SILAR AJALI CHAPTER B

 SILAR AJALI CHAPTER B

ALKAWARIN ALLAH

Sati biyu kawai aka kara kafin a ɗaura auren Imran da Rahanatu.  Ba’a yi wani shagali ba amma cikin sati biyun nan baba (mahaifiyar Haroon) ta kintsa ta da duk wani abin da ta san na gyaran jiki ne.  Fatar ta ya sha lalle don sati tayi tana Wanka cikin ruwan lalle. 

Mata ke ta shiga da fice wanda mafi yawansu yan uwa da makota ne da Baba ta gayyata.  Bayan sallar isha’i aka ɗauke ta zuwa ɗakin da aka ware ma Imran a cikin gidan.  Tana kuka inna mairo kanwar baba ta riko ta. Faɗi take “shiga da kafar dama kina mai ambatar bismillah”  haka suka shiga ɗakin da ya sha daɓe da fentin farar kasa.

Anyi kwanan amarci, amare da kawayenta, wa’inda duk kawayensu laminde ne. Washe gari daga cikin gida aka kawo masu abin kari, da kuma na rana,  bayan nan ne aka yi buɗan kai.  Da dare abokan ango suka shigo aka siya baki kafin a watse a barsu. Nan ne fa maganar kurame ya tashi don daga ita har shi ba wanda ke jin yaren wani.

Da safe baba ta tada su,  nan ta fito da farar zanen da basu san da zaman shi a ɗakin ba. “kwanta kar ki kuskura ki fito ɗakin nan,  mutuncinki zan nema miki a unguwar nan” Ta faɗi cikin raɗa.

Guɗa ta saki sanda ta fito daga ɗakin. Nan makota da sauran yan biki da basu tafi ba suka yi tururuwan shigowa. Da sauri matar megadi ta ɗaga zanin don ta tabbatar ma wainda ta ba labarin Rahanatu gaskiyarta amma sai aka samu abin da ba ta taɓa tunanin zata gani ba,  take ko ta furta “jini”  Sai kuma ta tuna tayi saurin kama bakin ta.

Nan fa gaɗa ya tashi, mata sai rera mata wakokin yabo suke, nan aka haɗa mata ruwan wanka na musamman, baba ta shiga ta chuɗata. Da zasu fito ta rungumo ta,  ita kuma ta langwaɓe kamar mai ciwo dagaske.2

“Yarinya kin zama babba,  haka duk wata ya ta gari da ta mika ma mijinta mutuncin ta ke ji,  Ubangiji Allah ya sa wajen zamanki ne,  yasa abokinki ne ya tona asirin darare” faɗin wata dattijuwa tare da mika turmin atamfa mai igiyar shanya.  Daga nan mutane su ka yi ta mika mata kyaututtukansu ana shi mata albarka.3

                           ****

Cikin wata uku da aurensu Rahanatu tayi ɓul-ɓul abinta, ta kara haske da cikowa.  Sa kanta da ta yi wajen koyon larabci ya sa take tsinta,  takan fahimci yaren amma maidawa kanyi mata wuya. Sun kasance karkashin gandun Mahaifin Haroon. Amma ta kan fita tare da su laminde su yi aikin wanke wanke da shara acikin gidan.

Duk zaman su babu abin da ya gitta tsakanin ta da mijinta sai dai duk wani kulawa da ake ba mutum ya zama ɗan gata tana samu hakan yasa ba ta san lokacin da son Imran ya shige ta ba, ta wani gari ne kawai ta tsinci kanta cikin halin matsanancin sonsa. Babu abin da tafi so sama da kasancewa tare dashi yana koyar da ita duk da bai sa wani isasshen lokaci don ya fara aiki a jami’ar Bayero da ke garin na Kano amma hakan yake sama maia lokacin karatunta. Hakan ya sata kara jajircewa wajen son koyon ilimin addini Dana boko.

                          ***

A Kwana a tashi ba wuya wajen Allah,  shekara ɗaya da auren Rahanatu kenan, hankalinta da na mijinta kwance suna masu kaunar junansu, tun bayan da ya samu aiki ya saka ta a firamaren matan aure ta higher islam take zuwa. Idan tana larabci sai ka rantse balarabiya ce haka in tana hausa ba ma zaka sa ta  jerin masu jin wani yare banda hausa ba.

Yau ma kamar kullum ya dawo bayan sallan la’asar, tankaɗe take a tsakar gidan suna hira da laure (kanwar laminde)  wacce ta kasance abokiyar aikinta tun bayan da aka wanke laminde.  Da sallamar sa ya shiga,  suka amsa masa  tare

  “marhabanbika ya rafiqie”  Ta faɗi tana murmushi. 

“Kaif” yace da ita yana kefta mata ido ganin yanda laure ta saki baki tana kallonsu. Bai jira amsar ta ba ya wuce ɗaki.

“ni ko Larabawa basu da kunya da tsare gida,  ji yanda yake wani kashe miki murya da murmushi.  Ai sai ki raina shi” faɗin laure wacce bata taɓa gani tayi shiru. Murmushi kawai Rahanatu tayi, ganin bata da niyyar bata amsa sai ta cigaba

“ko a musulunci ai kunya wajibi ne,  ku ba kwa ko kunyar a san mata da miji ne ku,  ba kwa ganin juna ku kauda ido, abin takaicin ma da yaren da ba mu ji kuke yi” dariyar  da Rahanatu ta yi ne ya tsayar da ita.

“menene kunya a aure in har za’a haihu iyaye da kowa yai murna,  ke ni raba ni don Allah,  miji na ne kuma Lada nake nema ta yi masa murmushi shima in ya min lada zai samu.  Raini kuma da kike magana mace mara tarbiyya babu abin da miji zai mata ta ki raina shi.  Ni zan shiga wajen shi ki karasa tankaɗen” Ta karasa tana mai kakkaɓe jikinta sannan ta wuce ɗakinta.

Nan ma wani sabon gaisuwa tayi masa, maimakon ya amsa ɗaga ta sama yayi yana zagaye da ita.  Sai da ya gaji ya sauke ta ya rungume yana sumbatarta ta ko ina

“mun samu gurbin karatu, zan yi doctur (PhD)  in na je sai in samo miki ighama (resident permit)  da kuma makaranta inda za ki yi sakandire ɗinki.” murna ya cika ta don cigaban da mijinta ya samu.  A wani ɓangaren kuma gabata sai faɗi  yake don basu taɓa nesa da juna ba.

Murnar ta bayyana tare da kwararo masa addu’a, nan ya shiga nuna masa takardun tafiyarsa da aka turo masa.  Yana mata bayani wasu ta gane wasu kuma bata fahimtar abin da yake nufi.

“Amma zamu je Sudan kafin ka koma karatun ko, ka ga wancan karan kai kaɗai ka je ya kamata a sanni” Ta faɗi gabanta na faɗi don ta san zancen da ya fi tsana kenan.

“ban sani ba ko ku a al’adanku an amince ma mace ta tambayi namiji dalilin yin abu ko ta umurce shi da yin abu, mu dai a Sudan ba ma haka” Ya faɗi  a hankali amma duk fara’ar da ke kan fuskarsa ya ɓace ɓat kamar anyi walkiya an ɗauke.

Durkusawa tayi tana rokon gafararsa,  tsoron ta ɗaya Fushin miji don malamin su yace ko sallah miji ya hana mace tayi ransa ya ɓaci ta mutu bata nemi gafararsa ba toh wuta zata shiga.  Shafa kanta yayi ya fita ya barta nan durkushe.

                             ***

Sati ɗaya ya kara ya gama haɗa komi na shi na tafiya sannan ya wuce. Tafiyar da ya sa Rahanatu zama shiru shiru,  kewan mijinta ke damunta duk da ya tabbatar mata da watanni kaɗan zai yi ya haɗa mata komi na tafiyar ta itama.

Cikin ikon Allah wata shida kawai ya ɗauka ya gama haɗa komi nata na tafiya.  Ko da ya dawo duk sunyi murna da ganin junansu.  Sai da suka ke ɓe sannan ya ce da ita”lafiya kika rame kikayi baki Rayhan?”  maimakon ta amsa sunan da y kira ta da shi yasa ta jin Daɗi sosai, don ta san shaukinta yake shi yasa ya laka mata suna

“sunanki kenan dashi na miki duk wani rajista, Rayhan T Imran. Hakan zan dinga kiranki don ki saba” Ya ce yana murmushi.

Shirye shirye take yi ba kama hannun yaro,  ta zazzaga mako ta Da suke shiri tayi musu Sallama saboda halin rayuwa.  Ko da ranar tafiyar su ta zo da kuka ta rabu da su Baba don kuwa gani take ta rabu da wani sashi na jikinta.  Karfe na tara na dare jirginsu ya tashi sai Kasar Saudiyya.Cikin nasara suka isa birnin Yambu, (yambus sana’iyyah) cikin ikon Allah bata kara sati ɗaya ba ta samu makarantar kulliya. Duk da ta ɗan samu matsala da farko amma da jajircewa da naci sai gata tana fahimtar karatun sosai.

Sannu a hankali ta fara wayewa,  nan ta gano da yawa daga cikin abubuwa da malaman ta na islamiyya ke faɗa musu na biyayya ga miji al’ada ce ba addini bane, kuma sun ci karo da addini  musamman ta fannin saɓa ma Allah don a faranta ran miji. Nan fa ta gane aure ibada ce,  bautar Allah ce ba bautan miji ba,  an shar’anta ma mace yin ma miji biyayya ne matukar ba wajen saɓon Allah ba ne.  Sannan mata ma na da hakki akan mazajensu kamar yanda maza ke da hakki akan su.  Duk ta zauna sai tausayin yan uwanta mata da ke Afirika ya cika mata kai don ana cutar su da sunan Musulunci,  ana tauye musu hakkin da musulunci ya basu a hana masu neman ilimi don kar su san musulunci yayi su yan gata ai ta azabtar da su. 

Ranar da aka koyar da su Darajan mata a musulunci na cikin ranakun da tai kwanan zubar kwalla.  Don ko ita ta kasance cikin wa’inda rashin karatun addini ko Ace juya al’ada zuwa addini ya shafa.  Hadi ya mata fyaɗe,  ga laifin zina akansa ga na fyaɗe amma duk aka barshi ya sha don shi ne mutum ita mace ba mutum bace. Tunanin girman Manzo SAW take da yanda yake shawara da mata kafin ya aiwatar wasu ayyuka nashi ciki kuwa har da abin da ya shafi jihadi. Ta kara auna darajar annabi,  taga ba’a yi ba kuma baza ayi wanda ya kamo kafarsa a daraja ba amma duk da haka yana shawara da matayensa ai sai ta ga lallai ko dai mazan Afirka basu da ilimin addini ko suna take sani wajen ba mata addininsu abin takaicin ma juya shi zuwa musulunci ya ce da suke yi.+

Ko da aka taɓo rayuwar mata sahabbai sai ta ga matan Afirika na kokarin kwatanta  biyayya ga miji sai dai garin son mallakar miji sai suka saka gaggawa a ciki hakan ya sa suka fara biyan yan 419 da sunan malamai wajen neman biyan bukata. Sukan manta addu’a da ibada a lokutan jin Daɗi sai matsalar aure ya taso su sai su fara biyan bokaye da yan bori suna neman taimako su kuma su damfare su.2

Haka dai tayi ta fahimtar abubuwa tana kara samun ilimi, nan rayuwar su ta kasance abin sha’awa abin jin Daɗi,  sukan yi duk wani nau’i na ibada don tsira tare gobe giyama. 

                            ***

Tana ajin karshe kulliya ta samu juna biyu,  murna wajen su ba’a cewa komi.  A shekaran ne kuma Iran ya samu aiki a jami’ar Tabouk. Ba tare da ɓata lokaci ba suka sake yin ighama suka koma can da zama.

Bayan wata tara ta haifi ɗan ta santalele mai kama da Ubansa, nan suka raɗa masa suna Salman.  Rainon Salman ya jinkirta mata komawa makaranta don ta so komawa ta haɗa digiri ɗinta.  Tana yaye Salman kuma ta sake samun wani cikin wanda ta haifi ya mace mai kama da ita. Wacce ta ci suna Salmah

Tun bayan haihuwar Salmah bata sake daukar ciki ba sai da Salmah ta yi shekara biyar  duniya.  Cikin sai ya zo mata da kasala da rashin son wanka.  Kasancewar wannan ne na farko da ya zo mata da matsala sai ta saki jiki maimakon ta daure ta dinga gyara.  Kafin a ce me ta zama kazama ta ajin farko.  Daga haka Imran ya dena zama gida,  ya fara kula mata tukari musamman yan Kasar Ethiopia da abin da ya kai su kenan.

Wasa-wasa y daina kula da hatta abincin da zasu ci. Sai da yake ta samu karantar da yaran shugaban jami’ar (lesson tutor)  sai take amfani dashi wajen kula dasu.

A tunanin ta bayan ta haihu abin zai canza amma ina ko bayan haihuwar Suhayl ba abin da ya chanza sai ma karuwa da yayi. Kullum addu’a take yi amma hakan bai chanza ba, anan ne ta shirya zuwa umra don ta kara rokon Allah ya shirya mata mijinta,  don lokacin kawo wata gidan yayi ya ajiye kamar matarsa kuma tana buɗe baki tayi magana zai ce in bazata iya zama ba ta tafi.

A wajen ɗawafi ne ta haɗu da Amina da mijinta wani ɗan majalisa ya biya musu. Tayi murna kwarai da gaske,  sun yi hira sosai na bayan saduwa sannan suka rabu bayan ta amshi lambar teleho din makotarsu amina.

Ganin abin na shi ba na karewa bane  bayan ta yaye Suhayl har ya shekara uku ya sa ta kira Amina ta tambaye ta ko zata iya rike mata Yaranta.  Ta ɓoye mata halin da suke ciki sai ce mata tayi rayuwar Saudiyya da tsada. Amina na amincewa kuwa ta shirya musu tafiya ba tare da Imran ya sani ba.  Ba shi ya ankara da rashin su ba sai da sukayi wata huɗu a Nijeriya. Nan ya sa mata bala’i da masifa akan sai ta bar masa gida ta nemo masa yaransa.  Ta na faɗa ma matar shugaban makarantar aka sama mata boys quarters take zaune da gurbin karatu a jami’ar.

                          ***

“Hmmmn!  Tayi ajiyar zuciya bayan ta gama tunanin rayuwar ta.

“gida zani,  in na je su kashe ni” Ta faɗi tana mai mike wa daga kwanciyar da tayi.

A watannin da su Salma su ka yi a marke sun saba da rayuwar chan.  Basu da wata matsala don Goggo bata bari su fita ko ina daga makaranta sai masallaci ga mazan. 

   Yau ma kamar kullum sunyi gungu suna tafe suna hira,  tasowar su daga makaranta kenan.

“Wai Salmah shike nan baza ku koma Saudiyya ba kenan?  Ni fa in ni ce uwata da Ubana ke wata Kasar toh bazan zauna ba.  Taɓ!  Chan fa an ce ya haɗu ba kamar nan ba.” Ummitr ta faɗi wacce dama kullum hiran ta Saudiyya, don bata da buri kamar shiga jirgi.

“Taɓ ba sai mutum na da uba bane zai je,  ai in shege ne haka za’a turo shi gudun yai rayuwar tukari” karaf farida Farha ta ce don da ma abin ya daɗe yana tsingulinta tun sanda Amma mai hura ta shigo ta  faɗa ma innarta cewan su Shegu ne.

Ummitr ta cire Hijjabinta ta ɗaura a kugu, ta tura ɗan kwalin ta zuwa gaba,  tayi tsalle ta chakumo rigar Farha, 

   “me kika ce,  yau sai kin faɗa mana inda kika jiyo”  faɗin Jiddo tana mai make ta a keya,  rufaida kuwa ɗebo kashin shanu tayi ta nufi bakin ta zata sa mata.  Nan fa ɗalibai suka taru  a wajen Salmah na kuka  ita ma Farha kukan take tana mai basu hakuri.  Se da suka yi mata ligis kafin suka kyale ta suka nufi gida.

Su ummitr na tsaka da cin abinci Zulai ta shigo da masifanta.

“Akan wani dalili ne  zaku yi ma Farha irin wannan cin zalin, ko dan kun ga ita kaɗai ce za ku zo ku yi mata taron dangi.” Ta faɗi tana jan kunnuwan Umitta da Rufaida da ke cin abinci.

“Wayyo!  Wayyo ni Allah na kunne na zai tsinke” ummitr ta faɗi da iya karfin ta.  Hakan ya fito da matan gidan

“lafiya Auta me ya same ki” faɗin hajiya babba, watau kakar Rufaida.

“Hajiya kya ce haka mana,  ai ku ke ɗaure ma ta gindi take ma duk wanda ta so tsaurin ido.  In ban da haka  ina ita ina dukan Farha, ai ko a girme ta girme ta” Ta faɗi tana haki ba tare da tayi la’akari da tsufan hajiyar ba.

“da yake ma ita sakarai ce sai ta zauna karamar yarinya kamar ummitr ta taɓa ta. Toh Wallahi akul ɗinki,  malam amanar ta ya bar mana ba zamu bari a zalunci marainiyar Allah ba” faɗin Indo mabi da hajiya babba.

Nan zulai ta fara gunguni don dai a haife duk sun haife ta, tsabagen son Yaranta ne kawai da ya mata yawa yasa ta tsallako ta zo rama ma ɗiyarta.

“Wai me ya faru ne,  zulai ai ba haka yaci ki yi ba, duk su duka abin ki hukunta su ne,  Farha, jiddo da Rufaida dai duk yaranki ne,  ummitr kuwa kanwar ki ce.  Amma fa in da kara” faɗin Habi mahaifiyar Ummitr kuma wacce tafi sauran sanyi da hakuri.

“fitsarar da ta saba zata mana, in ban da rashin hankali har ke ce zaki taɓa uwar Malam, duk da kasa ya rufe idanunsa ai butulu ne mai manta alkhairi ” Faɗin hajiya babba tana mai barin wajen gaba ɗaya.

Itama zulai bata ɓata lokaci ba ta ja tsaki ta bar sauran matan a tsaye.  Nan da suka fara cecekuce akan halin ta na rashin girmama manya.

                             ***

Tun da aka yi wannan, maganar bai sake tasowa ba har suka kammala ajin aka tafi hutu.  Nan aka fara azumi kuma wanda hakan yai daidai da hutun da suka samu a islamiyya. 

    Sam azumin bai wani damunta. Saboda da rana sukan je tafsiri da su Rufaida duk da su ne yan samun baya,  su kafa chafta duk wanda ya gitta sai anyi da shi.  Daga baya suka tsiri karanta littafan soyayya.2

Sallah na da saura kwana uku an rufe tafsiri suna hanyar komawa gida suka yi karo da wani a mota kirar Honda civic, gilashin motar baki ne kirin,  ko da suka iso kofar gidan sai mai motar ya yafito su, nan suka kalli juna ita da su rufaida.

“Muje in mun ga alamun mai Satar mutane ne sai muyi masa ihu”  faɗin jiddo ba ko alamun tsoro a tare da ita.

A hakan suka karasa da sallamar su.  Bakin gilashin da ke sanye a idonsa ne ya sa suka kasa gane fuskar sa ko da Ace sun san shi.

“Sako ne daga Saudiyya,  gashi RAHANATU ta ce a kawo ma su Salman, na cikin bakin ladan nan shi ne na goggo salame.  Tace a ce tana gaishe ku duka zata zo nan ba da jimawa ba” cikin saurin murya ta faɗi sakon nan da nan salma ta amsa.

“Don Allah ka ce mata mu aminan Salma muna gaishe ta,  ni Asmau umkitr,  sai Hauwa Jiddo sai Rufaida,  don Allah kaji baba,  ko kaine Baba Imran” Ummitr ta faɗi kallo ɗaya zaka mata ka san tana cike da farin ciki kila ma fiye da  Salma.

“Bara mu kira maka goggon ku gaisa” faɗin rufaida ganin sauran duk sun ruɗe.  Ai ko haka suka dunfari gidan da gudu suna haki suna faɗa ma goggo salame, amma kafin su fito babu shi babu alamun sa sai ma dai shaidar taya.

“kai ko dai aljanni kuka gani,  in ba haka ba Ace sako tun daga Saudiyya amma bai tsaya an gaisa ba” goggo ta faɗi tana mai daura hannu a kirji.

“Aljani  kuma goggo” suka tambaya a tsorace.

“Eh ko kuma ɗan shafi mu lera ba, ku wuce mu je gidan yaya kafin a buɗe  don ba zan buɗe  in ɓace ba” Ta karasa tana mai jawo kyauren gidan nata. 

                              ***

“Hmmmn!” Ajiyar zuciya yayi bayan ya sauka daga kan titi.

   “Ta ina zan wanke kaina in nemi gafarar ta, na shiga uku”  faɗin mutumin nan yana mai cire tabarau da saukar da gilashin motar, gumi ke keto masa duk da kasancewa akwai sanyi sanyi kasancewar damina ake.

Fari ne ba chan ba,  sai dai kallo ɗaya zaka masa ka san cewa baya tare da wahala. Sai dai wani ɓari na fuskar sa na nuna damuwa a tattare da shi.

Akwai abubuwa da dama da suka zame masa “bakar kaddara”  wanda in da za’a tambayi burinsa bai wuce Ace ya sa kilina ya shafe shi ba ko ya wanke kamar yanda ake wanke datti a tufafi.

    Jan motar yayi ba shi ya tsaya ba sai a garin Gusau,  tafiyar awa biyu daga kauyen MARKE. Ɗakin mahaifiyarsa ya wuce,  masu yi musu hidima na gaida shi amma ko kallonsu bai yi ba duk da ba haka ya saba yi musu ba.

“Abdoul wai mai ya sa ba zaka yarda da kaddara, mai yasa ba zaka yi yakini akan Allah ya amshi tubanka ba.  Ba zance kayi abubuwan cikin rashin sani ba, amma ka bar kuruciya ya dibe ka.  Duk ba ma haka ba,  kayi hakuri na tabbatar duk inda take tana cikin farin ciki wanda hakan kaɗai ya isa ya saka ka murna”  Ta faɗi tana shafa masa baya kamar karamin yaro.  Shekarunsa talatin da bakwai a duniya amma bata taɓa gajiya da lallashinsa ko kuma shagwaɓa shi. Duk da kasancewar sa ɗan ta na fari.5

Ajiyar zuciya ya ke saki,  hawaye masu zafi na kwarara daga idanunsa.  Sharewa tayi da tafin hannunta,  ta tashi ta ɗebo ruwan sanyi ta bashi ya sha.  Nan ta sa masa “LAA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAL ZALIMEEN”  a bakinsa yana maimaitawa. Sai da ta ga ya fara samun natsuwa sannan ta tashi ta je ta cigaba da aikin.Ba su zame ko ina ba sai gidan Hakimi Alh Yunusa Ladan.  Yanayin yanda suka shiga a firgice yasa matan gidan tambayar su ko lafiya.

“ina fa lafiya,  yaran nan sun jawo min jangwam” faɗin goggo zufa na keto mata ta ko ina.

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun,  Salame me ya faru” faɗin Hajiya aziza tana kallon yaran ɗaya bayan ɗaya tana neman gane yanayin da suke ciki.  Ko waccensu ɗauke take da firgici a kwayar  Idanunta.

“Gamo su kayi da aljani,  ina zaune sai gasu da murnar su wai yarinyar nan tayo musu sako daga Saudiyya,  in fito in gaisa da mutumin da ya kawo.  Ina fitowa sai na iske waje wayam. Wai kuma motar kirin ce ba’a ko ganin shi da abin da ke ciki” Ta karasa tana mai sakin ajiyar zuciya haɗe da mika ma hajiya ledar da suka shigo dashi. 

   

  Nan suka zazzage kayan, lesussuka ne da takalma masu kyau.  Da yadi na maza masu kyau da tsada. Ledan da aka sa takalman na da tambarin shago a garin jidda.  Ajiyar zuciya hajiya Aziza tayi haɗe da murmushi  sannan tace;

“Wallahi kun ban tsoro,  kila cikin sakon ne har da kada ya bari ku haɗu,  don duk kayayyakin nan ba na Nijeriya.  Sannan shagon nan marigayi Alhajinmu  na yawan siyayya a ciki.  Ke Salmah ba kuma Mahaifin ku bane”

Shiru tayi tana tunani, ita dai ta san ba zata wani gane mahaifinsu ba,  don wasu abin ma yanzu zama da su Ummitr yasa take ganewa.  Kenan kila Mahaifin nasu ya saki mahaifiyarsu ne irin na talle yayan ummitr. Tunda ita ma ance shi ya sa ya tafi birni ya barta da yaran ba ko abinci wai tana idda.

“ke Salmah baki ji bane nace ko Mahaifin ku ne? ” hajiya ta sake maimaita wa.

” ba shi bane,  amma kamar abokinsa ɗan funtua” Ta sami kanta da faɗin haka.2

“Ni sai yanzu ma na gane shi” Ta ɗaura ganin duk sun tsare ta da idanu. Hamdala sukayi sannan yaran suka fita zuwa gida yayin da iyayen suka sa Goggo a gaba suna tsokana ganin yanda ta firgice.

Shagon Ado tela aka kai ɗinkin gami da rokon arziki.  Haka ya ɗinke kayan tsaf safiyar idi suka samu.

                        Eid-l-fitr

Bayan mai alfarma  sarkin musulmi ya sanar da ganin wata,  kofofin rediyo da talabijin suka bada sanarwa,  nan aka samu mai shela ya zaga gari yana faɗi. 

  

Murna cike da ɗaukacin musulmin Kasar. Ciki har da al’ummar garin MARKE ciki har da Salmah,  Suhayl da Salman. 

Washe gari da sassafe suka yi wanka.  Nan sukayi kwalliya cikin kayan sallan su,  Salmah sanye take da bakin leshi,  mai jan duwatsu. Kayan ya fito da ita kasancewar ta fara, su salman da Suhayl kuwa yadi suka sanya mai ruwan sararin samaniya,  kafin suka ɗauki hanyar masallacin idi.

Salma sai da ta jira Aminanta suka zo sannan suka jera da goggo suna tafe suna kabbarbari.  Sun iske ana wa’azi,  bayan zuwan limami aka tada sallah.  Sannan suka tsaya huduba.  A hanyar su na dawowa ne suka ci karo da wasu da salma ba ta san su wanene ba,  ganin sun gaisa da goggo yasa suka gaishe su suka matsa gefe suna jiran goggo.3

“Wancan mai bakin leshin ce yar wajen RAHANATU?”  Ɗaya daga cikin su ta tambaya.

“Eh!  Salma kenan sauran yan uwan nata maza ne” goggo ta amsa da murmushi

“ga mutum har mutum amma shege,  Au shegun da yawa kenan aka turo miki,  aka yi ma hadi kazafi amma da yake ba halinsa bane gashi nan ta haifo ba ɗaya ba,  ba biyu ba,  Allah kadai yasan yawan su.  Kaico” Ta faɗi tana taɓe baki.

Kwaf!  Ta ji an make mata baki,  ɗagowar da ta yi idanunta ya sauka akan goggo idanunta tamkar gauta.

“kin ci albarkacin yau idi,  bazan ɓata ibada  ta da nayi kwanaki talatin ina yi ba,  amma duk ranar da kika yi gigin kiran jikoki na  da kyamataccen suna se na ci ɗammara mun ba hammata iska.” Ta faɗi tana karawa gaba tare da su salma duk rayukansu babu dadi. 2

Bayan tafiyar su mata suka taru suna maida labarin abin da ya faru,  masu son a san sun sani suka fara labarin ai karuwanci Rahanatu take a Saudiyya, wasu su ce ai Misra take ba Saudiyya ba.2

“Ni sheda ce,  Rahanatu aure tayi,  don ko da ta bar garin nan Kano ta tafi.  Akwai Haroon yaron limamin anguwar mu da abokinsa ya tsinto ta ya ce zai aure ta.  Da aka tambaye megida na sai ya faɗa musu ba nutsatsiya bace.  Nan ni ma na kara gishiri da magi amma na tozarta tozartawa mafi muni. Domin kuwa mijinta ya same ta cikakkiyar  mace,  aka yi shagali tun daga ranar matan unguwar suka tsangwame ni. Bamu iya kara wata shida a anguwar ba muka barta tsabagen tsangwama.  Naji ance mijin ya tafi karatu Saudiyya ban sani ba ko sun dawo” faɗin tabawa matar me gadi. Nan jikin wasu yayi sanyi yayin da wasu suka fara faɗin ai ta rabu da mijin ne ta fara karuwanci ciki kuwa har da Hajara matar Jamilu kanin Goggo.2

Tabawa batayi kasa a gwiwa ba taje ta faɗa ma goggo duk abin da ta sani dangane da zaman Rahanatu a Kano da abubuwan da ya faru a sanin ta da barinsu zuwa Kasar Saudiyya.  Goggo tayi murmushin murna don har ga Allah ta fara kokonto kar dai da gaske su Salmah Shegu ne.

                    ***

Tun daga abin da ya faru a masallacin idi gulma ya fara yawo a kauyen marke kan cewa su salma Shegu ne ba ta hanyar aure aka haife su ba.  Ba bu halin a gansu da yaran unguwa musamman ma dai salma iyayen zasu fara

“kar na sake ganin ki da Shegu,  shege ai kwashe albarkan ‘ya’ya yake, “4

Ko kuma su ce

” kuna biye ta Shegiyar yarinyar nan sai ta raba ku da mazajen aurenku don ita kam babu mai kwasar ta”

Hakan ya kara tada musu da hankali musamman ma goggo, nan kuma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura maTun daga abin da ya faru a masallacin idi gulma ya fara yawo a kauyen marke kan cewa su salma Shegu ne ba ta hanyar aure aka haife su ba.  Ba bu halin a gansu da yaran unguwa musamman ma dai salma iyayen zasu fara

“kar na sake ganin ki da Shegu,  shege ai kwashe albarkan ‘ya’ya yake, “

Ko kuma su ce

” kuna biye ta Shegiyar yarinyar nan sai ta raba ku da mazajen aurenku don ita kam babu mai kwasar ta”

Hakan ya kara tada musu da hankali musamman ma goggo, nan kuma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura ma Salma. Kullum faɗi ta ke

“Shegiyar yarinya mai bakin jini,  kin zama min bala’i ban san mai yasa ta saka miki suna na ba”2

Nan rayuwa yai ma salma kunci,  duk da karancin shekarunta ta san ta zauna tana tunani.  Kaɗaici yayi mata yawa,  in da abin da ta tsana yana bayan zuwa makaranta boko ko muhammadiyya don da wuya taje ta dawo lafiya.  Kawayenta ma sun daina biyo hanya da ita saboda tsawatar musu da iyayensu suka yi amma  kam a harabar makaranta suna tare da ita.  Sannan suka daina shigar mata faɗa don an hare musu kunne akan lallai da gaske ita Shegiya ce.+

                            ***

“Dalla Shegiya ki dena kallona kafin ki ɗebe min albarka, ko wani yace uwarki ta je yawon karuwanci, wa ya sani ko ba ku kaɗai bane don an ce da cikin Hadi ta bar marke” faɗin wata Hajjaris tana mai tunkuɗe Salma da tazo wucewa ta gabanta.

  “Zo nan Salmah”  faɗin malamin turancin su da ya gama jin komai.  Tun bayan dawowarshi daga hutun shekara ɗaya da rabi da ya yi ta kula ya ke bata kulawa  ta musamman don har an fara Gulman son ta yake.  Sum sum ta bi bayan shi hawaye na riga rigen gangarowa kan kuncin ta.

“me ke faruwa ne Salmah,  na kula kin yi duhu kin rame sannan kin rage zama tare da kawayenki, yanzu kuma ga kalaman er rakaɗin nan akanki me ke faruwa faɗa min” Ya na magana da gani hankalin sa a tashe yake. Maimakon  ta bashi amsa sai ta sa masa kuka,  wanda ita kanta ta san rabon da tayi irin sa ta manta don kuka ne wanda ake yayin da aka samu kafaɗan jingina akai.

“share hawayenki,  ni ma tamkar uba nake a gare ki,  ki faɗa min damuwar ki in bai fi karfina na ba zan magance miki” Ya faɗi  cikin sigar lallashi.

“tun sallar idi na bara wancan ne ake kiran mu Shegu,  a hankali har kowa ya yarda cewa mu Shegu ne,  kawaye na duk sun guje min wai ance shege na kwashe albarka.  Goggo kullum cikin hantarar mu take musamman ma ni,  gashi tun da muka zo garin nan kusan shekara uku sau biyu inna Amina ta zo,  tace innarmu zata zo har yau bata zo ba” Ta karasa tana mai kara sakin kuka.

“kai!  Je ka ss2 ka kira min Salman Imran” ya faɗi ma wani yaro da ya zo wucewa.

“ki yi hakuri,  ni nan sheda ne akan mahaifiyar ku,  mutuniyar kirki ce,  asali nine mutum na karshe da ta gani sanda zata bar garin nan.” Ya karasa yana mai ɗaura tabarau a idonsa.2

“ka san ta ne dama ” Ta faɗi da sauri

” Asalin mu yan garin nan ne,  ina da shekaru ashirin da ɗaya, kaddara ya raba ni da garin nan.  Da yawa ba zasu gane ni ba.  Amma dai RAHANATU yar halak ce,  ya ta gari ce,  kusan abu ɗaya mabambanta ya raba mu da garin nan.  Kullum… ” isowar Salman ne ya sa yayi shiru.

” Zauna” Ya ce masa bayan sun gaisa.

“shin ka san Mahaifin ku? ” Ya tmby shi direct

“zan iya tuna shi amma gaskiya ba zan gane shi ba”  Ya faɗi kamar ana tirsasa shi yayi magana.

“Suna tare da mahaifiyarku sannan shi ɗan asalin ina ne?  Ya sake tambaya duk da wani sashi na ranshi na faɗa masa ba zai samu amsar sa ba.

“ni ma ban sani ba,  kila da gaske mu shegun ne shi ya sa ta turo mu kusan shekara goma ba waige.  Mun zo ina da shekara takwas,  salma shida suhayl biyu da yan watanni. Yanzu shekaru na goma sha bakwai,  salma mai sha biyar ko kuda bai taɓa cewa y a na son ta ba,  sai yaushe?” shima ya sa kuka kamar karamin yaro.

Bai hana shi ba har sai da ya gaji ya yi shiru. Sannan ya ce

“kai ne babba,  zan biya maka kuɗin jirgi ka je umra,  se ka nemo iyayenku,  yanzu ka nemo lambar wayar Amina,  se mu samu na ita RAHANATU ɗin,  sai in kira in ce zaka zo”

“ai ina da lambar” Ya katse shi, bai jira cewarsa ba ya ruga a guje ya je ya ɗauko.

Nan ya amsa sannan ya sallame su,  nan suka fita cikin farin ciki da shi malamin albarka.

                        ***

Zaune su ke tana zuba masa fura shi kuma yana  ta zuba mata shagwaɓa.

“Abdoul da ace ban maka aure ba da na yarda da wannan shagwaɓar amma tun da na yi ka tashi ka je can kai mata ” Ta faɗi ganin yanda ya narke a kan kujera yana jiran furan.

” kai kai kai mamata ai ko tsufa mu kayi ba wacce, za ta ga shagwaɓar nan sai ke,  kai Allah ya kaimu Aljanna a can zai fi daɗin yi tunda ba ko ɗigon bakin ciki” Ya faɗi yana dariya.

“Aameen ya rabbi,  ya su Salmah,  da fatan kana kokarta wa, hakan zai sa Allah ya dube ka ya kawo maka komi cikin sauki” Ta faɗi tana dariya.

“Wacece salma kuma hajiya” faɗin wacce ta shigo wacce kallo ɗaya zaka mata ka hango kyawunta,  fara ce ba can ba,  tana da cikakken sura da ba ko wace mace ke da shi ba.  Sanya ta ke da bakar jallabiya ta yane kanta da gyalen shi hakan ya kara fito mata da kyawunta.  Zaman da tayi saitin kafar sa tare da jan masa yatsa ya ɗauke idanun Hajiya daga kan ta.

“yar mijinki ce” faɗin hajiya tana mai mikewa.

“Ya kuma?  Na shiga uku ni Zainabu ta ina zan fara” Ta faɗi a fili

“Abdoul da ma ban yarda da dawowarka garin nan ba,  ashe duk damuwar da ka ke nuna wa akan rashin haihuwa ta duk karya ce,  ka san kana da wasu ne,  munafuki azzalumi” Ta faɗi tana kai ma sa duka ta ko ina.

“Kinga,  ina da su ko da kika auren, ke kan ki matsala ce a gare ni balle in zauna ina faɗa miki matsala ta” Ya faɗi yana mike wa don ya ga tana shirin tara masa jama’a.

Ganin yana shirin barin ta wajen ne ya sa ta Mike haɗe da rungume shi.  “kayi hakuri masoyi na ka san ina bala’in kishin ka shi ya sa Kaga na damu”

Gam ya rike ta Sanan shi ma yayi mata raɗa da cewa ” ki kwantar da hankali ke kadai ce matata a yanzu,  asali ma su ɗin uwarsu na aure a Saudiyya. Ina son ki da yawa”  Ya fadi yana mai shafa bayan ta.  Aranshi faɗi ya ke ” ina zan iya da rigima”  ita kuma murna take,  nan take ta fara tallar makilin don ta gama yarda da shi ko don ba ta taɓa kama shi da laifin cin amanar sa ba tun haɗuwar su a bariki har zuwa aurensu.

                      ***

Cikin sati uku duk wani shiri na tafiyar salman an gama,  malamin su din da kan shi ya je yayi ma Goggo da hakimi maganar kuma duk suka yi Na’am da hakan.

Wasiku kala uku uku Salmah ta rubuta ma mahaifiyar su da mahaifinsu tana mai nuna musu Yanayin rayuwar da suke ciki na tsangwama da aibanta su da kiran su Shegu da ake. Sannan ta ce su aiko da kuɗi duk su koma gaban su da rayuwa.

Shagon Danladi mai hoto taje tayi Kala kala,  duk ta haɗa a embilo ta ba Salman ya sa  kayan shi.

Ranar Alhamis jirgin su ya tashi daga filin jirgin Aminu Kano da ke birnin Kano,  ya rabu da yan Uwansa cike da fargaban shin zai samu abinda ya je nema ko ba zai samu ba?Mutanen marke suka ɗauka, duk inda mutane suka taru ba mazan ba ba matan ba duk zancen kenan “Mahaifin su Salmah ya aiko da kuɗi Salman yaje” . Wasu su kara da “ai an ce bai da lafiya ne zai ɗaura shi a kan hidindimunsa ne” labari dai kala kala masu hassada su ce “ai so ya ke ya bautar da shi kamar yanda shi ma aka ce a wahale yake zaman Saudiyya.” nan fa yan son jin gulma suka fara tura ya’yansu zuwa ga Salmah in kuma suke da dama su ka fara zarya gidan Goggo.

Duk abin da ake Salmah ta kan ba malam labari su yi dariya. Don tun ranar da ya musu alkawari ta maida shi aminin ta, sannu a hankali har suhayl ya saba da shi. In yana cikinsu kuwa nan zaka ga tsantsan farin ciki a kan idonsa da yaran.

“Baba malam sai ka ji Batul wai ni take so da kawance, ka san de yanda ta fi kowa hantara ta da ita da yar kura. Anya ba wani munafunci ta zo yi ba? ” Ta karasa tana tagumi.+

Dariya yayi kafin ya ce mata

” ki bi su da yanda suka zo miki, banda wulakanci dai, Kinga duniya ba’a rike mutum gam gam, haka ba’a kin mutum da tsanani shi yasa. Ina su Ummitr, duk da na san fin karfi aka musu amma in aka ce zasu juya miki baya yanda suka amshe ki farkon zuwan ki zaki amince? Haka rayuwa ta gada, in na faɗa miki abubuwan da nayi a da Ina mai tabbatar miki ko kallo ba zan ishe ki ba. Saboda haka ko da yaushe ki bi kowa da fatan alkhairi.”

“ka yi rashin ji ne Baba? Kace ka san mamata, faɗa min ya take sanda take garin nan” Ta Yi saurin katse shi

“mutuniyar kirki, ga nutsuwa, ga son karatu, ke duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani ɗan adama bi ta hanyar duk saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi’arta ce zuwa makaranta, duk wani matashi dake kauyen da makwabtan kauyukan sun shaidata ne a matsayin daliba mai zuwa makarantar boko.

Da yawa daga cikin su suna ganin haukar iyayenta da suke iya barinta tana bata sauran adadin shekarunta a hanyar neman karatu.

Ta samu tarin makiya da mahassada a garin nan, wasu a dalilin sun furta suna son ta mahaifinta malam Tanko ya ce shi yar sa karatu take. Shi ya sa da ta haɗu da JARRABI mutane basu yi mata uzuri ba illa ma aka yi amfani da maraicin ta suka tozarta ta, ita kuma Goggo Kunyar nan da ake ma ya’yan fari ya sa ta taimaka masu wajen hantarar ta. Kar ki damu, duk Yanayin da take cikin Salman zai zo mana dashi. Mu cigaba da mata addu’a, Insha Allah muna tare da nasara. Allah ya muku albarka “

” Aameen ya rabbi ” Ta faɗi cike da murna, don ba’a taɓa faɗa mata kalamai masu cike da alkhairi ba dangane da mahaifiyarsu, nan take kaunar malam ya cika mata zuciya, don ta tabbatar da ba wanda ya kai shi son su.

***

Ko da Salman ya isa Kasar Saudiyya, gari mai tsarki ya fara isa yayi umra, inda ya roka ma iyayensa gafara da shiriya da kuma rahma. Ya roka ma yan uwansa da kuma sauran yan uwa musulmi. Malam ma ya sha addu’a da fatan samun biyan bukatun duniya da lahira. Daga nan ya shiga jirgi zuwa birnin Tabouk, cikin tafiyar mintuna hamsin suka isa. Anan ya iske mace sanya da nikabi amma sagale a wuyarta wani irin kwali ne an rubuta sunansa SALMAN IMRAN ɓaro-ɓaro akai.

Kamar yanda ta shaida masa a wayar da suka yi kafin ya taso, zuwa ya yi ya rungumota ta baya. Nan take kuma sai ya saka kuka. Itama duk juriyar ta sai da hawayen da ke makale a idanunta ya sauko.

Bayansa ta shiga shafawa alamun lallashi har sai da taji yayi shiru ba tare da tace da shi wani abin ba. Ganin yayi shiru ne ta ɗaga kansa ta kalle shi, duk da nikabi ya ɓoye murmushin da ke kwance a fuskar ta, idanunta sun gagara ɓoye kaunarta gare shi.

“yaro na ka girma, kana shirin fi na tsawo” Ta faɗi cikin farin ciki.

“Marhabanbika yaa khalilie ” Ta faɗi tana mai rungumar sa da kyau. Daga haka suka shiga mota zuwa gidanta. Idanunsa na kan gine-gine da tsare tsare da tun da yayi wayau bai taɓa cin karo da irin sa ba.2

STORY CONTINUES BELOW

Sun isa gidanta, yana ta zuba ido ya ga shigowar mahaifinsu amma shiru har ya ci abinci yayi wanka amma duk tsit, yaje ya sallaci magariba da isha’i a tunanin sa zai dawo ya iske shi amma shiru, ganin ba ta ce da shi komi ba shi ma sai ya basar amma can kasan zuciyar sa tsoro ya ke ji kar ya zo zancen mutanen marke game da su shine gaskiya. Da tunanin nan ya kwanta

Washe gari ma haka ya tashi cike da fargaba, bayan sallah ya koma barci inda bai tashi ba sai wajen karfe goma sha ɗaya. Nan ma dai abinci yaci, yayi wanka sannan ya zauna kusa da ita a falo.

“Salman ya sauran yan uwanka, da fatan kana kula da su yanda ya kamata, ka san ance babban namiji uba” Ta karasa tana dariya alamun tsokana. Shima dariyar yayi, ya tashi tsam ya ɗauko mata hotunan su da ya haɗo, wasikar salma da sauran ababen.

“Salmah ta girma da yawa, ta muku wayau ita ke kama da mahaifinku, amma duk ku muni na kuka ɗauko “Ta ce tana dariya.

” Ta ɗauko dariyar ki da tsokanar ki, salma duk ta fi mu hayaniya. Daga zuwan mu marke ta yi kawaye, farin jini a wajenta ba’a magana amma kwatsam mummunan jifa ya raba ta da dukkan farin ciki. Duk aka guje ta hatta Goggo ba ta kaunar ɗaura ido akanta” zaburar da tayi ne ya sa yayi shiru

“me aka mata? Wallahi duk wanda ya taɓa min ita sai na zama Silar Ajalinsa” Ta faɗi idanunta ya koma jajir na ɓacin rai.

“an ce wai mu Shegu ne” Ya faɗi a sanyaye. Dariyar da yaga ta yi ne ya sa shi yin shiru.

“bahaushen mutum na nan dai sa take laifin shi ya hango na wani. Yana nan da tunanin mace ba mutum bace shi yasa ku ba’a kyarar ku yanda ake mata ko. Za ka koma musu da labari mai daɗi, labarin da duk wani mai hassada hassadar sa zai zama ajalinsa.” Ta karasa tana mika hannu ta dauki wayarsa. Nan ta kira tayi larabci sannan ta aje. Haka tai ta tambayarsa ya na bata labari har aka kai ga zancen kayan sallah da na abinci da ake aikowa da sunanta.

Shiru tayi tana tunani, don ba’a yi kwana biyu ba da ta samu sakon wani da yayi ikirarin shi ne HADI SHEƊAN yana mai neman gafaranta.5

“HADI na marke har yanzu?”Ta samu kanta da tambaya.

“bana tsammani don sai dai mu ji ana ko ina kika kai cikin HADI ” Ya amsa a sanyaye.

Nan ta kwashe duk labarinta ta faɗa masa ba tare da ta ɓoye masa komi ba. Ko da ta kammala yana kuka tana kuka. Suka tashi suka yi sallan azahar sannan ta nema musu abinda zasu ci. Suna tsaka da ci ne sai aka yi sallama, ta ba da izini mutumin da ya shigo kamar an tsaga shi aka fitar da mutum mutumin sa ne Salmah.

Bai ko Kalle ta ba ya nufi wajen yaron shi ya rungume. Murna a wajensa ba ko kaɗan ba. Da gurbataciyar hausansa ya ke tambayarsa su salma.

“umminku ta sace ku ta kai ku inda ba’a san Darajan mutum ba” Ya faɗi da alamun ɓacin rai.

Bata ce uffan ba ya gama surutunsa ya yi gaba, can da ya yamma ya sake dawowa da kayan daɗi cike da leda. Sannan ya ce ya shirya washe gari wajensa zai kwana.

***

Cikin sati biyu da yayi tare da iyayensa yayi kyau ya ji daɗin zama da su, duk da bakin cikin sa ɗaya da yaji cewa aurensu ya mutu shekaru shida sa suka wuce.

An kai shi wajajen shakatawa da buɗe ido kamar su.

At tayma

Da sauransu. Ya dauki hotuna da karamar kyamarar sa da aka siya masa, faɗi yake ” da me zan saka ma malam, ya gama min komi”. A haka ya Share kwanakin da ya ka mata yayi ya fara shirin komawa gida.

Ko da ya fara shirin dawowa ba shi kaɗai ne ya kasance cike da kewa ba har su RAHANATU don ji take kamar ta biyo shi ta dawo cikin yan uwanta, amma karatun da take na daktaret ya sa dole ta fasa zuwa har sai wani lokacin . Sun masu tsaraba ba ko kaɗan ba sannan suka yi masa alkawarin zuwa karshen shekara inda zasu je Sudan don ganin dangin mahaifinsu.

KANO TA DABO TUMBIN GIWA

La’asar sakaliya jirgin su Salman ya sauka a birnin Kano, bayan sun sauka, ya iske Malam yana jiran shi. Gidan baki na tahir guest palace ya kaisu. Anan abinci mai lafiya suka iske sannan ya yi wanka suka sallaci magriba ya dauke shi suka fita zuwa gari. Duk da ba wanna ne zuwa sa na farko garin Kano ba, amma kasancewar wannan zuwan da wayonsa kuma ya fito birnin Saudiyya sai ya kara gane cewa Zazzau ta fi Kano haɗuwa. Washe gari Bayan sun kammala karin kumallo ne suka je gidan Inna Amina, nan ma dai sama sama suka gaisa don suna hanya.+

Murnar ta kasa ɓoyuwa yayi, faɗi take ba kakkautawa “Ɗana ka ga mahaifinka toh Ya wajen su RAHANATU” dariya kawai yake bin ta da shi tun da ya amsa mata da farko.

Ko da mijinta ya taso daga Barcin da ya ke bayan asuba ya ga salman din cewa yayi “Me ya dawo daku gidan nan bayan na sa katanga tsakanin ku da iyali na, ita in ba zata iya hakuri ba sai ta tashi ta bi ku” Ya faɗi yana zazzare idanu, a zuciyar sa addu’a yake Allah ya sa wannan ya samu ya haye Salmah. Bai karasa Mafarkin ido biyu ba ya ji abin da ya girgiza shi.

“Dawowarsa kenan daga Saudiyya, Mahaifin su ya turo masa kuɗin jirgi ka ga har umra yayo Wallahi” Ya ji inna Amina ta faɗi, hanjin cikinsa sai da suka murɗa don bai taɓa tunanin zasu rayu cikin gata ba bayan ya kore su, a tunanin sa sun gaji da gararanba ne suka dawo duk da Idanunsa sun karanto masa hutu a tattare da shi. Shiru duk suka yi sai chan yayi shahadar faɗin

“Zo ka fita min a gida, kuma duk sanda ido na ya sake tozali da kai a gidan nan tabbata sai na wulakanta ka” Ya karasa yana kumfar baki haɗe da nuna masa hanyar kofar fita.
“Amma… “3

” Kar ki damu inna, da mota muke a waje za’a kai ni har gida, Kinga ba sai mun ɓata masa lokacin sa ba, na barka lafiya baba ” Ya karasa Yana kallon baba cike da murmushi” yana fita kuwa suka ɗauki Hanya, anan yake bashi labarin da ba su samu damar yi ba tun bayan saukar sa, tiryan tiryan ya ke faɗa masa labarin tun da ga isarsa Saudiyya har dawowar sa. A cikin haka ya ce ” wai wanene Hadi sheɗan?”
Shiru ya ziyarci motar suna tafe sai karar iskar motar kawai ke tashi. Chan dai malam ya nisa ya ce
” Hadi na nan, ya shiryu in ka ganshi zaka rantse ba shi ne wancan dinnan ba” Ya faɗi Yana murmushin da bai wuce fatar bakinsa ba.

“Toh wai me ya faru bayan tafiyar ummi na, kwanaki kace mana kai ne mutum na karshe da ta haɗu da kafin barin ta marke. Ta bani labarin abin da ya faru zan so jin karshen” Ya faɗi yana mai maida hankali don ya ji komi.

“Hmmmn! Da tuki zanji ko da labari? Amma bari na faɗa maka a takaice”

MARKE MAY 1990

Tun bayan da ya rakata har motar su ta tashi zuwa Kano, ɓarin zuciya da ke faɗin gaskiya ta addabe shi, surata masa girman laifin da ya aikata musamman na karshen yake, sannan kuma take zuciyar sa ta kwaɗaitu da son gudan jininsa da ke kwance a cikin RAHANATU.

“Ta ina zan fara, in koma on bi ta ne ko, amma duka kuɗin hannu na na bata” Ya faɗi ma kansa. Chan dai ya tashi daga Kasan bishiyar da RAHANATU ta zauna ya yi hanyar hayin su.

“A gaida Hadi Shaiɗan in ka ga Hadi ka ga Shaiɗan! Ni duk garin nan babu matashin da nake kauna kamar ka, kayi mana maganin kafircin malam Tanko” aka faɗi a bayansa, waigowar da zai yi suka yi ido huɗu da liman.

“ka san duk wani ilimi da ba na addini ba haramun ne, sannan ko na addini yarinya ta iya kul huwallahu ya ishe ta ibada. Allah da ya ce wala tabarujjal jahiliyatil ula, Kaga kenan ita mace a bar ta a cikin gida, fita waje sau uku ne a rayuwar ta, in an haife ta a fito da ita limami yayi mata huduba, zuwa gidan miji, daga gidan miji zuwa kabari. In kuwa ba zata je ɗebo ruwa bane wanda a garin nan ai kai sheda ne kafin sallar asuba suke yi.
Toh shi malam Tanko bayan tura ta mace zuwa kafirci, yaki jin shawara haka zata dinga ketare manoma tana tsallake su zuwa makaranta. Garin haka ta ɗauki alhakin ka ta sa sha’awarka ta motsa, an nema maka aurenta yace karatu zata yi. Da Ace zancen cikin nan ya bayyana kafin rasuwar sa sai an yanke masa haddin barin yar sa tayi zina. Ai ka kwantar da hankalinka jihadi kayi, ai abin alfahari ne gare ka ita ke da abin tsiya” kalaman liman suka kara masa wani karfin gwiwa, da tinkaho cewan shi ɗin ya kai har ya isa. A haka ya isa gidansu matan Mahaifin sa suka kara hura masa kai.

STORY CONTINUES BELOW

A haka aka yi makokin malam Tanko, bayan kwana bakwai yan uwansa da suke uba ɗaya suka tattara duka gadon sa duk da ba wani abin a zo a gani bane suka ce ai mace ba ta a gado. Yayar mahaifinsa da ke birnin Kano ta ɗauke Amina, goggo salame ta shiga halin ha ula’i kafin ka ce me tayi baki ta rame. Koda ta gama takaba zaurawa suka mata chaa ba ciki kuwa har da liman da Mahaifin Hadi. Nan fa mata suka samu abin magana a duk inda suka taru, wasu su ce ita ta kashe mijinta don ta auri hakimi mai kuɗi wasu su ce ai liman ne ya kashe malam Tanko don ya aure ta. A haka wanta da ke aiki a garin legas yazo gida nan ya iske abin da ke faruwa bai yi wata wata ba ya ɗauki kanwar sa zuwa garin da yake aiki.

Hadi kuwa babu abin da ya chanza na daga halayen sa, sai ya zama ba dama yarinya ta gitta gaban sa zai san yanda zai yi ya samu hanyar sa a kanta. Ciki kuwa har da yaran liman biyu wanda tsit aka ji muryarsa. Duk da an ji labarin ɗaya daga cikinsu ta haife har Liman ya jefar da jaririyar a makabarta bayan ya kashe ta ta hanyar hana ta numfashi.
Ganin ba su tsira ba ya sa suka je har gida suka sami hakimi Mahaifin Hadi, bayan sun gaisa suka mika kokensu akan ɗabi’ar Hadi akan Yaransu mata. Shiru yayi yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya chan dai ya nisa ya ce

“kai Alu wanzami, ka tuna lokacin da aka haɗa baki da kai, ka shiga har ɗakin Salamatu ba da sanin ta ba don kawai a ɓata mata suna, duk da Ina son matata zaka iya tuna hukuncin da mahaifina ya yanke bisa shawarar liman? ” ya faɗi yana kallon Alu

” Eh ranka shi daɗe” Ya faɗi a muzance

“Toh don Allah ka faɗa mana mu ji” Ya ce yana murmushi cike da kasaita.

“Cewa yayi duk abin da namiji yayi ado ne, macece ke da abin kunya” Ya faɗi da kyar.

“Toh shike nan, liman ka yarda da haka? ” Ya tambaya yana kallon liman

” Eh! Amma… “

” A’a! Ban son jin komi Akaramakallahu, sanda na je umra kun haɗe baki akan duk abin da namiji yayi ado ne kuka kori yarinyar nan yar wajen mai gadi na malam Tanko, na nemi auren uwar don in fanshe abin da aka mata kun shiga kun fita. Ni ban ce Hadi ya kyauta ba amma kuma ku kuka lalata Hadi.
Nan Salamatu mahaifiyarsa ta zo tana min korafi akan yanda muka lalata mata yaro bayan mun kwato shi daga gare ta. Baba nalado ko zaka faɗa mana abin da ka ce mata? “

” ce mata nayi ɗa namiji ai baya taɓa lalacewa, ita da ta tun karo mu ne ke da alamar lalata don ba’a san mace da bin ba’a si ba. Ranka shi daɗe sai naga mu nan duka mazaje ne” Ya karasa yana mai sunkuyar da kai

“mazaje ne masu taimakawa wajen danne mata, mazaje ne azzalumai, Ace cikin shekaru biyar ba’a san duniyar da yarinyar nan RAHANATU take ba amma ku hankalin ku kwance sai da aka gama taɓa ku sannan zaku zo min da zancen kawo kamar Hadi. Yanzu ina son ku faɗa min hukuncin da za’a masa? Amma sai duk wacce ya ma FYAƊE ko ya yi zina da ita da amincewarta ta bar garin nan kamar yanda RAHANATU ta bar marke. In kun kora su sai a yi ma uban gayyar hukunci in har fyaɗen da yayi ba wani naui na jihadi bane. ” nan fa suka fara zazzare idanu kowannensu a muzance. Haka zaman ya tashi Dukkansu jiki a sanyaye.

***
Hadi na tsaka da barci mahaifinsa ya shigo ɗakin ya tashe shi. A firgice ya tashi don yayi tunanin ɓarayi ne ganin yanda ya banko masa kofa

“Hadi tashi magana zamu yi” Ya faɗi a sanyaye. Hakan ya sa hadi watsakewa ya tashi ya zauna yana mazurai

“ka san hukuncin ka kuwa ranar lahira? Wallahi zan iya rantsuwa cewa in ka mutu a yau wuta zaka je, zama ɗan hakimi ba zai kwace ka daga Azabar Allah ba balle kasancewar ka namiji.

Hukuncin zina, sata, karya da duk wani kaba’ir da kananan zunubi duk ɗaya ne a wajen namiji da mace, haka neman ilimi wajibi ne wajen mace da namiji. Saboda haka a musulunci babu wani zunubi da yake ado ga namiji qazanta ga mace. Duk dattinsu ɗaya, hanyar wanke su ma ɗaya, saboda haka tun wuri ka tashi ka nemi ruwan wanke dauɗan jikinka. Ka tashi ka shirya kayan ka, gobe da asuba ka tafi Kaduna wajen mahaifiyarka. Anan akwai islamiyyu da zasu koyar da kai musulunci, nima zaman da nayi a chan ne ya sa na bambanta da mutanen mu na nan. Nakan shiga majalisin Sheikh Abubakar Mahmoud gumi. Sheikh lawal Abubakar, nayi karatun alkurani wajen Sheik Alhasan said. Da sauran maluma da dama. Ina umurtanka a matsayina na mahaifinka da ka je ka nemi ilimi, mahaifiyarka zata sa ka a makarantar gaba da sakandire ka yi don shine burin ka. Ni dai ko yaushe ka samu dama ka zo ka ga lafiyata in har ina da rai in kuma rai yayi halinsa na yafe maka duniya da lahira, ka gaida min da mahaifiyarka, ka kai mata wannan takardun. ” Ya karasa yana mai mika masa embilo sannan ya rungume shi. Wannan rungumar tasa wata irin ni’ima ta shige shi. Hawayen sa suka sauka a kan kirjin mahaifinsa.

STORY CONTINUES BELOW

” Allah mai Rahma ne mai amsar tuba ne sannan baya kama mu da laifin da muka yi cikin rashin sani matukar mun gane gaskiya mun koma masa. Abdulhadi daga yau ba mugan halayen Hadi kaɗai suka mutu ba har suna Hadi sheɗan. Daga yau ɗa na Abdulhadi ɗan Salamatu ɗa nagari ɗan Aljanna shine a gaba na. Kayi min alkawarin hakan ” kankame shi da Hadi yayi ya tabbatar masa ya amshi alkawarin da ya ɗaukan masa.

Kwana biyu su liman suka tabbatar da babu Hadi a garin nan suka fara tsoron kar ya zo ya shirya musu wata makarkashiya ne shi yasa ya fitar da ɗansa daga garin. Hakan ya sa suka shirya kashe Hakimi suka yi tsubbace tsubbacensu da ya ke tsafi gaskiyar mai shi nan kuwa aka iske gawar hakimi wata biyu bayan tafiyar Hadi.2

An yi makoki an watse, Hadi na cikin wa’inda suke zaman makoki bai tanka m kowa ba kuma sun ga canji da alamun kamala a tattare da shi. Hakan ya sa yai musu kwarjini basu iya tunkarar sa da wani zance mara kan gado ba. Ko da aka zo zancen rabon gado, cewa yayi duk wani kashi na shi ya ba da sadaka ga mabukata ladan Allah ya kai ga mahaifinsa. Nan mutane suka saki baki galala suna kallon sa, ba su kai ga rufe baki ba ya sake cewa ” gidan da ke hayin makabarta inda malam Tanko yake da iyalinsa na mallaka ma Goggo salame in ta dawo. Daga yanzu kuɗin hayan gidan a fara tara mata”
“amma ka san dai ba kai kaɗai ke da gadon sa ba ko, ni ma ina da shi ” faɗin Alaranma baffan marigayi.

” Au ni ma namijin zaka fake da addini ka danne ni ne? Ai da da yanzu ba ɗaya bane, na fara neman ilimi zan dawo in na kai wani mataki za’a yanke haddin kisa ga wa’inda suke da hannu a mutuwar marigayi” Ya sa kai ya Barsu zaune gaba na dukan tara tara.

Yanda ya tsara haka akayi ya sa kai ya bar gari da wasu manyan littafan mahaifinsa da kayan sawa.
***
“Duk da shi ne Silar Ajalin kakanmu kuma Silar raba mahaifiyata da ga garinsu naji ina kaunar Abdulhadi, toh yana shigowa marke kuwa yanzu yana ina ne? ” Salman ya tambaya yana mai Share hawaye

” yana shigowa ko yau ina sa ran zai shiga, amma ka san mene? ” Ya tambaya

” A’a sai ka faɗi “

” Mutanen garin marke basu gane shi ba, don sai bayan shekaru goma sha sannan ya sake shiga garin, ya kammala karatunsa ya zama lauya mai zaman kansa. Ya shiga wajen su a matsayin Bako, burinsa kullum ya ga RAHANATU ya nemi gafarar ta. Ina tunanin shi ke turo muku kaya da sunan Mahaifin ku fa, amma ban sani ba” Ya karasa yana dariya.

“ka san kuwa sai da ummi ta ce haka, ni ya bayyana min kansa zan kaunace sa amma kuma salma fa ba karamar tsana ta ke masa ba” Ya amsa yana dariya shi ma.

Dariya suka yi gaba ɗaya, haka suka cigaba da hirar su wanda hakan yasa basu ga nisar tafiyar ba se ma ganin isowarsu gida ya katse musu hirarsu.

“Assalamu Alaikum warahmatullah”  Ya faɗi yana mai shiga gidan gwaggo,  ihun da Salma ta saki ne ya fito da Goggo da Baba Jamilu (kanin goggo)  daga ɗakin ta.

“lafiyanki?  Shegiya da idanu kamar… ” bata karasa ba ganin jakunkunar da yara ke shigowa da su.

” lale maraba da Salmanu sannu da dawowa kaabo! kaabo inji yarbawa” da dariya ya karaso ciki duk da idanun sa sun gane masa abin da ta yi ma salma kunnuwansa sun jiyar da shi kalamanta.+

“Oyoyo yaya Salman ” Suhayl ya shigo da gudu da abokansa da suke wasan bauni a waje.  Ɗaga Shi Sama Yayi Yana Murna Shima Don Gaskiya Yayi Kewan Kanninsa.

” Yaushe Su Ummi Zasu Zo Su ɗauke mu don mu huta Da gori” kwaf ta ji an gwaɓe bakin ta, ba kowa bane Goggo ce

“Makira,  da idanunta kamar na uwar uban ta.  Salon Ace muna musguna miki, ai yanda Jamilu ya zo da shawara haka za’a yi, aurar da ke zamu yi mu huta da Iskancin ki a gari” Ta karasa tana jan kunnen ta,  nan take hawayen ta ya fara zuba.4

Salman bai ce komi ba illa ya zauna a kujerar tayani gulma da ke tsakar gidan.  Alwala yayi ya ranka sallolinsa da ake bin sa,  sannan ya jira aka kira magariba ya sallata,  sai bayan Isha’i ya dawo ya iske goggo ta rarraba kayan.  Nan kuwa ya nuna mata sam ba haka bane don kowanne da sunan masu shi.

Nan ya cire na goggo ya bata, ya cire na kannensa sannan Ya cire na makota. Ahlin RAHANATU na Wattpad ma sai daya cire mu su dabino,  zamzam,  almiski da ta aiko masu na musamman.4

Tsaraban malam na daban ne,  shima a gefe ya sa da niyyar kai masa washe gari.  Cikin daren aka mimmika ma mutane tsarabar su.  Raba dare yayi da kannensa yana basu labari haɗe da nuna musu hotuna. Murna a wajen su ba’a ko magana. Tambayar sa suke yana amsa musu.

                         ***

Washe Gari gidan goggo ya zama wajen hawan arafa saboda yan zuwa sannu da zuwa wanda mafi yawan su suna zuwa ne don tsegumi da son karasa labari.

“Salma Kiyi hakuri Wallahi ina son ki,  ke ma kin san haka, wallahi raba mu aka yi se ɗazu ne fa baban Jidda ke ce wa ai zamu iya cigaba da miki magana amma banda shishigi.” ummitr ke faɗin haka tun safe take bin Salmah amma bata samu fuska ba daga Salma ba.

   “Albarka kike so na kwashe miki ko me ne?”  Salmah ta faɗi tana cin magani.

“Haba yar uwa,  yar fara yar duma duma ki yi hakuri mana don Allah, mu shirya ” faɗin Rufy da Jidda a tare.

” Ya halib ya asal,  yar balarabiya kyakkyawar malam Audu bature” cewan Ummitr.  Nan duk suka sa dariya.  Shike nan suka shirya,  ta ɗiba musu tsaraba mai yawa su kayan zaki da sauran ababen kalama.

                       ***

Sati uku da dawowar Salman daga Saudiyya farin jinin su ya dawo a garin marke,  sun yi sababbin abokai.  Yayin da kawu Jamilu ya bazama a gari yana neman ma Salmah miji.  Gidan liman yaje duk da kasancewar limamin da ya kora RAHANATU ya daɗe da rasuwa amma ɗan sa da ke limanci ya buga tsalle ya ce ai kafin rasuwar mahaifinsa ya bar wasiyya akan babu zuriar shi ba na malam Tanko.

    Ya tashi ya je gidan Alu wanzami.  Nan ma cewa akayi “ai wannan yarinya idanunta a buɗe ya ke ko anyi auren guduwa Saudiyya zatayi ta bar miji”

Haka yake ta yawo gidajen wa’inda a tunanin sa in sun aure ta zasu taya shi musguna mata amma a cikin shekara ɗaya bai samu wanda ya amince da auren ba.  Nan fa labari ya ɗauka a gari Salmah tayi kwantai duk anyi baikon kawayenta amma ita maza gudun ta su ke yi.

                    ***

A cikin haka ne aka sha bikin Rufaida da jiddo lokacin sun kammala aji uku na sakandire. Ummitr da Salmah ne kan gaba a duk wani shiri da aka yi na auren. An yi biki an shagale nan ne Salmah ta haɗu da yusuf abokin angon rufaida da yazo daga malumfashi. 

    Ba’a watse biki ba sai da suka daidaita kansu.  Murna a wajenta ba’a magana don ita kanta ta gaji da gorin da Goggo ke mata na cewa shekara goma sha biyar ba ta da mashinshini 

     Tun bayan haɗuwar ta da yusuf Goggo ta fara sarara mata,  ya kan zo sau ɗaya  duk sati biyu.  A haka suka fahimci juna soyayyar su tayi zurfi sosai.  Anan ne Hakimi ya sa baki a lamarin wanda tun farko bai ce komi ba goggo da kawu Jamilu ke kidin su da rawar su. Aikawa yayi a kira su har da su salma. 2

Bayan ya buɗe  taro da addu’a sannan ya kalli Goggo Salame ya ce

“Salame a iya sani na ni ne makwafin Mahaifin ki,  in kuwa hasashe na gaskiya ce toh lallai kina da na gaba,  haka kai ma Jamilu” Ya ce yana kallon inda yake zaune.

“Haka ne Alhaji” duk suka haɗa baki wajen faɗi

“Yauwa kuma ni na san na sauke hakkin ku da ke kaina,  na rungume ku tamkar ya’ya na tamakar kanne na kuma tamkar abokai na tun ban da karfin haka har nayi har zuwa yanzu da karfin ya kare,  haka ne? ” Ya sake faɗi yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya

” Eh!  ” suka faɗi a hankali 

” sannan cikin mata na na tabbatar da babban su Hajiya Azizah ta jawo ku a jiki ta rike ku da karfin ta da aljihunta ba tare da nuna gajiya akan abin da take ba,  haka ne? “

” Eh Alhaji,  fatan dai ba laifi muka yi ba”

“Eh toh ba laifi bane,  in har duk abin da na faɗi ba daidai bane,  amma in ko gaskiya na faɗi toh sai in ji dalilin ku da na yin abubuwa a gaban kanku” Ya faɗi yana kara haɗe fuska

Nan suka kalli junansu, idanu zuru zuru kamar mazari. 

“Wayyo ga ranar ummitr ba ta kusa ” salma ta faɗi a hankali don ta tabbatar da ummitr na wajen sai ta yi dariya.

“Tun zuwan yaran nan da farko ban amince da zaman su ba saboda halin da muka taso da shi na laifin mace shi ne laifi.  Har gida Azizah ta samo malami ya min wa’azi  bayan ta min doguwar nasiha akan hakkin mu na rikon yaran. Shi ma maganar ɗaya ya jawo Hadisai ingantattu da ya ce uwa ce da hurumin rikon Yaranta bayan mutuwar aure ko mutuwa,  bayan ita sai uwarta,  sannan yar uwarta mace se de in ba wa’annan ne dangin miji zasu shigo ciki.

Duk da kasancewar su hannun uwarsu ciyawar su wajibin Ubansu ne.  Haka tufatar da su da duk wani hidimansu.

Kun ga kenan ba mu san dalilin ta na turo su ba,  sannan kuma mu muka kore ta ba tare da mun waiwaye ta ba.  In tana da laifi ɗaya to mu muna da ɗari kuma dole sai mun amsa a gaban Allah,  sai yayi mana hisabi da malam Tanko akan amanar sa da ya bari,  mun rike ko kuwa. 

Tun lokacin na saduda amma ina kula da irin rikon da kuke ma yaran.  Har zuwa tafiyar Salmanu wajen uwar da Dawowa duk da baku sako mu ciki ba ina sane.

Bara sai naji ana yawo kwararo kwararo ana neman mai kwasar salma a matsayin mata,  duk nayi shiru na sa muku ido.  Jiya ina zaune sai ga wasu dattawa biyu sun zo wai a ja ma Salmah kunne ta rabu musu da yaronsu ba za su haɗa iri da Shegu ba. Ban yi kasa a gwiwa ba na kira lambar RAHANATU bayan na amsa hannun Salmanu.

Na ce ta shirya dawowa don tafiya da Yaranta kafin a hallaka mata su” Ya karasa yana kallon su ɗai ɗai

“Alhaji hallaka kuma,  duk kokarin mu na rikon yaran?

“kokarin ka wajen tallata su ga duniya ko wani irin kokari kake nufi.  Ina sane da abubuwan da kake yi fa.  Kar ka kaini bango in sa a kulle ka wallahi” Ya faɗi rai a ɓace2

“Allah huce zuciyar ka. Insha Allahu zamu kiyaye” suka faɗi

Nan dai ya zauna yana musu dogon nasiha sannan aka koma hira na zumunci.

“Ni ko Salma wannan wace irin rayuwa ce,  kin ga yanda kika koma kuwa” faɗin Shukra ta gidan Alhaji Aminu da tun zuwan su sallah Karama suka haɗu da salma a masallaci suka zama kewaye.  Duk da kasancewar ta yar birni yar gayu hakan bai hana ta kaunar Salmah ba tsakanin ta da Allah.+

” Kinsan kaka, wacce ta haifi uwa ? To itace mu taja mana masifa, Lakin duka laifin iyayenmu ne, da suka haifemu suka kasa rike mu A saudiyya, wai acewarsu saudiyya babu karatu, kuma ana 6ata kananun yara, To ita kakarmu babanmune bata so,  saboda asalin sa ɗan Sudan ne alhali su ne fa Silar haɗuwar Umminmu da shi.  Ba 

rashin ci ba sha, amman babu nutsuwar hankalin cin, Ita kawai mu tashi mu tafi makaranta, bata kula da dukkan damuwar ba, Sannan ta ɗaura mu kan tsoro, kullum muna daki ni da Suhayl,  yaya Salman ne kawai ke fita zuwa aiki, wlh ko makota bama shiga,  haka banta6a zuwa fati ko suna ko biki ba, koda na dangi ne hana karya tun bikin su rufaida da naje shi ke nan” Tayi shiru tana kuka wanda yafi jini ciwo.  Shukran ma dai hawaye take yi. A zuciyar ta mamakin kaka irin goggo take yi.  Rashin uwa bala’i ne

“Kawai ɗazu  muna daki ni da Suhayl, kinga tunda ta koya mana  haka ai akan tsoro zamu tashi ko?  Toh sai take ce mana munafukai Wai komai da munafunci mu ke yi,  Kee ko irin abin nan na mata na wata wata, gogg batasan ina  yi ba, wallahi dai dai da pad yayanmu ke kawo min,  in ya samu yan canjinsa in ba Haka ba ɗan kwali na nake amfani da shi.” chan Salmah ta ɗaura cikin gunjin kuka4

“Haba!  Wannan wace iri  rayuwa ce,  wai me ya ja wo miki wannan azabar ne?  Yaushe ta fara hakan don gaskiya ya kama ta a kwato muku hakkinku,  shi yayan ba zai iya kwatar muku hakkinku bane?” faɗin Shukra a kausashe ranta a ɓace.

“ku da yan birni daban ne,  ai dole mu zauna tunda ba mu da wajen zuwa. Duk manta wannan, shekara ɗaya da rabi kenan  wanta ya kira su ita da kawu Jamilu ya masu wa’azi a kanmu.  Tun lokacin ba mu sake samun wani matsala da ita ba, duk da dai ba dariya ba fita din amma ba zagi amma kuma ba kyara. 

Daga makarantar islamiyya sai na boko kawai ke fitar da ni,  yan kawaye na duk sun yi aure sai ni kaɗai, bayan nan sai mahaifiyar mu ta zo,  wannan zuwan nata ya tabbatar min da goggo munafukar mata ce,  kin san yanda ta ke Mana kamar zata mai da mu cikin ciki. 

Satin mahaifiyarmu tayi sati ɗaya  da zuwa ne ashe Malam Abdoul mai mana english shi ne ya zama Silar Ajalin kakanmu mai kaunar umminmu ba kamar goggo ba,3

Abinda ya faru kuwa shi ne zuwa yayi neman gafaran umminmu Ta rufe idanunta ta ci mutuncinsa,  goggo ma haka dalilin da ya sa bai Tsaya min ba kenan,  da har yanzu yana makarantar mu ai da baza’a taba min haka ba” Ta karasa tana sauke ajiyar zuciya

“Toh wai me yayi ne,  kashe kaka yayi ko ya aka yi ya zama Silar Ajalin sa” Shukra ta tambaya tana zare kunnuwa, burinta ta ji abin da ake jita jita a kai shin gaskiya ne ko zancen da Salmah ta fara faɗa mata yanzu.

“Se kin zo gobe zan faɗa  miki amma da wuri zaki zo,  kuma zaki  bani wayar ki na kira ummi na” Ta ce tana dariya.2

“zan baki habibti”

“Allah sarki  kin tuna min da Ummitr,  tana  chan cikin Larabawa da Haris ɗinta,  na san zai dafa mata ta cigaba da karatu ta haɗe kamar ki” Ta ce tana murmushi wanda ke kara bayyana yanke war kauna a tattare da ita.

Chan sai ta cigaba

“ina ss1 bayan tafiyar ummi na, goggo ta fitar da wani  salo na hana min sabulun wanka da wanki,  dalilin ta naje shagon makocinmu na karbi wayarsa na kira umminmu na faɗi mata abin da ke faruwa Shike nan laifin dana san na mata  ta tsaneni haka, ta rinka jamin bala’i kala kala, bara kiji kaɗan cikin  kalaman ta kaina,

“Salmah Allah ya haɗa ki da masifar data fi karfinki a duniya,

Salma Allah yasa a kaiki kabarinki na balbalin wuta,4

Allah yasa ki dauko abinda iyayenku zasu dawo, koda basu shirya ba (ciki)”

Burinta in  zama yar iska, sai Allah ya kare ni, Wlh Shukra a aike ka  kudi su faɗi, toh batasan kaddarar haka ba, inji wani dan karamin yaro Abban gidan bayan gidan na , wlh haka yace min Shukra  goggo batasan kaddara ba.

Lefi kalilan zan mata  in tun karfi takwas  na safe ne, wlh haka zata koro ni kofar gida

Tace inkika shigo sai ta kasheki

To me take nufi Shukra  na tafi karuwanci ko ?

To haka zamuyi ta bin bango,  Suhayl ya shigewarsa makwabta, Ba ci, ba sha, sai dare in yaya ya dawo, sai ya wuce damu cikin gida, haka zamu lallaɓa mu shige dakin mu, Shi kuma ya fita ya nemo mana awara ko shayi da bread mu ci,  daddare fa, Idan aka bashi kudin aiki, sai yaki kashewa, sai ya kawomana ya bamu duk dan muyi farin ciki. To kinji kadan ko, ki taya ni da addu’a.  In kin zo gobe zan baki labari.  Yanzu ki zo ki tafi kar goggo ta zo ta iske ki a gidan nan,  ki ja min bala’i.” Ta karasa tana dariya zuciyar ta na kuna.

Tashi Shukra tayi tana Share kwalla,  kuɗin hannunta ta mika mata tace “ki ɓoye wannan in Yaya ya dawo ki ba shi, sannan ya baki takardar sa na gama sakandire in zamu tafi kano Abban mu ya sa mu masa ko difiloma ne ya sama masa gurbin yi. 

Murna wajen Salmah ba kamar ta hadiye Shukra,  godiya take mata kamar ta mata kyautan duniya gaba ɗaya

                          ***

Washe Gari karfe goma na safe yai ma Shukra a gidan Goggo,  a zaure ta ci karo da Salmah tana Share hawaye goggo ta koro ta

“ki zo mu je hanyar Day ɗinku,  na ga akwai wajen zama, Share hawayenki,  ss2 fa kike Salmah mu Kinga kwalliyar da mu ke yi,  saboda yanzu ai mun yi jan wuya.  Saura shekara ɗaya fa mu gama mu shiga jami’a ” Ta ce tana kokarin sa ma Salmah farin ciki aiko sai da ta murmusa.

Yafito Suhayl tayi ya biyo su,  nan suka zauna suka ci dankalin turawa da kwai.  Basu taɓa ci da wayonsu ba, amma ba su so ya kare ba.

” Wai hanta ne wannan?  Me ye aka haɗa da shi? ” Ta faɗi tana kai loman karshe a bakin ta1

” kuna jin Daɗi a Birni abin ku,  da muna Saudiyya mu ma Haka zai kasance kenan ko” Ta faɗi idanunta raurau zata yi kuk

“Haba ya ta meye na kuka,  ki zama mai gode Allah a duk Yanayin da kika samu kanki,  kina son kashe kanki ne Salmah?”

Daskarewa tayi a wajen don sam bata taɓa  tunanin sake haɗuwa da shi ba.

“Baba Malam” Ta faɗi yayin da ta ga Suhayl ya rungume shi ta tabbatar shi ne yayansu ya kawo musu lokacin da suka fi kowa bukatar sa.

“Me kuke yi a nan?  Kun ci ko ku tuna da yaya yana chan yana neman muku kuɗi” Ya faɗi yana dariya,  nan ta rufe fuska duk da ta san shi sarai da tsokana.

“Wai labarin Umminmu zan ba kawata”

Shiru duk su ka yi tun ba shi Abdulhadi ba da ya ga kamar tonon asirinsa ne amma kuma ba komi ai tun da yaran ba su taɓa juya masa baya ba.

“Ni zan baku labarin tun da na san sanda akayi abubuwa da dama a ciki kuwa har da haihuwar RAHANATU ” ai ko sai suka sa dariya.  Tabarma suka Shimfiɗa a Kasar bishiya suka zazzauna sannan ya fara da cewa

Labarin Salmah da goggo is a true life story.  It happened to a sister ban kara komi akai ba,  even though rayuwar ta Tayi haske yanzu tana zaune da mijinta da Yaranta cikin kwanciyar hankali.  Muna rokon Allah ya sa duk kuncin da ta fuskanta ya zama mata kaffara ranar gobe kiyama.  Wani kuncin ma sai a babi na ashirin da ɗaya…Asalin RAHANATU

Asalin Malam Tanko ɗan kauyen Zangon Aya ne a can lardin Kasar zazzau.  Kakansa na cikin wa’inda suka kafa kauyen   MARKE. 

  Ya samo suna Tanko kasancewar sa shi kaɗai ne namiji a tsakanin mata.  Amma duk cikinsu shi kaɗai yai tsawon rai sai ya’yan yayyin mahaifinsa da sauransu dai.  Yana da shekara goma sha takwas Allah yai ma mahaifinsa rasuwa hakan ya sa bai samu yin karatun boko da mahaifinsa ya kwallafa rai a kai ba.  Yayar mahaifinsa ya damka  shi gadi gidan hakimi lokacin aminin yayan babansa ne hakimi.

Ko bayan rasuwan hakimi da na ɗa sabon hakimi Malam Tanko mai gadi bai bar gidan hakimi ba sai ma gata da yaga sabon hakimi ya masa na bashi gidan zama da kuma ɗaukan wasu Sabbin masu gadin.  Hakan ya ba shi daman yin aure in da ya auri salame mai fura.+

Malam Tanko fari ne kyakkyawa, don ya dauko hasken fatan mahaifiyarsa wacce ta ke Fulanin garin malumfashi,  dogo ne gashin sa a a kwance yake.  Duk da kasancewarsa mutumin da mara galihu in ka ganshi ka san Allah yayi halitta a wajen.  Hakan ya sa mutane ba su yi mamakin aurensa da salame ba kasancewar duk a sa’o’inta babu mace mai diri kamar ta.  Wankan tarwaɗa ce, idanunta fari kamar madara.  Mace ce mai kunya da natsuwa amma akwai ta da son a san cewa yayanta ya je makarantar boko da turawa,  bi ma’ana tana da son a san ita wata ce.

     An yi aure cikin kwanciyar hankali amarya ta tare a gidan nan.  Malam Tanko mutum ne mai daraja iyalinsa hakan ya sa duk wani sile da sisi da ya shigo aljihun sa a kan Salame ya ke karewa.  Suna cikin haka ciki ya bayyana a jikin Salame,  nan fa murna ba kama hanyar yaro a wajen malam Tanko.

Yayin da wasu ke fatan samun haihuwar maza shi malam Tanko tun da ya ji karatun sheikhin malamin nan Abubakar Gumi wata rana da ya je kauyen su da’awa ya ke cewa “Annabi SAW ya ce duk wanda ya dara haihuwar mace alamun Rahma na tattare da shi ne”  Ya ke rokon Allah wannan Rahman

Idan abokansa suka ce “Allah ba ka magaji” Ya ka ce “Allah ya min Rahma”. 

Bayan wata tara kuwa ta haifi yar ta mace mai kama da mahaifinta sai dai idanunta irin na mahaifiyarta ne.  Bayan kwana bakwai yarinya ta ci sunan RAHANATU.

Tun haihuwar ta kuwa ya nuna ma yan gari ita ɗin yar gata ce,  don rokon Hakimi yayi a haɗa masa ladan sa na wata uku ya siya rago.  Hakan kuwa akayi don rago  da bunsuru ya yanka mata.  Nan fa su liman suka samu abin faɗe wai ‘ya mace ko ba’a mata yanka ba ai ba komi amma don kaskanci ya yanka dabba har biyu a haihuwar mace.  Hakan bai sa ya kula su ba illa kara kaimi ya yi wajen kula da ita.

Tana da shekara shida Salame ta sake haihuwar mace,  wacce ta ci suna Aminatu  a shekarar ne kuma gwamnati ta gina makarantar firamare a filin da ke tsakanin marke da kauyen da ke gaba da ita don wadatar ilimi a yakin.5

A shekaran ne kuma yaron  hakimi da ke zaune waje  mahaifiyarsa  da hakimi aurota  sanda ya ke dawowa daga karatun da yaje. Aka mata sharri cewa wai tana kawo kwarto ɗakin ta ranakun da ba ita ke da girki ba.  Ganin ita kadai ke ɗa a gidan ga wani ciki.  Lokacin Hadi na da shekara huɗu, tun da ta sa kai sai da aka je aka kwato yaran biyu Hadi da kanwar sa Safiyyah.  Kwanan Safiyyah  biyu a marke chanjin yanayi ya zama Silar Ajalinta.

Dawowan Hadi ya sa malam Tanko sha’awar boko,  duk suka zauna da Hadi shi dai ya bashi labarin boko

“Wai baba Tanko da girman ka zaka shiga bokon ko ya kake so muyi” wata rana Hadi ya faɗi da ya gaji da jin tambayar.

STORY CONTINUES BELOW

“Kanwar ka nake so in sa,  ka ga in kai ka zama lauya ita sai ta zama likita ko ya ka ce” Ya  tambaye shi yana dariya.

“kuma fa zata yi kyau a likita.  Ka ga sai ta zama matar lauya mun zama haddadu ” duka da malam Tanko ya kai masa ne ya sa shi yin shiru

” shekaranka goma sha huɗu, ba ka kai ko ina ba kana sai ka zama lauya zaka yi aure,  ai nan da shekaru huɗu zuwa biyar ya kamata  kayi aure” faɗin Malam Tanko

“ashe dai baka so RAHANATU ta zama likita,  don kuwa in kana so sai ka ɗan jinkirta aurar da ita ka bar ta taje makaranta.  Ka ga in ta gama sakandire se muyi aurenmu ta karasa a gidanmu ko baba” Ya karasa yana rausayar da kai

“kai baka da kunya ne wai.  Ba’a fa maganar aure da iyaye.  Yanzu dai kana ga ba matsala tayi boko.  Ina so fa tayi ilimi sosai ” Ya faɗi cikin rada

” Malam Tanko karatun ta ba matsala,  ni a matsayi na na uban Kasar marke na baka dama,  RAHANATU tayi ilimi sai ka shirya ka aurar da ita.  Ba wanda ya isa ya hana. 

Ka ga in ta yi ilimi zata ɗauke  maka dukkan nauyin da ke kanka,  ilimi na da Daɗi kuma malamai sun faɗi yanda yake wajibi ga namiji haka yake a wajen mace.  Kada ka damu” Hakimi ya faɗi da ya tsinkayo hirarsu.

“Mun gode ranka shi daɗe Allah ya kara girma. Ya sa ka fi haka ” 

Haka dai ya yi ta godiya har hakimi ya wuce shi zuwa rangadi da suka fito yi.

                              ***

Sanda RAHANATU ta cika shekara goma lokacin an yi ma da yawa da ga sa’o’inta baiko, wasu an sa musu ranar shekara ɗaya wasu biyu haka dai haka dai.  Ita kuma malam Tanko ya daura ta akan keken sa ya kai ta makaranta ya mata rajista.

   Nan fa mutane suka jefa magana wasu suka tunkari malam Tanko da sunan ya kawo kafirci marke, 

“in banda kafirci mace in dai ta iya Fatiha da kulhuwa ai ya ishe ta ibada amma kai don kafirci ita kenan zuwa karatu boko ta dawo ta je wani tambada wai islamiyya,  karatu dai in dai Muhammadiyya ne ai Allo ne,  za’a kawo mana fi’ili a gari.” limami kenan kuma babban malamin allo na garin marke yayi takakkiya har gida wajen malam Tanko amma duk yai burus da su ya cigaba da karfafa ma RAHANATU gwiwa.  Kullum ya zaunar da ita ce mata yake

karatun ki shine hanyar ceton mu, ke kamar gona ce da muke shuka muke fatan girban albarkacin noman mu anan gaba, karatun ki ne zai sa mu san dadin cire kudi mu biyawa kanmu bukata, karatun kine zai sa wata rana mu daina lissafa abincin da muke ci, karatun ki ne zaisa wata rana mu iya siyan sutura har mu manta adadin wadda muka mallaka, karatun kine zai hana mu kwana da yunwa, karatun kine zaisa a rika tunawa damu a matsayin masu rufin asiri. Dan haka kada kiyi wasa da karatun ki rahanatu”

Tun bata fahimtar kalaman sa har ta haddace su har suka dasa zuciyar ta akan akidar boko. Garin siya mata kayan karatu da sauran tallafi babu yai sallama a gidan su,  suka rasa komi daga gatarin da malam Tanko ya gada hannun wan mahaifinsa sai ku tukunyar su Kwara daya kacal wanda ba kullum ya ke ɗaukan zafin wuta ba.  Amma hakan bai sa ta karaya ba kalaman mahaifinta ya zama mata jijiya da ke gudanar da wucewar jini a jikin ta hakan ya hana jinin daskarewa.

STORY CONTINUES BELOW

A kwana a tashi Duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar. Kasancewar  nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi’arta ce zuwa makaranta, duk wani matashi dake kauyen da makwabtan kauyukan sun shaidata ne a matsayin daliba mai zuwa makarantar boko. Nan wasu suka fara kiranta “yar boko”  wasu su ce mata “karuwa”  haka dai har ta kai aji huɗu,  lokacin tana da shekaru goma sha hudu a duniya.  Hadi ya dawo ya kammala karatunsa na sakandire. Ya dawo da wasu ɗabi’u da kare ba zai ci ba dalili kuwa shi ne sanda suke makaranta akwai cikin malaman da suke manya ne a majami’a wanda su basa yin aure,  hakan ya sa suke amfani da ɗalibai maza wajen gusar da sha’awarsu. 

   Wannan ya kawo luwaɗi yankin arewa ya kara karfafa zina (ku kalli film first October don tabbatar da zance na,  turawan nan ta missionary schools suka cusa ma yan nigeria ɗabi’ar homosexuality) 

    Anan ya wata rebiren sista ta sa shi a lungu ta ɗanɗana masa ni’imar da ke tattare da mace,  tun kwanyarsa bata iya fassara wa har dai ta tarjama masa babu abin da ya kai mace daɗi  a duniya.7

Dawowansa marke ne ya ya sa shi far ma yaran gari masu talla ta hanyar juye,  zai ɗebo silallan mahaifinsa ya siya kayan tallan yarinya ya biya bukatarsa a kanta. 

Ana cikin haka ne wata rana RAHANATU ta zo wucewa zuwa makaranta ya tsayar da ita,  yai mata alkawura  da dama tare da nuna mata ai mahaifinta ya riga ya bashi ita amma tayi fir ta ki amince masa.

                          ***

Bai tsaya ko ina ba sai wajen mahaifinsa ya ce masa yana so aje a nema masa auren RAHANATU.  Hakimi bai yi gardama ba ya aika aka kira malam Tanko.  Da ya iso ya ce da shi

   “Malam Tanko na kira ka ne ina so ka bamu auren RAHANATU, Hadi ya zo ya ce ka masa alkawari kuma shi yanzu a shirye yake.  Ganin shekarunsa ashirin da biyu yasa na maka magana in ka tashi aurar da RAHANATU sai mu zo ayi komi” 

Shiru ya ratsa wajen kafin dai malam Tanko ya tattaro karfin hali ya ce da hakimi

“Alkawarin mu da Hadi sai ta gama karatun sakandire ne,  ranka shi daɗe yanzu take aji hudu a firamare ” Ya faɗi yana sunkuyar da kai

” tab sai ta kunso ciki zaka aurar da ita ko mai kake nufi Tanko?  Ai ko a musulunci shekara bakwai aka ce annabi ya auri Aisha RA” faɗin liman yana kumfar baki2

“Toh a shekara nawa ta tare?  Sannan a shekara nawa manzo SAW ya aurar da fatima,  sannan akwai sahabbai da har suka mutu basu yi aure ba,  maza da mata kuma Allah ya musu alkawari Aljanna.

Ko ka manta cewa Maryam uwar Annabi isah tana cikin mata uku da Allah ya ce sun fi kowa ɗaukaka kuma bata taɓa aure ba.  Ni dai tunda an shaidi natsuwar RAHANATU ko bayan raina Hadi bai da mata sai ita a duk lokacin da mahaifinta ya shirya aurar da ita.  Ka bamu malam Tanko? “

” Eh ranka shi daɗe,  ban yafe ba in har ta auri wani bayan Hadi ” Ya fadi yana mai nuna alamun biyayya. 

Haka dai taro ya watse mutane suka shaida hakan.  Sannan kowannensu ya sami nashi ya fada masa alkawarin da suka dauka ma junansu su.

                             ***

Kwana biyu da wannan alkawari RAHANATU na hanyar ta na dawowa makaranta tana tafe tana waka, taji an fisgo ta zuwa cikin duhun masara da ya zama hanyarta.

Duk yanda ta so ta kwaci kanta kasawa tayi don ba karamin riko ya mata ba.  Sai fa ya daure bakin ta sanna ya bude fuskar sa ta ganshi “Hadi sheɗan wasu su ce Hadi aljan” 

“kin san dai ni ne mijinki,  gwada miki abin da zamu dinga yi akan gado zan yi” Ya fadi yana shafa mata ciki yana zuwa sama.

Fisge fisgenta bai kuɓutar da ita ba har ya tube ta ya fara neman hanyar sa.  Ba tare da natsuwa ba ya yi nasaran sace mata mutuncinta.  Bai tsaya haka ba sai da yayi fiye da sau uku ya tabbatar da ta suma sannan ya sa mata riga duk jini ya kai ta kasan bishiya ya yar yayi gaba.3

Ba ita ta tashi ba sai karfe huɗu,  kuka take ta rasa ya zata yi da ranta har sai da  adama matar malam basiru ta zo wucewa ta dawo daga kauyen su ta ganta yashe  a wajen Zazzabi ya rufe ta. Ita ta tallafa mata har zuwa gidan ta,  ta kimtsa ta sannan ta tsoratar da ita akan kar ta faɗa ma kowa don zata zama abin wulakantawa. Sannan ta kai ta gida ta ce Zazzabi ya rufe ta takai ta gidanta. Sanin halin zumunci na yan marke ya sa basu yi wani dogon tunani ba suka amince.

                            ***

Sai da tayi sati daya tana jinya kamin ta koma makaranta,  amma tun lokacin ta gwammace ta zagaya ta bi dogon hanya da ta sake bi ta cikin gonaki.  Wata biyu bayan haka ta fara masassara malam Tanko ya dauke ta zuwa asibitin kauyen nan ne komi ya faru.  Hadi ya zama Silar Ajalin malam Tanko,  Silar korar RAHANATU daga marke da kuma yanzu ya zama Silar kuncin rayuwa na su Salmah,  duk da ya tuba hakan bai sa ya yafe ma kansa ba. 

                         ***

Nan ya zauna ya cigaba da fada musu abin da Ya faru da Hadi har zuwa rasuwan mahaifinsa,  da komawarsa Kaduna da cikar burinsa na zama lauya babba mai zaman kan shi.

“Yanzu abin da ya rage ma Hadi shi ne ya cika alkawarin iyayensu ya auri RAHANATU amma ko jiya yana Saudiyya ta ki sauraren sa.” Ya faɗi yana share hawaye da bai san ya gangaro kuncin sa ba sai da ya ji lema.1

“ai Insha Allahu sai ya aure ta,  ku ce amin ” faɗin Salman yana murmushi.  Nan suka haɗe baki da faɗin Aameen.  Sai nan ne Salmah ta tuna bala’i da zata iske wajen goggo.  Amma hirar da malam ya dauko yana mai mika musu tsaraba ya sa ta sake.  Anan suka yi azahar da la’asar sannan ya tafi su kuma suka jira sai gab da magriba sannan suka wuce gida gaba na faɗi ɗar ɗar

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE