SOYAYYAR MU CHAPTER 2

SOYAYYAR MU CHAPTER 2

WANENE ALIYU? Alhaji Bashir kankia ya kasance attajiri kafin Allah ya dauki ran shi da matar shi Hajiya Nafisa. Kafin su rasu sun kasance da yara uku ne a duniya, Alhaji Ibrahim shine babba sai mai bi mashi Alhaji Muhammed sai autar su Hajiya Mariya. Su Ibrahim sun kasance yara masu gata a rayuwa, sun samu ilimin boko da na addini mai zurfi, ko kafin mahaifin su ya rasu sun riga sun tara dukiya tasu ta kansu. Bayan mutuwar mahaifin su ba da dadewa ba ita ma hajiya Nafisa ta rasu. Su Alahji Ibrahim sun yi rashi na iyaye amma ba rashi na kudi ba domin sun gaji dukiya mai tarin yawa.+ Alhaji Ibrahim ya auri matar shi Hajiya Halima wadda aka fi kira Mummy, Mummy mutumiyar Katsina ce, yaran su uku. Amina, Mustapha da auta Muhammad Kabir. Alhaji Ibrahim yana da gidaje dayawa a cikin garin katsina da Kaduna. yana zaune a daya daga cikin danqararrun gidajen shi dake nan cikin GRA ta Katsina. Alhaji Ibrahim yayi aikin banki a bankin Zenith Bank, sai da ya kai matsayin ED. Bayan yayi ritaya ne ya fada siyasa. Yaran shi sun samu ilimi na zamani da addini. Babbar diyar shi Amina tana auren Nura mutumin Kano ne wanda yana aiki a can qasar UK, suna zaune a can da yaran su guda biyu Farida da Mukhtar. Mustapha yanzu haka yana aiki a NNPC ta jihar Portharcourt, sai autan su Kabir wanda yake Soja yana nan a Jaji cikin Garin kaduna. Alhaji Muhammed ya auri matar shi Hajiya Fatima wadda suka fi kira da Ammi wanda suka zauna a garin Abuja, Hajiya Fatima asalin bafillatanar Bauci ce. Sun haifi yara biyu, Nafisa da Aliyu. Alhaji Muhammed ya kasance kafaffe ne a siyasa wanda idan har ya tsaya maka toh ka haye. A rayuwar shi bai taba tsayawa takara ba amma Allah yayi yawa da mutanen da ya tsayar, gwamnati ta sha canzawa da niyyar dora shi minista amma ya qi, a lokacin da ya dulmiya dan uwan shi Alhaji Ibrahim shi kuma ya tilasta mishi akan ya karbi Ministan ko da shekara hudu ne shima ya dana. Da tilastawar Yayan shi ne Alhaji Muhammad ya karbi Ministan Abuja. Alhaji Muhammad da matar shi Hajiya Fatima sun kasance suna bala’in son yaran su guda biyu, sun dora su akan ilimi na boko da na addini mai zurfin gaske, basu bari dukiyar su ta rufe musu ido ba. Hajiya Fatima wadda ake kira Ammi ta kasance kyakkyawar bafilatana, fara sol ga gashi irin na fulanin asali, Aliyu shine ya dauko kamannin ta amma kuma ta fi shi haske yayin da Nafisa ta dauko kamannin mahaifin su da kuma hasken uwar su. Nafisa ta ba ma Aliyu tazarar shekaru har biyar. Dalilin da yasa tun suna yara yake kiran ta Anty Feena kenan. Nafisa da Aliyu sun fara makaranta a cikin garin Abuja wanda har sakandire duk a nan Abujan suka yi, Nafisa ta wuce University ta Gwagwalada inda ta karanci Business Admin. Shi kuma Aliyu yana kammala sakandire ne Alhaji Muhammad ya tura shi Oxford university a UK domin karantar Archietecture. Bai samu matsala a can ba a dalilin ‘yar uwar shi Amina da ke zaune a can. Nafisa da Aliyu sun kasance masu ladabi da biyayya, duk da matsayin da uban su yake da shi a garin Abuja basu wulaqanta kowa ba. Karatun su shi suka sa a gaba tare da girmama mahaifan su. Bai dade da sauka daga ministan Abuja ba Alhaji Muhammad ya rasu. A dalilin hatsarin mota da suka yi a kan hanyar su na dawowa daga Katsina inda suka ziyarci ‘yan uwan su. Wannan tafiya yayi ta ne tare da mai dakin shi hajiya Fatima da kuma Nafisa, A lokacin Aliyu yana UK. Da yake dan Adam baya wuce lokacin sa anan take Alhaji Muhammad ya cika. STORY CONTINUES BELOW Hajiya Fatima da Nafisa sun dan ji rauni wanda a sanadiyan hatsarin ne har yanzu Nafisa tana dangyasa kafa kadan wanda idan ba kana tare da ita ba ne bazaka gane hakan ba. Zamu iya cewa an ji mutuwar Alhaji Muhammad a qasa Najeriaya musamman arewacin ta domin dai mutum ne wanda yayi fice a siyasa. A lokacin da mahaifin Aliyu ya rasu yana UK yayin da yake rubuta jarabawar shi ta kammala makarantar. A kan idon shi su Amina suka shirya zuwa Najeriya har yake ce musu su jira shi tunda kwata kwata saura kwana biyu ya kammala jarawbawar amma suka qi, sunyi mishi booking din jirgin shi akan yana kammala jarabawar ya taho, tun a lokacin jikin Aliyu yayi sanyi musamman da ya kira wayar mahaifin shi ya ji shiru, ko da ya kira Ammi sai tayi qarfin halin ce mishi komai lafiya kar ya damu. A daddafe ya kammala jarabawar shi ya taho, kafin ya iso Ammi ta sanar mishi akan ya sauka ta Katsina domin dukkan su suna katsina. Ko da Aliyu ya iso gida yawan mutanen da ya gani a qofar gida ne suka tada mishi hankali wanda nan take ya fara tambayar direban da ya dauko shi abinda ke faruwa. Jin an fara mishi gaisuwar rasuwan mahaifin shi ne ya zame ya fadi. Aliyu dai bai qara ganin kowa ba sai ganin shi yayi a gadon asibiti, kwana daya yayi a asibiti aka sallamo shi. Bayan ‘yan watanni da rasuwar Alhaji Muhammad ne Aliyu ya shirya komawa qasar UK domin fara aiki a can wanda a da ya qi amma kuma a yanzu yaga dacewar hakan. Ita kuma Nafisa ta cigaba da kula da wasu harkokin da mahaifin su ya bari a nan garin Abuja. A cikin haka ne ta hadu da wani mutumin Bakori mai suna Yusuf Abubakar wanda yake aiki a nan National Steel and raw materials exploration agency a cikin garin Kaduna. Sun fahimci juna sosai, Ammi ma ta yaba da halayen shi. Har Katsina ya je wurin Daddy sun gaisa kuma suma sun yaba da halayen shi. Nafisa ta shaida ma Aliyu ta waya game da haduwar ta da Yusuf amma ta gaya mishi bazata aure shi ba matuqar bai yi mishi ba. Ko da Aliyu ya zo hutu ya hadu da Yusuf kuma a yadda yaga yayar shi tana son Yusuf din shima sai ya ji yana son shi. Ba tare da bata lokaci ba aka kai gaisuwa katsina aka sa ranan biki.1 Lokacin bikin Nafisa ne da Aliyu ya zo aka raba gadon Maihaifin su, Bayan bikin ne aka kai ta gidan ta a nan Unguwar rimi GRA kaduna. Ammi ma ta koma Bauchi wurin ‘yan uwan ta, a nan ne kuma zawarawa suka sa ta a gaba da neman ta amince ta aure su. Gaba daya Ammi bata da niyyar sake aure a rayuwar ta don haka ne ma bata bada fuska ba, Baffan ta ya lallashe ta akan ta amince tayi auren amma ta qi. A cewar ta duk ba don Allah suke son ta ba sai don dukiyar ta da ta ‘ya’yan ta. Da haka ne baffan ta ya kyale ta domin shima ya lura da hakan. Bayan Aliyu ya koma UK domin fara aiki Allah ya taimake shi domin yana da qoqari sosai wanda yasa cikin shekara biyar ba qaramin kudi yayi ba. Tuni yayi shawara da Daddy akan yana so ya fara gini a garin Kaduna wanda yayi haka ne saboda ya zauna kusa da ‘yar uwar shi Nafisa. Daddy yayi na’am da wannan shawarar. Ba tare da bata lokaci bane ya turo da zanen ginin da yake so tare da kudade masu yawan gaske aka fara gini a nan Ishaku road dake Malali GRA Kaduna. Ammi da Nafisa basu san Aliyu yana gini ba. Haka kudaden shi masu yawa na gado yayi amfani da su ya gina kamfanin tsara gine gine guda biyu a Kaduna da Katsina. An tsara masa ginin sa yadda da ka kalla kasan ba qananan kudade aka kashe ba. Tsarin Gidan Aliyu Muhammad an gina shi benaye uku ne kowanne a cikin get din shi a kan layi daya, amma kuma akwai qananan qofofi a cikin gidajen wadanda suka sada kowanne da dayan (ma’ana ba sai ka fita ta babban get din daya sannan ka shiga dayan ba) gaba daya ginin iri daya ne, abin da ya bambanta su shi ne kala na fenti. An tsara kowanne bene da lafiyayyun faluka guda biyu a qasa da dakunan bacci guda biyu, kicin da store da dinning. A Sama kuma akwai falo daya da kuma dakunan bacci guda uku sai wani daki da aka ware Na musamman Wanda turawa ke kira (study). A saman gidajen akwai wurin shaqatawa na musamman wanda turawa ke kira lawn wanda aka qawata shi da kayan hutawa. Kowanne daki a gidan Yana da kewayen shi lafiyayye da dressing room. Kayan alatu da aka wadata gidajen abin kallo ne. Aliyu ya Sa an zuba komai da komai a gidajen guda biyu, dayan kuma aka bar shi babu komai. A wani bangare Na gidajen an shuka furanni kala-kala wadanda suka kewaye wani swimming pool mai masifar kyau, gabadaya qasan wurin carpet grass ne. STORY CONTINUES BELOW A tsakar kowanne gida an sa wannan famfon na zamani mai feso ruwa (Fountain) gwanin ban sha’awa. An rufe ko ina na tsakar gidan da lafiyayyen interlocks. Daga gefe kuma aka kafa wata rumfa ta zamani wadda daga gani kasan gareji ne na motoci. Akwai kuma dakuna a gefe na ma’aikata wato staff quarters sai dakin mai gadi da ke can bakin get. Katangan gidan a zagaye take da wayar security (electric Fence) wadda sai da dare ake kunna ta. Gate din gidajen Aliyu kowanne da remote ake bude shi kuma a dukkan gidajen akwai masu gadi wadanda akayi hayan su daga ofishin security wadanda suke saka uniform. A gaskiya ko maqiyin Aliyu dole ne ya yaba ma tsarin gidajen nan. Abun ka da mai zanen gidajen da kanshi. Aliyu ya ajiye aikin shi na UK domin ya dawo gida Najeriya ya fara tafiyar da kamfanonin sa guda biyu. Garin Bauchi ya fara sauka inda ya nemi izinin tafiya da Ammi Kaduna domin a cewar shi yana buqatar ta a kusa da shi kuma bazai jure zama ba tare da ita ba. Baffanin ta sun amince domin zaman ta kusa da ‘ya’yan ta ba qaramin kwantar mata da hankali zai yi ba. Dangin Ammi babu laifi suna da arziki kuma duk da haka Aliyu yana kyautata musu matuqa shiyasa suke ji da shi. Tuni motocin shi sabbin fitowa sun shigo har guda biyar. (Mota tana cikin abubuwan da Aliyu yake so a rayuwar shi). Ammi tayi matuqar mamakin ganin tsarin gidajen da Aliyu ya gina. Yayi mata bayanin cewa gida daya nata ne wanda shima zai zauna tare da ita a ciki kafin yayi aure, daya kuma nashi ne idan yayi aure sannan kuma na ukun na Nafisa ne da mijin ta wanda yayi haka saboda baya son yin nisa da su. Aliyu ya roqi mijin Nafisa wato Yusuf akan su dawo gidan da zama ba don ya raina inda ya ajiye ‘yar uwar shi ba sai don yana so tana kusa da shi domin ya shaqu da ita. Aikuwa amincewar Yusuf bai zama matsala ba domin dama yana da shiri na musamman wanda ya tanadar ma su Aliyu. (Masu karatu menene shirin? Ku biyo ni ku sha labari) Aliyu Muhammad Kankia ya tashi cikin gata da soyayya ta iyayen shi da ‘yar uwar shi Nafisa, ya kasance mai ladabi da biyayya. Mahaifin shi Allah ya jiqan shi yayi la’akari da ilimin shi da addinin shi tare da hankalin shi wanda yasa shi tunanin lallai duk inda ya je bazai lalace ba, wannan ne ya sa ya tura shi UK karatu ba tare da tunanin wani abu ba. Aliyu kyakkyawan saurayi ne wanda sai an tona za’a samu mai kyau da aji irin nashi, irin shi ne ake kira one in town. Dogo ne kuma ba mai jiki ba, yana da gashi mai laushi da yawa a kan shi wanda yasa duk sati sai ya je an rage mishi. Ma’abocin saje ne a fuska wanda ya hadu da gemun shi ya kwanta a kan fuskar shi da dan gashin bakin shi lafiyayye, idan fuskar shi ta sha gyara sai ka rantse baqin balarabe ne. Aliyu bai kai Ammi da Nafisa haske ba amma kuma ya fi su kyau. Tun yana yaro Ammi take ce mishi baby na shiyasa har ya girma Babyn Ammi ake kiran shi. Ya kasance ma’abocin son gayu tun yana qarami, a rayuwar shi yana son sa qananan kaya (mutane na danganta hakan da zaman shi a turai amma Allahu a’alamu), babu yadda Ammi bata yi da shi akan ya dinga sa manyan kaya ba amma ya qi. Da ta takura mishi ne ya dinka yaduduka kala-kala ya zuba a durowa amma sun gagare shi sakawa. Aliyu baya siyan kaya ko wanne iri, komai nashi designer ne kama daga kayan sawa, takalma,turaruka, man shafawa kai hatta brush na wanke baki. Aliyu baya da hayaniya ko kadan kuma baya son a ishe shi da surutu, mutane wadanda basu san halin shi na miskilanci ba sukan danganta hakan da wulaqanci amma kuma sam ba haka bane. Asali ma abun hannun shi bai taba rufe mishi ido ba, yana da kyauta sosai da son taimakon talakawa. Abu daya ne baya so shine ka ja shi fada kuma ka qi bashi haquri, toh idan kuwa irin haka ta hada ku sai ya mayar da kai abin kwatance a gari. Banda addinin shi babu abinda Aliyu ke bala’in so a duniyan nan irin mutane biyu, Ammi da Nafisa sai kuma qila matar da zai auro wacce bai riga ya gan ta ba tukun. Haka kuma yana bala’in son mota a rayuwar shi, da zarar mota ta fito toh idan fa tayi mishi duk tsadar ta zaka gan shi da ita. STORY CONTINUES BELOW Shaquwar da ke tsakanin shi da Nafisa har mamaki take ba Ammin su. Rabuwar su ta farko ita ce lokacin da ya tafi UK wanda da tilastawan mahaifin su Allah ya jiqan shi ya tafi. Har zazzabi suka yi na rabuwa da juna wanda shi Amina tayi zaman jinyar shi a can yayin da Ammi tayi zaman jinyar Nafisa a nan. Wani hali kuma na Aliyu shine mugun Sabo, yayi mugun sabo da abincin gidan su wanda duk inda ya je ya gwammace ya zauna da yunwa, shiyasa tafiyar shi UK sai da Ulcer ta kama shi wadda tayi mishi mugun kamu. Lokutta da dama idan ta tashi har suma yake yi, tun mahaifin su yana raye sun sha zuwa UK duba shi a duk lokacin da ta tashi, dalilin da yasa ya koma gidan Amina da zama kenan duk da a wurin ta ma ba wani cin abincin yake yi ba. Ammi kadai take sa shi a gaba ya ci abinci shiyasa har gobe take kiran shi babyn ta. Kyau da aji irin na Aliyu ne yasa mata suke mutuwan son shi, a lokacin da yake UK ya sha wahala da ‘yan mata shiyasa a koda yaushe yana cikin daki yana karatu, idan ka gan shi a waje toh lakca ya shiga. Abokanen shi Sulaiman da Bilal har tausaya mishi suke yi. Akwai wata Asma’u ‘yar Najeriya da take bala’in son shi a lokacin amma ganin baya kula mata ne yasa ta haqura har ta nemi da ta zama qawar shi akan cewa zata taimaka mishi ta korar mishi ‘yan mata masu nacin da ke bin shi. Asma’u tayi nasaran kora mishi su akan cewa ita ce budurwar shi wanda a wurin Aliyu shiri ne amma kuma ita a wurin ta addu’a take ta zama budurwar shi a gaske. Zamu iya cewa Asma’u ita kadai ce macen da Aliyu ya sakar ma fuska a dalilin raba shi da tayi da ‘yan naci. A lokacin har su Bilal sun zata akwai soyayya a tsakanin su amma ya gwada musu babu komai sai zumunci. Aliyu ya bar makarantar lokacin Asma’u tana aji biyu. Ko da ya bar makarantar bai sake waiwayar ta ba tunda dama babu komai tsakanin su kuma dama shi mata basu gaban shi. Da ya dawo Naijeriya ma matan basu bar shi ba, haka kuma har yanzu babu wadda tayi mishi. A cewar shi duk macen da ta zubar da mutuncinta ta nemi namiji da ya so ta ba matar aure bace. Shi kam har yanzu bai ga matar aure ba. Burin shi akan matar aure tun yana yaro bai wuce na son auren mace wadda zata so shi tsakani da Allah ba, sannan wadda zata kula da shi yadda yakamata sannan kuma mai dogon gashi domin kuwa a rayuwarshi yana bala’in son mace mai dogon gashi (toh Aliyu, Allah ya baka irin wadda kake nema) A yanzu haka shekarun Aliyu ashirin da tara a duniya wanda idan an fadi maka zaka yi mamaki ganin tarin dukiyar da Allah ya mallaka mishi. Kamfanonin shi sun fara aiki, ya zuba ma’aikata graduates wadanda suka qware a fannin gine gine, da admin da kuma accounting. Abokanen sa wadanda suka yi karatu tare wato Suleiman da Bilal duk da suna ayyukan su suma ya basu bangarori daban daban a kamfanin suna kula da shi a dalilin sun qware sosai a harkan zanen gidaje. Dayake bayan sun kammala makarantar sun dawo najeriya sun samu aiki yayin da shi Aliyu ya yi aiki a can UK din. Cikin lokaci qanqani kamfanin Aliyu yayi fice a arewacin Najeriya, ya samu projects masu yawa musamman daga Abuja a dalilin manyan abokanen mahaifin shi, wannan ne yasa ya fara gina branch a nan garin Abuja domin aikin yana ma ma’aikatan shi na Kaduna da Katsina yawa. A shekarar da ya dawo ne ya biya musu Hajji da shi da Nafisa da Ammi harda Yusuf dukda sun sha zuwa lokacin mahaifinsu yana raye. A yanzu haka Nafisa tana da wata qatuwar Plaza anan cikin garin Kaduna wanda Aliyu ya zana mata sannan ta gina a cikin kudin gadon ta. Plazan tana dauke da shaguna guda tamanin wadanda tuni an kame su. Idan baku manta ba Alhaji Ibrahim da Alhaji Muhammad suna da qanwa mai suna Hajiya Mariya, Hajiya Mariya tayi aure ne a garin Lagos. Maigidan ta Alhaji Umar Salisu ya kasance yana da mata Hajiya Umma sannan ya auro ita Hajiya Mariya. Hajiya Umma ta kasance masifaffa wadda hatta maigidan zama a qarqashin ikon ta yake yi. Hajiya Mariya tayi zaman haquri da Hajiya Umma har ta kai lokacin da ita Hajiya Umma tayi sanadiyyar sanya Alhajin ya sake ta saki uku ba tare da wani qwaqwaran dalili ba. Ta dawo Katsina da cikin ta wata hudu. ‘Yan uwan ta sun yi baqin cikin abinda ya faru domin suna bala’in son ‘yar uwar su. Bayan dogon bincike ne suka gane cewar sharrin Hajiya Umma ne ya fidda ‘yar uwar su daga gidan mijin ta sai suka haƙura suka bar ta da Allah shi kuma Allah ya kubutar da shi daga sharrin ta. Hajiya Mariya saboda damuwa da tasa a ran ta ne hawan jini ya kama ta. Ga wahalan da cikin yake bata. Babu kyakkyawar kulawan da Alhaji Ibrahim bai bata ba wanda a gidan shi take zaune amma kamar ana qara zuga ciwon ne. Alhaji Muhammad ne ya bada shawarar a fitar da ita turai kawai domin ta ga qwararrun likitoci, Likitocin sun yi iya qoqarin su wurin sama masu lafiya ita da abinda ke cikin ta. Sun yi nasara tunda har cikin ya kai wata takwas. A watan shi na takwas din ne aka yi mata aiki domin ciro abinda ke cikin ta wanda yayi sanadiyar rasuwar ta. ‘yar jaririyar da hajiya Mariya ta bari kyakkyawa mai kama da ita sak, aka ba Mummy ita ta cigaba da rainon ta. Allah sarki Alhaji Ibrahim da Alhaji Muhammad sun ji mutuwar ‘yar uwar su Mariya, dole suka yi haƙuri suka bi ta da addu’a. ‘Yar jaririyar marigayiya Haj. Mariya ta ci sunan uwar ta Maryam amma ana kiran ta Hanifa, ta girma a gidan kawun ta kuma mahaifin ta Alhaji Ibrahim. Idan ka gan ta a gidan zaka rantse ita ce autar Mummy ba Kabir ba. Hanifa tayi karatun ta a APTI a garin Adamawa inda ta karanci fine art. Tun tana qarama take masifan son Aliyu, kullum maganan ta daya biyu baya wuce na Aliyu. Har yanzu da ta girma bata canza zani ba, gashi shi kuma Aliyun bai san tana yi ba. Kabir kuma tun da Hanifa ta tashi a gidan su yake mutuwar son ta. Burin shi idan sun girma su yi aure. Mahaifin ta Alhaji Umar ya rasu a lokacin tana da shekaru goma a duniya wanda sai da ya zo ya nemi gafara a wajen su Daddy da ita kanta Hanifa. Hanifa ta kasance ‘yar gata gaba da baya, Kowa yana tausaya mata domin kuwa marainiyar Allah ce, babu abin da ta nema ta rasa a rayuwar ta. Shekarun Hanifa a yanzu Ashirin da daya, tun da ta ji Aliyu ya dawo kaduna ta koma gidan Ammi da zama kuma tana aiki a kamfanin shi dake nan Kadunan. A kowanne ƙarshen wata Aliyu yana ziyartar kamfanin shi na Katsina domin ganin yadda abubuwa ke tafiya a zahiri duk da yana sane da komai da ke faruwa a kullum ta yanar gizo da sauran kafofin sada saƙonni na nasara. Tare da Nafisa yayi tafiyar a dalilin ta na ta dade bata je Katsinan ba. Gashi kuma a wannan karon ya hadu da Aisha wadda ta bata mishi rai. Washe gari bayan sun kammala breakfast suna zaune a falo, Umma da Salma da Aisha yayin da Abba ya fita Kasuwa, Aisha ce tace “Umma amma dai yakamata Ummi ta bi ni Kaduna tayi hutu tunda an bada hutun makaranta ko?”+ Umma ta kalli Salma tare da fadin “gaskiya yakamata, ai ta kwana biyu bata je ba” Kai tsaye Salma tace “ai dole ma in je ko don hankali na ya kwanta” Aisha ta kalli Salma da sauri tare da yi mata nuni akan lafiyar ta kuwa take magana a gaban Umma? Umma tace “me ya same ki a nan Katsinan da kike son hankalin ki ya kwanta akan shi?” Anan ne Salma ta ba Umma labarin abinda ya faru tsakanin ta da Mubarak tun daga farko har qarshe. Aikuwa Umma tayi mamaki har tana fadin “ka ji sakarai, shi wa ya gaya mishi ana irin wannan qaryan a zamanin nan…” aikuwa nan da nan ta sa su Aisha dariya, Aisha ta sa baki tana cewa “ai Umma sai na nemo shi na ci mishi mutunci ma” Umma ta daga ma Aisha hannu tace “babu ruwan ki da shi sarkin rigima, ku bar shi da Allah kawai, ke kuma Salma Allah ya baki wanda ya fi shi” Aisha tana dariya suka amsa da Ameen. Da wannan ne Aisha ta cire zancen zuwa wurin Mubarak daga ran ta. **************** Bayan sati biyu ne su Aisha suka fara shirin komawa kaduna, ranan da zasu tafi ne bayan sun kammala hada kayan su Abba ya kira musu wata mota da yayi musu shata wadda zata kai su har qofar gidan Inna. Bayan sunyi sallama da su Umma ne suka shige mota suka kama hanyar Garin Gwamna. ******************* KADUNA STATE Aisha dai bata tashi tuna saqon Inna ba sai da suka kai gadar Kawo kaduna. Salatin da Salma ta ji ta yi ne yasa ta tambaye ta “ke lafiya??”, Aisha ta kalli Salma tace “Ummi na shiga uku Inna zata zane ni, na manta mata saqon ta…” Salma ta fashe da dariya tare da fadin “Allah ya shirye ki Aisha, Umma ta bani ai, kwantar da hankalin ki” Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “huh… Thank God” suka yi dariya gaba dayan su. Sun isa gida lafiya, Inna tayi murnan ganin Salma sosai. Shi kuwa Zaid mutumiyar shi ya sa a gaba yana tuna mata wani cartoon da za’a fara qarfe takwas na daren yau. Salma tana ta mamakin wannan irin mugun kallon cartoon da suke yi. Inna dai sai da ta ga garin kukan ta sannan ta qyale Aisha har Salma na fadin da an biye mata kuwa sai dai ta sha zana. Suka dinga dariya. Baba ma da ya dawo yayi murnan ganin Salma domin a cewar shi ma bata son zuwa Kaduna amma yau ta wanke kanta. ***************** Yusuf ya cigaba da zuwa gidan su Inna, tun Aisha tana kauce mishi har dai suka saba a dalilin wasa da raha da yusuf ya qware a kai. Idan ka gan shi a gidan ana hira da shi sai ka rantse dan uwan su ne na jini. Ya lura da Aisha mayyar kayan zaqi ce, shiyasa a kodayaushe idan zai zo gidan da qatuwar leda yake zuwa. Amma da yake Aisha akwai wayau sai ta tofe kayan da Addu’a sannan take ci, a cewar ta idan ma ya zuba magani ba zai kama ta ba. Su Inna suna shan dariyar wannan al’amarin (Aisha kenan) STORY CONTINUES BELOW *************** Akwai wata ranar asabar tun da safe Aisha da Salma suka tashi da wuri domin su hada kek wanda tun jiya suka yi cefanen kayan hadin sa. Sun shiga kicin sun fara hadawa ne suka ankara da babu baking powder wanda a sanin su sun siyo shi. Salma ce tace ”lallai manto shi muka yi a shagon da muka yi siyayyan nan, gashi Zaid yana baccin shi na mamaki da ya karbo mana ai”. Aisha ta ce “ai laifin mai shagon ne tunda shi ya hada kayan, yanzu dai tunda na yi wanka bari kawai in je in duba idan sun fito sai in karbo ko kawai in siyo wani” Ta wuce daki ta shiryo cikin baqin jeans da wata qaramar T-shirt green, ta sanya after dress baqa sannan ta nado gyalen ta dan qarami shima kalan green, babu abinda ta shafa a fuskar ta, wallet dinta ta dauka sai makullin mota ta fita. ***************** Aisha tana tafe a mota tana jin waqa, dayake bata cika son kalle kalle ba sai ta dage gilas din motar sama, ta hau kan titin Ogbadu street ta iso daidai inda Ishaku road ya hadu da titin, bata ankara ba sai kawai ta ji ta yi karo da wata mota qirar sabuwar BMW baqa wadda kwata kwata bata wuce watanni biyu da shigowa Najeriya ba, A lokacin kuwa motar tana shirin hawa Ogbadu street daga Ishaku road. A nan take mai motar ya taka birki yayin da ita ma ta tsaya, tuni mutane sun taru a wurin domin sasanta rigima. Mamallakin motar ya fito daga motar shi rai a bace yayin da Aisha ma ta fita daga motar ta ba tare da kallon mutumin ba ta fara zazzaga mishi masifa tana fadin “malam meye haka zaka shige mun gaba har kayi mun barna?” Shima duba tashi motar yakeyi yace “na miki barna ko kika mun barna?” Dagowan da suka yi suka kalli fuskokin su ne Aisha zaro idanuwa tace “you??”, ba wani bane face Aliyun Ammi. Ran shi a bace yace “ya salam, ba ke ce kika katse mun meeting dina a katsina ba last month?.” Nan da nan ‘yan kallo suka fara ba Aliyu haquri.. kallon su yayi sannan yace “kowa ya kama gaban shi ku bar ni da ita” aikuwa kowa ya juya yayi tafiyar shi tunda dai sun ga al’amarin ya fi qarfin su. Bayan kowa ya watse ne ya juyo ya cigaba da fadin “…..Wato ma har biyo ni kika yi nan Kaduna, wai ke wacce irin mayya ce ne? Me kike so? Haka kawai ki yi ta bin mutum..” Aisha cikin bacin rai ta ce “kai malam dakata, meye matsalarka da ni ne? Banda qaddara babu abinda zai sa in bi ka domin baka isa in bi ka ba, asali ma kai yakamata inyi ma wadannan tambayoyin” Aliyu ya katse ta tare da fadin “haka nan baku iya tuqi ba ku dauko mota ku yi ta buga ma mutane kuna ja musu asara”. Aisha dai ran ta ya gama baci cikin fushi ta ce “kar ka damu zan biya ka kudin barnar da na maka” Aliyu wanda yake shirin komawa cikin motar shi don kar ya bata lokacin shi a banza ne yayi mamakin jin abinda Aisha ta fadi. Juyawa yayi don ganin da abinda zata biya shi barnar da tayi mishi. Ta koma cikin mota ta fiddo wallet din ta, tana qoqarin budewa ne ta ji muryar shi yana fadin “dubu dari da hamsin kudin barnar da kika yi mun na fasa mun wutar mota” Da sauri Aisha ta dago tare da zaro idanuwa. Yace “what? Baza ki iya biya bane? hakan ma da na gaya miki sai na cika”. Ya koma wurin motar shi ta gefen mai zaman banza ya bude glove compartment ya zaro naira dubu dari a bandir dinta na ‘yan dubu daya ya nufi motar Aisha ya jefa kudin ta windon motar ta sannan ya dawo inda take tsaye yace “kiyi amfani da kudadden can domin duba lafiyar motar ki” STORY CONTINUES BELOW Har ya juya zai tafi sai kuma ya dawo ya ce “idan canji ya ragu don Allah ki yi qoqari ki biya kudin mota dasu ko ki sha mai domin ki koma katsina saboda kar mu sake haduwa a nan garin, because i assure you.. you won’t like our next encounter” Aisha wadda ta cika da mamaki tayi saurin dakatar da shi tare da shan gaban shi tace “malam ina so ka sani cewa insha Allah zan biya ka kudin barnan da na maka” Ta juya zata dauko mishi kudadden shi da ya jefa mata a motarta ne yayi murmushi tare da fadin “All the best” Ya wuce ya shiga motar shi yayi reverse don komawa gida ya canza wata motar tunda dai Aisha ta bata mishi wannan. Ya tafi ya bar Aisha riqe da kudi tana tunanin inda zata samo dubu dari da hamsin ta hada mishi da dubu darin shi ta mayar mishi (ku ji Aisha da rigima) Ta koma mota ta tarar da wayar ta tana ringing har ta tsinke, Salma ce. Da ta kira ta ne take tambayan ta “Lafiya na ji ki shiru?” Aisha cikin sanyin murya tace “yi haquri Ummi ga ni nan” ************** Salma har ta gaji da jiran Aisha ta dawo falo inda suke ta hira da Inna sai ga ta nan ta shigo da sallama. Salma ta tambaye ta “haba sis ya aka yi kika dade haka?” Aisha tayi murmushi tace “hold up ne ya bata mun lokaci”. Inna tace “hold up da safen nan? kuma ma ranar asabar?” Salma dai ta fahimci akwai magana don haka ne tace “tunda rana ta yi gashi zamu girka lunch gara mu bar kek din sai gobe kawai”. Aisha ta wuce kicin ta ajiye baking powder din sannan ta wuce daki. Kwance take a kan gado idanuwan ta a rufe tana tuno abinda ya faru tsakanin ta da Aliyu, babu abinda take fadi sai “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”. Salma ta shigo tana tambayar ta “Aisha lafiyar ki kuwa?” Aisha ta taso daga kwanciyan da ta yi ta kalli Salma ta ce “na shiga uku Ummi, na sake haduwa da gayen nan wanda muka yi rigima da shi a kamfanin da Mubarak yake aiki a Katsina” Salma cikin mamaki tace “dagaske?? Bani labari” anan Aisha ta zayyana mata abinda ya faru tun daga farko har qarshe. Salma ta saki ajiyar zuciya tare da fadin “Aisha ba kya jin magana, laifin ki ne kuma kin sani, me ya hana kawai ki bashi haquri a wuce wurin? Yanzu ina zaki samo dubu dari da hamsin ke ba aiki ba, ni kaina da na fara aikin kwata kwata nawa gareni a account balle ke”. Aisha cikin sanyin murya tace “wallahi Ummi na san ban yi daidai ba kawai rai na ne ya baci amma Insha Allahu dole in nemi aiki kuma in biya shi kudin shi..” Salma tace “Allah ya baki sa’a, sarkin rigima” Aisha tayi murmushi tare da fadin “amma fa Ummi gayen nan ya hadu wallahi, yau na qara kallon shi da kyau, wallahi Ummi ban taba ganin kyakkyawan namiji kaman shi ba” Salma ta ce “hmmm… su Aisha kenan, har ya fi ki kyau?” ta zaro idanuwa tace “Ummi ni ai fari ne ya sa ake ganin kyau na, wannan gayen ya taka ni kyau nesa ba kusa ba, kawai dai yayi kyan dan maciji ne tunda babu hali mai kyau” Salma tayi dariya sosai tace “ni dai ban yarda yana da mummunan hali ba domin dai duk rigimar da ta shiga tsakanin ku ke ce mai laifi, Allah dai ya raba ku lafiya”. *************** Aliyu ne kwance a kan cinyar Ammi da yamma yayin da take shafa kanshi tana tambayar shi “babyna ko dai a kira Dr. Sadiq ne?” Yace “haba Ammi ciwon kai ne fa kawai, bari in sha magani qila ya sauka” tace “toh ai baka ci abinci ba, idan ka ci sai ka sha maganin”. Yace “bana jin yunwa” tace “kayi haquri ka ci babyna, ni zan baka da kai na ka ji?” Yace “toh Ammi”. STORY CONTINUES BELOW Ammi ta kira mai aikin ta Hafsat tace mata ta shirya ma Aliyu abinci a dinning. Aliyu ne yace a kawo abincin falo kawai. Hafsat ta jera mishi abinci kala-kala a gaban shi da robar fresh milk da ruwa, Ammi tace mata ta kawo mata First aid kit. Aliyu wanda ya tashi zaune ne yace “Ammi duk wannan abincin ni kadai?” Tace “zaba zaka yi ai baby na, bance sai ka cinye duka ba” Ta bubbude warmers din yayinda take tambayan shi “wanne zan zuba maka?” farar shinkafa ya nuna mata da miyan hanta. Ammi ta zuba mishi tana bashi a baki. Nafisa ce ta shigo falon tare da fadin “babyn Ammi yau kuma shagwaba ake jin yi ne?” Ammi tace “Nafisa Babyna ne ba lafiya” a rude ta iso wurin shi ta zauna ta dafa kan shi tana fadin “Subhanalillahi, bros me ke damun ka? Ko dai rashin hutu ne?” Yayi murmushi tare da fadin “kwantar da hankalin ki Anty feena, ciwon kai ne kuma idan na sha magani zai sauka”. Cikin siyasa Ammi ta dinga tura mishi abincin har ya cinye dukda ma wanda ta zuba mishi babu yawa, daga nan ya sha magani ya ce musu bari ya je daki ya kwanta. Har dakin shi Nafisa ta raka shi sannan tace “idan kana buqatar wani abu ka kira ni ka ji?” murmushi yayi yace “thanks anty Feena” ta shafa kan shi sannan ta wuce ta fita. Bayan Nafisa ta dawo falo ne ta taras da Hafsat tana kwashe kayan abincin da Aliyu ya ci, har qasa ta durqusa ta gaida Nafisa sannan ta nufi kicin. Nafisa ta zauna kusa da Ammi tana fadin “wallahi Ammi babyn ki harda rashin hutu yake sa shi ciwon kai, baya hutawa” Ammi tace “toh ya zanyi da shi kin dai san yadda yake son aikin nan nashi, Allah dai ya ba shi lafiya” Nafisa tace “Ameen, wai ina Hanifa ne?” Ammi tace “kin san Hanifa da son zuwa salon, wai gashin ta yayi datti shine ta je wankewa”. Nafisa tace “Hanifa hooo… wannan gashi yana shan wanki, duk sati tana salon” Ammi tayi dariya tace “Hanifa kenan” ************ Ya farka daga bacci ne ya gan ta zaune a kan resting chair dinshi ta kafa mishi ido kamar wadda ke gudun kada a sace shi, ganin ya farka ne ta tashi da sauri ta dawo kusa da shi tana fadin “yaya Aliyu ya kan, ya daina ciwo?” addu’ar tashi daga bacci yayi yayin da yake kallon ta yana murmushi yace “Ya daina ciwo Hanifa, kin dawo daga salon din?” Tace “eh yaya Aliyu, Ammi tace mun kana bacci wai kan ka na ciwo shine na shigo in gaishe ka”. Yayi murmushi yace “Ammi kenan, yanzu haka har Katsina nasan ta kira don ta gaya musu ciwon kan nan” Hanifa ta fashe da dariya tace “ai kai babyn ta ne, what do you expect” Sun dan taba hira kadan aka kira Sallah. Hanifa ta wuce daki don gabatar da Sallah yayin da shi kuma ya shiga wanka ya yi alwala don tafiya masallaci. ************** Yau kusan kwana uku kenan Aisha tana tunanin yadda zata bullo ma matsalar da ta jefa kan ta a ciki. Tana zaune a falo ta yi tagumi kamar wata marainiya. Yusuf ne yayi sallama wanda bata ji ba har sai da Inna ta fito daga daki tana fadin “Aisha baki ji ana sallama bane?” Aisha ta zabura tare da fadin “wallahi Inna ban ji ba” ta miqe da sauri tare da daura gyalen ta a kai ta leqa, ta amsa sallamar tare da bashi izinin shigowa. Inna tace “a’a Yusuf ne, sannu da zuwa” bayan sun gaisa ne ta wuce kicin wanda dama can ta nufa… a dalilin jin sallama ne ta tsaya falon. Suna gaisawa da Aisha ne Salma ma ta fito daga dakin su ta zauna suka gaisa. Hira suke yi amma Yusuf ya lura hankalin Aisha baya tare da ita. Tambayar Salma yayi “wai me ke damun Aisha ne yau? Naga kamar tana cikin damuwa” Salma ta kalle ta tayi murmushi ta ce “hmmm, ai sis dinnan tawa rigima ta janyo ma kanta wanda taurin kai irin nata ne ya ingiza ta”. Cikin mamaki Yusuf ya gyara zama yace “wacce irin rigima?” A nan Salma ta zayyana mishi labarin rigimar Aisha da Aliyu tun daga farko har qarshe. Yusuf yayi dariya yace “dadi na da Aisha akwai courage da determination, shiyasa take birge ni. Ai wannan ba wani abu bane, yanzu idan na fita zan ciro miki kudin a banki sai in biyo in kawo miki ki bashi kudin shi” Aisha tayi caraf tace “a’a ni bazan karbi kudin ka ba, idan na karbi kudin ka ai na saba alqawarin da nayi ma kaina na cewa zan fara aiki wanda da kudin aikin ne zan biya shi” Yusuf da Salma suka kalli juna cikin mamakin hali irin na Aisha. Yace “toh yanzu gaya mun akwai wani taimako da zan iya yi don in taya ki cika alqawarin?” Aisha ta kalle shi tace “da dai zaka iya taimaka mun ka taya ni samun aiki”. Yusuf yace “an gama gimbiya, dauko takardun ki zan kai miki wani kamfani, Insha Allah zasu dauke ki” Cikin murna ta miqe da sauri tace “thank you so much bari in je in dauko” kafin ma ya amsa har ta ruga daki. Salma tayi murmushi tare da fadin “an gode Yusuf Allah ya saka da alkhairi” Yusuf yace “babu komai Salma, ai kai aka yi wa”. Salma ta kalle shi tare da maimaita maganan da yayi a ranta. Aisha ce ta fito da takardun ta a envelope ta miqa mishi. Bayan ya tafi ne Salma take tambayan Aisha “me ke tsakanin ki da Yusuf dinnan ne?” Aisha tayi mata wani irin kallo tace “me kuwa ke tsakani na da shi banda mutunci??” Salma tayi murmushi tare da fadin “anya kuwa ba son ki yake ba?” Nan da nan Aisha ta hada rai tace “idan ma so na yake wallahi ya daukar ma kanshi kaya” Salma tace “toh meye matsalar shi?” Tace “baya da wata matsala Ummi amma ni dai bana son shi, kin san an ce soyayya gamon jini, ni kuwa nawa jinin bai gamu da nashi ba”. Salma tace “wato jinin ki bai hadu da nashi ba shine kika dora mishi nauyin samo miki aiki ko?” Aisha ta kalli Salma cikin mamaki tace “wannan yayi ne don Allah don haka mu bar zancen ma” Salma ta fashe da dariya tace “Aisha kenan, you are funny i swear”. ************ Yusuf yayi nasarar samo ma Aisha aiki a wani kamfani mai zaman kan shi, ya kawo mata appointment letter har gida wanda akan takaradar sai ranar laraba wanda yayi daidai da rana ta farko a sabon wata ne zata fara zuwa. Abinda Aisha bata lura da shi ba shine sunan kamfanin wanda aka rubuta akan takardar wato ‘AMK COMPANY NIGERIAN LIMITED’ Aisha ta sanar da su Baba aikin da Yusuf ya samo mata sun kuma yi murnan jin wannan labari. Ta kuma kira su Abban ta a waya ta shaida musu kuma su ma sunyi farin ciki sannan sun mata nasihohi akan ta riqe amana a wurin aikin nata sannan ta kare mutuncin ta, Allah kuma ya bata sa’a.+ *********** Ranar litinin da safe Ammi da Aliyu zaune a kan tebir suna breakfast yayin da Hanifa ta fito sanye cikin english wears wanda ita dama shigar ta kenan a kullum, ta iso cikin sauri tace “good morning Ammi, good morning yaya Aliyu”. Ammi ta amsa tare da fadin “ke dai Hanifa ba kya rabuwa da wadannan kayan, ni dai naga ko Amina da tayi karatu a turai ba haka tayi ba gashi har zama ya kama ta a can, wai a Adamawan haka ake gayu?” Aliyu yayi murmushi jin maganan Ammi. Hanifan kuma ta bata rai tare da fadin “Ammi ki duba fa ki gani daga sama har qasa jiki na a rufe yake, gashi na rufe kaina” Ammi ta ajiye kofin shayin da ke hannun ta tace “na gani Hanifa amma ina so ko da dogayen rigunan nan na zamani da ‘yan mata ke yayi kiyi qoqari ki dinga sakawa, kwanaki ma naga da nayi miki magana har kin fara sa abaya amma yanzu kin watsar” Aliyu ne yace “toh ai Ammi ko da ta fara sakawa can take rataye ta a hanga a ofis” Hanifa cikin shagwava tace “wallahi nauyi suke mun shiyasa bana son sakawa” Ammi cikin lallashi tace “ki dinga koyi da Addinin mu, kada ki biye ma yahudawan nan, ki kare mutuncinki a duk inda kike wanda shi zai sa mutane su ga girman ki kin ji Hanifa?” tace “toh Ammi bari in je in sa after dress” Bayan ta koma daki ta saka abaya ne ta dawo ta kammala breakfast din sannan ta miqe ta ce “Boss ni na tafi ofis, sai kazo” Aliyu yace “Alright”. Bayan sun kammala breakfast ne suka dawo falo suna kallon TV. Nafisa da Yusuf ne suka yi sallama, bayan sun gaisa da su Ammi da Aliyu ne Yusuf ya wuce ofis. Nafisa ce ta kalli Aliyu ta ce “ai nayi zaton ka gudu ne” Yayi murmushi yace “ai Ammi ta hana ni guduwa” Ammi tace “ai gara ka tsaya ayi maka check up dinnan, ka daina wasa da lafiyar ka”. Ba wani suke jira ba face likitan Aliyu mai suna Dr Sadiq wanda yake zuwa ko wacce ranar litinin domin duba lafiyar shi. Da farko ofis likitan yake bin shi wanda lokutta da dama idan ya kira shi akan gashi nan zuwa sai yace mishi yayi zaman shi ya bari sai sati mai zuwa, wata rana ma har sai likitan ya zo sai a bashi haqurin shi Aliyun yana meeting bazai samu ganin shi ba. Da Ammi ta lura da hakan ne ta mayar da check up din gida, A yanzun ma watarana guduwa yake bata sani ba. Toh da alama dai yau anyi sa’a bai gudu ba. ************* A bangaren su Aisha kuwa tun a jiya ne Inna ta bata saqon kaya akan ta kai gidan wata hajiya Fatima da ke No 30 ishaku road (idan baku manta ba sana’ar Inna kenan sayar da atamfofi da sauran su), atamfofi ne guda bakwai da ita hajiyar tace a kawo mata wadanda zata ba ma wani dan uwanta gudumuwa domin ya sa a lefen auren shi. Tun da safe kuwa bayan Aisha ta sauke Zaid a makaranta ta wuce ishaku road. Tana tafe tana duba lambobin gidajen, aikuwa tana kaiwa No 13 sai ta tsaya. Ta fito daga motar, sanye cikin baqar jallabiyya mai kyau wadda tayi fitting din jikin ta, ta nade kanta da gyalen jallabaiyan ta fito balarabiyar ta sak. Ta bude qofar bayan motar ta fiddo ledan atamfofin sannan ta rufe motar. STORY CONTINUES BELOW Abun da ya bata mamaki shine tsarin gidan da take shirin shiga wanda gidan irin shi guda uku ne, N0 12,13,14 sai dai kowanne da kalan shi. A ranta ne take fadin “ikon Allah, wai duk wannan gidan mutum daya ne, qila mata uku ma gare shi. Lallai masu kudi suna hutawa”. Ta nufi get din gidan ne ta danna qararrawa, nan da nan maigadi ya bude wata ‘yar qaramar windo a jikin get din domin ganin ko waye. Anan ta shaida mishi cewa tazo wurin Hajiya Fatima ne, maigadin yace ta saurara. Intercom ya kira wanda a can bangaren Nafisa ce ta amsa, bayan ya gaishe ta ne yace “Anty dama wata yarinya ce tace wai an turo ta wurin Hajiya babba” Nafisa tace “kace ta shigo” Aisha dai tana taka qafar ta cikin gidan hankalin ta ya tashi sakamakon wani irin danqararren gida da ta gani, tun daga interlocks din gidan nan har zinc din gidan abun kallo ne, cikin ranta ne tace “anya Inna nan gidan ta aiko ni kuwa??”, anan ne ta ce ma maigadin “sunan hajiyan da nazo nema fa Hajiya fatima, nan ne kuwa?” Maigadin yayi murmushi yace “nan ne ‘yan mata, ga qofar can idan kin isa za’a yi miki jagora”. Aisha ta danna qararrawar qofar Ammi, Hafsat mai aikinta ce ta bude qofar, bayan sun gaisa ne Hafsat ta mata izinin shiga. A lokacin da Aisha ta shiga lokacin shi kuma Aliyu ya fito daga dakin shi yana haurawa sama domin ganin Dr sadiq wanda ya ke jiran shi a falon sama. Aisha ta samu kujera ta zauna yayinda ta ke ta bin falon Ammi da kallo tana mamakin dukiyar da aka narka a ciki. A ranta ta cigaba da fadin “zan so in ga mamallakin gidan nan” Maganan Nafisa ne ya katse mata tunani inda taji tana fadin “sannu da zuwa baiwar Allah, daga ina?” Cikin qanqanin lokaci Aisha ta qare ma Nafisa kallo wanda a ran ta tace “lallai kam kin dace da wannan gidan”. Ta yi gyaran murya tace “Ina kwana” Nafisa ta amsa sannan Aisha ta ce “dama an aiko ni wurin Hajiya Fatima ne” Nafisa tace “mu je tana sama” Nafisa tana gaba yayin da Aisha ke biye da ita, Aisha ta lura da dangyasa kafa da take dan yi wanda sai ka kula sosai zaka gane, a ranta tace “Allah sarki kila hatsari ta samu” A lokacin da suka hauro saman Dr sadiq yana qoqarin yi ma Aliyu bayanin abubuwan da zai cigaba da kiyayewa, kujerar da Aliyu yake zaune ita ce wadda hanyar da dakin Ammi yake bayan ta, don haka ne har Aisha ta samu damar wucewa bai gan ta ba. A dalilin motsi da ya ji ne ya waigo wanda a lokacin bayan ta yayi nasarar gani. Aisha ta shiga dakin Ammi cikin sallama yayin da Ammin ta amsa sallamar. Nafisa ce tace “Ammi wai an aiko ta wurin ki” Aisha ta durqusa har qasa ta gaida Ammi” ta amsa tare da fadin “tashi ki zauna kin ji”. Fuskar Ammi da Aisha ta gani yayi mata masifan kama da ta maqiyin ta wanda har ta fara zargin ko gidan su ne tazo sannan wannan mahaifiyar shi ce. Bata ankara bane suka ji muryar Aliyu yana fadin “Anty Feena na tafi ofis”, Nafisan ce ta fita tare da fadin “har an gama check up din?” yace “eh, na ma yi latti sosai” yana sauka daga steps ne ya ce ”ki gaya ma Ammi na tafi sai na dawo” tace “i will, take care” har qasa ta raka shi. Muryar Aliyu da Aisha ta ji tayi tunanin kamar ta taba jin ta a wani wuri. Ammi ce tace “wa ya aiko ki?” Tace “dama kaya ne Inna Hajara tace in kawo miki” cikin mamaki Ammi tace “anya ni kuwa?” anan ne Aisha tace “eh toh bari dai in kira ta in ji qila ma nayi batar hanya”. STORY CONTINUES BELOW Aikuwa ko da Aisha ta kira Inna sai tace mata “No 30 nace ba No13 ba, da na sani da hausa na gaya miki” Aisha dai saida tayi dariya. Bayan ta kashe waya ne tace “yi haquri Hajiya ashe No 30 tace, gashi sunan ku daya ne” Ammi cikin fara’a tace “haba babu komai, wanne irin kaya ne? Na sayarwa ne?” tace “Eh, atamfofi ne” anan ne Nafisa ta shigo tana gaya ma Ammi “babyn ki yace ace miki ya tafi” Aisha cikin mamaki ta kalli Nafisa a ran ta tace “yanzu mai wannan muryar da naji shine babyn? Lallai kam wannan shagwababe ne, kodayake yanayin gidan da ya taso ne ba sai an fadi ba dan gata ne gaba da baya” Ko da ta miqe zata tafi ne ta ji Ammi tana fadin “mu ga atamfofin wanne iri ne?” Aisha ta fiddo atamfofin ba tare da tayi magana ba saboda dai a zahiri ba sanin sunayen su tayi ba tunda ba saka irin su take yi ba. Ji tayi Nafisa na fadin “Super wax ne Ammi masu kyau kuwa”. Ammi tace “gaskiya sun yi kyau” ta kalli Aisha tace “idan kin samu lokaci ki kawo mun guda ashirin kin ji” Aisha tace toh” Nafisa tace “kinga mun huta da zuwa kasuwan ma ko Ammi?” tace “eh wallahi nima tunanin da nayi kenan”. Nafisa ta tambayi Aisha sunan ta wanda ta fadi Mata sannan tayi musu sallama ta tafi. ************* A bangaren Aliyu kuwa lokacin da ya fita daga gidan ya tarar da motar Aisha a waje wadda ya qare ma kallo tas har yake tunanin ina ya san motar, da ya kasa tunawa ne ya hau titi yayi tafiyarshi. ************** Aisha ta kai saqon Inna ta dawo gida. Inna ta ce “Aisha sarkin shirme an dawo?” Tayi murmushi tace “aikuwa dai Inna yau shirme na yayi miki babban kamu duk da ban san na nawa bane” Inna tace “fadi inji” Aisha ta gyara zama yayin da ta zayyana mata yanda suka yi da Ammi. Cikin murna Inna tace “eh lallai kin yi mun babban kamu” Salma tana ta dariya. Aisha ce tace “wai nawa ne atamfofin?” Salma tace “da yake ba kya daura atamfa ya za’ayi dama ki sani, dubu talatin da hudu kowanne guda daya” Aisha ta zaro idanuwa tace “shine hajiyar tace a kawo mata guda Ashirin?? Kuma fa wai kyauta zata yi da su, lallai masu kudi suna shagalin su”. Anan ne ta fara basu labarin gidan Ammi wanda suka dinga mamaki. ************* Washegari Aisha ta kai ma Ammi saqon ta da rana, Ammi da Nafisa sun yaba sosai da kayan. Ammi ta ba Aisha dubu dari bakwai, wanda a ciki ta bata kyautan dubu ashirin, dubu dari shida da tamanin kuma kudin atamfofin. Aisha tayi godiya. Kafin ta tafi ne Nafisa ta karbi lambar wayar ta itama ta bata nata. Bayan Aisha ta tafi ne Ammi ta ce “amma yarinyar nan tana da kyau wallahi, gashi da alama tana da hankali. Dama babyna ya neme ta don kuwa sun dace wallahi” Nafisa tayi murmushi tace “wallahi kuwa Ammi, ina son yarinyar, gata ‘yar qarama daidai Aliyu, perfect match. Yakamata dai ya fara shirin aure, nayi mishi magana a Katsina sai ce mun yayi wai sai Mustapha ya fara yi sannan zaiyi tunanin yi” Ammi tace “what? ai kuwa bai isa ba” Nafisa tana dariya tace “Ammi matsalar Aliyu fa ko kallon mata baya yi balle har yaga wadda tayi mishi, ga girman kai na bala’i, gani yake kamar zubda aji ne ya tsayar da mace yace yana son ta” STORY CONTINUES BELOW Ammi tace “ashe kuwa zanyi mishi auren dole kwanan nan, ya za’a ce duk kudin da Aliyu ya tara baya da mata, gaskiya zan fara takura mishi akan maganan aure” Nafisa tace “kin kyauta Ammi, gara a takura mishi in yaso sai a hada bikin shi ma da na Mustapha kawai” ************* Rana bata qarya yau laraba, yau ne ranar da Aisha zata fara zuwa aiki a kamfanin maqiyin ta wanda bata da masaniya a kai. Bayan tayi wanka ta shafa mai ne ta bude wadrobe tana tunanin wanne kaya zata sa, ta tsaida tunanin ta akan wata doguwar rigar material shara shara mai kyau, Ta fiddo wandon jeans dinta baki tare da dan qaramin gyale. Bayan ta shirya tsab ne Salma ta shigo dakin tana murmushi tace “sis kin ga yadda kika yi kyau kuwa, kamar wadda zata je gasar kyau. Anya yau idan mai kamfanin gaba daya yayi ido hudu da ke bazai qwanqwasa ba kuwa??” Aisha ta bata rai tare da fadin “haba Ummi babu fa abinda na shafa a fuska balle ki ce nayi kyau sannan kin san dai mai kamfani irin wannan dole tsoho ne mai mata dayawa, ya za’ayi in fada ma tsoho??” Salma ta fashe da dariya tace “ai idan ma kin yi kwalliya gaba daya ofis din rikita su zaki yi, kuma kar kiyi mamaki idan kika ga mai kamfanin ba tsoho bane kamar yadda kike tunani. Ni dai zan ja miki kunne, kada dai ki je kiyi ta jan fada tunda dai kin san abinda ya kai ki” Tayi dariya tace “ai dole in yi qoqari in mayar ma Mr Handsome kudin shi, ban ma baki labari ba gidan Ammi da naje kai atamfofin nan jiya wallahi idan kika ga Ammin sak kamar su daya, qila ma Umman shi ce” Salma tayi dariya tace “lallai Aisha ban taba jin kina maganan namiji kamar wannan ba, anya??” Aisha ta miqe ta kama hanyar fita tana fadin ” nothing Ummi” Salma ta bi ta da ido tana dariya. Bayan sun yi breakfast ne Baba yayi sallama da su domin zaiyi tafiya zuwa Abuja wanda daga ofis din shi ne aka tura shi domin ya wakilci rector dinsu, kafin ya tafi sai da ya ja ma Aisha kunne akan ta kula da kan ta kuma ta kare mutuncin ta a wurin aiki sannan yayi mata addu’ar fatan alkhairi. A yau kuwa Salma ce ta sauke Zaid a makaranta ta sauke Aisha a ofis sannan ta dawo gida domin zasu je kasuwa da Inna anjima. ************ AMK COMPANY NIGERIA LIMITED babban kamfani ne wanda fasalin shi kadai ma abun kallo ne balle kuma idan ka shiga ciki. Aisha ta shiga kamfanin tana ta kallon yawan mutanen da ke kai da komowa wanda wadansu ma’aikata ne wadansu kuma clients ne. Tsarin kamfanin yana mata kaman ta taba shiga irin shi, tana cikin wannan tuananin ne receptionist tace “hajiya barka da zuwa, wa kike nema?” Aisha ta zaro takardan aiki ta miqa mata tare da fadin “an bani aiki ne a nan” matar ta duba sannan ta ce “sannu da zuwa, inventory Office aka tura ki don haka ki miqe hallway zaki ga hanya a hannun hagun ki sai ki bi, zaki ga HR Office” Aisha tayi godiya ta karbi takardar ta sannan ta nufi inda aka tura ta. Bayan ta iso ofis din ne ta qwanqwasa qofa aka bata izinin shiga, Head of HR din ta samu. Don haka bayan sun gaisa ne ta miqa mishi takardan tare da yi mishi bayani, cikin fara’a yace “barka da zuwa AMK company” Ya karbi takardar ya sa mata hannu akan takardar sannan ya miqa mata tare da fadin “yanzu sai ki kai ma boss ya sa miki hannu sannan ki dawo” Yayi mata kwatacen ofis din sannan ta fita, ta koma hall ne ta hadu da wani yana wucewa wanda da alama ma’aikaci ne, ta tsayar da shi ta gaishe shi sannan tace “Don Allah boss din kamfanin nan nake tambaya, ya shigo kuwa?” STORY CONTINUES BELOW Mutumin yace “bai iso ba tukun, amma ki zauna ki jira shi because nan ba da dadewa ba zaki gan shi” tayi godiya ta samu wuri ta zauna. Aisha tana nan zaune tana jira ne taga wata kyakkyawar yarinya ta fito daga wani ofis tana masifa, tana fadin “ai wannan rashin mutunci ne, ya ma za’ayi ina da sakatariya amma ace wai kullum ina rigan ta zuwa aiki, this has to stop”. Nan ta kira daya daga cikin ma’aikatan kamfanin tace mishi ya je wurin Head HR ya gaya mishi cewa a rubuta takardar sallama kuma a nemo mata sabuwar sakatariya yanzun nan. Ta juya zata koma ne ta hango Aisha zaune wadda take kallonta. A zahiri ba wani abu ne ya sa Hanifa son yi ma Aisha magana ba sai don birge ta da tayi. Hanifa ta tako zuwa inda Aisha take tayi mata sallama tare da tambayan ta “baiwar Allah wa kike jira ne?” Aisha ta amsa sallamar tare da fadin “na samu aiki ne a nan shine aka ce in jira boss ya zo yasa mun hannu” Hanifa ta karbi takardar aikin a hannun Aisha ta duba sannan tace “you are welcome, ki jira shi yanzu zai zo. Ni sunana Hanifa” Ta nuna ma Aisha ofis dinta tace “ga ofis dina can, nice to meet you Aisha Abdullahi” (dayake taga sunan Aisha a kan takardar) Aisha tace “the pleasure is all mine Hanifa” Bayan Hanifa ta koma ofis dinta ne Abba ya kira Aisha a waya. Bayan sun gaisa ne yake qara yi mata nasiha game da sabon aikin ta, tayi godiya yayinda ya miqa ma Umma itama ta fara yi mata nasiha, tana sauraron nasihar Umman ta ne ta ji wani daddadar qamshin turare ya bugi hancin ta, da sauri ta juya don ganin mai wannan masifaffen qamshin. Aliyu Muhammad Kankia shine ya wuce ta gaban Aisha yayin da yake magana da wani akan wasu takardu da zai sa hannu, Aisha dai bata yi nasaran ganin fuskan shi ba sai bayan shi da kuma qamshin da ya bari a hall din. Yana tafe yana amsa gaisuwar ma’aikatan shi wadanda tun da ya shigo suke ta gaishe shi, wannan ne ya bata tabbacin lallai wannan shine boss din, toh amma abun mamaki shine a zaton ta boss din wani tsohon attajiri ne sai kuma ta ga sabanin haka. Bayan Aliyu ya haura sama ya shige ofis din shi ne Aisha ta miqe ta haura saman itama, ta samu Ibrahim sakataren Aliyu tayi mishi bayanin abinda ya kawo ta. Ya dauki waya ya kira Aliyun yace “Oga ga sabuwar ma’aikaciya nan tana son ganin ka” Cikin mamaki Aliyu yace “ma’aikaciya? Mace? Wane department?” Ibrahim dai yasan dole Aliyu yayi wannan tambayoyin domin kuwa kowa yasan baya son aiki da mace a kusa da shi. Ya duba takardar Aisha yace “oga Inventory ne” a dalilin Aliyu baya damuwa da bangaren ne yace “okay, kace mata ta shigo” Ofis din Aliyu ya kasance fuska daya gilas ne, sauran fuskokin uku kuma bango ne lafiyayye. Yayi ma fuska daya gilas ne saboda a ta nan ne yake hangen abinda ke faruwa a qasa, wannan gilas din yana da ‘yar qofa wadda wani lokaci idan yana so yayi ma ma’aikatan shi magana yakan tara su a hall ya bude qofar ya fadi abinda zai fadi ba tare da ya sauko ba. A lokacin da yake buqatar sirri yakan danna wata na’ura dake dishar da gilas din ta yadda bazaka hango shi ba daga qasan sannan shima bazai hange ku ba. Aisha ta qwanqwasa qofar wanda a lokacin yana tsaye ne yana kallon ma’aikata da clients ta bangon gilas dinshi yayin da yake magana da wani a waya. Ba tare da ya waigo ba yace “yes come in”. Ta tura qofar ta shiga, ta doso wajen table dinshi yayin da zuciyar ta ke ta dakan uku uku, gaba daya Aisha ta sha’afa a kallon ofis din wanda ya qeru iya qeruwa, wani sanyi hade da qamshi yake ta ratsa ta yayin da take cigaba da yaba kyaun da ofis din yayi. STORY CONTINUES BELOW Bata ankara ba sai ta ji takardar dake hannunta ta zame ta fadi. Da sauri ta duqa har qarqashin tebir din don ta dauko ta wanda a daidai lokacin ne Aliyu ya gama wayar ya juyo. Ga mamakin shi bai ga kowa ba, motsi ya ji qarqashin table din, duqawan da zai yi don ganin ko waye ne suka hada idanuwa daga ta qarqashin tebir din. Gaba dayan su suka taso har Aisha tana bigewa da tebir din tace “you??” Cikin bacin rai ne yace “me kike nema ne? Wai ma in tambaye ki, lafiyar ki kuwa? Ikon Allah, ban taba ganin mayya irin ki ba” Aisha ta daga mishi hannu tace “ni ba wurinka nazo ba aiki na samu anan, an ce in samu boss ne….” Ita kanta sai da ta dan dakata sannan tace “kaine boss din?” Cikin bacin rai Aliyu yace “ke! Fita daga ofis dinnan yanzu” Tace “ai ba sai ka kore ni ba, bana ma burin in qara minti biyu anan. Banda ma qaddara me zai sa in zo inda kake”. Ta wuce zata fita ne ya dakatar da ita tare da zuwa ya tsaya a gaban ta yace “idan kika bari na sake ganin ki a garin nan sai na wulaqanta ki saboda na lura ba kya jin magana, stupid girl” Ran Aisha ya baci jin Aliyu ya kira ta stupid girl, aikuwa nan da nan tace “Malam kada ka qara zagi na” Ya matsa daf da ita yace “idan na zage ki me zakiyi?” Ta matsa baya tana fadin “ni dai na gaya maka” Ya sake matsowa yace “aren’t you a stupid garl? Answer me” ta qara matsawa kenan tana shirin yin magana sai ta ji ta jingina da bangon gilas din ofis dinshi wanda kafin ta ankara sai ta ji qofa ta bude ita kuma ta tafi zata fado, ihun da tayi ne ya ankarar da mutanen dake qasa yayin da Aliyu yayi saurin riqo hannun ta. Aisha dai tuni ta fara kuka, a tunanin ta ma ta fado dayake idanuwan ta a rufe suke, jin alamun an riqe ta ne ta bude idanuwanta ta ga Aliyu riqe da hannun ta. Fuskar shi a murtuke yace “me kike cewa?” Cikin kuka tace “ban ce komai ba”. Murmushin mugunta yayi yace “ki bani haquri in cece ki” saboda taurin kai irin na Aisha kai tsaye tace “idan na qi…” Kawai sai ya saki hannunta ta fada sannan ya daga kai ya kalli ma’aikatan wanda kallon yana nufin kowa ya koma bakin aikin shi, ya janyo qofar shi ya koma ya zauna. Aisha kam ihun da tayi ya razana mutane amma kuma dayake suna tsoron kar su rasa aikin su babu wanda ya matsa kusa da ita sai Hanifa. Da sauri Hanifa ta nufo wurin Aisha tana mata sannu, sa’ar Aisha guda bisa wasu kwalaye ta fado da ta karye. Cikin tsanar Aliyu ta miqe tana share hawayen da ke fuskar ta yayin da Hanifa tace mata “sorry Aisha, baki dai ji ciwo ba ko?” Tace “babu ciwo thanks” Hanifa ta ja Aisha zuwa ofis dinta tace “ya akayi hakan ta faru?”. Aisha ta sake fashewa da kuka. Da Hanifa dai ta lura Aisha bata da niyyar yi mata magana ne tace “ina zuwa” Aliyu yana latse latse a laptop din shi ne Hanifa ta shigo tace “haba yaya Aliyu meyasa kayi haka? me Aisha tayi maka ne da har kayi mata haka?” Ba tare da ya kalle ta ba yace “bata da kunya ne” tace “amma fa wurgota kayi, idan da ta karye fa?” Wannan karon ma bai kalle ta ba yace “na ga kwalayen ai shiyasa na sake ta” Sai yanzu ne ya kalli Hanifa yace “wa ya bata aiki a kamfanin nan? Bana son sake ganin ta a ofis dinnan, I want her fired right this moment” Hanifa zata yi magana kenan ya daga mata hannu yace “just do it Hanifa”. Hanifa ta miqe jikinta a sanyaye zata fita yace mata “meet me at the conference room in ten, muna da meeting da mutanen nan da suka zo daga china” tace “toh” Aisha dai tana zaune a ofis din Hanifa aka kawo mata takardar sallama wanda dama ko ba’a sallame ta ba tafiyar ta zata yi. Hanifa ce ta bata haquri tare da yi mata fatan alkhairi. Tare suka fito daga ofis din yayin da ita Hanifan ta kama hanyar conference room. Aisha ta kama hanyar fita ne ta hango Aliyu yana saukowa domin halartar taro da baqin shi na China, ko kallon inda take bai yi ba ya wuce ya shige conference room. Ran Aisha ya masifar baci, tana tafe wata zuciya tana ce mata “me zai sa ki amince da samun galaba da akayi akan ki na fadan da baki yi komai akai ba?” Har ta kai wurin reception wanda tana tafe ma’aikatan kamfanin suna ta yi mata sannu, kawai sai ta juyo ta nufi hanyar conference room din. Wani ma’aikaci mai suna Mansir ne ya dakatar da ita yace “Hey, dont go in….” Ta dakatar da shi tace “kar ka damu i need to fight this”. Mansir ya bi Aisha da kallo cikin mamaki tare da fargaban abinda zai biyo baya. Aisha ce ta bude qofar dakin taron ta shiga, Gaba dayan su kuwa suka dago daidai domin ganin ko waye ya shigo. Ganin Aisha ce Hanifa ta miqe da sauri tare da fadin “Aisha lafiya? Wa ya baki izinin shigowa?” Aliyu ya dakatar da ita da hannu tare da ce ma clients din shi “excuse me please”+ Cikin bacin rai ya nufi wurinta yace “wai ke whats wrong with you ne? Ba kin karbi takardar sallaman ba, me kike so ne for crying out loud?” Cikin ido ta kalle shi wanda har sai da tsigar jikinta ya tashi, ba wani abu ya janyo hakan ba sai masifar kwarjini da Aliyu ya mata. Ta saita murya tace “aiki na zaka dawo min da shi” A yanzu kuwa murmushi yayi, Cikin rashin fahimta yace “ban gane ba, akan wanne dalili? Kin manta cewa kamfanin nan nawa ne kuma ni ke da ikon daukan ma’aikaci ko in sallame shi?” Tace “eh nasani, a qa’idance bai kamata ace an dauki ma’aikacin da bai fara aiki ba kuma ace an sallame shi ba tare da yayi laifin komai ba” Ran shi a bace yace “kin yi mun laifi amma kina da gaskiya tunda laifin ba wanda ya shafi aiki bane don haka you are right, zan dawo miki da aikin ki” Anan ne ya karbi takardar tare da miqa ma Hanifa sannan yace “a kawo mata appointment letter yanzun nan, she will be my secretary henceforth” Cikin mamaki Hanifa ta kalli Aliyu domin dai kowa ya sani cewa a duk ma’aikatan da ke aiki kusa da shi babu mace ko daya sai Hanifa, itama saboda ‘yar uwar shi ce, duka matan da ke aiki a kamfanin suna bangarorin da bai cika damuwa da su ba, hatta sakataren Aliyu namiji ne sai gashi yau da kan shi ya dauki Aisha a matsayin sakatariyar shi. Hanifa ta karbi takardar zata fita ne yace “ki sa a mayar da Ibrahim (sakataren shi) inda aka ba ta da farko” Cikin ‘yan mintoci ne Hanifa ta dawo da appointment letter, a lokacin Aliyu yana magana a waya yayin da Aisha ta qura mishi ido ba tare da ya san tana kallon shi ba, a ranta tana fadin kyakkyawan mutum mai aji, ga murya mai dadi amma sai wulaqanci, mugu kawai Bayan ya kammala wayar ne ya karbi takardar daga hannun Hanifa sannan ya fiddo biro daga aljihun shi yayi rubutu akan takardar, ya miqa ma Aisha tare da fadin “Na qara sharadi akan sharuddan da ke kan takardar nan, sharadin shine na dauke ki aiki a matsayin sakatariya ta wadda nan da kwana uku idan kin kasa kika sallami kanki da kanki toh zaki biya kamfanin nan Naira dubu dari da hamsin kin amince?” Hankalin Aisha ya masifar tashi, kafin tayi magana ne taji yace “idan baki amince ba ga qofa nan a bude, kya iya tafiya” Ba Aisha ba hatta Hanifa tayi mamakin dalilin da yasa Aliyu yayi haka domin kuwa ta san cewa aikin da ibrahim yake yi ma Aliyu ba kadan bane musamman bangaren computer, ga dukkan alamu dai yana so ya qure Aisha ne. Har ya juya zai koma wurin clients din shi ne ya ji tace “na amince, zan yi aiki a kamfanin nan kuma na amince da sharuddan ka” Ran shi ya baci sossai domin bai taba tunanin cewa zata amince ba, ba tare da ya waigo ba yace “aikin ki zai fara daga gobe” ya wuce ya zauna tare da ba clients din nashi haqurin bata musu lokacin da yayi. Aisha kuma ta juya zata fita ne ta ji muryar Hanifa tana fadin “congrats dear, you are welcome” Aisha tace “thanks Hanifa” ta wuce ta fita yayin da Aliyu ya danna ma Hanifa harara wanda ita kuma ta mayar mishi da murmushi. STORY CONTINUES BELOW ************ Aisha ta koma gida coke da fargaban abinda zai biyo baya, ta taras da su Inna a falo. Bayan sun mata barka da dawowa tare da tambayan ta yanayin aikin nata wanda ta gwada musu komai lafiya lau, Ta wuce daki domin ta huta. Ko da ta shiga dakin gado ta haye ta kwanta a rigingine ta rungume filo tana tunanin kalaman Aliyu. Salma ce ta shigo dakin ta taras da ita a hakan wanda har sai da ta taba ta sannan ta dawo daga duniyar tunanin. “lafiyar ki kuwa?” Salma ta tambayeta. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta miqe zaune tace “Ummi na shiga uku, kin san kamfanin waye na samu aiki?” Salma tace “sai kin fada” tace “Mr handsome” Cike da mamaki Salma tace “dagaske??, wanda kuke rigima da shi?” Anan ne Aisha ta zayyana ma Salma abinda ya faru tun daga farko har qarshe. Salma ta ce “ni dai da zaki biye mun da kin bar aikin nan kawai domin dai nasan gayen nan bazai qyale ki ba” Aisha tace “gaskiya Ummi nima nayi tunanin in bari amma wallahi idan na bari zai dauka naji tsoro ne, kuma insha Allahu I will defeat him.. it’s a game and we shall play it to the finish” Salma tayi murmushi tace “dadi na da ke taurin kai, Allah ya baki sa’a”. Anan ne kuma Aisha ta shiga ba Salma labarin kyan shi, har Salma na fadin “ke dai fadi gaskiya ko dai kin fara son shi ne?” Bata rai tayi tace “bana son mugu irin shi” ta sunsuna hannun ta da ya riqe ta tace “bari ma in je in wanke hannuna da ya riqe, duk sai qamshin turaren shi hannun ke yi, haka wancan karon ma da qyar na rabu da qamshin” Salma tayi dariya ta miqe tare da fadin “toh dama irin su ai kin san designer turare suke sakawa, ba haka nan qamshin turaren su ke bacewa ba, Wa ya sani ma qila son qamshin kike” Aisha tace “Allah ya tsare ni da son qamshin mugun mutumin nan” Salma tace “muna nan dai magana zata fito ba da dadewa ba” Aisha ta tabe fuska. Bayan Salma ta fita ne Aisha ta qara sunsuna hannun ta tare da lumshe idanuwa. Ajiyar zuciya ta saki sannan a fili tace “gayen ya hadu don haduwa amma na tsane shi” ************* Washegari Aisha ta iso ofis da wuri. An nuna mata work station dinta wanda daga nan din ogan ta yana hangen ta daga zaune ma, ba sai ya tashi ba. Gaba daya ofis din anyi mamakin ganin Aisha a matsayin secretary din Aliyu domin kuwa an san yadda baya son aiki da mata, wasu har tausaya mata suka yi domin sun san wahala zai bata. Ta zauna bisa kujerar ta tayi addu’ar neman sa’a sannan ta fiddo wata qatuwar roba cike da su chocolates ta dora bisa table din daga gefen computer dinta. Ta bude chocolate daya tana ci yayin da take duba wasu takardu wanda zasu taimaka mata wurin aikin ta, Hanifa ce ta shigo kamfanin yayin da ake ta gaishe ta tana amsawa, ta qaraso wurin Aisha cikin fara’a tace “hajiya good morning”. Aisha ma cikin fara’a tace “good morning madam” wanda har ta sa Hanifa dariya tace “Ya aikin? Har an fara?” Aisha tayi dariya tace “ga shinan dai ina duddubawa” tace “toh Allah ya taimaka, ogan ki ma ya kusa shigowa bari in shiga ofis dina”. Bayan sunyi sallama ne Aisha ta cigaba da dudduba takardun wadanda gaba daya duk ta gane abinda aikin nata ya qunsa saboda dama dai kun san Aisha akwai ilimi. STORY CONTINUES BELOW A lokaci guda ta ji hayaniya ta ragu, haman kuwa yasa ta daga idanuwanta domin ganin dalilin, ba wani abu bane illa boss din su da ya shigo kamfanin wato Aliyu Muhammad. Aikuwa nan da nan aka fara gaishe shi yayin da yake daga musu hannu a dalilin he was on a call. Daga nesa Aisha ta qura mishi ido tana mamakin kyakkyawan gaye irin shi amma mugu, gaba daya gayun shi ya masifar birge ta, sanye yake da wandon suit baqi da shirt baqa sai neck tie harda falmara duk baqaqe yayin da yake riqe da suit din shi a hannu wadda itama baqa ce, tun da ya shigo qamshin turaren shi ya gauraye harabar kamfanin. Lokacin da ya iso wurin Aisha ta gaishe shi wanda ko kallon ta bai yi ba ya wuce, ta bi shi da ido tace “ikon Allah, gaisuwar ma bazai amsa ba. Mugu kawai”. Bayan ya shiga ofis din shi ba da dadewa bane Mansir wanda yake account department ya kawo ma Aisha wasu takardu masu yawa a cikin file wanda zata kai ofishin Aliyu domin ya gani. Ta miqe riqe da file din ta nufi ofis dinshi, ta qwanqwaso qofar ya bata izinin shiga. Bayan ta zauna ne ta miqa mishi file din tare da fadin “Mansir ya kawo daga Account” ba tare da ya kalle ta ba ya karba ya fara dubawa, ita kuwa Aisha sa mishi ido tayi kamar wadda ke kallon TV. Anan ne ta ga wani dan tag a bisa table dinshi wanda aka rubuta sunan shi a kai, a ran ta ne tace dama sunan ka Aliyu Muhammad. Sai yanzu ta tuno appointment letter dinta Wanda a qasa aka rubuta ‘Aliyu Muhammad Kankia- CEO & MD…’ da signature dinshi. Yana cikin dubawa ne ta ga ya dauki waya ya kira Mansir, da suka gaisa ne ta ji yace “na ga report din ku, banda time din dubawa daga farko zuwa qarshe amma ga dukkan alamu komai yayi, Good job kuma nagode” Aisha a cikin ran ta tace “ikon Allah shi kuma Mansir dinnan dan gaban goshin shi ne kenan tunda gashi har yabon shi akeyi ana mishi godiya” Gani tayi ya turo mata file din tare da fadin “kiyi typing wannan cikin minti talatin sannan kiyi copy guda goma ki kawo” miqewa tayi tare da fadin “toh”. Aliyu bai zata zai ji ta amsa ba domin yasan aikin ba qarami bane, Hakan yasa shi saurin dagowa ya kalle ta cikin mamaki wanda ita har ta dauki files din ta nufi hanyar fita. Ta isa table dinta wanda daga inda Aliyu yake zaune yana hangen ta. Waya ta dauka ta sa alarm minti talatin masu zuwa sannan ta fara typing. Yanayin yadda ya hango tana taba keyboard din Computer din ne ya tabbatar mishi da cewa ta qware sosai, ran shi ya baci da ganin haka domin ko shi da ya ke qwararre wurin typing toh kuwa Aisha ta fi shi.1 Duk da saurin ta ya san bazata iya gamawa cikin minti talatin ba, da wannan tunanin ne ya cigaba da aikin shi. Aliyu dai bai ankara ba kawai sai ya ji ana qwanqwaso mishi qofa, ya bada izinin shigowa, Aisha ce ta shigo riqe da takardun da tayi printing har copy goma sha daya, da qyar ta iso gaban teburin shi da su saboda nauyi, domin kuwa har kusan zubarwa ma tayi, Allah ya taimaka dai basu zube ba. Ta kalli Aliyu wanda ga dukkan alamu ya ji haushi tace “na gama” Ya sa hannu ya dauki guda daya ya bude, gaba daya inda ya karanta babu kuskure. Ya dago ya kalle ta yace “guda nawa kika yi?” tace “guda goma sha daya, saboda filing room ne yasa na qara daya” Dukda Aisha ta birge shi kuma ya yaba da aikin ta bai nuna mata hakan a zahiri ba sai cewa yayi “kin dai bata mun resources saboda ba ke kika siya ba ko? Je ki” Ya juya ya cigaba da aikin shi yayin da Aisha ta fita tana murmushi, a ranta tace “maimakon kayi godiya na gama aikin ka cikin minti ashirin da daya, shine kake mun gori” STORY CONTINUES BELOW Bayan fitar Aisha ne Aliyu ya daga kai ya kalli agogo ya ga ko minti talatin bata yi ba ta gama aikin, tsaki yayi yace “she is good, barin ta ofis dinnan zai yi wuya. I have to find a way to send her away cos I hate her” *************** Abun da Aisha ta lura a ofis din shine gaba daya ma’aikatan Aliyu da ke shiga ofis din shi maza ne, banda Hanifa babu wadda ke shiga ofis din shi, kuma ta lura idan yana magana da Hanifa har dariya yana yi, wannan ne yasa ta fara tunanin ko budurwar shi ce. Yanzu ma tana zaune tana wani aiki a computer yayin da take hangen su daga inda take, hira suke yi sosai har ma zagayawa Hanifa tayi ta gefen shi tana nuna mishi wani abu a waya yayin da shi kuma yake murmushi. Aisha a ranta tace “lallai ma Hanifa, wannan mugun kike so kuma. Kodayake da alama yana sonki ai qila bazaiyi miki halin nashi ba”. Haka dai Aisha ta cigaba da aikin ta har suka fito tare, Aliyun yana gaba yayin da ita Hanifa take biye da shi riqe da Tab din shi a hannun ta. Ko kallon Aisha bai yi ba ya wuce, Hanifa ce tace “Aisha bari mu shiga wani gajeren meeting” tace “okay, sai kun fito”. *************** Wuraren qarfe uku Aliyu ya fito daga ofishin da suke amfani dashi wurin qera gidajen da suka zana wanda zaka gansu kamar da gaske amma da robobi, kwalaye da sauran su ake qera su. Ya wuce ta gaban table din Aisha inda ya ji suna hira ita da Hanifa tana cewa “qarfe hudu idan an tashi nake so in yi sauri in je gida saboda akwai aikin da zamuyi ni da sister na” Hanifa ce ke zolayar ta “yanzu ke har wani aiki zaki iya yi yadda kike kamar ajebor?” Aisha tayi dariya sosai sannan tace “ai babu abinda ban iya ba musamman fannin girki, idan kika dandana abinci na sai kin manta sunan ki don santi” Wannan karon Hanifa ce ta fashe da dariya, ganin Aliyu ya wuce ne tace “bari in je in ga boss” Ta wuce ofis din Aliyu. Tana shiga ofis din shi tun kafin ta zauna ta ji yace “sarkin sabo da mutane, yau kawai da fara aikin ta anan har kin sakar mata fuska. Yarinyar sai rashin kunya” Hanifa tayi murmushi tace “wai yaya Aliyu me Aisha ta maka ne? She is a nice girl fa ” Yace “nope, she’s a stupid girl, ta kusa barin ofis dinnan ma” Kafin Hanifa tayi magana ne wayar ofis din shi tayi ringing ya amsa, A dayan bangaren muryar Aisha ce ta daki kunnuwan shi inda tace mishi “dama cikin Schedule dinka da Ibrahim ya bani ne naga kana da meeting anjima da qarfe biyar, shine nace bari in tuna maka kuma tunda na ga lokacin tashi ya kusa maybe akwai abinda zan maka kafin a tashi” Bai ce komai ba ya ajiye wayar. Hanifa ya kalla yace “wallahi na manta da meeting dinnan, thank God ta tuna mun” Hanifa tace “amma kuma shine ko kace mata ka gode yaya?” Kallon ta yayi cike da mamaki sannan yayi murmushi ya maida idanuwan shi kan laptop din shi. Hanifa cikin ranta tace “ikon Allah, ni na rasa meyasa yaya Aliyu baya son Aisha kuma gashi da alama tana da qoqari” miqewa tayi tace “yaya Aliyu bari in je in rubuta report dina na yau kafin lokacin tashi yayi” yace “idan zaki tafi ki zo ki dauki files din can ki kai mun gida” ta amsa da “toh” sannan ta fita. ***************** Qarfe hudu daidai ma’aikata suka fara tafiya gida, wadanda basu gama aikin su ba kuma suna ta qoqarin kammalawa kafin su tafi. Lokacin da Aisha ta kashe Computer dinta tana shirin zuwa ofis din Aliyu don yi mishi sallama ne Hanifa ma ta iso wurin domin daukar saqon Aliyu. Tare suka shiga ofis din nashi inda Hanifa ta wuce don daukar files din yayin da Aisha ta ce mishi “zan iya tafiya gida?” ba tare da ya kalleta ba yace “a’a” Hankalin Aisha a tashe tace “akwai aikin da ban gama bane?” wannan karon ya dago kai ya kalle ta yace “baki ma fara ba ai” Waya ya dauka ya kira security yace ya tafi gida sai gobe, kar ya damu da sauran awowin da suka rage kafin shift dinshi ya qare. Hanifa ce tayi saurin cewa “Oga sir yau da kanka kake sallaman security kafin shift dinshi ya qare? Ba sai qarfe bakwai ne shift dinshi zai qare ba?” Aisha ya kalla yace “wuce ki tafi car park, ke zaki canji security din da na sallama yanzun nan”1 Aisha ta zaro idanuwa yayin da Hanifa tace “haba oga, Aisha zata yi aikin security? Akwai hadari a garin fa, any moment ruwa zai sauko” kallon ta yayi yace “dauki files din da kika zo dauka kiyi sauri ki tafi gida kafin ruwan ya sauko toh” Ya juya ya kalli Aisha yace “ke kuma wuce kiyi aikin da na sa ki, idan kuma kin ga bazaki iya ba ga qofa nan”. Cikin bacin rai da haushin Aliyu ne Aisha ta fita ta wuce car park don yin aikin da ya sa ta, a cewar ta gara ruwan ya sauko ya bige ta akan tayi losing game dinnan. Haka Hanifa ta tafi tana tausaya ma Aisha domin dai tasan Aliyu yayi haka ne don ya kore ta daga kamfanin. *********** Kusan kowa ya tafi banda wandanda aikin su ya shafi meeting din da za’ayi. Aisha tana tsaye a wurin ajiye motoci yayin da take nuna musu inda zasu ajiye motocin nasu, dayake baqin nashi ‘yan China ne ganin Aisha da suka yi tana aikin Security bai basu mamaki ba tunda su a can qasar su babu aikin da matan su basu yi. Wuraren qarfe biyar saura ne ta ji yayyafi na ruwan sama ya fara zubowa. Hankalin Aisha a tashe yayin da ruwan ya fara zubowa sosai, ta so ta koma rumfar motocin ta fake amma da ta tuna da Aliyu sai ta cigaba da aikin ta. Daya daga cikin wadanda suka halarci meeting din ne ya nufo inda take tsaye da leman shi a hannun shi yace mata cikin harshen turanci “baiwar Allah ki tashi daga wurin nan kada ruwan sama ya sa ki ciwo mana” kafin ta amsa ne Aliyu ya iso wurin tare da wani wanda ya riqe mishi lema yayinda shi kuma mutumin yasa kayan ruwa na leda, yace ma mutumin cikin harshen turanci “sannu da zuwa Mr Cheng, ku shiga ciki gani nan zuwa” Mr Cheng yace “yauwa Mr Aliyu, don Allah kasa yarinyar nan ta koma qarqashin rumfa tunda ruwa akeyi” Aliyu yayi murmushi tare da fadin “okay” ya kalli Aisha cikin ido wanda ita Aishan ta duqar da kanta yayin da take ta kyarmar sanyi. Bayan Mr Cheng ya shiga ne Aliyu yana murmushin mugunta yace “duk rawar sanyin da kikeyi ba zai sa in ji tausayin ki ba saboda haka ki cigaba da aikin ki” ya juya ya tafi. Aisha dai shiru tayi tana tunanin irin muguntar da Aliyu yake mata, tayi nadamar rashin kunyar da tayi mishi gaba daya. Nan da nan hawaye suka wanke mata fuska, bata ankara ba sai taji qarar mota a gaban ta ana yi mata hon akan ta matsa. Dayake ta riga ta tsorata, daskarewa tayi tare da runtse idanuwan ta domin a tunanin ta ma an riga an bige ta. Bata ankara ba ta ji an janye ta daga wurin da qarfin gaske. Rungume yake da ita yayin da take ta kyarma tare da sauke numfashi, da sauri ta bude idanuwanta ta dago don ganin ko waye ya cece ta dukda kuwa ta ji qamshin turaren shi. Ba wani bane illa Aliyu wanda shima ruwan saman ya sauka akan shi. Ture ta yayi cikin masifa yace “ba kya gani ne? Da an bige ki fa? Haka nan kin sa na jiqe” yayi tsaki ya juya ya wuce yayin da mutumin da ya kusa bige Aishan ya bi shi suna gaisawa tare da ba shi haquri. Aisha dai bata bar ofis din ba sai wuraren qarfe bakwai saura, dukda wahalar da ta sha bai sa ta yi tunanin barin aikin ba sai ma qwarin gwiwa da ta samu akan sai ta ga bayan muguntan Aliyu.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE