SARAUTAR MATA COMPLETE BY MAKAWA
Gidane irin ginan wani lokaci da, can baya, wanda yake nuna cewa,a lokacin baya gidan yana a,cikin jerin gidajen da suka dan yi tashe a wancan zamanin,
Sai dai a wanan zamani ya zama kamar ginan kauya,a,gare mu,
Tsufan gidan ya,sa har shafin da,akaiwa gidan yana dan banbara yana zubewa, don tsufa,
Wasu bangare na katangar gidan har sun zube an sa tsufin kwano a,rufe gurin dashi,
Tsakiyan gidan akwai iccen durumi, wanda ya baje yana bawa mutanen gidan inuwa da sanyi,,,
daga gefen dakin ta waje akwai randan ruwa, suna rufe da,wasu manyan kwanukan lokaci da, can baya, wanda yake nuna cewa,a lokacin baya gidan yana a,cikin jerin gidajen da suka dan yi tashe a wancan zamanin,
Sai dai a wanan zamani ya zama kamar ginan kauya,a,gare mu,
Tsufan gidan ya,sa har shafin da,akaiwa gidan yana dan banbara yana zubewa, don tsufa,
Wasu bangare na katangar gidan har sun zube an sa tsofin kwano a,rufe gurin dashi,
Tsakiyan gidan akwai iccen durumi, wanda ya baje yana bawa gidan iska da innuwa mai dadi, daga gefen dakin ta waje akwai randunan ruwa, suna rufe da,wasu manyan kwanukan iri na da,, sai wani rumfan dake ta gaban dakin wanda ke bawa dakin sanyi again,,
Wata mata ce mai dan shekaru sai dai ba can ba ta fito daga dakin, tana saye a cikin wani kodadden zani da riga na atamfa,
Sai dai zani daban riga daban dankwali ma,daban,
Hannunta yana dauke da,wani stohon kwanon silver wanda daga saman shi duk ya dan mokade sosai,
Tsakin jan masara ce dauke a,cikin kwanon ba,wani mai yawa ba can, sosai,
Wani stohon kujera yar tsugunno irin na mata ta,tsakar gida,shi ta nufa tazauna a kai a hankali, tafara dan gyaran tsakin dake a cikin kwanon,
Sallaman da,akayi daga kofan dakin ne yasa ta saurin dago kanta da yake a,duke da farko, bakinta yana karba sallaman a hankali,
Dan ta Hamza ne ya shigo gidan hannun shi yana dauke da wata yar bakar leda bag karama wanda zaka iya hango ganyen miyane a cikin ledan,
Fuskan shi tar akan mahaifiyan nashi yayin da ya nufi inda take zaune, yana mata sannu da gida Umma,
Takara dago kai a cikin fara,a tana cewa Baba na an dawo lafiya ?
Kafin ya karba mata sai ya zube a kasa yana cewa, Umma sannu da aiki, an wuni lafiya yana kokarin aje ledar da ya,shigo da ita a hannun shi daga gefen ta, ta ansa mai da fadar Alhamdullahi,
Kardai yau ma kana azumin ta fada cikin kashe shi da idanuwan ta tar a kan shi,,
Murmushi yayi yana maidan dukar da kai yayin da,ya zauna hannayen shi suna harde da junan su, yake cewa cikin hade wani miyaun bakin ciki,
Umma ai gara nayi azumin don koda banyi ba, ba,wani abu zanci ba don kasuwan yanzu sai a hankali wallahi,
Allah ya taimaka tace tana mai kokarin mika hannu ta don ta,bude wanan ledan dake a,gefen ta,
Gayen miya ne yakuwa da,yar alaiho sai tattasai atta da albasa a cikin ledan,
Ta dago kai tana cewa duk wanan haka muka,samu, Baba na,
Ubangiji Allah ya ummfana Allah ya sa maku albarka Allah ya tsare muna ku ya shirya muna ku tafarki mai albarka,,
Ya amsa da Amin Umma yana saka hannun shi a,cikin aljihun wandon shi inda yafito da,kudi sai dai duk canji ne kudin ba wasu kudi masu girma,daga ciki,
Mikawa uwar yayi yana cewa mama ga wanan kasuwan duk ta chushe yau duk naira dari da hamsi na samu sai na,sayo wanan kayan miyan don nasan kina dabukatar su,
Wanan kuma nace bari na zo maki dasu kyasai wani abin dashi anan
Shiru tayi tana mai kura mai ido a cikin tausayawa, dan nata duk da gashi mai karancin shekaru amma yasan yadda zaiyi ya taimaka masu,
Babana kabar wanan kudin ka,samu ka dan sai abin buda baki dashi idan kasha ruwa, don kaga ga tsakin masara nan shi nake gyara muna mu samu na dan tabawa ,
Kaga wanan ganyen yai daidai da faten da nake son muna,dama,babu ganyen da zan saka muna a cikin sa hakana zanyi yanzu kaga an samu abin hadi Allah yasa,albarka a cikin sa,
Kai ya girgiza yana fadin Umma ki karba duk abinda aka dafa a gidan nima shi zanyi buda bakin dashi,
Ta ce Babana Allah ya sa wanan wahalan da kake muna yama tushen alherin ka a rayuwan duniya da lahira yace Amiiln cikin jin dadin adduan mahaifitan nashi a kullun tana masu adduan fatan alheri shi da yan uwan,
Tausayin sune ya kamashi, don zai iya cewa yau kusan kwana,biyu ke nan yana yan bugabuga amma bai samu wani kudin da zai dan sayo masu abinci ba kamar yadda ya,saba da taimakon mahaifiyan nashi da yan kannen shi dake gidan yanzu,,,
Wanda zai ce kusan shekara bakwai tun yana karami shike dauke da nauyin gidan nasu, a komai,
Duk da ita,ma mahaifiyan tasu tana nata kokarin gurin dan ciyar da yan marayun yayan nata,
Tun bayan rasuwan mijin ta wanda ada can su masu haline da rufin asiri amma mijin ta yana rasuwa yan uwan shi suka wawashe duk wani dan abinda ya,barwa iyalin nashi,
Saboda cin amanan maraya,da,sunan wai yaran basu isa rike dukiyan a hannun su ba a lokacin,,,
Bayan yan shekaru “yar ta zatai aure babu dukiyan babu labarin su dole hakana akai bukin akai ta,babu komai don dangin mahaifin su sun ciye komai nasu har gona da filayen su duk sun sayar da sunan wai za,a biya mai bashi dasu,,,
Yan uwan ta ne suka dan hada mata gudun mawa suka bata shine akadan yi sayayya dasu,
Adduan da mahaifiyan nashi ke mai sune suka jawo hankalin shi gare ta daga dan tunanen da yakeyi a lokacin,
Cikin dan sauke ajiyan zuciya yake cewa mama yanzu kasuwan baici shi yasa nake son na canza wata sana,a ko zaifi wanan din karbuwa,
Tace cikin dago kanta Babana wani SANA,A, zakaiya canzawa yanzu don kaga da wanan din ka,saba nagani,
Yace wa mahaifiyar tashi Umma zan duba da zaran naga wanda yake da,daukuwa zan maki magana,
Ya mike yana cewa bari ya dan gyara dakin shi kafin magriba ya gabato gare shi,
Bayan shi Umma,tabi da kallo a,cikin tausayawa dan nata wanda yataso maraya ga,aikin wahala da yai mashi yawa a,rayuwan shi tun yana yaro karami,
* * ***
Kiran sallah magrib ne duk ya karade ko ina a cikin garin baka jin komai sai karan speakers dake tashi ladanai na kiran sallah,
Daga gurin da yake zaune ya rike da dabino kwara, biyu a hannun shi yana mai tofa addua daga bakin shi, a hankali,
Daga gurin da yake zaune, yana alwala malam Ayuba yana kalon shi har zuwa lokacin da ya dauki ruwa yaddan kora,
Abinda yasa shi gane cewa azumi yaron yayi a lokacin yana buda baakine,
Shidai har kullun wanan yaron yaba,shi sha,awa,sosai a rayuwan shi, ba,yau ba koda yau,she daban yake da,sauran yaran uguwarnan,
Bayan an idar da,sallah ake cigiyan duk wanda keda sha,awan zuwa gonan mai uguwa gurin aiki kwadago,,
A take Hamza yaba,da sunan shi don yana da bukatan haka ba yau ba,
Amma sai mutanen gurin suka,fara sokewa wai bazai iya komai ba kada a,sashi a,cikin su, sai malam Ayuba ne wanda fitowan shi ke nan daga cikin masallaci yake cewa a,yi hakkuri asa sunan shi idan an gwada,anga bazai iya ba,sai a cire shi daga cikin su,
Da,sallama dauke a bakin shi ya,shigo gidan inda yake gaida mahaifiyan shi da aikin gida,
Tun a tsaye take cewa ,a Baba na barka da shan ruwa Allah ya karba muna bukaun mu na alheri ya amsa dacewa Allahuma Amin Umma daga haka yakai zaune daga gefen ta, a hankali,
Bayan yasamu guri ya zauna ne yake fadawa mahaifiyan shi cewa zasu tafi aiki a gonan mai unguwa dasafe indan Allah ya kai mu,
Da,sauri Umma dake kokari jawo mai langan abincin shi dake rufe daga gefe,,,
Tai wani irin saurin dago kai tana kallon shi a cikin mamaki da tausayawa saboda tana ganin kan,kantar dan nata,
Tasan cewa mutuwa ce takai rayuwan su a hakan don da ace mahaifisu yana da rai da duk irin haka bai faru da su ba,,,
A cikin wani irin murya yayin da take aje yar langar abincin nashi take cewa anya Baba na zaka iya irin wanan aiki kamar fa kayi karamii da wanan aikin,
Murmushi yayi yana kokarin wanke hannun shi da ruwan dake gefe guda, yake cewa Umma adduan ki kawai nake bukata ,
A sanyaye tace tau Allah ya tsare yasa albarka ga al,amari yace Amin Umma yayin da yake kokarin bude kwanon abincin dake gaban shi,
Duk da faten ba,wani kayan hadi taji ba dan tsakine sai attarudu danye, da alaihuu sai gyada kadan da aka watsa a ciki,
Amma sai ga kamshi dadi yana tashi daga cikin kwanno tun kafin yaci yar miyaun shi sai ta katse,
Muryan shi da Rakiya kaunar shi taji yadan sata fitowa daga daki tana kokarin cire hijab din dake saye a kanta,
Sai a lokacin hankalinshi ya kai a kanta yana cewa a,a Rakiya andawo daga makarantar ashe ?
Yaya Hamza ina wuni ya kasuwa yace lafiya kalau Alhamdullahi ina, Abdul halan ma,
Tace yanzu yafita karbo wa mama kalanzir din fitillah ta,
Sallaman da akayi ne daga kofa ya,dakatar dasu daga zancen su inda Ummaa take karbawa da cewa a,a,
Kardai nace, Aisha ce tafe a yanzu cikin daren nan ta karba tun daga nesa da cewa,
Yarinyar da,akakira da,Aisha take cewa nice maman Abdul, mamace ta aikoni wai na kawo maku wanan abincin don yai muna yawa bazamu iya cinyewa,ba,,
Masha Allahu Umma ta ambata yayin da take kokarin karban kwanun daga hannun yar matashiyar budurwan,
Sai famqn zabga godiya take da sa albarka ga matar da ta Aiko masu da abincin,
Muryan yarinyar ce ta ke cewa Dan wakene mai zafi a a wani roba an rufe shi daban yarinyar ke cewa wanna wanna na marmarine mama tace akawo maki,
Dan wake ne yaji mai da yaji sai kamshi ke tashi daga cikin robar,
Inda dayan kulan yake shake da farar shikafa da miiya daban miyar busashen kifi, yaji curry,,
Sai da Umma ta wanke kwanukan tsab duk da dai, yarinyar tana cewa Umma ta bari ai zasu wanke da safe, ma,
Fitar yarinyar gidan wace ke cewa Umma sai da safe yayi daidai da waigowar Umma inda yake zaune tana cewa hamza to kaga ga abin buda baki Allah ya kawo maka sai ka dauka kaci wanda kake so,
Sauke ajiyar zuciya yayi tare da,dan kara gyara zaman shi yana cewa Alhamdullahi Umma don wanan da kikayi yai min dadi sosai a raina,
Duk yadda uwar taso ya dan ci abinci amma yaki tana lura dashi wanan halin sa ne baya son cin abincin nan da ake kawo masu daga makwabta duk da yasan cewa abincin yana taimaka masu sosai a,fanni da dama,
Saukin abin ma, ya yaba kwarai da halaiyar mahaifiyan yarinyar dake kawo masu abincin don bawai sai, wanda ya rage suke kawo masu ba har wanda aka dafa wani lokacin da zafin shi zata debo masu,
Baibar gurin ba yana kallon yadda yan kannen shi ke wawason abincin cikin jin dadi da annashuwa,
Yayin da,suka,bar na mahafiyar su dan faten da ta hahada tai masu iya karfin ta,,
Kwanon dan wake Umma tadangware mai a gaban shi tana cewa kai kaci wanan tunda bazakaci shimkafa ba,
Baida yadda zaiyi don kada yai mussu da mahaifiyan nashi dole ya dan jawo kanon yafara kai hannun shi a,hankali,
Dan waken yana da zafi inda ya dauki guda yakai bakin shi,
Balaifi a hankali yake dan taunawa dan waken yana da,dadi sosai yana tauna yana tunanen Allah ya azurta shi shima ya,dinga taimakawa mahaifiyan shi da yan uwan shi,
Ya danci ya kai rabi, sosai ya mikawa uwar duk da yana son karawa amma yabar mata don itama taci, saboda yasan danwake cimar tane sosai,
Murmushin jin dadi uwar tayi don ganin cewa yaron nata yaci sosai duk da bawai ya damu da cin abincin makwabta bane kasafai irin hakan nan,
** *
Washegari tunda safe, Hamza ya,shirya don zuwa gonan mai uguwan da zasu yi wanda da wanan zancen ya kwana a ranshi,
Duk da ba,wani abin karyawa suka kwana dashi ba a gidan dan sauran chanjin da Umma ta bar mai a,daren jiya ya,sayi abin buda baki shine tun daren jiya ya,sayo yar kwaki da,sugar don tafiya zuwa gonan,,
Kattan majiya karfine su kayi shirin zuwa gonar maigari gurin aikin gonan daga ciki Hamza ne kawai yaro karami wanda shima da daurin gindin malam mudi makwacin su ya samu shiga wanan aikin ,,,
Acikin mota mai budaddan baya akwa kwashe su su ashirin da biyar zuwa gurin aikin,
Ba laifi don Hamza ya kwarzanta saboda duk yadda masu karfi sukayi aiki shima bai yarda anbarshi a,baya ba,
Don ya turza tukuru anyi komai dashi yadda ya kamata,
Duk aikin da akai wa mai, uguwa a tare da Hamza akayi shi har tsawon sati guda,
Wanan ne yasa Hamza hada dan kudin masu yawa inda ya dan ware naira dari ya,sayowa malam mudi wanda yai sanadin zuwan shi wanan aiki goro farare masu kyau ya kai mai har kofan gidan shi,
Malam Mudi yayi murna sosai da wanan hikimar ta wanan yaron maraya mai albarka,
Don sam bai tsanmaci cewa Hamza din zai iya jure irin wanan aikin wahalan ba ,
Idan anyi la,akari da yadda yaran yanzu suke masu son saukin al,amari ba masu morewa jikin su ba,
Abinda Hamza ya samu a aikin gonar mai uguwa dubu daya da dari biyar ya saiwa malam mudi goro ya bawa Umma dari uku “yan kannen sa ya ba su hamsi su sayi silifas a kafan su,,
Ya mayar da,sauran kudin cikin leda ya kulle tare da daurewa ya saka a,aljihun sa,
Abu na farko da ya fara yi, shine biyan kudin littatafan da,suka,dakatar dashi daga zuwa makaranta,dari biyu da hamsim,
Washe gari kwastsam Umma ta ga ya fito da shirin zuwa makaranta abinda yadade baiyi ba tun bayan wata uku da,suka shude,,
Tausayin yaron nata ya kama ta don dama tasan cewa karatun yana a,cikin ransa rashin kudi ne kawai ya dakatar dashi,,
A makarantar ma sai da kyat ya samu suka karbe shi tare da ja mai kunnen dakatar da zuwa makarantar da yakeyi,
Allah mai iko Hamza yana karatu yana dan juya kudin ahi a hankali inda duk ranan kasuwan garin su zai fitar da kudin shi ya dan juya su a,wani fanin ,
A haka sai Allah ya sa mai albarka kudi dubu daya ya fara zama dubu biyu, uku, hudu,,,
Hakan ya bashi sha,awan yin noma a dan gonan da ya rage masu na mahaifisu,
Kafin ma yan uwan nasu su yarda da zancen noman nashi sai da suka ja masa rai iya son ransu,
Wata gwagon shi ce ta saka baki har suka yarda da zancen noman nashi,,
Noma da can baya ba noman kashin kudi bane irin na wanan lokacin yanzu wanda a da can baya sai dai mutum.ya sa karfin shi yayi noma ba wai kudi ba,
Inda Allah ya kara sawa abin nasa albarka shine da Umma ta tafi kauyen ganin yan uwan ta tazo masu da iri (Seed) mai kyau irin ta mutanen kasar bauchi,
Masara ce ya fara sakawa wanda Allah ya sa wa noman albarka sosai don gonar ta haihu matuka,,
Duk wanda yaga gonar sai yayi magana a kan gonar saboda irin yadda masaran ta samu guri ta haihu tai goyo gwanin ban sha,awa da kyau,,
Abinda ya haddasa bakin ciki ke nan ga yan uwan mahaifin nashi da suka dauki kyashin da hassada da bakin ciki suka dagwara ga iyalan dan uwan haihuwan su mai tausayin su da tallafa masu a lokacin da yake da rai,
Wanda su sam badu kaunar irin wanan rayuwan sun fi son suga cewa suke da irin rufin asirin da yake dashi, a lokacin,
Hassadan ganin yadda yai noma kuma noman ta karbe shi yasa su yin dana sanin bashi wanan filin ya noma a cikin sa,
Don haka suke cewa wani shekara sai dai ya canza guri ba zai kara noma a,wanan gurin ba, kuma su zasu noma abin su,,,
A lokacin da aka cire wanan amfanin gonan ta Hamza kusan kowa ya girgiza ganin yaro karami kamar hamza yai wanan irin noman haka mai albarka,
DOWNLOAD COMPLETE BELOW ⬇️