Soyayyah a kasar hausa

SOYAYYA A KASAR HAUSA

Soyayya wata aba ce mai qarfi da tasiri a zukatan jama’a, wanda ke kawo farin ciki da nutsuwa a tare da masu gudanar da ita. Qarfin soyayya kan iya kawo rikici da fitina wanda zai iya girgiza al’umma. A kan iya fadawa rikece-rikice ko yaqi a kan soyayya. Soyayya ita ce ke kawo zaman lafiya da cigaban al’umma. Ita kalmar soyayya ba wai ta tsaya bane tsakanin namiji ko mace, ta qunshi duk wata qauna dake tsakanin al’umma.

Malam Bello Sa’id a cikin littafinsa Dausayin Soyayya ya bayyana ma’anar So da “Qawa-zuci, ko tsananin qauna da buqatar kusanta ga wani mutum, ko wani abu daban.” Anan zamu iya tabbatar da haka a nau’in soyayya daban-daban. Misali Soyayya tsakanin da da mahaifi, ko jika da kakarsa ko miji da mata ko mutum da karansa, ko bawa da ubangijinsa da sauransu.

Idan muka yi duba a wannan zamani a qasar Hausa, kalmar soyayya ana yi mata duba akan wani abu na kyama wanda wasu mutanen sukan ji kunyar a ce suna soyayya. Ko tsakanin miji da mata, wasu na ganin sun fadi idan suka dinga nuna qauna ga matansu ko mazansu. To abin tambaya anan shi ne, shin akwai kuwa soyayya a qasar Hausa? Babu wasu isassun bayanai da za su tabbatar cewa akwai ingantatciyar soyayya wanda ta amsa sunanta soyayya a qasar Hausa, koda kuwa a daruruwan shekaru da suka shude. Asali dai a qasar Hausa mutum kan auri mata ba tare da ya santa ba ko ta san shi, balle a kawo batun soyayya. Da yawa daga cikin iyaye da kakanni da suka yi aure kamar shekaru hamsin da suke wuce, da yawansu sai da suka shiga dakin matansu suka fara ganinsu. Amma duk da haka aurensu kan dore, a kan iya cewa “mutu ka raba”. Duk da cewa ba za’a ce babu birbishin soyayya a qasar Hausa ba, sai dai a ce ba ta da karfi ko tasiri. A inda akan iya ganin soyayya a qasar Hausa bai wuce kamar a dandali ba, in da samari da ‘yan mata kan hadu. A irin wannan guri saurayi kan fara nunawa budurwa soyayya, wanda idan sun aminta da juna sai budurwa ta nuna ta ta soyayyar. Ko a wannan lokaci da yawa daga cikin samarin ba sa iya furta soyayyarsu ga wadanda suke so, sai ta hanyar abokansu ko kuma qawayen wadanda suke so. Mafi akasari ko an samu fahimtar juna soyayyar ba a budeta koda bayan aure.

Idan muka yi duba a wannan zamani akwai ‘yanci na auren soyayya, akwai birbishi na soyayya a cikin al’umma, amma duk da haka mutuwar aure a qasar ta Hausa ya yawaita. Wannan yasa dole a qara tunani cewa akwai kuwa soyayya a qasar Hausa?

Kamar yadda na yi bayani ita soyayya kan kawo farin ciki da nutsuwa, wanda idan har soyayya ta amsa sunanta soyayya mai yin ta na begen zama da wanda yake so. Sannan idan ya ga wanda yake so ko ya kalle shi zai ji wani farin ciki, koda maganarsa kuwa ya ji. Idan har soyayya ta kai soyayya babu maganar cutar da wanda ake so, babu zancen ka kaurace masa ko ka yi nisa da shi. Asali ma koda tafiya ka yi, begen wanda ka ke yi na damqare a zuciyarka wanda zai dinga bijirowa a duk wasu daqiqoqi ko sa’oi kwatankwacin son da ake. Idan akwai so a kan yi haquri da wanda ake so koda kuwa yana batawa masoyinsa. Wannan yasa hausawa ke cewa “so hana ganin laifi”

Zuciya kan dimauta idan ta rasa wanda ta ke so, ko kuma wanda ake so ya qaurace ma ta. Wasu mutanen idan har suka rasa wanda suke so, to suma qarshen zamansu a duniyar ya zo.

Idan na dawo kan batu na akan soyayya a wannan zamani, zamu ga cewa akwai abubuwa da suke nuna akwai soyayya. Wataqila saboda finafinai da littafai da ilmi da wayewa da ake samu ya sa a kan kamanta. Amma maganar gaskiya ba wai soyayya ba ce ke samuwa ba, illa kawai sha’awa. Duk da cewa sha’awa kan rikide ta zama soyayya, amma kafin a kai ga haka a kan ci karo da wasu matsaloli. Misali namiji kan ga mace ya ji sha’awarta saboda wasu siffofi na ta, sai zuciyarsa ta raya masa yana son wannan mace. Anan sha’awa ta yi tasiri a tare da shi, sannan samuwar soyayya a tsakaninsu ba abu ba ne mai sauqiba koda kuwa za su kasance tare. Mafi akasari akwai wasu abubuwa a aikace wanda za su taimaka wajen samuwar soyayyar. Wadannan abubuwa sun banbanta daga mutum zuwa  mutum, ko daga jinsi zuwa jinsi. Misali idan na auri mace saboda kyan qirjinta, sai ya kasance ba na samun wasu abubuwa daga gareta, kamar tarayraya da damuwa da ni, to ba lalle ba ne wannan sha’awa da nake mata ta rikide ta zama soyayya ba. Domin me yuwa ni ina da bukatar a tarayraye ni a nuna an damu da ni, ko a nuna ana tausayina. Wanda idan da ya kasance cewa ana tarayrayata da kula da ni kamar kwai, wannan sha’awa za ta rikide ta koma qauna mai qarfi.

A qasar nan akwai qabilu da dama, amma idan aka yi duba sai a ga mutuwar aure tafi yawa a qasar Hausa musamman a gurin bahaushe. Baya ga wannan addini musulunci ya bamu dama na auren mace har guda hudu, amma duk da wannan garabasa ba ma iya jure zaman aure. Sai kuma can wadanda mace daya suke aure a rayuwar su ba sa fuskantar wannan matsala. Akwai wata samina da muka taba shiryawa a Qungiyar Matasa da Cigaban Mahalli  a kan dalilan mutuwar aure a qasar Hausa. Tunanin wannan samina ya zo mana bayan wani mai unguwa da ya kawo mana kukansa cewa a iya unguwarsa daga watan Janairu zuwa watan Agusta an samu mutuwar aure har tamanin da uku (83). Wannna ba qaramar masifa ba ce da ke bukatar a yi ma rubdugu ba. Abin lura ana shi ne muna cikin babbar matsala ta mutuwar aure.

Dalilan mutuwar aure na da yawa wanda warware wannan matsala sai an yi duba na gaskiya ba tare da son rai ba. Amma tushen warware wannan matsala na ga samun tabbatatciyar soyayya. Sai mutanen mu sun daina tunanin So ba gaskiya ba ne, sai mutanen mu sun fara nuna halaye na soyayya. Halayen da suka hada biyayya, da amana da tausayi da kwalliya da kamun kai da aiki da hankali da tunani mai kyau da bai wa mace haqqinta da kuma adalci da kunya da mutunci da son addini tare da aiki da shi, da dogaro da kai da sauransu.

Idan za a samu wadannan halaye zai taimaka wajen samuwar soyayya mai qarfi, wanda za ta dinke barakar da ake da ita. Domin samuwar ingantatciyar soyayya ne zai kai ga auren nan na “mutu ka raba”. Wani masanin soyayya ya ce “So ya kan tura saiwoyinsa cikin zuciya ne, saboda haka idan aka tunbuko shi, shi ma sai ya tunbuko zuciya.” Tabbas idan akwai makamancin irin wannan Son, mutum ba zai so rabuwa da masoyinsa ba.

A qarshe nake jan hankalin mutane da su daina kyamar kalmar “So” domin ba qarya ba ce. Allah da ya halarci dan adam ya sanya masa dabi’a ta so, zamu iya ganin hakan a cikin littafinsa mai tsarki.

“Kuma yana daga cikin ayoyinsa, da ya halitta muku matanku daga jinsin ku domin ku rayu (tare da su) cikin nutsuwa, ya kuma sanya soyayya da jin kai a tsakaninku.”

*Abdullahi ismail salanke*

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE