SARAUTA TAH CE CHAPTER 8 BY NUCEELUV

Hankalin sa sosai ya maida kan bilqees da suke tafiya a yanzu Kai kace Wani bodyguard dinta ne yadda yake kulawa da gaba d bayanta ko kuma Wani dogari. Ganin
yadda yake gaba Yana baya bilqees ta juyo a tsanake tana Kare Masa kallo tace,
“ka nutsu gefe daya Dan Allah.”
Yatsina fuska yyi yana Bata rai yace,
“banason Wani Abu ya taba ki ne”
Ya furta Hakan d kulawa. Wara ido bilqees tayi kafin tace, “sai kace wata sarauniya me tafe da dogari?”

Ji yyi kansa yyi Wani irin sarawa d hanzari ya dafe kan yana er Kara auccch.., d sauri bilqees takai hannu tana rike shi ya kwace hannun sa yana cije lips dakyar, bilqees tace,
“meya sameka? Kanka ke ciwo ne?”
Duk ta furta Hakan a rude. Kokarin saita kansa yyi cikin ransa Yana mmkin kalaman d bilqees ta furta ya sashi Wannan sarawar kan ko kuwa Wani Abu ne daban?
“Kayi mgn Mana.”
Bilqees ta furta Hakan d damuwa. Yake yyi mata Yana gyara tsayuwar sa yace,
“ba komi.”
Sauke ajiyar zuciya bilqees tayi kafin tace, “Toh muje.”
Sun danyi taku kadan kafin suka iske inna dake jiransu tun dazu. Suna karasawa inna habi ta dubesu gaba1. Kafin ta dubi bilqees tace,
“ku jirani Anan kofar gida bari naje na fito.”
Gyada Kai bilqees tayi inna ta shige gidan. Ita kuma bilqees ta nunawa yareema yaseer dakalin gabansu su zauna. Zama
sukayi har lkcn yareema yaseer be daina cije lips ba sunan sarauniya da dogari yyi masa kama da Abinda ya taba sani can Baya, Amma Kuma ya manta. Idan yyi kokarin tunowa da meye Hakan ke nufi? Sai yaji kansa na sarawa, haka dai babu yadda ya iya yyi shiru yana kawar da tunanin a ransa Domin samun saukin sa. Inna habi ce ta fito tare da Wani namiji.
Bilqees na ganin su ta mike da sauri tana gaishe shi tace, “barka da dare kawu.”
Kawu isa yayan inna habi yace,
“bilqees kwana biyu baki leko mu ba.”
Murmushi bilqees tayi tana dukar d kanta batace komai ba. Zama sukayi Suma inna habi ta dubi kawu isa tace,
“Wannan ne yaron yaya, idan da hali Dan Allah a taimaka Masa dukda dai bansan asalin yadda suka hadu d bilqees din ba.”
Gyada Kai kawu isa yyi yace,
“Ah..Toh ai wanna babu matsala habiba, ke bilqees taya kuka hadu da Wannan yaron? Domin musan ta Inda zamu taimaka Masa.”
Bilqees tayi shiru tana tunanin kawu isa yace,
“ki saki ranki bilqees yadda kikayi niyyar taimako muma haka mukeso mu taimaka Masa ko Allah zaisa a gano asalin sa.”
Gyada Kai bilqees tayi kafin daga bisani ta fara sanar dasu asalin yadda ta hadu da yareema yaseer. Daga inna har kawu isa babu Wanda beyi mmkin jin Wannan lamarin ba. Inna habi tace,

<!–more Keep reading fantastic post–>

Amma meyasa tun farko baki sanar dani Hakan ba bilqees? Baki San boyemin Hakan d kikayi ya jawo Mana cin mutuncin da mahaifin ki keyi Mana ba? Ai da ace tun farko kin sanar dani d tuntuni an Samo mafita bilqees, Amma sai kiyi shiru????”
“Kiyi hakuri inna.”
Bilqees ta furta Hakan a hankali tana dukar da kai. Yareema yaseer daya juya masu baya ya juyo d sauri yana kallon bilqees jin yanayin
muryar ta ya canja kamar me shirin kuka ya koma kallon sa kan inna habi d keyin fadan sai kuma ya Kawar dakai d sauri sbd yadda yaga tayi Masa kwarjini saiya kasa yin kudirin d yyi niyya akan kamo hannun bilqees din su tafi.
“Shikenan habiba yanzu ba batun fada za’ayi ba, batun mafita ake nema.”
Inna habi taja numfashi kafin tace,
“kana ganin akwai damar ya zauna a dakin naka na kofar gida?”
Kawu isa yace,
“Wannan ba matsala ya zauna dama ba kowa a ciki.”
“Alhamdulillah”
Inna habi ta furta ranta a Sake tace,
“toh saimu sa cikiyar shi a kewayen kauyikan mu ko Allah zaisa aga Wanda ya sanshi ko?”
Kawu isa yace,
“Nima Abinda nake tunani kenan Kuma Insha ALLAH zamuyi iyakar kokarin mu n ganin an Samo waye shi tunda baya cikin tunanin sa.”
Sosai bilqees taji dadin tattaunawar su akan yareema yaseer, Hakan yasa tace,
“Mlm Idi ma yace zai tayamu Addu’a d Kuma mgnin Karya sammu domin yace Wannan juyawar tunanin baya wuce Asiri ko sammu.”
“Ba shakka tabbas biri yyi kama da mutum”
Cewar inna ta furta da Al’ajabi, tana ci gaba d fadin,
“Abinda yake ta yawo a Kaina kenan ace mutum kamar shi ya kasa sanin waye shi? Dole akwai wata a kasa.”

Bilqees ta girgiza kai, yyinda kawu isa yace,
“Duk tsanani duk wuya Bi’izinillahi ta’ala zai warke Harya tuna asalin sa.”
Inna habi tace,
“tohm Allah ya datar damu.” “Ameen Yah hayyu yaa qayyum.”
Suka furta Hakan a tare. Dakin kawu Isa ya nuna masu gashi nan fes sai taburmar Kaba a ciki sai daga can gefe akwai gadon bunu irin Wanda ake cikashi da yayin Nan, da pillow na bunu shima Wanda aka cika da yayi aka kulle Dan aji dadin kwanciya.

<!–more Keep reading fantastic post–>
Bilqees ta juyo gefen yareema yaseer daya harde hannu da murmushi kan fuskar ta tace,
“ga Inda Zaka dinga kwana Annur gurin yyi kyau ko? Ba wari ba kazanta komai fes.”
Ta Karasa mgnr cike dajin dadi. Ganin yadda Duk ta saki ranta akan wajen ya sashi daurewa Amma badan yaso ba ya gyada mata Kai Yana murmushin yake alamar yyi, bilqees ta washe baki domin dama tsoron ta kada ya sake musanta wajen dan haka tace,
“shiga ciki bari nazo.”
Tana gama fadin haka ta koma wajen su inna da suke shawara da kawu isa, da murnar ta tace,
“Zai zauna a wajen kawu.”
“Toh madallah”
kawu Isa ya furta Hakan yace,
“ki Shiga gidan idan larai ta gama sallar kice ta baki tuwo na bakon d nace a kwasa Masa.”
Bilqees tace, “Toh.”
Juyawa tayi da sauri yyinda su Kuma suka bita da ido. Shiga dakin yyi yana karewa yanayin wajen kallo. Ginin kasa ne na tubali, saman dakin rufin tumba ne irin Wanda ake Dora

<!–more Keep reading fantastic post–>
itace a mannne da kasa hade da yayi sai kofar window ‘yar karama. Kamar dai tun farko gadon na gefe sai taburmar Kaba katuwa da aka malale dakin da ita.

Zama yyi yanajin zuciyar sa ta aminta da wajen kawai ya kishingida akan pillow din yayin da akayi. Mikewa yyi d sauri jin tsinke ya soke shi a damtsen hannun sa, yatsina fuska yyi yana janye rigar hannun sa a daidai lkcn bilqees ta shigo da kwano a hannun ta,
Ajewa tayi da sauri ganin yanata faman cire Abu ya kasa. Zama tayi a gabansa tana riko damtsen nasa tace,
“Lpy? Meya faru? Ko cinnaka ne ya cije ka?”
Rintse ido yyi be iya yi mata mgn ba bilqees ta haska wajen da aci bal-bal din data shigo da ita. Irin fitilar Nan da akeyi da gwangwanin Madara a sa mata lagwani a ciki, cikinsa Kuma kalanzir. Wara ido yyi yana matsawa gefe hade da kwabe fuska kamar zaiyi kuka ga sokewar tsinke ga zafi d hayakin fitilar aci bal-bal duk abin ya isheshi.
Bilqees Bata kula d Hakan ba tasa hannu a hankali ta zare tsinken daya soke Masa damtse tana dagowa sama ta kalleshi sai kuma tasa dariya.
Mmki ne ya isheshi, Hakan ya sashi zuba mata ido beyi mgn ba. Bilqees tace,
“Akan Dan wanna Abu kke shirin yin kuka? Gsky duk yadda akai a zahirin ka rago ne.”
Harara ya balla mata Yana Kawar d Kai. Bilqees ta shanye dariyar ganin yaji haushi, tace,
“oh..na manta kaifa jarumi ne sbd kayi fada da manyan barayin daji.”
Juyowa yyi a Hankali Yana kallon yadda take ta boye dariyar da take Masa ya cije lips a hankali Yana kokarin kwanciya Dan duk ya gaji.

Bilqees tayi saurin dakatar dashi tana kwaso abincin data shigo dashi tuwo ne na dawa da miyar kuka Wanda yasha man shanu sai kamshi yake ta dire Masa a gabansa tana budewa tace,
“Ya kamata yaudai Kaci Wani Abu me nauyi a cikin ka.” Gwalo ido yyi yana kawar da Kai bilqees tace,
“baka ci?”

<!–more Keep reading fantastic post–>
Yatsina fuska yyi yana janyewa gefe alamar bayaso. Yaushe ma zai iya cin Wannan abun a cikinsa? Ga Abu Nan sai kace Dutse da wata Miya tamkar daurayen gantsa kuka wai yaci tabdin. Bata rai bilqees tayi tana rufe kwanon tace,
“Ttunda baza Kaci ba shikenan na tafi.”
Ta furta Hakan tana kokarin tashi Duk zuciyar ta babu dadi. Ganin yadda ranta ya baci ya sashi matsowa d sauri yana gyara zaman sa a gaban abincin yace,
“zanci.”
Ya furta Hakan kasa2 badan yaso ba. Juyowa tayi a
tsanake, yadda taga ya furta a takure saiya Bata tausayi. Kuma izuwa yanzu har mmkin gudun bacin ranta d yakeyi take. Ikon Allah, zama tayi ta bude Masa kwanon ta tura a gabansa tana sakin ranta yadda zaici din tace,
“Toh gashi nan, Kawo na zuba maka ruwan.”
Ta daga kofin ruwan data zo dashi tana tura Masa wata roba Inda zai wanke hannun sa. Mika hannun yyi kamar baya so ita kuma tahau tsiyaya Masa a nutse yyinda ta bangaren sa Kuma ya zuba mata ido Yana karewa fuskar ta kallo.
“Yauwa yanzu sai Kaci ko?”
Ta Ida zancen tana dagowa taga ya kafeta da ido. Wara idon nata tayi tace,
“kana jina kuwa?”
Firgigit…ya motsa Yana gyada Kai yace, “Eh.”
Bilqees ta Kawar da Kai tana mikewa tace,
“Inna tana jirana a waje, Kaci abincin Saida safe zamu hadu kaji? Kada ka tafi ko Ina kaji? Zan dawo da safe Insha ALLAH, duk abinda kke bukata kawu Isa zaiyi kafin na dawo kaji?”
Yanayin fuskar sa ce ta canja gaba1. Bilqees ta dauke kai domin ta fahimci baya son tafiyar tata, yoh Banda Abinsa baligi dashi so yake ta kwana dashi? A haka tabar wajen Bata waiwaiye shi bama bare ya Bata tausayi.

Kamar yyi kuka haka yareema yaseer ya kwabe fuska Yana Bata rai, hararar tuwon gabansa yyi tamkar shi yyi lefin haka ya ture gefe beci tuwon ba Yana shirin komawa ya kwanta wata zuciyar ta tuna Masa bilqees, dukda bata wajen sai yaga bazai iya mata Hakan ba tunda ya Tabbatar mata da zaici din. Tashi yyi a tsanake ya zubawa tuwon ido Yana mmkin Wanne irin abinci ne wannan? Shifa zuciyar sa tafi aminta da kayan fruits din d bilqees ke bashi domin yafi jin Hakan a ransa kamar d can ya saba da ci saidai bazai iya tuna yanayin ba.
Gutsuro tuwon yyi yasa a baki a hankali ya fara taunawa dakyar tamkar ya samu mgni. Ba karamin kokari yyi ba Yana zare ido haka ya hadiye tuwon kamar dole. Haka ya sake daurewa ya gutsuro Wani, Ana ukun kuwa kasawa yyi, ji yyi cikinsa ya kulle waje daya, ba shiri ya janye kwanukan gefe Yana yatsina fuska a haka kawu isa ya shigo da sallama.
Dagowa yyi da Dan sakin fuska ya Amsa Masa sallamar. Kawu Isa ya zauna kusa dashi da murmushi yace,
“harka koshi ne?”
Gyada Kai yareema yaseer yyi batare daya furta komai ba. Kawu isa ya dubi gurbin daya gutsira bana kirki bane, yace,
“Annur ai bakaci na kirki ba”
Dan murmushi yareema yaseer yyi kafin yace,
“Na koshi kawu.”
Ya furta Hakan kamar yadda yaji bilqees ta ambata. Kawu isa ya girgiza Kai yace,
“Tohm Madallah”<!–more–>
kafin yaci gaba da fadin,
“Mun gama mgn da mahaifiyar bilqees zamu je mu baza lbrin ka ko’ina cikin Wannan kauye namu da kewaye ko Allah zaisa a samu Wani Wanda ya sanka ko Wanda ya San lbrin ka.”
Yareema yaseer ya Kawar da Kai beyi mgn ba. Haka kawu Isa ya gama bayanin sa kafin yyi Masa sallama bayan ya sanar dashi akwai ban daki a gefen Inda dakin yake idan yanada bukatar zagawa. Amsa Masa yyi da Toh sannan shima ya tafi.

Zuciyar sa babu dadi ya lumshe ido bayan ya kwanta, besan meyasa ba amma baya Wani murna da Wannan binciken da suke Masa wai asalin sa? To dama mutane sunada Wani asali ne? Ai yadda ya ganshi haka kawa, Gani yake kowa ma haka kawai yake ba Wani asali ko lbrn sa ko dangin sa d suke ta faman furtawa tun bayan daya shigo kauyen Nan. Mtwss yaja tsaki Yana Kara gyara kwanciyar sa a takure a haka bcci ya dauke shi.
Tunda suka koma gidan Kuma sai habaici ke tashi daga inna Zabba da mlm Musa. Inna Zabba tace,
“Gsky kinji kunya habiba ace harda ke za’a aje zabgegen saurayi a kauyen Nan? Mutumin da ko asalin sa baku sani ba? Sbd tsabar neman Suna ne ko gindin zama?”
Banza inna habi tayi mata Bata Amsa Mata ba tayi wucewar ta daki tana janyo hannun bilqees din.
Matan makotan su da suke zaune a tsakar gida anata gulmar goyon bayan da inna habi ta bawa ‘yarta wata daga ciki anace da ita rakiya tace,
“ke kuwa zabba’u Ana neman da
namiji ba’a samu ba sunga tsuntsu daga sama zasu makale Masa.”
Zabba’u tasa dariya tace,
“Ba shakka nan gaba sai tace ita ta haife shi.”
Dariya sauran suka saka Suna ci gaba da gulmar su inna habi na jiyo su Amma Bata tanka masu ba. Ko wanne irin cin mutunci zasuyi mata Mlm Musa ne ya jawo mata ta barsu da Allah kawai.
Bilqees duk ta damu da yadda ake yadawa mahaifiyar ta mgn, ba Abinda ta tofa nata Albarkacin bakin ba inna habi bazata bari ba, haka dai ta karaci takaicin ta ta kwanta bcci hade da tunanin yareema yaseer data baro a gidan kawu Isa.
Bam..bam..bam….., Daga waje suka dinga jiyo Ana girgiza kofar gidan tamkar za’a ballata ta, 6mlm Musa daya gama shan kokon safe ya mike a fusace yana nufar wajen yace,

Uban uban waye me shirin ballemin kofar gida??”
Lauwali daya dawo daga daji ba shiri ya ware murya sosai yace,
“lauwali ne.”

<!–more Keep reading fantastic post–>
Shanye jarabar sa Mlm Musa yyi ba shiri ya fara washe bakin dole bayan ya zare sakatar gidan yace,
“auhoo Ashe kaine.”
Fuska a daure lauwali yace,
“Eh nine.”
Mlm Musa yasha jinin jikinsa Hakan ya sashi fara zuba ba shiri yace,
“Nake fada maka Wlh ba yadda banyi ba yarinyar Nan ta yage bakon Nan daga jikinmu Amma tayi min kunnen uwar shegu, Dan iya shege ma mahaifiyar ta ce ta Samar Masa mafaka a gidan Dan uwanta.”
Lauwali yace,
“Meyasa
tun wuri baka kirani na saita masa hanya ba?? Ko ka manta bilqees yanzu a
matsayin matata take? Taya za’ai kayi irin Wannan sakacin harta nemi taimakawa Wani shirgegen Kato can wanda ba’a San asalin sa ba?”

Mlm Musa yace,
“Wa billahillazi lauwali ba irin kokarin da banyi maka ba, ai na fada maka tun farko karshe ma Korar su nayi ita d bakon….”
“kace me??”
Lauwali ya furta da karfi Yana zare Masa ido. Mlm Musa yace,
“Ina nufin ta mayar dashi Inda ta ganshi ai ita bilqees a gida ta kwana.
“Toh ai inace harda ita ka kora da anyi hawan bori a kofar gidan Nan yaseen.”
Mlm Musa ya girgiza Kai da sauri yace,
“idan kanaso ma saina Kira maka ita.”
“Da dai yafi”
Lauwali ya furta hakan yana gyara tsayuwar sa. Da sauri Mlm Musa ya juya cikin gidan Yana rarakawa bilqees Kira.
Bilqees data samu bcci ya dauke ta d safe ta mike a firgice tana juye2 Mlm Musa ya bankade labulen dakin su yace,
“kinaji Ina zabga maki Kira bazaki taso ba?”
Mikewa tayi d sauri ganin yana shirin afkowa dakin ta janyo hijab dinta ta saka tana fadin,
“Yi hakuri banji bane.”
Dogon tsaki yaja Yana ja baya yace,
“jeki wajen ja’irin yaron Nan Yana kofar gida.”
Ko be ambaci suna ba ta fahimci da lauwali yake. Hakan yasa ta Bata rai sosai tana daure fuska ta sanya silifas dinta ta fito.
“Baalkiii…lbrn da nakeji a gari gsky ne?”
Lauwali ya furta Hakan yana tsareta da ido. Banza tayi dashi tana kawar da Kai, lauwali ya dawo ta gefen da take ta matsa d sauri yace,
Hankali na ya tashi Baalkiii kinsan yadda nake sonki kuwa? Taya Zaki min haka? Meyasa Zaki biyewa bakon da ko kadan baki San asalin sa ba? Idan Mugu ne fa??”
Harara ta banko Masa tana sake kauda Kai a ranta tana fadin wai Mugu, Toh idan akwai Wanda yafi cancanta da a kirashi da Mugu Toh ya biyo bayan Kai…..,<!–more–>
“Baalkii dake nake mgn fah? Kinsan a kanki billahillazi Ina iya kashe shi.”
Juyowa tayi a razane lauwali ya gyada Kai alamar Tabbatar wa kafin yace,
“Toh meye Dan na sheke shi?”
Da sauri bilqees tace,
“kada ka fara tunanin haka lauwali.” Da mmki ya dubeta yace,
“Sbd ya fini a wajen ki?”
Girgiza Kai bilqees tayi d sauri ganin yana hade fuska ta sassauta nata fushin Dan taga alamar dgske sai ya iya neman yareema yaseer da fada Kuma fada dashi ba kyau. Dan haka tace,
“baka fahimce ni bane lauwali”
lauwali yace,

“Toh inajin ki, ki fahimtar Dani.”
Bilqees ta sauke ajiyar zuciya kafin tace,
“Taimaka Masa zanyi fah? Bako ne Wanda besan asalin waye shi ba ya manta tunanin sa.”
Tabe baki lauwali yyi yace,
“toh sai me? Kinga nifa wlh bazan yadda da Wannan kusancin naku ba Baalkiii, haka kawai naje yamin illah.”
Bilqees ta daure fuska kafin tace,
“Shikenan idan ka tabashi saidai a kawo gawata gidan ka.” Gwalo ido lauwali yyi yana rike haba yace,
“Baalkiii? Akan shi bakon?”
Gyada Masa Kai tayi alamar Tabbatar wa,
“Shikenan, naji zan kyale ki
Amma Wlh ya kiyayeni kada ya shige miki da yawa idan ba so yake nayi gunduwa-gunduwa dashi ba.”
Wara ido bilqees tayi a tsorace lauwali yace,
“Dan fa kece, da Wlh saidai ki nemi bakon Nan ki Rasa tun dare zansa a dauke min shi aje can a cillar dashi Wani wajen yaje ya karata.”<!–more–>
Kasa cewa komai tayi domin lauwali wanna ba karami aiki bane a wajen sa tsaf saiya aikata.
“Kuma da nace sai Nan da wata daya ayi bikin mu Wlh na fasa Nan da kwana uku za’a daura iyakar hakurin da zanyi kenan na dinga ganin ki da Wannan bakon…”

<!–more Keep reading fantastic post–>
zaro ido bilqees tayi a firgice jin kalaman lauwali, lauwali yace,

“kwaraii gwarama kiji da kyau Kuma kisan yadda zakiyi dashi Dan ba binki zaiyi ba atoh, Dan naji lbri yadda kasan bindi haka yake binki duk Inda kikaji Toh ki sanar Masa billahillazi akuyar sa ta kiyayi Ramata.”
“Lauwali…?”
Bilqees ta furta Hakan hankalin ta a tashe, lauwali yace,
“kinada abin fada ne?”
Bilqees tace,
“yanzu bazaka tayani tausaya Masa ba? Shifa yadda kasan jariri haka yake besan a wacce duniya yake ba.”
“Toh Kuma sai me? Ubansa ne ni dazan damu dashi? Toh ko uwar mu daya uban mu daya dashi naga Yana kokarin shishige maki Wlh sare Masa Kai zanyi…”
ya furta Hakan yana zare takobin bayan sa. Ja Baya tayi a mugun tsorace lauwali ya kwashe da dariyar mugunta yace,
“kwantar da hankali ai kekam ko kuda ya nemi takura maki, fille Masa Kai zan domin babu Dan shegiyar daya isa tabaki matukar Lauwali Yana Nan, Wannan takobin jinin masu shiga gonata take sha.”
Kasa mgn bilqees tayi domin tsantsar gksyr sa yake fada Hakan yasa ta juya Baya tana dafe kirji can ta hango yareema yaseer a bayan wata bishiya ya harde hannayen sa idonsa a kanta fuskar sa a daure tamau.
Gwalo ido tayi kirjinta na bugawa tana fatan ace kada lauwali ya ganshi ta dawo da hankalin ta kan lauwali dake shafa takobin sa a hankali fadi yake,
“Wlh jini take bukata Wannan ‘yar amanar.”
A kidime bilqees ta juya da nufin yiwa yareema yaseer alamar ya tafi Dan bataso su hadu abin bazaiyi kyau ba sai kuma taga ya fara takowa Inda suke gadan-gadan fuskar Nan ya sake daureta sosai tamkar Wanda aka aikowa da sakon mutuwa.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE