SHAGALTATTUN DUNIYA CHAPTER 1 BY MOMYN YUSIF
📲-“Umma wai don Allah TALAUCI LAIFI NE? ban san me yasa duk inda muka shiga ba an dinga tsangwamar mu da kyarar mu.
Allah fa shi ya kad’d’ara mana zama talakawa kuma ba don baya san mu ba.
Shiru Umma tayi ta na saurare na kafin tace.”Ummi Allah shine yarzuqu man ya sha’u idan yaso ya azurta ko ya talauta.
Ko ya jarrabeka da tsananin kyawo ko a kasin hakan wannan duk kad’an ne daga cikin ikon sa.kar wannan ya dame ki Ummi ki sani Allah badan baya san mu ba yayo mu a haka su kuma masu arzik’i ba dan yafi k’aunar su ba yayo su a haka ba.
Domin kuwa ki stani arziqi ba komai bane
Shima yana daga cikin jarabawar da ubangiji yai wa d’an Adam.
Inda Arziqi wata aba ce mai daraja.to da Allah ya ba annabawansa.Musamman manzon Allah (SAW)
Ki duba kissar Annabi Musa (As)tunda yazo duniya bai tab’a jin dad’i ba har ya koma ga ubangijin……………To jikar malamai….irin haifar ‘Yaya mata.
“Yaya mata ko wahala. ‘yayan da zaka zauna sai dai kai kai ta fama n wahala da su.
“Yanzu yadda nake kafinntar nan babu yadda za’ayi in samu mai koda buga min k’usa.ni wallahi banga amfanin haihuwar ‘ya’ya mata ba.
Su zo ma su girma kai da ka haife su bnja lallai ka mora ba sai dai ka kuma wata wahalar ta siyen gado da katifa.
Mahaifina ne tsaye yake ta faman fad’a shi kad’ai a tsakar gida.
Umma tayi shiru ba ta re da ta ce mishi uffan ba. to abu ne da mun riga da mun saba da irin wannan halin nasa ba bak’on abu ne a wajen mu ba.
Kukan Amira ya katse shi daga sababin da yake.
” Da sauri na k’arasa i zuwa gare ta tare da ruk’o hannunta.
“Amira Lafiya?
Anty Ummi an kore a daga makaranta saboda ban biya kud’i ba.
Dafe kai mu kayi ga ba d’aya, hankalin Umma ya tashi sai ma ni da na yi jatumtar lallashin Amira.
Baba ya ju yo ya dube mu, ” An kore ki makaranta?
Ya kyal-kyale da dariya kafin yace, “Kinga ba cin bak’in hali irin na uwar ku da a ce ita wata ce da sai ta ri k’a yi miki a wara a k’ofar gida ya fi ye muku wannan banzar makarantar da banga amfanin ta ba.
Umma ta juyo ta zuba mishi ido sai kuma ta girgiza kai ba tare da ta kuma ce wa uffan ba.
Fakam-fakam ya sa b’i takalman sa yana sababi ya fice.
‘Daki Umma ta kira ni Tace. “kinga Ummi maza jeki gidan Hanne dillaliya ki ce ta zo taga gado na ko zata siya.
Shiru nayi ina d’an nazari daga bisani nace.” Umma ki sani fa a halin yanzu gadon nan shine kad’ai ya rage miki taya zaki siyar da shi? Duk wasu kayan ki na d’aki sun k’are a dalilin mu ya rayuwa zata yuwu a haka Umma………hannu ta saka ta rufe min baki tare da cewa.”Umarni na baki ba shawara ba.Maza tafi aiken da nayi miki.
Badan rai na ya so ba na fito waje.
A wata majalissa nan ne inda na tarar da mahaifina zaune a majalisar, wacce ko wa yasan dubinnan ‘yan caca ne zazzaune a wajen wanda Baban nawa ya kasance d’aya daga cikin su wanda har kawo yanzu babu abinda cacar ta amfana masa.
“Ummi “Ke Ummi maza zo nan.gantalalliya yawon ta zubar d’in za’a ne.hhhhhh!na san tsiya irn ta uwar ki har yanzu kila bata samar muku d’an abinda zaku ci ba ko?
Wasu zafafan hawaye suka k’araso zubo min a fuska “Wai wai wanda ya kasan ce jigo uba a gare ni shi ke jifa na da miyagun kalamai irin wannan. Hawaye na soma yi shaaa! tsaye nake bai bani umarnin tafiya ba kuma na tabbata haqiqa da na sake na tafi, ba tare da ya bani umarni na tabbata sai ya wulaqanta ni wulaqnci mafi muni.
Hasken wata dalleliyar mota ne ya haske min ido. duk da cewa rana ce amma hakan bai hana da ka qura ma motar ido ta kashe ma ido, da gani ba tambaya motar sabuwa ce dal.
Mamallakin motar ya fito.duk kafatainin jam’amar majalissar tafi suka hau yi.
Sai kayi Alh.Mika’il Duniya dad’i
DUNIYA DA’DIshine inkiyar sa.
Daga cikin masu sara mishi harda mahaifina, Abin haushi abin baqin ciki zube wa mahaifina yai qasa ya dage yana ta zafga mishi kirari…ko da na had’a ido dashi tsawa ya daka min zaki tafi koko sai nayi kutuball da ke ‘Yar shegiya.
Idon Alh.Mika’il Duniya dad’i Kur!a kaina.
Na juya da nufin tafiya naji ya ce.”Dakata.
Yammata ina zuwa haka?
Banza nayi na zo da niyyar tafiya ta.Sai dai kuma tsawar da naji mahaifina ya daka min had’e da Ashariyar da ba lallai kaji mutum mai ilimi yayi ba. yasa ba arziki na tsaya cak!
Mika’il Duniya dad’i ya juyo yana mamakin.
“Me yasa shi da yai min magana banji ba amma karon farko ya ji Kwakis(sunan mahaifina da ‘Yam majalissar ke ce mishi)
Shi ya a kayi yai min magana naji?
‘Yarsa ce fa! Wani daga cikin jama’ar dake wajen naji ya Ammbata.
Wata irin dariya naji Alh.Mika’il ya b’ab’b’ake da ita.kana daga bisani ya kaiwa Babana duka yana cewa. “Shege K’wakis.” Ashe kana da d’ank’walwliyar kaza haka, kak’i saka mana ita a gasa?.
Da ka saka mana ita na rantse ba k’anana kud’ad’e zan saka ba musamman idan na ga k’irar jikinta.
“Ke zo d’an cire hijab d’in naga yaya zuben ki yake?
Abin baqin ciki na bud’e baki da nufin bal-bale Alh.Mika’il da musifa.sai me?
Wata gigitacciyar tsawa mahaifina ya daka min wacce ta razanani ” Za ki cire hijab d’in ya ga k’irar jikin naki ko sai .nayi kutubal dake?”……………..
__________Kiraye-kirayen Sallar azahar ya karad’e unguwar gaba d’aya.Haj.Kubra ta fito waje a domin d’auro Alwala.
Sai me? Tana dosowa sa shen Sumayya.
Kide-kid’e da ya tarwatsa kunnuwanta.shi ya d’aure mata kai wanda har bakajin kiran sallar da ake rangwad’a wa a cikin unguwar sam illah karar kid’an kamar gidan DJ.
Dif!Dif!!.duk da cewa sa shen nata da na sumayyar A kwai ta zara sosai.
K’araso wa tayi cikin sauri. Ta isa d’akin.
Sumayyah ta gani, daga ita sai brea.tasha tayi mank’as ta fita daga hayyacinta.sai tiqar rawa take kamar mahaukaciya.
Zare soket d’in Haj.Kubra tayi, cikin takaici da baqin ciki take duban ‘yar tata Sumayya.
A zafafe Sumayya ta juyo tare da danna wata iriyar a shariya……sai dai ganin Haj.Kybra da tayi ya sata kasa qarasa cewa uffan.
“Haba Mum! Why, why?Ki ke min haka.kina takura min sam kin hananin wal-walata Mum…
Mika’il DUNIYA DA’DIya turb’une fuska kamar kashin shanu yana duban Haj.Kubra.tare da nuna ta da d’an yatsa manuni.
“Ke yanzu Kubra duk gargad’in da nake miki akan Summy bakyaji? “Wallah, “Wallahi da a ce ba ke ce ki ka haifi Summayya ba, da tuni nayi waje dake na rasa irin wannan tsana da kike mata.”Shin me ta tsare miki ne?
“Uhum Alh.Kenan “na rantse da girman Allah hanyar da ka ajiye Sumayyya ba me b’ullewa bace.ta ya kana matsayin mahaifinta ta zo a ga banka da u sani Summy BABU TALAUCI a gidan ku a kwai ‘Ya’yan talakawa da dama masu son dama irin taki su fantama, ba su samu damar ba ta ya ke Allah ya baki ba zaki yi Amfani da itaba.?
“Ki huta Babyna ya fad’a tare da d’aukar ta cimak ya a za saman gado ya jawo bargo ya rufa mata yace.”I dan kin tashi barcin kyaje kiyi sallar.
“Ke kuma ya juyo ga Haj.Kubra.Muddin ki na san zaman Lafiya ki fita harkar Sumayya ki barta ta sarara gidan mahaifin ta take rayuwa idan bata ji dad’i a nan ba ina zataDUNIYAd’i?
” Don haka gargad’e me zafi muddin ki ka kuma takura wa Sumayyah wallahi ni Alh.Mikai’l sai na d’auki mataki mai zafi a kanki duk da cewa ke ki ka haife ta, Fakat!.
Kuka na saki mai zafi na takaici da baqin cikin wannan rayuwa.”Wai mahaifi na wanda ya kamata a ce yafi kowa sanin mutunci na shine tsaye a gaba na yana tirk’a ta a kan na bud’e kyakyawar surar da Allah yai min a gaban wani k’ato.wanan wacce iriyar rayuwace?
“Ke wacce irin banzar yarinya ce mai kalar hali irin na uwarta?” Don ubanki arziki na kiran ki tsiya irin ta uwa ta hana, ki cire hijab idan komai yai ma Alh.Mikai’l zam zam kinga ai uwarki ta huta kwana da yunwa ya fad’a ya na b’ab’b’e baki yana dariya.gaba d’aya wajen ya d’auki sowa kowa yana dariya.banda Alh.Mika’il da hankalinsa ba ma waje na yake ba yana chan ya lula izuwa wata duniya sabo da , koda ban cire hijab ba, ba kowanne namiji ne zai iya yi min kallo d’aya ba ya kauda kai,mn
.. bare Mika’il da kamar bunsuru yake idan yaga mace……tunani na ya tsaya dai dai lokacin da naji kututturen hannun mahaifina a jikina ya na qoqarin yaye min hijab d’in dake jikina, yana duban Alh.Mikai’l yana fad’ar Alh.Matso ka gani tayi maka?Amma ina Alh.Mikai’lu ya shiga duniya ta daban wanda ya ma kasa tantance waye ke magana.
Ni kuma takaici da bak’in ciki ya hanani koda motsi wanda kuka nake sosai wanda duk wanda ke wajen yana jin sautin kuka na amma babu wanda ya kula illah dariyar su da suke ta faman yi.”Oh! Duniya ina zaki damu?”Ya Allah ka kawo min d’auki Allah kawo wanda zai a gazamin “Wanne irin mahaifi gare ni ni “Ummi?wanda ko a fin ko Hausa novel ban tab’a jin irin sa ba.
“Subhanallah!Subhanallah”
Sautin wata zazzak’ar murya na tsinkaya ya doso wajen da muke.d’aga kai na da zanyi nayi katari da wani kyakkyawan saurayi a jin k’arshe.
Ruqo hannun mahaifina yai yana fad’ar, “Haba Malan meye haka?
Wani d’an tsomololo ya taso cikin tawagar su Baba na ya riqe hannun kyakkyawan saurayin yana cewa ” Malan ina ruwanka?
Mahaifinta ne fa.
“kai k:arya ne.” Don Allah ku kyale yarinyar mutane me tayi muku.
“To idan kaji k’arya ka tambaye ta.
Ido ya zuba min qur!” Da gaske shi d’in mahaifinki ne?
Kai na d’aga mushi alamar “Eh”
Ja yai da baya cike da mamaki.da kuma tsoro da Al-ajabi…