SATAR FITA COMPLETE HAUSA NOVEL
Da gudunta ta fito daga gidan hannunta dauke da qatuwar jaka tayi bakin titi, keke nepep ta dauka da sauri ta shige ba tareda sunyi ciniki ba tace malam gandun Albasa zaka kaini.
Tafiyar mintina 5 ce ta kaisu gandu tana fitowa ta miqa masa 70 naira ta shiga gidan da sauri. A tsakar gida taci karo da mamansu Aisha tana shara. Har qasa ta tsugunna ta gaidata matar ta amsa da fara’arta tace mata Aisha tana ciki.
Da sauri ta shiga ciki a daki ta iske aysha a bakin mirror tana kwalliya, ihu aysha ta saka ta rungume HINDATU sannan suka fada kan gado. Saida suka gama ife2nsu sannan aysha ta kalleta da kyau tace keh shegiyas na zata bazaki zo ba.
Baki ta tabe tace kedai bari wlh saida na jira umma ta shiga toilet sannan na fito.
Dariya suka sa gaba1 aysha tace Hindu wato ke bazaki taba canza halinki ba koh?
Tabe baki tayi tace sae randa gyatumaina suka canza halinsu na kulle sannan nima zan canza.
To naji, dan Allah tashi ki shirya da wuri kinga 8:15 nima da qyar na tsara ummi ta barni saboda baffa bayanan.
Da sauri hindatu ta bude Jakarta ra dauko ankonta na material pinki n purple ta zura ta tsantsara kwalliyarta tayi masipar kyau.
Aysha dake amsa waya ta juyo ta kalli hindatu a fili tace Wow!!! Shegiyas kinyi kyau dole kisa abokan ango suji jigi jigi! Keh idan ta kama har angon ma.
Dariya suka kwashe da ita suna tafawa Hindu tace Aysha bakida kirki wlh idan banda tsabar iskanci ina ni ina ango koko so kike mairo tayi sammako gidanmu taci ubana.
Murmushi Aysha tayi tace wlh kuwa kinsan maryam akan wannan mijin nata, sae wani kurantashi takeyi tunfa muna secondary suke tare, yaseen ya hadu.
Tabe baki hindatu tayi tana jujjuyawa gaban mudubi tace haka kurum umma zataimin buqulun ganin hadaddu, kinsan wlh maqasudin zuwana bikin nan saboda n qure qaryar mairo amma daga yadda naga kamunta naga Alamu babu qarya.
Muje plz aysha ta fada tana qara balbalawa Hindu turare suka jero. A falo sukaci karo da
da ummi ta kallesu da kyau ta tabe baki tace Ku kula da kanku d kyau dan Allah kunga dai duniya babu gskia sannan dan Allah kafin 10:30 ku tabbatar kuna gida.
Murmushi sukayi tareda cewa insha Allah ummi. 2k ta miqa musu tace kuyi kudin mota suka amsa suna godia.
A qofar gidansu Aysha saurayin nata yai parking motarsa aysha ce gaba Hindu na binta a baya suka bude motar suka shiga.
Sama 2 suka gaisa d hindatu dan ita sam bata sakarwa maza fuska a cewarta batason raini koda kuwa samarin qawayenta ne kokuma en uwa. A cewarta a shekarunta da basu wuce 19 ba soyayya bata lokacine tunda tsarin baffanta ne dole sae mutum ya gama first degree ko HND dinsa sannan zaiyi aure.
Data gaji da hirar da Aysha takeyi da saurayinta kamal wayarta ta zaro ta zura earpiece ta kunna waqa.
Cikin en mintuna qalilan suka qarasa babban hall din da ake taron dinner din qawarsu maryam amma tsabar ji da kai da nuna su manyan yarane a cewarsu saida suka kwashi kusan 1 hour a cikin motar, a cewarsu hadaddu basa zuwa gurin taro da wuri sae an kusa tashi.
Saida suka qarawa fuskokinsu powder sannan suka shiga gurin taron suna takunsu daidai mai Jan hankali.
Aysha farace Tass kamar zabiya amma batada wani kyau sae kwalliyar balaee, wannan farin nata kuwa jarine babba a gareta domin yawancin mazan kano babu abunda yafi birgesu kamar farar mace, batada tsayi sosae amma ba gajeriya bace jikinta daidae musali dass ta ita.
Hindatu kam baqace amma ba sosai ba saidae ALLAH ya zuba mata madarar kyau tako wani fanni matsalarta 1 ce tsantsan tsiwa da futsara saboda duk girman mutum idan ya tabota zata antaya masa rashin mutunci ne shiyasa wani lokacin friends dinta sukance mata miss no nonsense.
Hankalin kowa a gurin saida ya dawo Kansu ban dauke ango da amarya ba saboda en matan 2 badai iya tsara kwalliya ba abunka da en matan kano, wannan ya basu damar dage kawunansu suna shan qamshi musamman hindatu wadda dama halinta ne idan taga mutane
can gefe suka nemi gurin zama, duk table mutane 4 ne suke zama amma cikin sa’arsu nasu table din su 2 suka zauna.
Kusan yawancin yan matan dake gurin sun sansu dan yawanci tare sukai secondary wasu kuma har yanzu tare suke schooling amma tsabar iya shege sae suka nuna kamar basusan anyi ruwansu ba sukai fuska suna hirarsu qasa2, can dae suka miqe sukaje suka gaisa da amarya da ango suka dawo, ananma sun kwashi en kallo dan ba qaramin yaqar mutanen sukaiba daga mazan har matan.
Wasu daga cikin friends din nasu sunzo sun gaisa yayinda wadanda sukeji da nasu kalar girman kan sukai banza dasu.
Kida mai tashi akasa a wurin bikin MC ya kira amarya da ango suka cashe dakyau, hindatu ta dauko purse dinta ta miqe ta shiga filin rawar, ga mamakin kowa kudine en 502 sababbi gall 2 ta dinga liqawa aiko gurin ya dauki sowa sosae wasu daga cikin abokan angon suka rufeta da yayyafin kudi,Aiko M.C ya dinga kurantata en baqin ciki suna harare harare, ganin abun yaqi qarewa yasa Aysha tashi ta janyota suka koma suka zauna.
Qasa 2 Aysha take cewa wato dan iskanci kudin ankon habeeban kike liqewa koh? Wani qayataccen smile Hindu ta saki har saida dimples dinta suka fito sannan tace haba Aysha sae kace baki sanniba, wannan abun da nayi ba qaramin kankarowa kaina mutunci nayi ba, dubi yadda su zuby suke harare2 kamar idonsu zai fado.
Ta gefen ido Aysha ta kalli bangaren dasu zubaidan suke ta fara dariya qasa2 tana cewa mutum ba ido ba yace zaiyi dariya.
Suna cikin hirarne wasu abokan ango suka qaraso gurin da sallamarsu.
Aysha ce ta amsa dan Hindu gefe tai da kanta tana kallon yadda biki ke gudana.
Dan Allah en mata idan bazaki damuba kidan ara mana friend din taki mana akwai maganar d zamuyi da ita.
Nan danan Hindu ta tsuke fuskarta sosae dama Aysha ta tsammaci hakan sai tace mlm kayi haquri qawata kurma ce bata magana.
Cikeda rashin yadda suke kallon Aysha dayan yace amma kuma ya akae ta gane an saka kida har taje tayi
an saka kida har taje tayi liqi?
Murmushin yaqe Aysha tai tace mlm ae tanajin mgn mayarwa ne bata iyawa.
Murmushi guy din ya saki yace aeta kwana gidan sauqi wlh indae tana sona a shirye nk zan aureta a hakan.
Dariya ce ta matso Aysha Hindu tai saurin taketa da qafarta aeko ta hadiye dariyar zatai mgn guy din yace ba saikince komae ba numbern ta kawai zaki bani.
Sum2 Hindu ta miqe ta fice daga hall din suka bita da kallon mamaki zasuyi mgn wayar Aysha ta fara ringing, miqewa tae tace musu tana zuwa tabar gurin da sauri tana amsa kiran kamal da yake ce mata yazo.
A bakin gurin suka hadu da Hindu babu bata tym suka shige motar kamal Aysha tace Hindu zamu fara saukewa a gidansu.
Qarfe 8:15 baffa ya dawo daga masallaci hannunsa riqe da carbi yana lazimi ya zauna a falo yana kallon labarai umma ta shigo. Sannu da shigowa tayi masa ta samu guri ta zauna ta fara qwalawa hindatu kira. Hindu!! Hindu!! Fito ki daukomin kulolin abincin baffanki a kitchen. Shiru taji ta qara maimatawa dan haka ta tashi da kanta ta shiga dakin ta fara laluben Hindu amma taga wayam hakan ya bata tabbacin hindatun ta tafi gantalin data saba.
Fitowa tae da kanta ta kwaso kulolin ta dire gaban baffa ta fata serving dinshi yace ina hindatun take?
Ban ganta ba, babu mamaki ta tafi yawon gantalin data saba.
Cike da takaici baffa ke kallon ummi! Ke wata irin uwace da erta zata fita bata saniba! A garin gaba 2 muke? Haba da Allah! Masipa sosae baffa yakeyi ta inda yake shiga batanan yake fitaba saeda ya kwashi kusan minti goma yanayi sannan ya juyo ya kalli umma yace safiyyah dakefa nakeyin magana.
Wani malalacin murmushi umma ta saki ta kalli Baffa tace yallabai me kakeso nace mk? Sanin kanka ne idan hindatu tayi niyyar fita dole saeta fita ko kaine a gidan nan. Nagadai ba daureta zanyi a gefen zanina na dinga yawo da itaba, kuma hindatu bawai yau ta fara gantalinta ba kuma nida kakemin masipa bawai fa nice hindatu ba
DOWNLOAD BELOW 👇