bilqees suke boye.
Kyakkyawar ajiyar zuciya bilqees ta saki tana kokarin barin jikinsa taji ya riketa gam…, Dagowa taso yi Nan ta kasa domin habarsa akan kanta yake.
“Ha’a.. sake ni Mana”
Cewar bilqees data fara kokarin kwace kanta.
Idonsa a lumshe ya dora habarsa a kanta yana cije lips a hankali. Jijjiga shi da tayi yasa shi dagowa a nutse yana kokarin matsawa saidai wajen ya musu kadan.
Alama tayi kasa da ido zuwa wajen tace,
“mu fita sun tafi.”
Tana gama fadin haka ta fito. Biyo Bayanta yyi shima Yana shafa sumar kansa duk kura tahau Kai sbd kogon da suka shiga. Bilqees mika Masa Dan kwalin kanta bayan ta cire tace,
STORY CONTINUES BELOW
“karbi Wannan ka goge kanka yyi kura.”
Ta Ida mgnr tana Masa nuni da kansa. Gani tayi ya yamutsa fuska Yana Yana kade gashin nasa da hannu sai kawai taga ya juya Inda kogin bayansu yake.
Da sauri tabi bayan nasa tace,
“dakata kada fa ka fada, Wannan kogin yanada zurfi.”
Be kulata ba Dan haka kawai ya matsa jikin kogin Yana tsugunnawa gefe ya fara kwara ruwan a kansa Yana lumshe ido. Harde hannayen ta tayi kawai ta jingina da Wani Dutse Dake gefe tana kallon yadda yake wanke kansa. Saida ya gaji ya mike Yana matse idanu.
Bilqees ta miko Masa Dan kwalin again tace, “Toh ka goge ruwan.”
Karba yyi ba musu ya fara gogewa a hankali Harya gama. Bilqees taja numfashi a nutse lkcn Yana zaune akan Wani dutsi Yana jefa wasu fararen duwatsu zuwa cikin ruwan gabansu. Tace,
“ni zan tafi.”
Be dago ya kalleta ba bare tasa ran zaiyi mgn. “Bawan Allah ni zan tafi.”
Ta sake fadin Hakan da Dan karfi. Har yanzu be jiyo ba. Hakan yasa ta matso tana girgiza shi hade da daga Masa hannu alamar bye-bye batare data sake Wani furucin ba ta juya Dan zuwa kauyen su yaya atika.
Tsayawa yyi da jifan duwatsun kamar daga sama taji yace, “Bilqees…”
Tsayawa tayi hade da juyowa d mmki, sai kuma taga ya taho Inda take.
Kafe shi da ido tayi tace, “kana bukatar Wani Abu ne?” Girgiza Kai yyi, bilqees tace, “zaka bini ne?”
Gyada mata Kai yyi alamar eh. Shiru tayi
Tana nazarin yadda tafiyar tasu zata kasance, ita tunani take idan aka ganta dashi me zatace? Wacce Irin Amsa zata bawa mutane? Amma dake kauyen su yaya atika ne tana ganin ba Wani matsala zataje dashi.
“Shikenan”
Ta furta Hakan a takaice tana takawa a hankali shima yabi bayanta.
MASARAUTAR MANARAS
Da mmki sarki Abdallah ya dubeta a tsanake beyi mgn ba.
Hajia Mairo tayi saurin yin murmushi tana gyara zamanta tace,
“Allah ya baka yawan rai kana ganin Hakan yyi maka?” Maimartaba yace,
“me kikeso kice? Hajia Mairo tace,
“Ina nufin gani nayi binciken yarima yaseer yanada muhimmancin da baza ayi sakaci dashi har haka ba, Ina laifin ka samu kwararrun amintattun ka a boye suyi maka binciken a nutse? Ni a shawarata Hakan shine zaifi bawai Ina kushe zabin ka bane tabbas itama uwargidan sarki zata iya, Amma kasan dayawan lokuta Bata cika zama a kasar ba tohm taya binciken zai tafi a haka?”
Shiru maimartaba yyi na Wani lkci Yana nazarin Hajia Mairo Toh Amma zuciyar sa na bashi tabbacin mama sarauniya zata iya domin ita din ta kasance me kaddamar da Abinda ya sata cikin gaggawa batare da tayi gardama ba, koda kuwa ace bataso, sannan itace macen da bayan mahaifiyar su bega me kulawa da lamarin su ba sama da ita din Dan haka sam-sam bayajin ko dar bare fargaba akan mika mata lamarin yarima yaseer da yyi domin yasan zata iya….,
“Tuba nake ranka shi dade Ina fatan b laifi nayi ba game da lafuzzan Dana gama furtawa yanzu.”
Hajia Mairo ta katse shirun da yyi. Kamar ba zaiyi mgn ba sai kuma ya girgiza Kai a nutse yana gyara kwanciyar sa domin ji yake kirjin sa na daurewa a hankali yace,
STORY CONTINUES BELOW
“Bani da wata tantanma ko shakku akan Abinda na aikata domin Hakan shine nake ganin ya dace.”
Ya furta mata Hakan a takaice Yana lumshe ido a hankali.
Ido ta zuba Masa yanayin fuskar ta na canjawa a hankali cije lips tayi tana dan numfasawa ta mike bayan ta gyara masa hannun sa daya karkace ta fito waje.
Kadan ya rage suyi karo da jakadiya dake bakin kofar tana matsawa da sauri sai yake take tamkar sabuwar kamu.
Binta tayi da ido tana watsa mata Wani irin kallo jakadiya ta Sosa kanta tace,
“kin fito kenan hajia.”
Dan karamin tsaki Hajia Mairo taja kawai batare data tanka mata ba ta wuce sashen ta Kai tsaye.


“Baby na damu kwarai akan bacewar frnd.” Suhaima ta yatsina fuska kamar zatayi kuka Tace, “Ya Naseer kullum da abin nake kwana a raina Wlh.”
Naseer da jiya ya dawo daga Abuja beji lbrn bacewar da wuri ba sai daya iso gida shine kawai ya taho masarautar Kai tsaye yanzu kuma zasu fita da suhaima. Yace,
“Amma ace har yanzu ba’a iya gano munafukan da sukayi garkuwa da prince ba?”
Suhaima tace,
“har yanzu binciken akeyi…Amma ni Ina suspecting wata….”
“Sannun ku suhaima naji kamar kince kina suspecting wata…?”
Cewar yareema Yazeed da isowar sa kenan wajen su zai wuce yaji Suna mgnr zuciyar sai harbawa take Yana washe bakin dole.
Hannu Naseer ya mika Masa suka gaisa,
“yaushe a gari? Kwana biyu bana ganin ka Naseer” Naseer yace,
“eh ai bana garin naje Abuja.”
“Allah sarki, sai kuma kaji lbri marar dadi ko?”
Yareema Yazeed ya furta Hakan fuskar sa dauke da Alhinin abun Kai kace har ransa yakejin babu dadin Rashin yareema yaseer.
Ajiyar zuciya Naseer ya saki zuciya babu dadi yace,
“hakane, fatana Allah ya tona asirin masu sa hannu a cikin batar da yareema da akayi.”
Kasa amsawa yareema Yazeed yyi yana duban suhaima da sauri yace,
“Yauwa suwaye kike suspecting? Ki sanar min da wuri domin ya kamata ayi tsatstsauran bincike akan su.”
Suhaima zatayi mgn Naseer yace,
“No..Wannan ba mafita bane Yazeed zato zunubi ne koda ace ya zama gsky, kai tsaye be kamata a ware gefe guda ace za’ayi bincike ba Dan kawai Ana zargi kamata yyi ayi kan me uwa da Wabi babu Wanda ya tsallake Wannan binciken akaf fadin Wannan masarautar.”
“Eh…Toh..Kuma fa hakane kanada gsky Naseer.”
Ya furta Hakan da sauri2 yana gyara wular kansa yace,
“Ni bari na Karasa fada yanzu.”
Naseer ya gyada Kai kawai Yana binsa da kallo. Suhaima ta sauke ajiyar zuciya. Naseer yace,
“Irin Wannan baby ba komai ake mgn akai Kai tsaye ba.” Da mmki tace,
“ban gane Abinda kkeso kace ba ya Naseer?”
Naseer yace,
“Ina nufin be kamata ki juya Alkibla daya kice Nan ne kike zargi ba, Abu me muhimmanci kamar Wannan duka mutanen masarautar Zaki hada kada ki cire kowa, tunda kika ga an iya dauke yareema yaseer a cikin Wannan daula ta masarauta me cike da matakan tsaro ciki da waje Toh kuwa ba karamin gagaruman manyan makiya yake dashi a katakafanin gaba1 masarautar MANARAS ba, Ya kamata ayi nazari sannan a zuba ido a nutse.”
STORY CONTINUES BELOW
Numfashi ta sauke a hankali tana jinjina mgnr tashi a ranta tabbas yanada gsky, ya zama dole su iya takun su.
Shigewa motar sukayi Sannan suka fice daga masarautar gaba1.
* “Mami…mami”
yareema Yazeed ya furta Hakan yana cilli da hular kansa wacce Tasha rawani, mikewa tayi da sauri tana kallon yanda ya shigo fuskar sa a daure tace,
“lpy Yazeed?”
Zama yyi a kan kujerar gabanta tuni bayin dake parlon suka fice yace,
“Mami wai har tsawon wanne lkci za’a sauka kafin a Dora ni akan Wannan karagar mulkin?”
Mami ta saki ajiyar zuciya tana girgiza kai Tace,
“kashhh gsky ni ka dagamin Hankali Wlh. Toh meye abin gaggawar? Inace tuntuni mun kawar da ciwon idon dake damun mu? Waya sani ma kila Naman jeji sun cinye shi ko yyi mushe tunda a yadda ka bani lbri jejin da kuka barshi akwai dabbobin daji a ciki.”
Dan sassauta fushin sa yyi kafin yace,
“ni Duk ba Wannan ba mami, mutanen nan fa ba a zaune suke bafa, har yanzu bincike suke akan bacewar sa harda cewar Suna suspecting wata.”
Gwalo ido kwarkwara sa’adiyya tayi tana gyara zamanta tace,
“sun fada maka Wanda suke zargi?” Girgiza Kai yarima Yazeed yyi yace,
“No, Wannan banzan Dan maulan Naseer ya Hana suhaima ta sanar dani.”
Tsaki kwarkwara sa’adiyya tayi tace,
“Tohm kada ka damu zanyi mgnin Hakan. Kuma game d hawanka kujerar mulki Nan da Wani lkci zaka iya hayewa domin akwai Wani babban shiri da nakeyi akan Maimartaba sarki Abdallah. Ko ka manta shirin d akeyi a kansa?”
Gyada Kai yarima Yazeed yyi yana murmushi hade da tuno kwalbar magnin data nuna Masa kwanaki Wanda za’a dinga sirkawa sarki Abdallah a cikin abin shansa ta yadda zai shanye batare daya sani ba,
ba komai bane a Wannan kwalbar face gubar sihiri…guba ce wacce idan Yana sha zata dinga kakkarya Masa garkuwan jikinsa a hankali tun Yana jin karfin jikinsa zai dawo dakyar zai iya motsawa.
Babu Wanda zai fahimci guba ce tayi sanadin Hakan saidai kowa yyi tunanin tashin hankalin Rashin yareema yaseer yasa shi fadawa Wannan yanayin, a daidai Wannan lkcn za’a bukaci yyi murabus a Dora yareema Yazeed akan karagar MULKIN masarautar MANARAS.
*KAUYEN JIRAGO*
Duk Inda ta jefa kafarta haka shima yake jefa tashi kamar Wani me koyon tafiya Yana binta a Baya shiru ne ya ratsa Tsakanin su bilqees ta juyo a nutse saiya dakata Yana jiran abinda zata ce.
Dawowa daidai saitin hannun sa tayi suka jeru sannan tace, “muje.”
Beyi Musu ba haka sukaci gaba da tafiyar a jere bilqees tace,
“na Rasa da wanne Suna zan dinga kiran ka bakon gari.”
Shiru taji yyi beyi mgn ba, Hakan yasa ta dago tana kallon sa taga Wani side din yake kallo.
Kallon wajen tayi saita ga wasu tattabaru ne kyawawa ke shawagi a Wani shinge.
Murmushi tayi domin tattabara tana birgeta tace,
“ko kuma kunada irinsa a Yankin ku?”
Sai a lkcn ya juyo yana kallon ta sai kuma ya yatsina fuska a cikin ransa kamar yasan abin saidai ya manta Inda ya Sani.
Bilqees tace,
“muje ka kama mun”
tayi mgnr tana wucewa gaba suka nufi Inda tattabarun ke shawagi.
Ja yyi ya tsaya daga nesa Yana harde hannayen sa be Karasa jikin shingen ba.
Bilqees ta waiwayo tana murmushi tace,
“kodai tsoro kke?”
Gani tayi yyi murmushi beyi mgn ba Kuma.
Dauke idonta tayi domin ji tayi kirjinta ya buga a Duk sanda yyi murmushi saita ji Hakan a kirjinta.
Hannu takai zata kama su sai suka tashi gaba1 Suna komawa Wani side din. Bilqees ta sake komawa wajen Nan ma Suka gudu…, juyowa tayi tana haki Tace,
“bazan iya ba Wlh mu tafi kada dare yyi.”
Tabe baki yyi kawai yabi bayanta batare da yyi mgn ba. Dan hararar sa tayi tana mgn kasa2 tace,
“Sai ka dinga Wani fisgewa sai kace jinin sarauta..Toh Allah dai ya ragewa Aya zaqin ta da ba’asan Kuma me zakayi ba.”
Ta Karasa mgnr tana juyowa gareshi sai kuma ta hango shi a Baya ya tsaya cakk fuskar sa a hade.
Da mmki ta koma Inda yake tana wara ido Tace, “Kai lpy? Meya faru kke Bata rai?”
Banza yyi da ita be tanka ba. Bilqees tace,
“mgn nake fa, bazakace komai bane? Nifa matsalata dakai kenan ayita mgn kamar Wani dutsi idan ka gaji ne kayi zaman ka dama ban nemi taimakon rakiyar ba.”
Tana Ida mgnr ta juya a zuciye…
“Bilqees…”
taji ya furta sunanta da sauri yana jawota baya.
Wata katuwar macijiya ce ta haro kansu kadan ya rage ta sari bilqees din yarima yaseer ya cafe ta a gaggauce Yana tsallakawa can gefe take santsi ya kwashe shi suka fara gangarawa cikin ramuka da kwazazzabo.
“Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un”
Abinda bilqees ta dinga nanatawa kenan a ranta tana rintse ido a daidai lkcn da taji ta gwaru da katon Dutse take ta saki karar azaba tana Kara kankanme yarima yaseer da shima yaji ciwo a sassan jikinsa.
Sun dauki tsawon lkci Suna gangarawa kafin suka tsinci kansu a Wani bangare na Wani dajin da basu san Inda yake ba.
Inda Allah ya taimake su akwai Kogi ta wajen Hakan yasa yarima yaseer ya mike cikin dauriya Yana cije lips dinsa ya cire bilqees a hankali data kankame shi Yana isa gaban kogin ya Debo ruwa a hannun sa Yana watsawa akan fuskar bilqees. Saida yyi Hakan sau uku kafin bilqees taja doguwar ajiyar zuciya tana salati.
Ja gefe yyi ya zauna Yana dafe goshi jini na fita a ciwokan da yaji duk ya kukkurje sai cije lips yake cike da dauriya Amma be damu daya gyara ciwon ba.
Bilqees da sai yanzu idonta ya washe ta ganta kwance a gefen yarima yaseer daya dafe goshi.
Mikewa tayi da sauri sai kuma taji kanta ya Sara Yana zugi. “Ya ilahi.”
Ta furta hakan cike da azaba tana rintse ido.
Dubanta yyi a tsanake yaga tana fitar da kwallar azaba sai yaji duk ta bashi tausayi ya matso kusa da ita Yana kokarin cire mata hijab dinta bilqees ta kama da sauri tana girgiza kai.
Mmki ne ya kama shi, Toh shi dazai taimaka mata?
“Just want to help you.”
Ya furta Hakan a nutse yana sake kokarin cire mata hijab.
izuwa yanzu Jiri ne ya fara dibanta Hakan yasa Bata da karfin Hana shi Dan haka ya samu nasarar zare mata hijab din a hankali….

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE