SOYAYYAR MU CHAPTER 3
SOYAYYAR MU CHAPTER 3
“No one can compete with you on being you. Most of life is a search for who and what needs you the most” ◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇ Ta isa gida a jiqe yayin da ta danganta jiqewar da rashin samun abun hawa kuma ta nemi Zaid da Salma a waya domin a zo a dauke ta amma babu network ga kuma dare nayi wanda yasa kawai tayi tahowarta. Bayan sun koma daki ne ita da Salma ne ta bata labarin ainihin abinda ya faru tun daga farko har qarshe. Salma dai ta fara tsorata da al’amarin domin har ce ma Aisha tayi ta bar aikin saboda kada Aliyu ya salwantar mata da rayuwa, amma kuma ita Aishan ta qi, cewa ma tayi yanzu ta fara aikin. Babu yadda Salma bata yi da ita ba amma ta qi dole ta haqura ta qyale ta.+ ************ Aliyu cikin motar shi a kan hanyar komawa gida wuraren qarfe takwas bayan an gama meeting din wanda yayi shi a jiqe, yana tuqi yana tuno abinda ya faru. A zahiri Aliyu mutum ne mai bala’in tausayi, dalilin mugun tausayi irin nashi ne ko kuka baya so ya ga mutum yana yi. Ya tausaya ma Aisha halin da ta shiga a lokacin da ruwa ya bige ta musamman da yaga tana kuka amma kuma saboda rashin kunyar da tayi mishi shiyasa ya qyale ta. Ko da ya iso gida bayan ya faka motar a parking lot ya dade a cikin motar yayin da yake tunanin abinda yayi mata wanda yasan bai kyauta ba. A qarshe ne ya tsayar da tunanin shi wuri daya tare da fadin “kada ka bari tausayin yarinyar nan yayi tasiri akan ka, ka hukunta ta daidai rashin kunyar da tayi maka wanda babu wata ‘ya macen da ta taba yi maka irin shi”. Ya shiga gida ya tarar da Ammi da Hanifa suna ta hira. Ammi tayi mamakin ganin shi a jiqe wanda a sanin ta bai kamata ace ya jiqe ba tunda cikin motar shi yake kuma akwai lema wadda zaiyi amfani da ita, balle kuma ma a lokacin da ya dawo ai an gama ruwan saman. Tambayar shi tayi “babyna lafiya ka jiqe haka??” Yace “lafiya Ammi” ya wuce dakin shi. Hanifa ta tashi ta nufi kicin don hado mishi tea mai zafi yayin da Ammi ta bi bayan shi. Ammi tana zaune tana jiran shi, ya fito daga dressing room din. A yanzu ya canza kayan jikin shi. tana kallon shi tace “zo ka zauna nan” Ya je wurin ta ya zauna, ta dauko tawul mai laushin gaske tana goge mishi gashin kanshi kamar wani qaramin yaro tace “me yasa ka shiga ruwa bayan kasan har zazzabi yake sa ka?” Shiru yayi domin bai da amsar da zai bata. Jin ta damu ne yace “yi haquri Ammi na bazan qara ba, i promise” Tace “good” Hanifa ta shigo da kofin tea mai zafi ta miqa mishi yayin da Ammi tace “toh maza ka sha kada temperature din ka yayi rising”. ************* Wuraren qarfe takwas bayan sun gama cin abinci, Ammi ta haura sama yayin da ta bar Aliyu da Hanifa suna hira. Aliyu ya tambayi Hanifa lambar wayar Aisha domin akwai aikin da zai sa ta. Hanifa ta bashi lambar har tana fadin “yaya Aliyu naga alama dai sai Aisha ta bar ofis dinnan zaka huta, amma dai ruwan sama bai bige ta ba dazu ko?” Miqewa yayi tare da fadin “idan kun hadu gobe ki tambaye ta, i just dont like dat girl” ya wuce dakin shi yayinda ya bar Hanifa tana mamakin wannan irin tsana da yayi ma Aisha. ************* Wuraren qarfe tara saura na dare Aisha tana kicin tare da Salma da Zaid yayin da suke hada snacks wanda suke sakawa a fridge domin baqi, wayar Aisha ce ta fara ringing, ko da ta duba lamba ta gani wadda ake kira Special number har tana ce ma su Salma “ga wata special number na kira na” STORY CONTINUES BELOW  Zaid ne yace “ko dai ta masu shan jini ce?” Salma tana ta dariya. Aisha ta amsa wayar cikin sallama, muryar da ta amsa mata sallamar ce ta sa ta firgita har sai da su Salma suka yi mamaki. Ba wani bane illa Aliyu. “zan turo driver na da aiki wanda zaki yi mun kuma gobe da safe zaki kawo su gida kafin ki tafi ofis saboda zan biya ta masauqin baqina na China in basu kafin su tafi, kiyi mun text din adireshin gidan ku yanzun nan” Bai jira ta yi magana ba ya kashe wayar. Bin wayar tayi da kallo tare da fadin “oh ni Aishatu” Bayan ta ba su Salma labari ne Zaid yake fadin “qila ma son ki yake shiyasa yake neman adireshin ki” Aisha ta zaro idanuwa tace “so kuma? Wannan gayen da ya tsane ni kamar ya kashe ni? Mugunta ce dai kawai irin nashi, so yake kawai in gaji in bar kamfanin kuma bazan bari ba” Cikin mamaki Zaid yace ban gane ba “baku shiri ne da ogan naki?” Aisha tayi murmushi tace “kar ka damu zan baka labari” Salma dai dariya kawai take yi. Direban Aliyu ya kawo ma Aisha aikin wanda dai ba wani abu bane illa typing, ko da ta gani sai tayi murmushi tace a ranta “i impressed him this morning amma saboda miskillanci irin nashi shine ko yayi mun godiya” Bayan ta karbi adireshin gidan Aliyu ne tayi sallama da direban ta shiga gida. Ta dawo kicin domin su cigaba da aikin da suke yi ne Salma tace “har kin gama aikin ne?” tace “a’a, typing ne ai ba wahala” Salma tayi murmushi tace “hala yasan qwararra ce ke shiyasa” Aisha tayi murmushi tace “oho mishi” Zaid ne yace “ni fa yakamata a bani labari ko in yi fushi” nan dai Aisha ta bashi labarin komai da komai da ya faru tsakanin ta da Aliyu. Zaid yace “lallai wannan mugu ne ba qarami ba. Ni ma na goyi bayan ki sis, kada ki yadda kiyi losing game dinnan. Ina nan zan taya ki da addu’ar samun nasara” Aisha da Salma suka dinga dariya. ************** Washe gari tun da safe ne Aisha ta shirya cikin wata doguwar riga wadda bata qarasa kai qasa ba sannan ta sanya wandon jeans ta nada gyale a kanta kamar kullum, ta bala’in yin kyau. Ta dauko takadar adireshin Aliyu ta duba, ganin lambar gidan ne yasa ta zaro idanuwa tare da fadin “Ummi kalli abun mamaki, kin san cewa adireshin gidan Aliyu shine na gidan Ammi?? Wadda na kai ma atamfofi ashirin?” Salma tace “haba?” Aisha tayi shiru tana wani tunani sannan tace “haba no wonder, babu shakka Ammi mahaifiyar shi ce domin suna bala’in kama” Tayi murmushi tace “amma kuma ya fi Ammi kyau sosai ma” Salma ta harare ta tace “Allah ya shirye ki Aisha, ni dai ina kyautata zaton son gayen nan kike, duk da muguntar da yake miki amma ke har kina ganin kyan shi” Aisha tayi dariya tace “wallahi Ummi gayen nan yana da kyau, idan kin gan shi zaki tabbatar da hakan” Salma tace “ni??? A ina zan gan shi? Ni da zan koma gida next week, ke dai Allah ya barku tare” Aisha ta bata rai tace “ba amin ba”. A dalilin Aisha ta san adireshin gidan Aliyu ne ta bar takardar a kan Vanity table din dakin su ta wuce. ********** Aisha ta iso gidan Ammi, dayake maigadin ya gane ta nan da nan ya bata izinin shiga. Ta shiga da sallama ta samu Ammi a falo tana kwance akan kujera tana kallon tashar CNN, bayan sun gaisa ne Ammi cikin mamaki tace “Aisha ce da sassafe haka?” tayi murmushi tace “ni ce Ammi, dama saqo ne na kawo ma Aliyu, yace in kawo kafin in tafi ofis” STORY CONTINUES BELOW  Ammi tace “ikon Allah, ashe ma a kamfanin babyna kike aiki” Aisha a ranta tace “babynki? Lallai ma ashe shagwababbe ne shiyasa yake wulaqanta mutane yadda yaga dama” Ji tayi Ammi na fadin “amma dai baya takura muku ko?” tayi murmushi tace “a’a Ammi”. Ta dauki waya tana neman layin Aliyu domin ta shaida mishi zuwan Aisha, tana kan neman layin nashi ne take gaya ma Aisha “ai yana ma Garden tun dazu, tunda lokacin zuwa ofis yayi nasan ma yanzu zai shigo” Bayan ta sanar da shi zuwan Aisha ta kashe wayar ne ta ce ma Aisha “ina so inyi miki wata tambaya amma ina so ki gaya mun gaskiya”. Aisha tace “Allah yasa na sani Ammi” tace “zaman ki a ofis din Aliyu kin lura ko yana da budurwa?” Aisha tayi mamakin wannan tambayar amma kuma da ta lura Aliyun murdadden mutum ne qila shiyasa Ammin tashi bata gane inda ya sa gaba ba, don haka ne tayi murmushi tace “eh toh akwai dai wata Hanifa wadda nake tunanin suna soyayya ne” Cike da mamaki Ammi tace “Hanifa? Shine basu taba gaya mun ba?” Aisha tace “kin san ta ne Ammi?”, tace “Hanifa ai ‘yar uwar Aliyu ce, nan gidan ma take ai. Yanzu haka ma qila tana shirin zuwa ofis” Kafin Aisha tayi magana ne Aliyu ya shigo sanye da wandon three quarter baqi da t-shirt fara mai ratsin baki, ya rataya wani qaramin tawul a wuyan shi.. yayi bala’in yin kyau, riqe yake da robar fresh milk. Aisha ta gaishe shi yayin da ya amsa a daqile shima saboda Ammi da take wurin. Ta miqa mishi saqon wanda sai da ya dudduba sannan yace mata “sai mun hadu a ofis” Aisha tana mamakin halin Aliyu na rashin godiya. Ammi ce tace “Baby na ashe Aisha kamfanin ka take aiki?” Yace “eh, kin san ta ne?” tace “ai ita ce wadda ta kawo atamfofin nan da na aika dasu Bauchi” bai ce komai ba ya kalli Aisha ya harare ta sannan ya nufi hanyan dakin shi. Ya kusan shiga dakin shi ne yaji Ammi tana fadin “kafin ka tafi ofis zan yi magana da kai” ya juyo yace “toh Ammi”. Hanifa ce ta sauko da sauri domin tafiya ofis, ganin Aisha tayi murmushi tace “Aisha ina kwana, kin kawo ma boss saqon shi kenan” Aisha tayi murmushi tace “lafiya lau hanifa, har na bashi ma” tace “weldone, kizo muyi breakfast mana sai mu wuce tare” Aisha tace “gaskiya a qoshe nake, bari dai in jira ki sai mu tafi”. Ammi ta kalli Aisha tace “da alama ke ba mai cin abinci bace, naga jikin naki tabarkalla” Aisha tayi dariya tace “ina dan ci Ammi”. Anan suka cigaba da hira har Hanifa ta cinye abincin sannan sukayi ma Ammi sallama suka tafi. Ita dai Ammi tana bala’in son Aisha, banda zancen Hanifa da taji yanzu taso ace Aliyu ya nemi Aisha ************ Aliyu yana zaune a dinning yana cin abinci, Ammi ta kalle shi tace “wai me ke tsakanin ka da Hanifa?” cokalin da ke hannun shi ne ya kufce, cikin mamaki ya kalli Ammi yace “babu komai Ammi illa zumunci, me kika gani?” tace “naji ance kuna soyayya, ai abun farin ciki ne don me zaka boye mun?” Ran Aliyu ya masifar baci domin dai yasan ba wata bace ta fadi wannan maganan banda Aisha. Saita muryar shi yayi yace “wanda ya gaya miki hakan bai fadi daidai ba, ki tambayi Hanifan ki ji” Ammi tace “toh shikenan”. Bayan ya gama breakfast din ne yana shirin fita Nafisa da Yusuf suka shigo, Nafisa ta riqe hannun Aliyu tare da fadin “Allah sarki bros rabo na da ganin ka tun jiya da safe, me yasa baka dawo da wuri ba?” Yace “yi haquri Anty feena, na tsaya wani meeting ne kuma da na dawo nayi trying wayar ki bata shiga ba” Suka gaisa da Yusuf sannan yayi musu sallama. Nafisa har mota ta raka shi sannan ta koma cikin gida. STORY CONTINUES BELOW  Aliyu dai ya qudiri niyyar hukunta Aisha akan laifin da tayi mishi na shiga rayuwar shi. ************* Ran shi a bace ya shiga ofis domin ko gaisuwar ma’aikatan shi ma bai amsa ba wanda tunda suka kula da hakan suka gane ran shi a bace ne. Lokacin da ya iso work station din Aisha bata nan don haka ya wuce ofis din shi. Wani ma’aikacin shi ne ya kira shi a waya ya shaida mishi cewa ya isa wurin ginin da za’a canza ma fasali kuma yanzu haka yana tare da injiniyoyin. Aliyu yayi magana da ogan injiniyoyin sannan ya gaya musu cewar yanzu zai turo musu yanayin aikin da zasu yi a takarda. A zaune inda yake ya hango Aisha ta dawo kujerar ta tana duba wasu takardun da ta karbo daga wurin su Mansir, ran shi a bace ya kira ta a waya ya ce tazo ofis dinshi yanzu. Tun kafin ta rufe qofar ofis din ta ji muryar shi cikin masifa yana fadin “ke kina da hankali kuwa? Uban wa yace ki sa mun ido? Wa ma ya baki izinin yi mun shishigi a rayuwa?” Aisha cikin rawar murya tace “me nayi maka?” yace “akan wane dalili zaki fadi ma Ammi cewa ina soyayya da Hanifa, mu muka gaya miki haka?” Cikin rawar murya tace “kayi haquri na dauka…” “shut up” abinda yace kenan, ya cigaba da fadin “kin dauka me? Toh bari kiji, dalili daya ne yasa bazan kore ki daga kamfanin nan ba yau, takardar sharadin da na riga nasa hannu akai amma banda wannan babu abinda zai sa ki cigaba da aiki anan” Aisha dai saboda tsoro har idanuwan ta sun ciko da hawaye. Ya fiddo wata takarda ya jefa mata, “ki samu direba a waje zai kai ki site inda ma’aikata ke aiki. Ki kai ma injiniya Bala kuma kada ki dawo sai ya gama aikin shi ya rubuto mun report sannan ki karba ki dawo nan, that way i will keep you away from me” Ya juya ya cigaba da latsa laptop din shi yayin da ta dauki takardar jiki a sanyaye ta fita. Aisha ta nufi table dinta ta dauki jakarta ta kama hanya. *********** Aisha ta isa site din inda ta tarar da ma’aikata suna ta aikin su. Ta tambayi wani daga cikin su inda zata ga injiniya Bala, ma’aikacin yace mata yana sama. Aisha ta fara haurawa yayin da ta bare chocolate dinta tana ci tare da waige waigen inda zata gan shi. Da ta gama zagaye ne bata gan shi ba sai ta kira lambar wayar Aliyu domin ya taimaka ya kira mata injiniyan a waya don ya sanar da shi zuwan ta. Aikuwa tana kiran shi ya amsa tare da yin tsaki yace “lafiya kike damuna?” Tace ” yi haquri dama ban ga injiniyan bane shine…” Katse ta yayi yace “dan Allah ki qyale ni, neman shi zaki cigaba da yi har Allah yasa ki gan shi. Kuma kar ki sake kirana” Ya kashe wayar. Aisha tace “mutum har mutum amma sai mugun hali”. Ta cigaba da neman injiniya yayin da ta isa har can sama, cikin rashin sani ashe ta baro shi a hawa na farko. Kafin kowa ya ankara ne katakai suka fara fadowa yayin da ginin yayi kamar zai rushe, ma’aikatan sun lura da hakan shiyasa suka fara sauka da gudu suna fita daga ginin. Injiniya Bala yayi directing dukkansu su fita yayin da shima ya fice da gudu. Wani katako ne ya fado kusa da Aisha, nan da nan tasa ihu ta jefar da jakar ta da chocolate din dake hannun ta tana qoqarin sauka amma ta kasa a dalilin wani qaton katako da ya tokare hanya. Ta shiga wata qofa wadda a tunanin ta zata fitar da ita amma tana shiga ta tarar ba haka bane, tayi qoqarin fita daga dakin ne wani katakon ya fado ya tokare qofar shima. STORY CONTINUES BELOW  Ta sa duka qarfin ta wurin ture katakon amma ta kasa, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, kuka take yi babu sassautawa Ma’aikacin da Aisha ta hadu da shi lokacin da tazo wurin ne yake tambayar injiniya Bala “akwai wata yarinya da Oga ya aiko wurin ka, baka ganta ba?” Injiniya yace “gaskiya ban ga kowa ba, asali ma kowa ya fita daga ginin nan don haka duk ku tafi gida sai an canza tsarin yadda za’a yi sannan za’a kira ku”. ************ A wannan lokacin Aliyu yana hanyan zuwa airport domin dauko dan uwan shi Mustapha wanda zai iso daga portharcourt, babu yadda Aliyu bai yi da shi ba akan ya bari direba yaje ya dauko shi amma ya qi, a cewar shi Aliyun da kan shi zai je ya dauko shi idan kuma ba haka ba yana sauka zai wuce Katsina. Wannan ne yasa Aliyun ya tafi domin dauko shi. Tunda ya fita ya sa wayar shi a silent saboda kada a matsa mishi musamman Aisha, a lokacin ne Injiniya Bala yayi ta kiran shi domin ya sanar mishi da abinda ke faruwa amma bai amsa ba. *********** Bayan Aliyu ya dauko Mustapha sun dawo gida Nafisa da Ammi suka yi ta murnan ganin shi domin ya kwana biyu bai zo arewa ba. Suna zaune a falo suna ta hira har Aliyu yana fadin “Mutumina har qiba ka yi wallahi” Ammi tace “toh ai shi ba irin ka bane wanda hankalin ka baya kwanciya saboda takura ma kanka da kake yi da aiki” Mustapha da Nafisa suka yi dariya yayin da Mustapha yace “ai wallahi Aliyu kana qoqari, mutum kamar wani mai shekaru arba’in, baka hutawa ko alama. Kodayake mun ga handwork dinka tunda gaba daya arewa ana alfahari da kamfanin ka” Aliyu dai murmushi yayi yace “buri na kawai nake cikawa” Nafisa tace “kana dai buqatan hutu bros”. Mustapha yayi tambayan Hanifa aka ce mishi tana ofis. Ammi ta tambaye shi “amma dai zaka yi mana kwana biyu ko?” yace “eh toh qila su bar ni in kwana biyu, don nasan nan da jibi zan fara jin kiran waya” tace “Allah ya taimaka, ya maganan aure kuma??” Mustapha ya kalli Aliyu yace “Anty Feena zata samo mana mata ko Aliyu?” Aliyu yayi murmushi yayin da Nafisa tace “rufa mun asiri, gara ma kai zan iya nemo maka amma babyn Ammi ai neman matar aure sai shi da kan shi, haka kawai in kawo mishi ‘yar mutane ya raina mata aji” suka fashe da dariya. ************** Lokacin tashi aiki ya wuce domin har an rufe kamfanin Aliyu, Inna, Salma da Zaid zaune a falo suna maganan rashin dawowar Aisha. Salma ta kira wayarta amma bata shiga, Zaid ma ya kira shiru. Da suka ga shirun yayi yawa ne Salma da Zaid suka dauki mota domin zuwa dubo Aisha a kamfanin Aliyu. Ko da suka isa maigadi kawai suka samu, ya kuma sanar musu kowa ya tafi gida shima yanzu yazo domin ya canji maigadin na safe. Jikin su a sanyaye suka dawo gida suka shaida ma Inna halin da ake ciki. Hankalin Inna ya masifar tashi, Salma ce ta miqe da sauri ta nufi dakin baccin su ta dauko takardar adireshin gidan Aliyu da Aishan ta bari akan Vanity table. Nan da nan ta fito tace ma Zaid “tashi muje gidan Aliyu mu ji me ke faruwa, Aisha ma’aikaciyar shi ce kuma haqqin shi ne kula da ma’aikatan shi” Zaid ya miqe suka fita yayin da suka bar Inna cikin tagumi tana addu’ar Allah yasa dai lafiya. ************* Aisha dai tana can cikin duhu, saboda tsoro kanta ta nutse cikin gwiwowinta tana ta addu’o’i yayinda take ta rusa kuka, tayi ihun neman agaji amma shiru. ************* Salma da Zaid sun isa gidan Ammi yayin da shi zaid ya zauna a mota ita kuma ta shiga, da taimakon maigadi ne ta isa cikin gidan. Salma ta yaba ma tsarin gidan qwarai. Hafsat ce ta bude mata qofar yayin da tayi mata jagora zuwa falon sama inda ‘yan gidan suke. Sallamar Salma yayi daidai da waigowar Mustapha wanda daddadar muryarta ya daki kunnuwan shi, miqewa yayi da sauri tare da amsa sallaman cikin mamaki yace “kamar nasan fuskan nan” yayi dan gajeren tunani yace “Salma Abdullahi right?” Nafisa da Hanifa suka kalli juna suna dariya. Salma tace “a’a Mustapha kwana da yawa” anan Salma ta gaida su Ammi sannan tace “don Allah Aliyu nake nema” Ammi ta kira Hafsat tace “je ki kira Aliyu, ki ce yayi baquwa” ta juya ta kalli Salma tace “ga wuri ki zauna mana”. Bayan ta zauna ne Mustapha ke tambayanta “ya gida ya kwana da yawa?” tace “lafiya” yace “na nemi lambar ki bayan bikin nan amma ban samu ba, da mun dinga gaisawa ai”. A lokacin Ammi har ta shiga dakin ta sai Nafisa da Hanifa wadanda suka dinga kallon juna suna dariya. Mustapha ya kula da su amma bai damu ba, yace “idan bazaki damu ba ki bani lambar wayar ki mana” Salma ta bashi. Aliyu ne ya hauro sama yana mamakin wadda ta zo neman shi a wannan lokacin, sanye yake da wandon sweatpant baqi da wata Navy blue t-shirt, takalmin qafar shi Navy blue kalan t-shirt din shi sak, ya bala’in yin kyau. Kallon shi da Salma tayi ne ta gasgata zancen Aisha na kyan shi, lallai kuwa kyakkyawa ne kamar yadda ta fada. Salma ta gaishe shi tare da fadin “sunana Salma, yayar Aisha” cikin rashin fahimta yace “wacce Aisha?” tace “wadda take aiki a kamfanin ka” Nafisa ce ta ce “a’a daman yayar Aisha ce?” Hanifa tace “kuma basu kama ai da mun gano”. Ran Aliyu a bace yace “lafiya” Salma tace “dama lokacin tashi aiki ne ya wuce kuma har yanzu Aisha bata dawo ba shine nace bari in zo in ji…” cikin mamaki yace “bata dawo ba?” anan ne ya tuna rabon shi da ita tun lokacin da ta kira shi a waya da safe. Hanifa yasa ta dauko mishi wayoyon shi a daki, bayan ta kawo mishi ne ya duba yaga missed calls sun fi talatin wanda duk bai ji qarar ba saboda silent da ya sanya wayoyin. Missed calls kusan goma sha daya duk daga injiniya Bala ne, da sauri ya kira layin injiniyan. Yana amsawa yace “Oga ina ta kiran wayar ka shiru, dama aikin nan da muka fara ne nake so in gaya maka cewa an samu matsala saboda fittings din sama sun fara fadowa domin ginin ya tsufa dayawa, dalilin da yasa kenan muka rufe ginin sai an sake tsari”. Aliyu yace “ba komai zamu duba” Injiniyan yace “oga dama ina so in tambaye ka wani ma’aikaci na yace yaga wata yarinya wai ka aiko ta wurina amma a zahiri har muka fito ban….” Kashe wayar Aliyu yayi hankalin shi a tashe ya kira layin Aisha a kashe, da sauri ya nufi hanyar fita yayin da su Nafisa ke tambayan shi “lafiya?” “ina zuwa” abinda yace kenan. Salma dai hankalin ta ya masifar tashi domin ko zama ta kasa yi, su Nafisa ne suke ta lallashinta. Ammi ta fito daga dakin ta tana tambayar abinda ke faruwa wanda suka bata labarin abinda ya faru. Aikuwa nan da nan itama hankalinta ya tashi, Addu’a ta dinga yi Allah yasa Aliyu ya gano ta. ◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇ Cikin minti goma Aliyu ya iso saboda gudun da yayi kan titi. Da sauri ya fito daga motar shi ya ruga a guje ya shiga ginin wanda har yanzu katakai suna ta fadowa, shi kanshi yana tafe yana kaucewa kada su fado mishi. Da wayar shi ya dinga haskawa domin dai wurin ya riga yayi duhu. Ya haura sama yana ta kiran sunanta+ Jin ana kiran sunanta kuwa ta miqe da sauri tace “gani nan, don Allah ku taimaka min” Aliyu dai yana tafe ya ga jakar Aisha da kuma chocolate din da ta jefar, ya dauki jakar ya duba wayar ta wadda ta riga ta mutu. Ya ajiye jakar yayin da ya cigaba da neman ta, hankalin shi kuwa ya tashi matuqa. Tafe yake yana Addu’ar Allah yasa babu abinda ya same ta domin idan har ta shiga mummunan hali bazai taba yafe ma kan shi ba. Ya iso saitin qofar dakin da take ne ya ji muryar ta cikin kuka tana fadin “don Allah ku taimaka mun kada in mutu anan” Ajiyar zuciya ya saki sannan ya fara qoqarin cire katakon da ya tokare qofar, da qyar ya cire shi ya shiga, ko da ya haska fuskarta gani yayi duk ta galabaita tayi ja saboda kuka da ta ci. Ya isa wurin ta ya kamo hannun ta ya janyo ta suka fito. Bata ankara da wanda ya cece ta ba sai da suka fito harabar ginin sannan ta lura da ba wani bane illa maqiyin ta Aliyu. Fizge hannun ta tayi zata koma cikin ginin. Da sauri ya sake kamo hanun ta ya fizgo ta. A galabaice tace “ka sakeni, waya ce kazo ka cece ni? Mugu kawai azzalumi, ai kasan cewa hakan zata faru shiyasa ka turo ni nan” Hannuwanta ta sa ta tura shi yayin da ta cigaba da fadin “ban taba tunanin cewa tsanar da kayi mun ya kai har kasa rayuwa ta a cikin hatsari ba, banda qaddara me zanyi a kamfanin ka, kamfanin mugun mutum mai wulaqanta mutane. You are a monster and I hate you…, I hate…” Cikin jin haushin kalaman Aisha ne ya riqe hannuwan ta da qarfi yace “shut up… an gaya miki nasan hakan zata faru? Idan da na sani zan bari ma’aikata na su zo nan din ne?” Ya qara matse hannun tare da fadin “for your kind information I hate you too because ba kya jin magana…” Anan ne fa Aisha saboda tsananin jigata da tayi da kuma hannuwan ta da Aliyu ya matse wadanda tuni sunyi ja kawai sai ta fadi a jikin shi sumamiya. Fadowar da tayi jikin shi yayi daidai da tashin tsikar jikin shi gaba daya, da sauri ya dago fuskar ta yana kiran sunan ta amma shiru. Qura mata idanuwa yayi wanda duk haduwar shi da ita bai taba yi mata kallo irin wannan ba, anan ne yaga masifar kyau da take dashi. Dukda baya kallon ‘yan mata sosai bai taba ganin wadda ta kai Aisha kyau ba dukda kuwa ta sha wahala a yanzu. Ajiyar zuciya ya saki sannan ya dauke ta da sauri ya saka ta cikin mota ya kwantar da ita sannan ya zagayo ya shiga. *************** Ya hau kan titi ne ya kira Mustapha a waya ya sanar musu ya gan ta don haka yace ma Salma su hadu a gidan su. Jin wannan labarin ya kwantar ma kowa da hankali musamman Salma da har ta fara kuka, nan da nan ta miqe tare da yi musu sallama. Mustapha ne yace “jira in kai ki mana” tace “ai qani na yana jira na a waje kar ka damu” har mota kuwa ya raka ta suka gaisa da zaid wanda shi hankalin shi yana kan Salma wadda take yi mishi bayanin abinda ke faruwa. Bayan sunyi sallama da Mustapha ne suka nufi gida. STORY CONTINUES BELOW  Aliyu yana tuqi yana tuno halin da ya tarar da Aisha wanda ba qaramin tausaya mata yayi ba, haushin kan shi ya ji na mumunar halin da yasa ta a ciki. Yayi ma kan shi alqawarin ba zai sake matsa mata ba, a fili ne yace “i quit” *************** Ya iso gidan su Aisha wanda ya sani a dalilin text din da ta tura mishi lokacin da zai aiko direba don kawo mata aikin da tayi mishi. Ya fiddo ta ya shiga gidan tare da yin sallama, gaba dayan su suka taso suka zagaye shi a rude. Ya tambaye su inda dakin Aishan yake don ya kwantar da ita amma babu wanda ya amsa shi, da ya lura kamar ba wanda ya saurare shi a cikin su ne yayi gaba abun shi don neman dakin nata. Bayan ya gano dakin ne ya shiga ya kwantar da ita bisa gado wanda har gyara mata filo yayi yadda kwanciyar zai mata daidai. Ya fiddo wayar shi daga aljihu ya kira likitan shi Dr sadiq sannan yayi mishi bayanin halin da Aisha take ciki tare da yi mishi kwatancen gidan. Yana kashe waya ne Inna ta fara mishi masifa tace “aikin da Aisha take yi a kamfanin ka shi yasa ta shiga wannan halin, idan wani abu ya samu Aisha wallahi duk arzikin da kake taqama da shi toh kotu ce zata raba mu da kai” Aliyu dai shiru yayi yana sauraren ta domin yasan idan Aisha ta shiga wani hali shi da kan shi ma bazai taba yafe ma kan shi ba balle ‘yan uwan ta. Ta koma kusa da Aisha ta zauna tana addu’a yayin da Salma da Zaid suka riqe hannuwan ta suma suna ta Addu’a. Aliyu dai yana nan tsaye yana kallon su yayin da shima yake nashi addu’o’in a cikin rai Dr sadiq wanda ya iso gidan ne ya kira shi a waya ya fita domin shigowa da shi. Da sauri likitan ya qaraso ya duba ta yayi mata wata Allura sannan yace “kada ku damu zata Farfado, suma tayi a dalilin wahala da ta sha, don haka ku kwantar da hankalin ku” Ya miqa musu magunguna yace “ga wannan idan ta Farfado ta ci abinci ku bata ta sha” Inna ce tayi ma Likitan godiya yayin da suka fita tare da Aliyu, Zaid ma ya bi su. Bayan Aliyu yayi sallama da zaid ne ya rufe gidan sannan ya dawo. Bayan minti talatin da tafiyar Aliyu ne Aisha ta Farfado. A firgice ta miqe tare da fadin “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” su Inna ne ke ta yi mata sannu. Cike da mamaki tace “wa ya dawo da ni gida?” Salma ce tace “Aliyu ne”. Anan ne tayi shiru tana tuno abinda ya faru. Sun tilasta mata ta dan ci abinci ne ta sha magani Inna ta fara masifa tana fadin “gobe idan Allah ya kaimu zaki kai musu takardar barin aiki” A razane Aisha ta kalli Inna, Inna tace “kina kallona bazaki ajiye aikin bane?” Salma ce tace “ai Inna ba sai kin fadi ba, dole ne Aisha ta ajiye aikin nan saboda ran ta yana gaba da komai” Zaid ma yace “gaskiya Aisha dole ne game dinnan naku ya tsaya haka nan saboda akwai hatsari a cikin al’amarin” A rude Aisha tace “wallahi babu laifin Aliyu ko daya, qaddara ce kawai” Inna ta harare ta tace “ai babu wanda yace laifin shi ne, aikin ne aka ce ki ajiye, na gama magana” ta miqe cikin fushi ta nufi dakin ta. Zaid ma yayi musu sai da safe ya tafi dakin shi. Salma ce ta qura ma Aisha idanuwa wadda duk ta bi ta damu saboda an ce ta bar aikin kamfanin Aliyu. Matsowa tayi kusa da ita tace “Aisha me ke faruwa ne? Kar ki ce mun ba kya son barin aikin? ko dai magana na ya fara zama gaskiya kin fara son Aliyu ne?” ◇◇◇◇◇◇◇◇◇ Washe gari ranan litinin, har su Ammi suka gama breakfast Hanifa bata sauko ba. Nafisa ce da Yusuf suka shigo lokacin Aliyu da Mustapha suna dakin Mustaphan suna sallama domin yau ne zai wuce Katsina. Bayan su Nafisa sun gaisa da Ammi ne take tambayar ta “Ammi ina yaran ki suke ne ban ga ko daya ba? Hala Aliyu har ya tafi ofis?”+ Tace “yanzun nan muka gama breakfast, suna dakin Mustapha. Hanifa kuma bata sauko ba” Cikin mamaki Nafisa tace “bazata je ofis din bane yau?” Ammi tace “zauna dai ku ji abinda ke faruwa, ni na ma rasa yadda zan bullo ma al’amarin” Ammi ta basu labarin abinda ya faru. Cike da mamaki Nafisa tace “dama Hanifa tana son Aliyu amma kuma ban taba sani ba? Ammi bari in je in dubo ta” Nafisa ta haura sama yayin da ta bar Ammi da Yusuf suna maganar. Nafisa ta qwanqwaso qofar dakin Hanifa ta shiga, ta same ta a kwance cikin bargo da alama sanyi take ji. Da sauri Nafisa ta yaye bargon tare da tambayan ta “lafiyar ki kuwa Hanifa?” a sanyaye Hanifa ta miqe tare da fadin “Anty Feena me yaya Aliyu yace? Idan yace baya sona na shiga uku I am going to die…” dakatar da ita Nafisa tayi tace “ina zuwa” ta miqe ta fita daga dakin. Ta samu su Ammi a falo wanda a lokacin su Aliyu sun fito yayin da shi Aliyun yake niyyar tafiya ofis. Nafisa ce ta dakatar da shi tare da fadin “gaskiya akwai matsala fa, Hanifa bata jin dadi” ta kalli Aliyu tace “tana so taji amsar ka” Cikin bacin rai yace “Anty Feena don Allah ku qyale ni, its simple bana son Hanifa, what part of my statement don’t you guys understand? ya kuke so inyi toh?” Yusuf ne ya riqo hannun Aliyu ya zaunar da shi ya ce “haba qani na, me zai sa kace baka son ‘yar uwar ka? Okay nasan dalili, saboda baka da ra’ayin macen ta zata fara furta maka kalman so kafin kai ka furta mata? Idan kayi la’akari Hanifa ‘yar uwar ka ce ta jini, tasan ka fiye da yadda wata a waje zata san ka, tasan abubuwan da kake so da wanda baka so. shin akwai abunda yasa baka sonta wanda mu bamu san dashi ba?” gaba dayan su sunyi shiru suna sauraron abinda zai ce wanda shi kuma ran shi a bace kamar zaiyi kuka. Aliyu ya dan yi shiru sannan yace “bros inlaw ina neman macen da zata iya kula da kanta ta kula da ni har ‘ya’yan da zamu haifa, ina neman macen da ta iya dafa abinci, natsatsar mace mai hankali. Hanifa bata iya duka abubuwan da na lissafo ba. Bana so inyi auren da nan gaba zan yi da na sanin yin shi” Ya kalli Anty feena yace “ba tun yau ba kin san burina na son auren macen da ni da kaina zan gan ta in ce ina son ta amma ba ita tace tana so na ba saboda haka ban ga dalilin da zai sa in auri Hanifa ba bayan nasan bazan ji dadin auren ba” Mustapha dai babu abinda yake yi banda dariya. Yusuf yace “Aliyu ka sani cewa Hanifa marainiya ce, kuma sonka take tsakani da Allah. Kayi haquri ka aureta, ni nasan nan gaba zaka so ta fiye da yadda take sonka ma, yanzu idan har Hanifa ta koyi abubuwan da ka lissafa zaka aure ta?” Aliyu dai hankalin shi ya dade baiyi irin tashin da yayi ba yanzu, ita kanta Nafisa bata so haka ta faru ba domin ta fi kowa sanin burin Aliyu akan matar aure. Cikin bacin rai yace “koda na auri Hanifa ba don itace macen da nake burin aure ba sai don kawai in cika mata nata burin na son aurena” Wannan maganar tasa su dariya. Mustapha ne yace “ka amince kenan?” STORY CONTINUES BELOW  Miqewa yayi tare da fadin “toh ya zanyi?” Straight dakin shi ya wuce domin dai da alama ma yau ya fasa zuwa ofis din. Dukda Ammi bata so yadda Aliyu ya gwada baya son Hanifa ba taji dadi akan ya amince zaiyi aure domin dai dama ta gaji da ganin shi babu aure. Tayi ta sa ma Yusuf albarka tare da yi musu fatan samun zuri’a na gari shi da Nafisa. Nafisa da Mustapha ne suka bi Aliyu dakin shi inda suka gan shi kwance cikin bargo. Ganin shi cikin bargo ne yasa Mustapha yace “lallai yau babyn Ammi yana cikin wani hali domin kuwa duk abinda zai sa shi shiga bargo ba qaramin abu bane” Nafisa tayi dariya. Ko da suka yi mishi magana qyale su yayi, sai da Nafisa tayi magiya sannan ya dan bude bargon. tace “bros kayi haquri, Insha Allah zan tabbatar da cewa Hanifa ta koyi duk abinda kake so” Mustapha ne ya cigaba da fadin “banda abinka Hanifa is not bad ai, gata ‘yar qarama da ita. Kun dace da juna, don haka please ka sa a ranka cewa ita ce mafi alkhairi a gareka” ajiyar zuciya ya saki sannan yace “ni dai abinda nasani shine you guys are forcing me into something i dont like don haka babu abinda zan ce muku kuma” Nafisa ta tausaya ma dan qanin ta domin tasan irin burin da ya sa wurin aure, tambayar shi tayi “bazaka je ofis din bane?” yace “me zan je yi a ofis bayan ga irin tashin hankalin da kuka sanya ni a ciki” Mustapha dai dariya ya dinga yi wanda anan ne ya miqe “yace ni dai bari in kama hanya, zan biya in dauki Salma mu wuce” Nafisa tace wace Salma? Yayar Aisha mutuniyar Aliyu?” yayi dariya yace “ita” ya kalli Aliyu yace “ni na ma dauka Aishar budurwar Aliyu ce” Harara Aliyu ya danna mishi. Mustapha yana dariya yace “sai munyi waya, Nafisa ma tana dariya tace Allah ya kiyaye hanya, ka gaida su Mummy” yace “zasu ji”. ***************** Ammi da Nafisa sanar da Hanifa cewar Aliyu Aliyu amince zai aure ta sannan suka lissafa mata sharuddan da ya bayar kuma ta amince zata koyi duka. Ammi tayi mamakin irin son da Hanifa take ma Aliyu wanda a dalilin hakan har ta amince zata koyi girki, domin kowa ya sani cewa Hanifa bata qaunar shiga kicin ko alama sai gashi yanzu Aliyu ya sa ta dole ta shiga (soyayya kenan) A bangaren Mustapha dai ko da yayi sallama da su Ammi gidan su Salma ya tafi wanda har falo ya shiga ya gaida Inna, Aisha ma ta fito sun gaisa. Bayan an sa kayan Salma a motan Mustapha ne suka yi sallama da su Inna suka tafi, Aisha har kuka tayi saboda Salma ta tafi, Inna tana ta yi mata dariya. Har gida Mustapha ya ajiye Salma sannan ya wuce gida wanda suka yi akan cewa daddare zai je fira. Ko da ya isa gida Mummy taji dadin ganin shi domin dai ya dade bai zo arewa ba, bayan ya ci abinci ne suke labarin Aliyu da Hanifa wanda tuni Ammi ta kira ta a waya ta shaida mata komai, Mustapha ne ya ba ta labarin yadda akayi aka shawo kan Aliyun ya amince yayinda take kwasar dariya. Anan ne Mustapha ya ba Mummy labarin Salma wanda tayi murna qwarai da jin zancen domin dai yadda Ammi ta matsu da son ganin Aliyun ta yayi aure haka itama Mummyn ta matsu taga Mustapha yayi. Da daddare da Mustapha yazo wurin Salma ne suna hira shine yake gaya mata dangantakar shi da Aliyu. Salma ce cikin hiran take gwada mishi rashin kirkin Aliyu wanda shi kuma ya nuna mata ba haka yake ba, Asali ma mutumin kirki ne shi dukda dukiyar da ya tara baya wulaqanta mutane. A cewar Mustapha shima yayi mamakin rigimar shi da Aisha domin shi ya ma zata budurwar shi ce don sunyi bala’in dacewa. Maganar har dariya ta ba Salma. Sun dade suna hira wanda ga dukkan alamu sun amince da juna, soyayya mai qarfi suka qulla a tsakanin su. STORY CONTINUES BELOW  *********** Washegari Aisha zaune a falo tana kallon cartoon, lokacin Zaid Yana makaranta. Inna kuma tana dakinta. Sallaman qawayen ta Yusra da fiddausi taji, cike da murna suka rungume juna. Yusra tace “Aisha baki da kirki wallahi, ba kya son zumunci, rabon ki da gidan mu har na mant” Aisha ta tsugunna har qasa tace “don Allah kuyi haquri, na dan fara wani aiki ne amma na bari ma” Fiddausi ce ta fashe da dariya tace “dama banda abinki ai ba zaki jure wani aiki ba, ajebor kamar ki” Aisha ta tabe fuska tace “wallahi i am hard working Fiddausi, matsala dai aka samu na bar aikin” Yusra ce tace “toh me ya samu wayar ki ana ta kira shiru” Aisha ta ce “bari dai in baku labarin abinda ya faru” nan da nan ta basu labarin abubuwan da suka faru tsakanin ta da Aliyu. Cike da mamaki Yusra tace “wannan Aliyun ne ya miki haka?, aikuwa dai mutumin kirki ne kodayake ma kusan laifin ki ne a dukkan abinda ya faru” Aisha cike da mamaki tace “kin san shi ne?” Yusra tayi murmushi tace “dama dai mun zo mu gaya miki an sa ranan aurena da Mansir” cikin murna Aisha tace “wooow… congrats nayi miki murna sossai” Yusra tace “thank you, Mansir din da zan aura a kamfanin Aliyu yake aiki” Anan ne Aisha ta dakatar da ita tace “Mansir?? Ai na ma san shi, mutumin kirki wallahi. Na ma lura Aliyu yana ji da shi a ofis din. Gaskiya kun dace Allah ya sanya Alkhairi.” Ta kalli Fiddausi tace “hajiya ke fa sai yaushe?” Fiddausi tayi dariya tace “ke nake jira” Aisha tayi dariya tace “ashe kuwa kina da sauran jira, dukda ana nema a hada ni da wani, soyayyar ma ban san ya take ba wallahi, Ku dan gaya mun yadda take mana” Fiddausi da yusra suka fashe da dariya yayin da Aisha ta miqe tace “ina zuwa”, ta kawo musu drinks da kayan ciye ciye kala kala, harda su chocolates. Yusra ce tace “su Aisha har yanzu dai ana nan ana cin kayan zaqi” Fiddausi ce tace “kalli Tv ki gani, har cartoon din ma bata bari ba” suka yi dariya. Aisha tace “ni dai ba wannan ba, a gaya mun yadda soyayya take” fiddausi ta kalli Yusra tace “yar uwa ba Aisha labarin soyayya, gaya mata yadda kike ji game da Mansir” Yusra tace “well nothing much, idan har kin fada tarkon son wani toh zaki ga kullum kika rufe ido fuskarshi kike gani, tunanin shi baya fita daga zuciyar ki, zaki ta son ganin fuskar shi a koda yaushe kuma duk laifin da zaiyi bazaki taba ganin hakan a matsayin laifi ba, a taqaice kenan” shirun da Aisha tayi ne Yusra da Fiddausi suka kalli juna, Fiddausi ce tace “hajiya kin kamu da son wani ne?” Aisha ta saki ajiyar zuciya tace “wallahi gaba daya abinda Yusra tace akan Aliyu haka nake ji amma kuma ni ba son shi nake ba” Yusra da Fiddausi suka qara fashewa da dariya yayin da Yusra tace “Hajiya in gaya miki gaskiya, labarin da kika bamu na wahalan da kika sha wurin Aliyu da kuma yadda kika kasa ganin laifin shi kadai ya isa ya nuna cewa son shi kike” Fiddausi ce ta ce “sannan ma yadda baki so barin aikin ba banda tilastawan su Inna nasan da har yanzu kina aikin, kuma duk don kin fada a tarkon son shi ne” Aisha dai zaro idanuwa tayi tace “subhanalillahi, ni Aisha ina son Aliyu? Yau na shiga uku, in rasa wanda nake so sai wanda ya tsane ni a duniyan nan” su Yusra dai sun sha dariya. Inna ta fito zata shiga kicin ne ta ga su Yusra, suka tsugunna har qasa suka gaisheta. Bayan ta wuce kicin ne suka cigaba da hira tare da dauko maganan anko, Fiddausi ce ta kalli Aisha tace “hajiya sai kinyi anko fa, don nasan ki da rashin son sa kayan mu na hausawa. Inna ma zamu ba contract din fidda ankon” Aisha tayi murmushi tace “ashe kuwa zamuyi drama don gaskiya bazan sa wani kayan hausawan nan ba, haka kawai mutum ya bi ya takura” STORY CONTINUES BELOW  suka fashe da dariya “Yusra tace dadi na da ke dai akwai sa mutum dariya wallahi. Huta abinki, ni nasan dama baza ki sa ba” Aisha ta koma kusa da Yusra tace “yar uwa dan bani labarin Aliyu mana, nasan kina dan jin labarin shi a wurin Mansir dinki” wannan karon su Yusra sun tausaya ma Aisha domin dai ba sai an fada ba ta riga tayi zurfi a son Aliyu wanda ita har yanzu bata yarda da hakan ba. Yusra ta fara bata labarin Aliyu wanda a cewar Mansir wai Allah yayi yawa da ‘yan matan da ke son shi amma shi ko kallo basu ishe shi ba, kuma ma duk kudin shi shekarun shi ashirin da takwas Mutumin kirki ne domin gaba daya dukiyar shi bata rufe mishi ido ba, ance ma idan ka nemi taimako wurin shi ko sauraron dalilin neman taimakon baya yi saidai ya tambaye ka nawa kake nema kuma ya baka fiye da abinda ka nema din. Tuni Aliyu ya gama birge Aisha yayin da tace “ina ma in samu mai irin halin shi” Fiddausi ce tace “ga shi nan kin samu” ta zaro idanuwa tace “wa?? Wallahi yafi qarfi na, ai duk yadda na kai ga son namiji bazan taba tunkarar shi ince ina son shi ba” Yusra tace “toh ya zakiyi da son shi?” Aisha tayi sauri tace “wa ya gaya muku son shi nake wai?” dariya suka yi yayinda Fiddausi tace “wallahi Aisha son shi kike, kuma bazan yi kaffara ba. Allah dai ya zaba mana mafi alkhairi” Yusra tace “ameen”. Bayan sun tafi ne Aisha ta rufe kanta a daki tana ta tunanin maganar su Yusra, ita ta sani cewa tun ranan da ta fara ganin Aliyu akwai abinda take ji a game da shi a zuciyar ta wanda ta danganta hakan da tsoron shi da take ji a kan rigimar da ta shiga tsakanin su. Idan kuwa abinda Yusra ta fadi akan soyayya gaskiya ne toh babu haufi lallai ta fada tarkon son mutumin da bazata taba samu ba. ************** Nafisa da Hanifa zaune a falon qasa a gidan Nafisan. Hanifa ce tace “Anty Feena ina so in fara koyon girki” Nafisa tayi dariya “tace su soyayya manya, toh yanzu ina zaki je koyo?” Hanifa ta dan yi shiru sannan tace “wallahi Anty da naso inyi ma Aisha magana idan zata koya mun saboda a yadda ta bani labari ta iya girki kuma kinga Aisha batada matsala zan fi jin dadin koya a wurinta. Toh amma matsalan yaya Aliyu baya son ta” Nafisa tace “me ya ruwan shi da ita toh, ba dai shi yace ki koya ba? Kar ki damu zanyi mishi magana”. Tare da Nafisan suka je gidan Ammi inda suka tarar da shi tare da Ammi a falo suna kallon labaru. Wani ikon Allah tunda Hanifa tace tana son Aliyu ya rage walwala musamman idan tana kusa da shi. Yanzu ma da suka shigo ko kallon ta bai yi ba. Nafisa ce ta koma kusa da shi ta zauna tace “babyn Ammi how far” yayi murmushi yace “qalau Anty feena, ya akayi ne?” ta ce “dama maganan koyon girkin Hanifa ne muka yi shawara akan mu roqi Aisha tazo ta koya mata” tun kafin ta rufe bakin ta yace “wace Aisha?” Nafisa tace “wadda dai ka sani” yace “ku samo wata” Ammi ce tace “haba Aliyu, a tunani na rigimar da ke tsakanin ka da Aisha ta qare, meye dalilinka na rashin son ta koya ma Hanifa girki? Ka tuna fa, kai ka kafa sharuddan nan da kanka, don me zaka hana Aisha ta koya mata?” Hanifa tace “don Allah yaya kayi haquri, na amince da ita kuma nasan zata koya mun tsakani da Allah please” ba don ya so ba yace “shikenan” ya miqe ya wuce dakin shi. Hanifa cikin murna tace ma Nafisa “Anty gobe mu je gidan su mu tambaye ta ko?” Nafisa tace “Allah ya kaimu Hanifa”. Bayan Nafisa ta koma gida ne take ba Yusuf labarin abinda ke faruwa, aikuwa hankalin shi ya masifar tashi. Ba yanda baiyi ba akan su nemo wata tunda Aliyu baya son Aisha amma inaaa, Nafisan ce ma take gaya mishi Aliyun da kan shi ya amince da hakan. Ko da suka kwanta bacci Yusuf ya kasa baccin, tunanin shi yadda zai rabu da Nafisa ya auri Aisha. A yanzu haka dai yayi nasaran hana Nafisan samun ciki wanda yayi haka ne ta hanyar zuba mata magungunan hana samun ciki a cikin abubuwan sha kamar su juice, tea da sauran su. STORY CONTINUES BELOW  Wannan ne yayi sanadiyar rashin samun haihuwa shekara da shekaru. Kwanakin baya cikin ikon Allah da ta samu cikin sai ya zube,tun daga nan kuma shiru. Shirin shi na biyu shine ya kwashe dukiyar Aliyun da na Nafisan gaba daya sannan ya mallaki Aisha wadda yake bala’in so kamar ran shi. ************ Washe gari Aisha ta fito daga wanka ta sanya english wears wandon pencil jeans da wata ‘yar karamar top mai kyau. Shape din Aisha ya fito sosai a cikin wandon nan domin dama Aisha akwai qugu wanda ba’a ganin shi sai tayi irin wannan gayun. Kamar kullum dai bata yi kwalliya ba sai qamshin turare da take ta yi. A rayuwarta tana bala’in son turare shiyasa Aliyu yake qara birge ta, domin a koda yaushe qamshin turaren shi ne ke sanar da ita isowar shi. Ta dauki hair band dinta ta fito falo domin ta ba Inna ta taimaka mata ne suka ji sallama. Aisha wadda ta bude qofa kuwa ta cika da murnar ganin Hanifa da Nafisa. Bayan sun gaida Inna ne suka zauna. Aisha ta wuce kicin don dauko musu lemu da abubuwan ciye ciye. Hanifa da Nafisa suka kalli gashin Aisha cikin mamaki Hanifa tace “Anty kin ga gashin Aisha kuwa? Ashe duk gashi ne take boyewa cikin nadin gyalen nan” Nafisa tayi dariya tace “shine Aliyu yake ce mata mai qaton kai” Inna ta fashe da dariya tace “ai gashin nan na Aisha tabarkallah” Da Aisha ta dawo ne ta ajiye musu tray cike da abubuwan motsa baki, ta koma wurin Inna tare da miqa mata hair band din tace “don Allah Inna taimaka mun” Cikin masifa Inna tace “ni kuwa ina son ganin ranan da zaki koyi saka daure gashin nan mu huta” su Nafisa suna ta dariya. Cikin shagwaba ne Aisha tace “toh Inna ba nace in yanke gashin ba kun hana ni, bazan iya daure shi ba wallahi” Inna ta kalli su Nafisa tace “kun gani ko, aikin kenan, idan ba ni ba toh sai qanin ta, mu kenan kullum daure gashi. Idan kuma bata samu mai taimaka mata ba har neman kuka take” Aisha tace “haba haba Inna, yanzu har wannan maganan sai kin fadi?” Inna tace “idan kin ji haushi ki koya mana” su Nafisa dai sun yi dariya har sun gaji. Aisha ce ta ce ma Inna “nasan baki san su ba, Anty feena ce da Hanifa, sisters din Aliyu wanda nayi aiki a kamfanin shi” Inna tace “ikon Allah, aikuwa dai dan uwanku bai kyauta ba abinda yayi ma Aisha” anan ne Nafisa tace “kuyi haquri Inna, insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba” Inna tace “babu komai ai ya wuce”. Nafisa tace “dama dalilin mu na zuwa shine akwai alfarma da muke nema a wurin Aisha” Nafisa ta nuna Hanifa ta cigaba da fadin “Hanifa ce zasuyi aure da Aliyu… ” tun kafin Nafisa ta qarasa magana ne zuciyar Aisha ta buga.. Nafisa ta cigaba da fadin “…dayake yana son ta qware akan wasu abubuwa kaman girki da sauran su, shine muka yanke shawaran zuwa domin mu roqe ki akan ki ba Aisha izinin zuwa tana dan koya mata” Inna ta dan yi shiru sannan tace “naji bayanin ku, kin dai ga ni qanwar mahaifin Aisha ne kuma bai kamata inyi mata izini ba tare da an shawarci iyayen ta ba saboda haka kuyi haquri zuwa gobe ko jibi duk yadda ake ciki sai ta kira ku a waya ta sanar da ku” su Nafisa sun ji dadin maganar Inna. Aisha dai tunda ta ji zancen auren Aliyu da Hanifa kan ta ya fara sarawa, gaba daya ji tayi hankalin ta ya tashi. Bayan sunyi sallama da Inna ne Aisha ta raka su har mota sannan ta basu sabuwar lambar ta (dama ta gaji da waccan wadda ta bace a dalilin ‘yan naci). Bayan ta dawo ne Inna ta tambaye ta “shin zaki iya zuwa ki koya mata girkin?” Aisha tace “Inna ai lada zan samu, idan su Abba sun amince ba matsala”. Ko da ta shiga dakin ta rufe qofa tayi ta haye gado ta dinga rusa kuka, a fili take fadin “I am in trouble yau na shiga uku Aliyu zai yi aure, ya zanyi da son shi?” Wata zuciya ce tace mata “toh yasan kina yi ne? Banda abin ki ya ma za’ayi Aliyu ya so ki” haka dai ta dinga sabbatu ita kadai wanda a qarshe ta koma roqon Allah ya yaye mata son Aliyu daga zuciyar ta. ************ Cikin ikon Allah ba’a samu matsala ba wurin amincewar Abba domin a cewar shi abin alfahari ne ace danka ya qware a wani abu mai kyau da har mutane suke so suyi koyi da shi. Don haka ne Aisha ta kira Hanifa a waya ta sanar da ita cewa Abban ta ya amince. Hanifa tayi murna qwarai, aikuwa duk ta bi ta ishi su Ammi da zancen koyon girkin wanda su Ammi sunyi mamaki domin kowa yasan yadda bata qaunar shiga kicin. Aisha ta gaya ma yusuf maganan fara koya ma Hanifa girki wanda yayi qoqarin hana ta a dalilin qiyayyar dake tsakanin ta da Aliyu amma ta qi, a cewar ta ai ba wurin Aliyu zata je ba balle ya mata wulaqanci don haka ma ita babu ruwanta da shi. Hakanan Yusuf ya haqura ya qyale Aisha, a yanzu haka dole ya san yadda zai yi kada ya hadu da ita a gidan Ammi. Da Aisha tayi waya da Salma ne take ce mata “su Aisha za’a je koya ma matar masoyi dahuwa” Aisha dai dariya tayi wadda bata kai ciki ba tace “ai dama ba masoyi na bane, maqiyi na ne” Salma tace “da maqiyin ki ne bazaki amince ki koya ma matar shi girki ba ai” tace “ba komai ai aikin lada ne, ko banza dai zan gan shi. Wallahi Ummi rabona da ganin shi tun lokacin da na kai mishi takardar barin aikin nan, I am dying to see him” Salma ta fashe da dariya tace “magana dai tana ta fitowa” Aisha dai babu yadda zata yi domin dai Salma ta riga ta gano ta don haka ne tace “Ummi ki taya ni addu’a Allah ya cire mun son shi daga zuciya ta” Salma tace “zan dai yi miki addu’a Allah yasa Aliyu ya zama rabon ki” ba qaramin dadi Aisha taji ba jin maganan Salma. Ranar da Aisha zata fara zuwa gidan Ammi koya ma Hanifa girki tun da safe Hanifa ta ke ta maganar, har Ammi na fadin “su Hanifa kamar dagaske, Allah dai yasa ki natsu ki koya da kyau” Aliyu yana sauraron su wanda maganan duk ta ishe shi ba don komai ba sai don an ambaci sunan yarinyar da baya so, miqewa yayi ya nufi daki domin shiryawa zuwa ofis.+ Bayan ya fito ne riqe da suit dinshi Hanifa ta dakatar da shi tace “yaya Aliyu tunda zan fara koyon girki yau ina ganin yakamata in daina zuwa ofis ko?” yace “yeah, ki rubuta takardar hutu ki aika ofis din” ya kalli Ammi yace “na tafi Ammi” tace “Allah ya dawo da kai lafiya baby na” yace “ameen” Har ya kai qofa ne Hanifa tace “haba yaya, wish me luck mana” ya juyo ya kalleta yace “All the best Hanifa, bye” ya wuce. Ko da Aisha tazo bayan sun shiga kicin, Hanifa tayi tunanin koyon girkin bazaiyi mata wahala ba sai ta ga sabanin haka. Gaba daya bata gane abubuwan da Aisha ke koya mata ba, asali ma bata sa kanta ta gane komai ba har a ranta tana tunanin anya zata iya kuwa?? Abincin da Aisha ta dafa kuwa a ranar gaba daya qamshi ya cika gidan, har Ammi na fadin duk wanda ya auri Aisha ya more mata. Wani ikon Allah har lokacin tashi daga aiki ya wuce Aliyu bai dawo ba, Aisha ta jira ta gani ko zai dawo amma shiru, haka nan ta haqura ta koma gida. Ganin cewa zata dinga samun sabani da Aliyu ne ta mayar da lokacin koyon girkin daga bayan la’asar. Duk da hakan kuwa bata samu ta gan shi ba. ************* Yau kusan sati biyu kenan da fara koya ma Hanifa girki amma har yau ko sau daya Aisha bata taba haduwa da Aliyu ba, gaba daya ma rashin ganin nashi duk yasa ta daina jin dadin koya ma Hanifan girki, gashi ita ma Hanifan tasa shiririta wurin koyon, kusan ma zamu iya cewa bata iya komai ba har yanzu. Abinda Aisha bata sani ba shine wasu ayyuka ne suke riqe Aliyu a ofis wanda har yana kai kusan qarfe tara na dare sannan yake dawowa. *************** Akwai wata rana Aisha da Hanifa suna kicin, a lokacin Ammi da Nafisa suna falon sama. Aliyu ne ya dawo daga ofis, bayan ya watsa ruwa ya shirya cikin wandon three quarter ma sweatpant hade da wata t-shirt mai kyau ya fito daga dakin shi, yana shirin haurawa sama ne Hanifa ta fito daga kicin riqe da waya a hannun ta wadda take ta ringing, ganin Aliyu ne tace “yaya sannu da zuwa” ya amsa sannan ya wuce sama yayin da ita kuma ta wuce falon qasa don amsa wayar. Ko da Aliyu ya haura sama bayan ya gaisa da su Ammi ne ya sauko domin zuwa dakin shi ya duba wani saqo da manajan shi na Katsina ya aiko mishi, kafin ya shiga dakin ne ya kira Hafsat don ta kawo mishi fresh milk din shi. Lokacin da ya iso wurin dinning ne ya fara kiran Hafsat din, muryar shi da Aisha ta ji ne ta razana, shiru tayi tana tunanin ko ta fita don jin dalilin kiran Hafsat da yake yi, jin alamun yana dosowa kicin din ne ta nufi hanyar fita domin ta shaida mishi cewa Ammi ta aike ta. A wannan lokacin kuwa ya doso qofar kicin din yana masifa, ba tare da sun ankara ba ne suka yi karo da juna wanda ita Aisha ta kusa faduwa. Da sauri ya riqe ta tare da fadin “careful” sai da ta dago fuska ne ya gan ta, fuskar shi a murtuke yace “ba kya gani ne?” Aisha dai zuba mishi idanuwa tayi tana qare mishi kallo yayinda jikin ta yake ta rawa, Aliyu ya qara yi mata kyau fiye da yadda tasan shi. STORY CONTINUES BELOW  Da qyar ta saita muryar ta tace “sorry, dama na fito ne don in gaya maka cewa Ammi ta aiki Hafsat” Ya juya zai tafi ne tace “wani abu kake so ne?” kafin yayi magana ne Hanifa ta iso wurin tana fadin “yaya Aliyu fresh milk ko? Bari in kawo maka” Ya wuce dakin shi yayinda Aisha ta qura mishi idanuwa. Ajiyar zuciya ta saki a ranta tace “I finally got to see him today, Allah ka yaye mun wannan wahalan”. A bangaren Aliyu da ya koma daki zama yayi akan resting chair yana tuno abinda ya faru yanzun nan, wani abun mamaki shine tun ranar da ya fara haduwa da Aisha bai taba jin mace mai dadin murya irin nata ba, bai san ya akayi dukda tsanan da yayi mata yana jin dadin sauraron muryar ta ba. Tsaki yayi sannan ya janyo laptop dinshi yace “stop it man, she is not worth your attention”. A lokacin da su Aisha suke dafa abincin gaba daya gidan ya bude da qamshin girkin, Aliyu zaune a falon qasa yana ta kallon labaru, su Ammi suka sauko daga sama. Bayan sun zauna a falon ne Nafisa ke fadin “lallai Aisha ta iya girki, wannan irin qamshi haka kamar irin manyan restaurants dinnan” Ammi ta kalli Aliyu tace “wallahi yarinyar kam ba laifi, gashi albarkacin ta babyna ma zai more aure” Da sauri ya kalli Ammin sannan ya mayar da idanuwan shi kan TV yayin da Nafisa take dariya. Su Ammi suna ta hirar su ne su Aisha suka fito, Hanifa na tafe Aisha tana biye da ita. Ammi ce tace “har kun gama?” suka amsa “eh Ammi” tace “toh sannun ku” Hanifa ce ta amsa yayin da ita Aisha hankalin ta ya tafi wurin neman wayar ta, hango ta tayi bisa kujerar da Aliyu yake zaune wanda gaba daya hankalin shi yana kan kallon labaru. Ta dade a tsaye tana kallon fuskar shi cike da fargaba. Nafisa ce ta ankara da kallon tace “Aisha lafiya kika tsaya a tsaye?” Cikin sanyin murya tace “dama waya na zan dauka” Nafisa ta lura Aisha tana tsoron zuwa daukar wayar ne wanda tuni ta hango ta a gefen inda Aliyu yake zaune tace “zo ki dauka mana” Ta zagayo ta iso wurin kujerar Aliyu wanda jikin ta har rawa yake yi, qamshin turaren ta ne da ya ji daf da shi yayi saurin waigowa ya kalleta yayinda ita kuma ta sa hannu zata dauki wayar, daga kanta da ta dan yi ta kalle shi ne bata ankara ba sai ji tayi wayar ta zame daga hannunta ta fadi qasa, tuni screen din wayar ya tsage. Nan da nan suka juyo don ganin abinda ke faruwa yayinda Ammi tace “subhanalillahi, lafiya?” Aisha ta duqa ta dauki wayar muryar ta na rawa tace “Ammi faduwa wayar tayi” Hanifa ce tace “hope bata fashe ba?” Aliyu ya kalli Aisha wadda ya tabbatar saboda shi ne ta kasa natsuwa har ta saki wayar. Miqewa yayi ya wuce dakin shi yayin da ya ji tana fadin “screen din ne ya fashe” Nafisa tace “aikuwa waya ta lalace”. Bayan Aliyu ya shiga dakin shi ne duk ya ji bai ji dadin fashewar da wayar Aisha tayi ba, duk da baya shiri da ita ta dan bashi tausayi musamman domin ya san dalilin fashewar wayar. Anan ne ya dauki wayar shi ya kira Mansir. ********* Bayan minti talatin da fashewar wayar Aisha ne aka danna qararrawa, A lokacin ma Aisha tana shirin tafiya gida. Hanifa ce ta leqa. Mansir ne, bayan sun gaisa ne tace “Ango ango”, yayi murmushi yace “Hanifa harda ke? Toh kin dana” suka yi dariya. Ya miqa mata leda yace “gashi wannan saqon ki ba oga” tace “bazaka shigo ba?” yace “wallahi sauri nake yi” bayan sunyi sallama ne ta dawo ciki. STORY CONTINUES BELOW  Ko da ta shigo dakin ta same shi yana cigaba da kallon labarun da yake kallo a falo, miqa mishi ledar tayi tare da fadin “yaya ga saqo inji Mansir wai a baka” Ba tare da ya kalle ta ba yace “ki ba mai koya miki girki” nan da nan Hanifa ta fara murmushi ta juya ta fita cikin murna. Tana isowa falo ta miqa ma Aisha ledar tace “ga shi inji yaya Aliyu, ina kyautata zaton sabuwar waya ce yasa aka kawo miki” Su Ammi sun ji dadin jin haka musamman Nafisa wadda bata son rigimar da ke tsakanin Aisha da Aliyu. Ba tare da Aisha ta karba ba tace “ni bazan karba ba” Nafisa ce tace “haba dai, ko har yanzu baki haqura da abinda ya faru bane?” Murmushi tayi tace “ba haka bane” Ammi tace “maza ki karba kada raina ya baci” Aisha ta miqa hannu ta karbi ledar sannan tace “nagode”. Anan ne tayi musu sallama ta wuce gida. ************ Ko da Aisha ta dawo gida ta tarar da Zaid da inna a falo suna kallo. Zama tayi gefen Zain tace “mutumina nayi sabuwar waya fa” nan da nan ya qwace ledar yace “mu gani wacce iri ce?” tace “oho, nima ban duba ba” Zaid yana ciro kwalin wayar ya zaro idanuwa tare da fadin “kut, sis wa ya baki samsung galaxy S9?” Inna ce tace “hala china ce ko?” Zaid yana dariya yace “Inna wannan wayar ko wata biyu bata yi da fitowa ba fa, yanzu haka kusan dubu dari uku take” Aisha ta zaro idanuwa tace “what, duba dai da kyau ka gani” yace “ni dai fadi mun wane mai kudin ya siyo miki ita?” Anan ne ta basu labarin yadda akayi. Inna ce tace “ashe dai Aliyun yana da kirki na mishi mummunar fassara” Zaid ne ya kalli Aisha yace “sis kin tabbatar gayen nan ba son ki yake ba kuwa? Domin dai babu wanda zaiyi kyauta irin wannan haka nan kawai” Aisha ce ta harare shi tace “ka manta bamu shiri da shi? Besides aure ma zaiyi” Inna ta miqe tare da fadin “Allah ya saka mishi da alkhairi” suka amsa da ameen. Zaid ya kalli Aisha yace “lallai Aliyun nan yana da kudi kuwa, haka kawai ke ba budurwar shi ba ya siya babbar waya irin wannan ya baki?” Aisha tayi dariya tace “halin kyauta gareshi, ban ma samu nayi mishi godiya ba Wallahi. Idan na gan shi gobe zanyi mishi”. Har Salma ta kira a waya ta bata labarin wayar da Aliyu ya siyo mata, nan da nan Salma tace “hajiya asiri kika mishi ko me?” Fashewa tayi da dariya tace “wallahi Ummi haka nan, dama an gaya mun mutumin kirki ne wallahi gashi kuma na shaida hakan” Salma tace nima haka Mustapha ya bani labari, wai mutumin kirki ne, Allah ya bashi lada” Aisha tace “ameen” anan ne suka cigaba da hirar su. ********** Washe gari ko da su Hanifa suka ga wayar da Aliyu ya siyo ma Aisha sun ji dadi domin dai a yanzu sun tabbatar ya daina jin haushin ta dukda wayar Aisha kuwa yafi na Hanifan tsada (wayar Hanifa S8 ce) ita Hanifan bata sa komai a ran ta ba. Bayan sun gama dafa abincin ne Aisha ta zauna zaman jiran dawowar Aliyu domin ta mishi godiya, har aka kira sallan magrib bai dawo ba don haka ne suka wuce dakin Hanifa don yin sallah, bayan Hanifa ta idar ta fita daga dakin ta bar Aisha anan wadda take sallah. Da Aisha ta idar da sallah ne ta miqe domin cire hijab, aikuwa dai tana jawo hijabin ya tafi da Hair band din kanta wanda nan da nan gashin ta ya warware. Cikin damuwa tace “ooooooh i am in trouble” zama tayi tana jiran Hanifa ta shigo ta taimaka mata. Da ta ji shiru ne ta dauki hair band din ta fita don neman Hanifa. Sauka tayi qasa tana ta kiran Hanifa, bata ankara da Aliyu ba wanda shigowar shi kenan yana qoqarin rufe qofa. Gashin Aisha da ya hango ne ya tsaya cak yana mamaki, tunda yake ganin ta yayi tunanin qaton kai gareta ashe gashi ne mai tsawon gaske take boyewa. Asali ma bai taba ganin mai tsawon gashin Aisha ba a Najeriyan nan, duk tsawon gashin Nafisa da yake gani na Aisha ya taka shi nesa ba kusa ba. Rashin ganin Hanifa ne duk ta bi ta damu, har lokacin bata lura da Aliyu ba, ta wuce ta nufi hanyar qaramin falo tana ta faman kiran Hanifa, wannan ne ya ba Aliyu damar sake kallon gashin Aisha wanda tuni ya gama birge shi. Muryar Hanifa suka ji tana saukowa tace “Aisha gani nan, na shiga dakin Ammi ne” a lokacin kuma ta ga Aliyu wanda ke tsaye bakin qofa tace “yaya Aliyu sannu da zuwa” Kafin ya amsa ne Aisha ta dawo tana fadin “don Allah ki taimaka mun da gashi na” a lokacin ne Aliyu ya nufi hanyar dakin shi wanda kafin ya shiga ne Aisha tace “sannu da zuwa” ba tare da ya amsa ba ya shige dakin shi. Bayan Hanifa ta sa mata hair band din ne suka haura sama wurin Ammi domin tayi mata sallama. Aliyu dai yana shiga dakin shi ya saki ajiyar zuciya tare da zama bisa resting chair dinshi ya dafe kan shi. Tunanin abinda ya gani yanzun nan yake yi, Aliyu yana bala’in son mace mai dogon gashi a rayuwar shi sai gashi wadda ke da shi kuma baya son ta. A yanzu ne ya fara tunanin dalilin da yasa baya son Aisha, me Aisha tayi mishi da ya tsane ta? Nan take ya ba kan shi amsa a fili yace “rashin kunya”, tsaki yayi yace “stop it man, don’t let her confuse you” ya miqe ya fita domin zuwa falon sama wurin Ammin shi. Yana haurawa sama ne ya hadu da Aisha tana saukowa zata tafi gida, anan ne ta saita murya tace “thanks for the phone” ta wuce abinta yayin da ya bi ta da kallo a ran shi yana fadin “crazy girl”.